← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 95

Sashe 66

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Master, akwai allurar nan da ka sayo mini ba ayi mini ba, mu je in raka ka ayi maka to"

Gyatsa ya saki, maimakon ya yi hamdala, sai ita ta ce "Alhamdilillahilazi aÉ—a'amana haza, Ubangiji Allah ya ciyar da mu kullum, ya bawa wanda bai samu ba"

"Amin" ya faɗa ƙasa-ƙasa zai kwanta, a sukwane ta ce "Dan Allah kar ka kwanta, mu je a duba ka, kar ka sha wahala, sauro ne yayi yawa a unguwar nan shiyasa muke ta zazzaɓi, dan Allah ka zo mu je a duba ka"

"Kai wallahi kina addaba mini, kin dame ni"

Jauhar ta kwantar da murya cikin sigar rarrashi ta ce "To na sani, amma ka yi haƙuri, na daina, dan Allah mu je a dubaka ka ji Mijin 'yar madara, ba ka ji yadda jikinka yayi zafi ba?"

Ya kalli yadda ta dafe kafaÉ—arsa, tayi saurin sakinsa, ya ce "Sai an yi sallar magariba"

"To mu koma falo, sai na saka maka maganin sauro a É—akin, idan ka cigaba da kwanciyar jikinka mutuwa zai yi"

Da ƙyar ta lallaɓo shi, suka dawo falo, ta kunna maganin sauro.

Ana idar da sallar magariba, ta É—aukko allurar, ta ce su tafi, ya ce ya fasa zuwa, shi ba zai iya tafiya ba.

Da ƙyar sai ka ce ɗan goye, ta lallaɓa shi suka fita.

Ta rufe ƙofar gidan, ta riƙe hannunsa ta ce "To mu je, kar ka ji jiri idan ka gaji ka yi mini magana sai mu tsaya ka huta".

Kallonta kawai yake yi, É—an hannun nata É—an mitsitsi a cikin nasa.

Suna tafe tana ƙara ba shi haƙuri, a kan laifin da ta yi.

Nasiru mai chemist na ganinsu ya ce "A'a jauhar, kin warware shi ne shi ma ya kwanta" tayi murmushi ta ce "Allura na kawo shi, ayi masa mai sanyi dan Allah"

Da jauhar ta san yadda yake ji a zuciyarsa idan ya ga tana tankawa mai chemist da ba ta yi ba, sai dai bai san dalilin hakan ba, kawai ba ya son ya ga wani yana kulata.

Aka gama yi masa suka fito za su tafi, ta tsaya tambayar mai É—anyen dankali nawa kwano.

Al'amin ya zaro kuÉ—in ya bayar, suna tafe tana godiyar dankali.

Da safe ta soya musu dankali da tea, ya gama karyawa, ya kalleta ya ce "Wannan matar da na gani a gidanku wacece?"

Ta ce "Wacce?"

"Mai baƙaƙen kayan nan"

"Anty zakiyya ce, matar Baba ce" ya jinjina kai bai sake cewa komai ba.

"Ka santa ne?" Yayi shiru bai amsa ba, daga haka ta ja bakinta tayi shiru.

Babu yadda ba ta yi ba, a kan ya je a ƙarasa allurar nan, amma ya ƙi. Da ya ji ƙwarin jikinsa ma, fita ya cigaba da yi.

Jauhar na zaune a falonta, tana tunanin ƙirƙirar sabbin styles na abun hannu da jigida, ta fara sayarwa.

Aka bubbuga mata gate, ta tashi ta je ta buÉ—e, ta ga wani mutum da ba ta san shi ba, fuskarsa sanye da facemask ya ce "Mai zamani yana nan?"

Ta girgiza kai ta ce "Ya fita"

"Ga wannan ki ajiye masa". Ya bata leda mai baƙi da fari.

Ta karɓa ta ce "In ji wa zan ce?".

"Idan ya zo zai gane, ki ajiye masa a É—akinsa, zan kira shi"

Ta ce "To shikenan"

Ta rufe ƙofa, kamar ta buɗe, sai ta fasa ta kai masa cikin drower sa, ta ajiye masa ta cigaba da sabgoginta.

Kayan da anty lubabatu ta bata ta ɗauka tana duddubawa, ta ɗan ɗanɗana abun, tayi shiru tana tunani, ita sam abun da ake faɗa a auren, ba ta ga alamar sa ba, dan shi ba ta tata ma yake yi ba, ya ƙule a ɗakinsa yayi shaye-shayensa ya ci abinci ya fita yawonsa shi ne kawai a gabansa.

Ta ɗan taɓe baki, ta ɗauki turaren wutar, ta tirara na gidan, ta turara na jikinta, ta ɗora girki.

Da daddare da wuri ya dawo gida, gidan sai ƙamshi yake yi na musamman, giftawar farko da tayi, sai da ya ɗaga kai ya kalleta, ƙamshin har cikin ƙwaƙwalwarsa ya ji shi.

Yau  faten dankalin ta yi, dan shi ne kawai da su, sai dai yayi masa daɗi bai taɓa sanin ana faten dankalin hausa ba, sai yau da ta bashi, har mamakin yadda take sarrafa abinci yake yi.

Ya gama cin abincin ta ce "Master yanzu allurar nan dai ba za a ƙarasa ba ko?"

"Eh" ya faÉ—a kai tsaye.

"Ai shikenan, thank God tun da ka warke ai. Ka yi mini addu'a mun kusa fara WAEC, Allah ya sa result É—ina yayi kyau".

"Sai ki yi karatu"

"Ina yi ai" ya kalleta ya ce "A hakan, kina shirme dai" ta gane da kayan beat É—in ta da stone yake, tayi murmushi jin yadda yau yake yi mata doguwar magana.

"Ina karatu sosai da sosai fa".

"Akwai kwaɗo a ƙarƙashin kujerar nan da ki ke" da sauri ta kalli kujerar, sai kuma ta yi dariya ta ce "Ai na daina jin tsoron" wai nan tsokanarta yake yi, amma fuskar nan a haɗe.

Har wajen ƙarfe goma suna tare, yana ta danna wayarsa, mai madannai, ita kuma tana jin radio tana aikinta, ba hira suke yi ba, amma kasancewar su a hakan ma, daɗi take yi mata.

Ya yi miƙa ya tashi zai tafi ɗaki ta ce "Tafiya babu sallama"

Ba tare da ya yi Magana ba, ya É—aga mata hannu, murmushi ta yi ta ce "Asuba ta gari mijin Angela" É—an rausayar da kai ya yi kamar zai yi murmushi ya shiga É—akinsa.

Ya kwanta yana shaƙar ƙamshin da bedsheet ɗin sa yake yi, bai taɓa tunanin zai yi aure ba, dan babu wannan lissafin a gabansa, ba dan albarkacin auren ba, da a cikin tsummokara zai kwana a can gidan da suke tare da su Walid.

Tsakar dare jauhar ta ji motsi, kamar ana watsi da kaya.

"Malam kar ka shiga wannan É—akin ba komai a ciki, mata ta ce a ciki, kuma babu in da shari'a ta baka damar shiga in da matata take"

Jin muryar Al'amin, ya sanya ta saukko daga kan gadon da sauri, wata irin dalleliyar fitila aka saka ana haske gidan.

"Shut up, kar ka sake magana, kar na sake jin bakinka"

Cikin ƙaraji ya ce "Sai na yi magana, wallahi ka shiga ɗakin nan, zan illataka".

Da gudu ta fito dan ta ga meyake faruwa, ma'aikata ta gani, har da jami'an tsaro, sun saka wa Al'amin ankwa sun durƙusar da shi a kan gwiwoyinsa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yallaɓai me yayi muku? Laifin me ya yi?"

"Ki koma É—aki Ki nemi hijjabi ki saka" yayi maganar cike da takaici.

"Oya ku yi searching ko ina a gidan nan, kar ki motsa daga in da ki ke"

Wani jami'in ne ya fito daga É—akin Al'amin, da wannan ledar da aka kawo aka ce a ajiye masa, ya ce 'Ga abun da muka samu sir"

Shugaban operation ɗin ya karɓa, ya zazzage sai ga ƙwayoyi, da allurai da wiwi da sauran tarkace sai kuma wata 'yar leda mai ɗauke da wani farin gari.

Ya ce "Good, mu tafi da shi mun samu abar"

"Yallaɓai, wallahi wani ne ya kawo su ɗazu, ba shi ya kawo su ba, dan Allah kar ku tafi da shi. 

Ko kallonta ba su yi ba, suka tasa ƙeyar Al'amin.

Ayshercool
08081012143

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

Biyo bayansu tayi, tana wani irin kuka mai ban tausayi, tana yi musu magiyar su sake shi, ba shi da laifi, amma babu wanda ya saurareta a cikinsu.

Maƙwabta na jiyo kukanta, amma babu wanda ya iya ko leƙowa ya ga abun da yake faruwa.

Shi kuwa Al'amin ko a jikinsa, kukan da take yi ne kawai ba ya so.

Suka saka shi a mota, ta ce "To Yallaɓai ina za ku kai shi dan Allah"

"NDLEA, daga nan zamu miƙawa 'yan sanda shi, su kai shi gaban kotu".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu dai sai kun kai shi NDLEA É—in kenan? Wancan karon baku kai shi ba sai yanzu, dan Allah ku duba lamarin nan"

Suka saka Al'amin a mota, suka tafi da shi, a falonta ta zauna, ta fashe da kuka, ta daÉ—e a wurin tana kuka, ganin hakan ba mafita bane, ya sanya ta tashi ta É—auro alwala ta koma É—akinta, tayi ta sallar da ba ta da tabbacin tana karanta ayoyin daidai saboda tashin hankali, ta É—aga hannu tayi addu'a, amma ta kasa kawai ta mayar da kanta sujuda ta fashe da kuka.

Har asuba ta yi idonta biyu, ta yi sallar asuba ta idar, ta zauna tana karanta duk abun da ya zo bakinta, wani abu mai nauyi ya tokare mata ƙirji, ta ji tamkar numfashinta zai ɗauke gaba ɗaya.

Bayan sallar asuba magidantan layin suka tsaya suna salallamin, jiya da daddare ma'aikatan sun shigo layin, amma babu wanda ya fito.

Malam lawan ya ce "Har kwa tambayi lafiya? Ai tun da ɗan daba ya tare muku a unguwa, sai abun da Allah ya yi, wurinsa suka zo, wataƙila ma wata ta'asar ya je ya tafka, suka zo suka yi masa ɗaukar amarya tsakar dare".

Suka yi ta salallami da fatan Allah ya kyauta.

Har rana ta yi haske, jauhar tana zaune a wuri É—aya, idanun ta sun yi ja, duk sun kumbura fuskarta tayi ja ta kumbura saboda kuka.

Maman halimatu da wata mata mai kallon gidan na jauhar suka shigo, sai da suka yi ta sallama, da ƙyar ta iya amsawa sam ba ta ji sallamar ta su ba ma, ta fito falo ta ce su shigo.

Maman halimatu ta ce "Jauhar, lafiya kuwa? Wai meyafaru ne jiya mun ji hayaniya, babu damar mu fito.

Take wasu hawayen suka ziraro mata ta goge su ta ce "Jami'an tsaro ne suka  zo suka tafi da shi"

"Subhanallah, laifin me yayi?"

Ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba"

"To ki yi haƙuri, ki samu ki ci abinci,  sai ki nutsu a san abun yi, Allah ya kyauta ya kiyaye gaba"

Ta amsa musu da to ta gode.
Chapter 66 · 0% Book details