Sashe 20
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɗan rikice ya ce "A'a mama, yi haƙuri kiran gaggawa aka yi mini, faɗan daba ya ƙara ɓarkewa, ƴan daba sun rufe unguwar babu shiga babu fita, yaran Aminu Viper ne da wani madaki, wai ƴan sandan da aka tura, sun kasa kwantar da rigimar, kin san am incharge of his case, shi ne zan je na ga abun yi"
"To ka kula da kyau, ni wannan aikin ya isheni, shikenan kai ba hutu, ni hankali a tashe".
Ya jinjina kai ya nufi ƙofar fita.
Jin an ambaci Aminu, ya sanya jikin Nabila ya hau tsuma, ya bishi da gudu ta riƙo rigarsa ta ce "DSP, amma ba kai kaɗai zaka je ba ko?"
"Eh, na yi waya za a ƙaro mini ƴan sanda"
"Ko mu je tare?"
Ya zaro ido ya ce "Ki yi me?"
Sai kuma ta rasa me za ta ce "Kawai dai ko zan iya taimakawa"
Murmushi ya yi ya ce "Ba fa kotu ba ce madam"
"Zaki sake shi ya tafi ko kuwa? Wane irin iskanci ne haka, Meye haka ne Nasir?"
Nabila ta saki rigarsa ta ɗan ɗaga murya ta ce "Take care, ka tsaya daga nesa nesa dan Allah, kar wani abu ya same ka, kar mu yi asarar ɗan ƙasa na gari"
Dariya ya yi, ya fita da sauri.
Mama ta hayyayaƙo mata "Wallahi ki kiyayeni da rashin tarbiyyar ki a kan ɗa na, na gaya miki" mama ta yi maganar tana nuna Nabila da yatsa.
Nabila a ranta ta ce 'Ni yanzu ba ke ce a gabana ba, akwai abubuwan da suka fiki muhimmanci a wurina"
Tayi gaba tana kiran lambar sumayya, ta sanar mata da halin da ake ciki, na rikicin faÉ—an daba.
Sai dai kamar kullum, faÉ—a suka yi, sumayya ta gargaÉ—eta a kan ta fita sabgar harkar faÉ—an daban nan.
Nabila tayi zuciya ta kashe wayarta, tare da jin da ita ƴar jarida ce, sai ta shiga unguwar nan, ta samo rahoto, tana matuƙar jin haushin yadda sumayya take ɗari-ɗari da gudanar da aikinta, sai dai ko ba dan sumayya ba, ya zama dole ta taimakawa Nasir, kuma ta taimaki tata career, dan idan ba ta rama abun da Najar bunkure tayi mata ba, ba zata huce ba dan haka za ta cigaba da bibiya.
Ayshercool
08081012143
[7/23, 1:37 PM] null: Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â
        *ƘARFE A WUTA*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Follow this link, to join autar manya channel, domin samun litattafanta na baya da na yanzu.
https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h
Masu neman book ɗin ƘARFE A WUTA daga farko, su bi wannan link ɗin, su yi following channel ɗin, za su samu previous pages👇👇👇.
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
9
Har ƙarfe goma na dare, Nabila tana kiran wayar Nasir, domin jin ko yana lafiya, amma shiru wayarsa ba ta shiga, abu kamar wasa hankalinta ya fara tashi, zuciyarta ta din ga raya mata wani abun ya same shi.
Da sauri ta tashi ta fita farfajiyar gidan, tana cigaba da kiran wayarsa.
"Ke Arfa, me ki ke yi a wurin nan da daddare haka?" Ta ji muryar Abba babu tsammani.
Cikin damuwa ta ce "Abba Yaya bai dawo ba, kiransa aka yi kwantar da tarzomar faÉ—an daba, kuma haryanzu bai dawo ba".
Abba ya ce "Yana nan lafiya in sha Allah, da ki ka dawo nan kina sintiri,ai ba bin sa zaki yi ki nemo shi ba, harkar aiki ne yana nan lafiya in sha Allah"
Abba yana rufe bakinsa, sai ga ƙarar motar Nasir, yana ta horn ba ƙaƙƙaitawa, gaba ɗaya suka nufi gate a tare.
Suka tsaye har ya shigo yayi parking É—in motar.
Ya fito yana kallon su da mamaki ya ce "Abba lafiya na ganku a nan tsaye?"
Major ya ce "Arfa ce ta fito tana jiran dawowarka, ya ya aka yi wayarka ba ta shiga gaba É—aya?"
"Tana cikin mota ne abba, ina ga network ne amma a kunne take"
Cikin zaƙuwa ta ce "Yaya, komai lafiya dai ko?"
Ya ce "Alhamdilillah, an sha artabu dai, yaran sun ninka yawan da muke tunani, mun kama wasu, wasu sun gudu, amma mun kama su da yawa".
Mama ce ta fito ita ma, tare da su sauda, suna yi masa sannu da zuwa yana amsawa.
Arfa ta ce "Amma dai ba su yi maka rauni ba ko?" Yayi murmushi ya ce "Da sun yi mini rauni, ai da baki ganni a haka ba"
Nabila ta ce "To Alhamdilillah, bari na je na kwanta na yi bacci a nutse, tun da kana lafiya"
Ya ce "Ki bar wayarki a kunne, za mu yi magana"
Ta jinjina masa kai ta bar su a wurin ta tafi, mama kuwa kamar ta bi Nabila ta naɗa mata duka, ta kalli yadda Nasir yake wani sassanyan murmushi kamar shashasha, shi ma ji ta yi kamar ta kwaɗe shi da mari, duk ƙoƙarin da take yi a kansa na nesanta shi da Nabila, abu ya ci tura.
Ta daure ta ce "Shiga ciki ka ci abinci, ka je ka nemi wuri ka kwanta".
"No na tsaya na ci abinci a hanya ma, sai da safe, gajiye nake kwanciya zan yi"
Major ya ce "To Allah ya tashemu lafiya" suka watse.
A galabaice suka koma mafakarsu, domin kuwa sun sha artabu da jami'an tsaro, duk da an kama wasu, wasu kuma sun tsira da ƙyar. Sai dai sun yi wa su madaki mummunar ɓarna, dan ma Aminu ya yi musu kashedin babu ruwansu da cewa za su kashe madaki, saboda ya san hatsabibancinsa.
Yana zaune suka faÉ—o É—akin, suna ta mayar da numfashi, jikin rigar É—an mama face-face da jini.
Walid ya ce "Boss, an yi aika-aika amma kwaɓarmu ta so yin ruwa, dan an kama da yawa daga cikin yaran nan da muka gayyato, amma fa yaran madaki sun yi ɓarna, dan sun taɓa wanda ba su ji ba, ba su gani ba, duk da mun yi yinƙurin daƙile hakan".
Maimakon Al'amin ya yi magana, kawai ya tashi tsaye ya shaƙo wuyan walid, ya haɗa shi da bango, ya ware masa idanunsa ya ce "Ina ƙwayoyin da ka kwashe a nan wurin?"
Cikin takaici walid ya ce "In fita yi maka aiki, in dawo da ƙyar amma ka shaƙe ni?" Yayi maganar muryarsa na fita da ƙyar saboda shaƙar da ya yi masa.
"Suna ina na ce?"
"Na kwashe su na fita da su, dan ba zan bari ka kashe kanka ba, allurar da ka ke yi wa kanka ma, ba abun da take yi maka sai ƙara maka zafin zuciya"
Fusata yayi da maganar Walid, ya ƙara shaƙe shi, Ɗan mama ya tashi da sauri yana yi wa Al'amin magiyar ya rabu da Walid.
Walid ya ce "Idan ka kashe ni ma, ba zaka huce ba, ai na yi maka alƙawarin kawo maka sabuwar ƙwaya, amma wannan kashe kanka zaka yi, idan ka cigaba da sha, dan ba ta karɓe ka ba." A fusace ya hankaɗe Walid ƙasa, ya koma ya zauna ya dafe goshinsa.
Wayarsa ce ta yi haske, ya ja wayar yana dubawa.
"Aminu ka daina wannan gangancin da ka ke yi, idan ka sake shiga hannun mutanen nan, kar ka yi zaton za su hukuntaka da adalci, dai-dai da abun da doka ta tanada, ka nutsu ka daina wannan mugun wasan, ka mayar da hankalinka a kan burinka" iya ƙarfin sa ya saka wurin yin jifa da wayar, ta dagargaje a tsakiyar ɗakin, ya tashi zai fita.
Duk da mugun ciwon da jikin walid yake yi masa, saboda artabun da suka yi, amma haka ya tashi ya sha gaban Al'amin ya ce "Ina zaka je ne?"
Hankaɗe Walid yake ƙoƙarin yi, amma walid ya sanya ƙarfin sa, ya tura shi baya.
"Ka rabu da ni walid, ya zan yi ne? So suke sai na haukace, waye wannan? Me yake nema da rayuwata? Wace manufarsa ce da su a kaina? Me kuma suke buƙata yanzu?"
"Easy master"
Cikin ƙaraji ya ce "Na ce kar ka sake kirana da wannan sunan"
"Sorry boss, na san komai ai, ka kwantar da hankalinka"
"How? Duk abun da suka yi mini bai ishe su ba, wai yaya zan yi ne? Kalli idona walid, ba na bacci fa, zuciyata kullum zafi take yi, ba na iya saka komai a bakina na ji ɗanɗanonsa, ya zan yi ne?"
Walid ya ce na sani, ya amsa yana yi wa É—an mama inkiya da idonsa.
Viper ya a sake cewa "Ka san kwana nawa na shafe ba na bacci? Ba kwanaki ban ba fa kawai, shekaru ne, ba na baccin da ya kai awanni biyar, ka san me nake ji kuwa?"
Walid ya ce "Ban sani ba, amma na san da yawa daga abubuwan da ka lissafa"
Jikinsa na tsuma ya ce "Wallahi zuciyata ci take yi da wuta, ka sani, wallahi idan na riƙe makami sai na yi kisan kai" yayi maganar yana rintse idanunsa, a lokacin da ruwan allurar da walid yake yi masa, ya fara ratsa jijiyoyin jikinsa.
A nan take jikinsa ya saki, ya zubawa walid ido.
Walid ya ce "Ko ba zaka yi baccin ba, ka rufe idanunka master, za ka samu releif" shiru yayi, domin ba zai iya motsa kowacce gaɓa daga jikinsa ba.
ÆŠan mama ya ce "Walid, anya ba zamu yi wani abu a kan lamarin nan ba kuwa? Ba za a kai shi ya ga likita ba? Kar ya haukace tuburan fa"
Walid ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa alamar ɗan mama ya yi shiru.
A hankali al'amin yake buɗe idonsa yana lumshewa, sai dai ya kasa ƙwaƙwƙwaran motsi.
***
YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR TOFA.
Cikin tsananin ƙyanƙyami take ƙarewa ɗan ƙaramin ginin ƙasar kallo, rabin katangar gidan ta zube, sai ciko aka yi da kara da buhu, aka rurrufeta.
Abunka da mutumin ƙauye, cikin mutunci da girmamawa, matar gidan ta karɓeta, tana yi mata sannu da zuwa.
Ta yi mata iso, har cikin É—akinta, ta ba ta abun zama.
Kamar ta zauna a kan kashi, haka ta É—an É—osana ta zauna, tana kame jikinta ta kalli matar ta ce "Baki gane ni ba ko?"
Matar ta ce "Eh ban waye ki ba"