← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 95

Sashe 30

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata drower ya saka mukulli ya buɗe, ya ɗaukko wata ƴar ƙaramar akwati, ya ajiye, ya ƙarasa ya ɗauki jakar Nabila, ya zazzageta yana neman inhaler, amma bai gani ba, ya ja uban tsaki ya tashi, ya sake buɗe wardrobe, ya ɗaukko inhaler, sai dai sai da ya tsaya yayi ta kallon inhaler, yana kallon Nabila, sannan ya ƙarasa kanta, ya tsaya, ya ɗagota ya fesa mata a cikin bakinta.

Kamar zata haɗiye inhaler, haka take sake buɗe bakinta, ya mayar da ita ya kwantar, ya ɗaga gefen rigarta, da wuƙarsa ta huda, ya saka auduga da spirit, ya goge jinin tsaf, ba wata huda ce ta kirki ba, kawai dai ta zubar da jini ne sosai.

Gaba É—aya suka zuba masa ido, ya zuba iodine a jikin audugar, ya saka a kan cikin nata, ya kawo plasta, ya saka.
Dama ya saba yi musu dressing, idan suka je aka sare su, a wurin rashin jin su.

Ya mayar da akwatin in da take, ya koma gefe ya kunna sigari. Mamaki yake da tunanin, uban me take nema a wurinsa, sai dai ya fi yarda da cewa, tarko ce ake son yi masa da ita.

"Amma ya aka yi, aka samu wannan coincidence É—in?" Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.

Duk suka koma gefe, suka zubawa sarautar Allah ido.

Tari ta fara yi, ta yinƙura ta tashi zaune, ta kalli kayan cikin jakarta, da suke a watse, ta fara tattara abun ta, sai kuma ta dawo hayyacinta,bayan da suka yi ido huɗu da shi.

A rikice tayi jifa da jakar, ta ƙwala wani uban ihu, nan take mafarkin da ta taɓa yi ya dawo mata, tabbas sai yanzu ta fuskanci inuwarsa take gani a mafarki.

Ƙoƙarin tashi take ta gudu, cikin zafin nama, ya bar in da yake ya cafkota.

Tausayinta ya kama Walid, tare da dana sanin kawo wa Viper ita, ko haɗa bakin aka yi da ita a cutar da shi, atleast ita macece ya ɗaga mata ƙafa, amma ya san in da ya matsa, sai Viper ya illata ta fiye da yanzu.

"Waye ya aiko ki?" Yayi maganar a kausashe.

Ta girgiza kai, amma ta kasa magana.

"Waye ya turo ki na ce?" Yayi mata tsawa.

A rikice ta ce "Wallahi ba kowa" tayi maganar tana zubar da hawayen tsoro.

"Me ki ke nema a wurina?"

"Dan Allah ka yi mini rai, na tuba na bi Allah, ba zan sake ba, dan Allah kar ka kasheni, wallahi ni marainiya ce, tayi maganar tana kawar da kanta gefe, ta kasa kallonsa, sai azabar bugu da zuciyar ta take yi, cikin tsoro da fargaba.

"Look up kalleni" muryarsa ba a iya kunnuwanta take jin ta ba, a tsakiyar zuciyarta take yi mata amsa kuwwa, gashi ya matso daf da ita, warin sigarin da yake yi, ya fara hautsina mata ciki.

"Kalleni" ya sake maimaitawa.

ÆŠan mama ya ce "Ki bi umarninsa, ba ya maimaita magana, kan ki farka a lahira".

Cikin karkarwa, ta ɗaga kanta, da gefen idonta kawai ta kalleshi, amma ta fashe da kuka "Wallahi tsoronka nake ji, ba zan iya kallonka ba, idonka tsoro yake bani, dan Allah ka yi haƙuri kar......

Tsit tayi, ta haɗiye wani irin mugun yawu, da ta ji tamkar ta haɗiyi wuta, biyo bayan ganin ya saita  kaifin wuƙa a kwaroron maƙogwaronta.

"Idan ki ka bari, na sake ganin fuskarki, ko a kan hanya, Wallahi sai na kashe ki!"

Nabila ta gama saddaƙar da gumin da yake bin ƙafafuwanta, fitsari ne ba gumi ba, gashi tun daga goshinta, har cikin jikinta gumi ne kawai yake yanko mata ko ta ina.

Ta jinjina masa kai, ya ja da baya, ya kalli Walid ya ce "Ta ƙara mintuna biyar a gabana, sai dai ka fita da gawarta"

Walid ya kalleta ya ce "Zo in fitar da ke hanya"

"To in É—auki jakata?" Tayi maganar cikin tsoro.

Walid ya ce "Hanzarta ki kwashe kayanki mu tafi"

Sai dai ta kasa motsawar, ta ƙame a jikin bangon ɗakin, jikinta sai tsuma yake yi.

A fusace Walid ya ce "Ki tattaro mu tafi mana"

Nabila ta fashe da kuka, ta ce "Wallahi tsoro nake ji, kar in durƙusa ya kashe ni, dan Allah ka bashi haƙuri, kar mu haɗu a wani wurin ban sani ba ya kasheni, ya rantse sai ya kasheni".

Walid ya ce "Na ji zan bashi, taho mu tafi"

"Wallahi na kasa motsi" tayi maganar hawaye na cigaba da zuba daga idonta.

Gaban wardrobe ya je ya tsaya, ya juya musu baya, ya saka hannayensa, ya kama ƙasan rigarsa zai cire ya canza wata, kamar wadda ya kwance daga ɗauri, dama idanunsa ne igiyoyin da suka ɗaureta, ta durƙusa ta kwashi kayan jakarta, da jakar ta fita da gudu, ta kwashi takalmanta, ta fyalla a guje, ta bar gidan.

Dariya ɗan mama ya ƙyaleƙyale da ita, ya yi wata irin ashariya ya buga ƙafa, sannan ya je gaban Viper yayi wata irin kururwa, cikin sara masa tare da kambama shi ya ce  "Maza gumbar dutse, ina gwanin wani ga nawa, gaba salamun baya salamun mutumina, zaki ka ke sarki a gida sarki a dawa, ina mazan suke, ga fa uban ɗakina wanda ake kira namijin gaske. Sun buga da kai sun barka mutumina, Allah ya baka duniya lahirar ma ka samu in sha Allah. Mahadi mai dogon zamani. Kai idan ba namijin gaske ba, kalli yadda ka mayar da mai hankali zararre cikin ƙanƙanin lokaci, kalli yadda yarinyar nan ta firgice ta koma zararriya lokaci ɗaya, ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya tararka uban gidana, mahadinmu mai dogon zamani, Allah ya baka tsawon rai, ya kaimu ranar da zamu ba da jininmu domin ɗaukar maka fansa"

Geɓare baki Viper yayi kamar zai yi murmushi, dan kirarin ya tuna masa wasu abubuwa da dama da suka shuɗe.

Walid kuwa gaba ɗaya daga Viper har ɗan mama haushi suka bashi, kamar ya ɗura musu ashar, Nabila ko da cunen aka yi musu da iya, shi yaƙi ai ɗan zamba ne, kuma ko ba komai mace ce, bai kamata ya razanata har haka ba, tun da ya san mazan ma razana su yake yi.

Takalmansa ya saka,  ya bi bayan Nabila, dan yadda ta fita a burkicen nan, komai zai iya faruwa, gashi ga dukkan alamu, ba ta da cikakkiyar lafiyar numfashi.

Viper kuwa, rigar jikinsa ya canza, Ɗan mama ya ce "Boss, wai ka taɓa karatun likita ne? Na san dai ka iya wankin ciwo, to kuma na ga yau kayi aikin likita".

Al'amin ya girgiza kai ya ce "Ko É—aya, na zauna da mai irin ciwon ta ne"

ÆŠan mama ya ce "Na fahimta, amma dai ba fita zaka yi ba ko?"

"Zaka hana ni ne?"

Da sauri ya ce "A'a wane ni, ka san idan wannan jarababben ya dawo, ya tarar ka fita, masifa zai ta yi mini" bai saurari ɗin mama ba, ya bi ƙofa ya fita.

Nabila kuwa tun da ta fita da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba, sai da ta fita titi, shi ma babu ababen hawa, haka ta cigaba da tafiya tana waige-waige, sai a lokacin ta ji gefen cikinta, yana ta yi mata zugi, ta É—aga rigarta ta ga plasta.

Ga jikin rigarta da jini, a hankali ta furta "Na shiga uku"

Addu'a ta din ga yi, tana cigaba da tafiya, cikin ikon Allah, Allah ya kawo mai a daidaita sahu, ta kama ta shiga, tana ta haki.

Sumayya tamkar yau ta shiga harkar aikin jarida, haka tattaunawar ta su da honorable Indabo take kasancewa, saboda yadda ya tsatstsareta da manya-manyan jajayen idanunsa, yana yi mata wani irin kallo, gashi daga shi sai ita a wurin.

Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Meyake damunki ne? Ki nutsu mana"

Ta jinjina masa ta kai, ta cigaba da yi masa tambayoyin da su aka yarje mata ta yi masa.

Sai dai ita kanta ta san amsoshin da yake bayarwa, na son zuciyarsa ne kawai, ba wani abu ba.

Jin ta yi shiru, ya sanya ya kalleta ya ce "Ya dai?"

Cikin girmamawa ta ce "Tambayoyin sun ƙare sir"

"Kamar bakinki akwai magana, akwai tambayoyin da ki ke son yi mini ko? Mu je zuwa ina saurarenki"

Ƙasan zuciyarta ta ce, ina ma da gaske ka ke, da ka ji ruwan tambayoyin da ko ka ƙi Allah, sai ka dangana da faɗar gaskiya, a zahiri kuwa ta girgiza kai ta ce "Babu sir"

Ya kalli kofunan gabansu, ɗauke da shayi, wanda shi yana yi yana shan nasa, ita kuwa ko taɓawa ba ta yi ba.

"Ya ba ki sha shayin ba? Ki sha mana"

Sumayya ta sake risunar da kai ta ce "A ƙoshe nake ne"

Ya ce "I see, amma na yi mamaki da ki ka ce mini baki da tambaya a gare ni, duk da yadda ki ka ƙaryata hirar da na yi kwanaki, ki ka ce ban yi ayyukan da na ce na yi ba, na ƙyale ki ne kawai saboda managernku yayi ta bani haƙuri, kuma ke mace ce yarinya ƙara ƴar cikina.
Siyasa mu tamkar business take a wurinmu baby girl, we invest to make a profit, ita kanta gidan radiyon da ki ke aiki da su, nike hannun jari mafi tsoka a cikinta, dan haka abun da nake so shi ake yi, kuma domin yi mini campaign ya sanya na zuba kuÉ—ina a harkar gidan radiyon"

Sumayya dai ta yi shiru, ba ta ce komai ba.

Ya miƙe tsam, ya zagaya ya zauna a kan kujerar da take kai, wanda hakan ya sanya ja da baya, tana maƙale jikinta.

"Mun gama abun da ya kawo ki, sai kuma abun da ya sa na ce a turo mini ke"

Da sauri ta É—aga ido ta kalle shi, tana mamakin abun da ya faÉ—a.

Ya ɗauki kofin shayinta ya sha, sannan ya ce "Yarinyar da na ganku tare, ranar da na yi zuwan ƙarshe, ita nake nema ba ke ba, amma ke ce tsanin da yakamata na taka na kai gare ta, wacece ita?"

A tsorace take kallonsa, ya ce "Ki amsa mini mana".

"Nabila ce, ƙawata ce, she's like a sister to me" ta faɗa a tsorace.
Chapter 30 · 0% Book details