Sashe 29
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sumayya ta dake ta ce "No, barrister, ba as ƴar jarida ba kawai, as a woman and one of your fans, ko ƙorafi ne da ni, ta yaya zan same ki ki tsaya mini, atleast ko mintuna uku ki bani mana, dan Allah. Na san ƴan jarida wasu lokutan mu na da zaƙewa amma a duba roƙona" kamar ta zagi Sumayya, ta tsani baƙin naci irin na ƴan jarida, amma sanin halin su na yanzu sai su samu abun ɗorarwa ta ɓata mata career ya sanya ta danne ta ce "Ina jin ki"
Fitowar honorable, ta sanya ta yin shiru, ya kalli sumayya ya ce "Mu je in da zaki É—auki program É—in"
Tana ji tana gani, Naja'atu ta tafi.
Can wani surƙuƙi ya ja ta, da sai da ta fara jin tsoro, sai dai duk in da suka ratsa, akwai ma'aikata.
Sumayya ta sha mamakin, irin dukiyar da aka yi ɓarna, wurin gida wannan gida da kamar ba za a mutu a bar shi ba.
Daga ita sai shi a ƙaton falon, mai ɗauke da ɓangarori daban-daban.
Yayi mata iznin zama, yana ƙureta da idonsa, ta fito da kayan aikinta, ta fara saitawa, tana ta addu'a a zuciyarta, dan kaɗaicewar nan ta su kawai, hankalinta a tashe yake.
Nabila kuwa, Walid sakata yayi a gaba, har suka zo ƙofar wani gida, a can bayan kamfanunukan nan, babu kowa a wurin, ba gida gaba babu a baya, sai ma wani uban dutse idan ka yi tafiya can gaban gidan, ba ta taɓa zaton akwai irin wannan wurin a kano ba.
Ya kalleta ya ce ta shiga.
Jikinta yana rawa ta ce ba zata shiga ba, sai dai ya kira wo mata shi nan waje, wanda har a lokacin idan ta ganshin, ba ta san me za ta ce masa ba, tsabar fitina ce da son ta ɗaukaka ko ta halin ƙaƙa ya sanya take wautar.
Wani makami ya zare mata, mai kama da kibiya ya buga mata tsawa ya ce "Ki shiga na ce" sai a lokacin ta tabattar da ta tafka babban kuskure, haɗi da wauta mara amfani, idan suka illata ni fa?" Ta tambayi kanta cikin tashin hankali, haka ta shiga, yana bin ta da wuƙa.
ÆŠan mama yana É—an matsakaicin tsakar gidan, yana wankin kayansu, jin kukan mace ya sanya shi É—aga ido, cikin tsananin mamaki.
Sai dai yayi wata irin zabura ya ja da baya, yana bin su da kallo.
Yana cikin ɗaki a tsaye ƙyam, kamar an gina shi, ya bawa ƙofar baya, yana kallon bango. Ya sha ya bugu, amma bai samu yadda yake so ba, tunanin da yake son dainawa ya kasa, dan haka yana tsaye, yana ta nazarin abubuwa daban-daban a cikin ransa.
ÆŠan mama biyo su yayi, yana bin Nabila da kallo.
Turus Nabila ta yi, duk da ba ta ga fuskarsa ba, amma yanayin suffar jikinsa, sai da ta ji tamkar ta zunduma ihu, kallo É—aya zaka yi masa ka san madakin maza ne, ingarman namiji ne, da Allah ya yi shi da tsawo da kuma kakkauran jiki.
Idonta ya sauka a kan miyagun makaman da suke ɗakin, kamar za aje yaƙin duniya, gefen katifar da take ɗakin kuma, sirinjai ne, da kwalaban allura a wurin, sai kuma satchets na magunguna da kwalabe da kwalayen sigari. Ban da warin sigari, da wani irin ƙauri da ba ta gama tantance ko na menene ba, babu abun da yake tashi.
Tirƙashi! Ai ko lokacin da aka rufta ta, aka turata dabar madaki, ba ta ga abun da ya razanata ba, kamar yanzu ba, dan tarin ƴan dabar da ta tarar na su wasa ne, ba su firgita ta ba, tun da ta samu ƙwarin gwiwar yi musu magana.
"Boss, ga ta na kawo maka ita, sai ka ji dalilin da ya sa take nemanka"
Babban abun da ya ƙular da Viper, bai wuce watsi da umarninsa, da Walid yayi ba, tun da fari ya gargaɗe shi, a kan kawo masa wata mace, dan ba shi da alaƙa da su, amma ya yi burus da maganar sa.
Kasancewar ya sha sai dai buguwar ta gagara yadda yake so, ya sanya ƙwayoyin suka taimaka wurin tunzura shi, ya waiwayo a fusace domin ya sauke wa Walid rashin mutunci.
Sai dai gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa, adadin bugun zuciyar sa ya ƙaru da sauri da sauri, wani irin gumi ya fara tsatstsafowa ta kafafen gashin sa, jijiyoyin jikinsa suka kukkumbura.
Shi dai ya san a farke yake, ba iya bacci yake mai nauyin da zai É—auke shi, har ya sa shi mafarki yake, balle ya ce mafarki ne, kuma ya san a hayyacinsa yake, domin kuwa bai yi buguwar da hankalinsa zai gushe ba.
Sai dai a zahiri, sam yanayin sa bai nuna irin halin da ya shiga ba, dan babu abun da ya canza a tattare da shi, ya zuba mata manya-manyan jajayen idanunsa.
Tirƙashi! Jin ka ya fi ganinka! Nabila za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba ta taɓa ganin mutum mai kwarjini da razanarwa kamarsa ba, kodayake ai ya wuce ta kira shi kwarjini, sai dai mai ban tsoro.
Yadda ake faɗarsa a baki kawai, ta ɗauka wani ƙaramin alhaki ne kawai, sai dai yanzu ta tabattar da ya wuce duk yadda ta yi tsammanin ganinsa sa.
Ashe waɗanda take gani ƙaryar daba suke yi, ga ɗan daba na gaske yau ta gani,kamar ta fashe da kuka a cikin zuciyarta ta ce "Na shiga uku, wani tsautsayin ne ya kawo ni? Daga ni sai su idan suka kashe ni fa? Na san ko gawata ba za a gani ba, balle ayi mini salla, kamar yadda addini ya tanada"
So take ta É—aga ido ta kalle shi, amma abu ya gagara, saboda daga kallo É—ayan da ta yi masa, ba ta fatan sake yi masa na biyu, duk da zuciyarta na azalzalar ta, ta sake yin hakan, ba zata iya tantance abun da take gani a cikin idanuwanta ba, da kuma ma'anar irin kallon da yake yi mata ba.
Ƙoƙarin sake satar kallonsa tayi, amma suka yi ido huɗu, tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, saboda mummunar faɗuwar gaban da ta ziyarci zuciyarta, tabbas cikakken mashayi ne duba da yadda launin idanunsa suke, sai dai Allah ya yi shi da siffar girma da cikar zati, ya isa a kira shi da cikakken namiji.
"Shi kuwa wannan meya haɗa shi da aikin daba, a irin ƙira da Allah ya yi masa, da aikin office ya dace, ko na tsaro, ya ɓata wayonsa, da ya ƙare a shaye-shaye da daba.
Duk da ta sunkuyar da kanta, a tsakiyar ƙirjinta take jin kallon da yake yi mata.
Walid ya zagaya saitin kunnensa ya ce "Ka ga abun da nake gaya maka?"
Jinjina masa kai kawai yayi, taku ɗaya yayi, ba tare da Nabila ta ankara ba ya danƙi wuyanta.
Ba wani riƙon kirki yayi mata ba, amma idanuwanta suka yo waje, jikinta ya hau kyarma, tamkar ana kaɗa mata gangi.
Ta saka hannunta ta riƙe nasa, numfashinta na fita da sauri da sauri, cike da tsoro take ta gwagwarmayar ƙwatar numfashinta, saboda yadda take jin yana barazanar barin ƙirjinta.
Ba ta ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da ta ji tsini a cikinta, ga wani irin azababben zafi da ya ratsa fatar cikinta.
Ba ta san bata tsorata ba, sai da ya buÉ—e baki yayi magana.
"Wacece ke? Me ki ke nema a wurina?!!"
Numfashinsa ya sauka a fuskarta, warin sigari ya daki hancinta, jikinta ya hau tsuma.
A rikice Walid ya ce "Boss zaka kashe ta fa, ka kalli abun da ka ke yi"
Bai saurari walid ba, ya sake buga mata tsawa, tare da ƙara nutsa wuƙar da ya saita a cikinta.
"Viper, jini ya fara zuba daga cikinta, ka dawo hayyacinka mana" yayi maganar yana ƙoƙarin kai hannu ya ƙwace wuƙar hannunsa.
Idan ka taɓa ni, kai zan cakawa!" Yayi maganar yana kallon idon Nabila da suka yo waje, ga jikinta ya saki, sai numfashi da take yi da kyar.
BuÉ—e baki tayi, da niyyar ta yi magana, amma jikinta ya saki, ta daina ganin komai sai duhu.
"Viper kar ka kashe yarinyar nan" Amma kan walid ya yi wani yinƙuri, Viper ya watsar da ita a wurin, ta faɗi sumammiya.
Ayshercool
08081012143
         *ƘARFE A WUTA*
AISHA ADAM AYSHERCOOL
Arewabooks : ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724
What's app :08081012143
What's app channel
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Paid book ne ₦500 via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda ba ss som group akwai special 1k.
13
Cike da takaici Walid ya nufeta da sauri, ya kalli Viper ya ce "Amma meyasa zaka yi haka? Da ka kasheta fa?"
Aminu ya kalli saman tsinin wuƙarsa da take ɗauke da jinin Nabila, bai kalli Walid ba ya ce "Ban gaya maka kar ka kawo mini kowa ba?"
Walid ya ce "Ka gaya mini, amma na tabatta ka ga abun da nake son ka gani, ai ko?"
"And so, me hakan zai amafana mini? Ka ƙaddara ban ga komai ba, kuma gargaɗi na yi mata a kaina, dole na san tana da manufar son haɗuwa da ni, wataƙila wata ƙulalliyar ce, sai dai amafani da mace ba zai hana in illata ta ba, idan ta shiga gonata"
Walid ya ce "Yanzu abun da ka gani, ba shi da muhimmanci kenan?"
"Ko kaÉ—an" ya bashi amsa kai tsaye.
Walid ya tsuguna a kanta, amma ya rasa abun da yakamata yayi.
Wani irin numfashi Nabila ta fara fitarwa, mai sauti wanda hakan yake tabattar da, numfashin yana ba ta wahala.
ÆŠan mama ya ce "Mun shiga uku, wane irin numfashi ne wannan,ko mutuwa za ta yi ne?" Walid ya sake dirircewa ya rasa abun yi.
Viper ya goge jinin Nabila da ke jikin wuƙarsa, a jikin rigarsa.
Ya É—aga kai, yana kallon yadda take jujjuya kanta, tana neman iska.