← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 95

Sashe 60

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanayin garin da sanyi saboda ruwan da aka yi, amma ya takure yana bacci.

Ta fitar da kwanukan, ta ɗaukko bargo daga ɗakinta, ta zo zata rufe shi, ɗan ƙura masa ido ta yi. Al'amin ba shi da wata makusa, da yake baccin nan ma he looks very innocent and calm.

Kasa rufe shi ta yi, ta tafi tunanin ya aka yi ya fara shaye-shaye, ya aka yi su mama suka samo shi ma, suka aura mata? A ina yake ina ne gidansu? Duk take tambayar kanta.

Tashi ya yi zaune kamar aljani ya ce "Meye ne kin zo kin sakani a gaba kina kallona"

Zabura ta yi ta ce "Yi haƙuri, na zata bacci ka ke yi, ba kallonka nake yi ba, na ga kamar kana jin sanyi ne, bargo na kawo maka" tayi maganar tana tsuma.

Ya miƙa mata hannu, ta bashi bargon, ya ware shi ya lulluɓa, ta fita tana mamakin al'amin idan yayi wani abun mamaki yake bata, har da ajiyar zuciya ta ji yana yi alamun baccinsa yayi nisa, amma kawai ta ganshi a zaune.

***
"Allah ya taimaki maigida"

"An gaisheka, ya ake ciki?"

"Komai normal, ba wani abu"

"Yaya za ayi? An kama Ja'afar da kaya, hukumar nan sun ƙi sakinsa, ba zan matsa ba, amma ina buƙatar a musanya shi da wani"

"Oga ba zan iya sakinsa kai tsaye ba, amma dole za'a samu wani a kama shi da kayan, sai a saki jafar a kama shi, ka san wannan karon shugaban namu, yana da sanya ido sosai"

"Shikenan, ayi abun da yakamata kawai"

"Ok sir".

Cikin ikon Allah, matar nan tela, tana biyan jauhar, duk da ba wani kuÉ—in kirki take bata ba, amma tana jin daÉ—i sosai da sosai, ta sayi katin tara kuÉ—i, É—an abun da tayi cefane, sauran sai ta saka a kati, kuma Allah ya saka mata albarka a ciki.

Yaran maƙwabta idan sun shigo, tayi musu tsifa da kitso, babu ko sisin iyayensu.

Ta duƙufa tana aikinta, ba ta ji motsinsa ba, sai jefo mata bargo yayi a ka.

A razane ta tashi, bargon kuma ya cukuikuyeta.

Ya ce "Zaki taka kwaɗo" Ihu ta saka ta samu ta cire bargon da ƙyar, tana dube-dube, yana tsaye yana kallonta, kamar ba shi yayi maganar ba.

Ta ce "Ina kwaÉ—on?" Ya yi shiru bai ce komai ba.

Ta kalli yadda stone ɗin ya zube kamar ta yi kuka ta ce "Kalli yadda ka saka na zubar da kayan sana'ata." Ta durƙusa za ta kwashe, sai kuma ta yi sauri ta hau kan kujera, ta maƙale ƙafafuwanta ta ce "Ina kwaɗon ya shiga ne?"

Haryanzu shi dai bai daina mamakin yadda kwaÉ—o ya zama abun tsoro ba.

Hanyar fita ya nufa, ta gane tsokanarta yake yi, nan ta ƙara jinjinawa ƙi faɗinsa, har ya iya ya tsokaneta, amma ya sha kunu ba fara'a.

"Master" ta kira shi. Ya tsaya bai waiwayo ba.

"Dan Allah idan Allah ya yassare, ka taho da omo, zan yi mana wanki".

Yanzu ma bai yi magana ba ya fita, ta naÉ—e bargonta, ta cigaba da aikinta.

Zakiyya kuwa, kamar zata zare, Rahila na ta janta wuraren malamai kala-kala, yadda za su samu, Hafsa ta auri Alhaji mu'azzam da zarar ya dawo.

Har sha É—aya na dare, jauhar na aikin jera stone É—in ta a kan gadonta, dan tun tana jin tsoron zaman gidan, har ta saba, sai da ta ji bacci yana kama idonta sosai, sannan ta tashi ta ajiye kayan, tayi wanka ta fito tana shirin kwanciya.

Ji ta yi ana buɗe ƙofa, dan haka ba ta damu ba, ta san mai gidan ne, sai dai bayan wasu mintuna ta ji kamar yayi jifa da wani abu a falo, yana ta haki mai kama da kakari, gabanta ya faɗi ta fito da sauri, ta tarar da shi ya riƙe hannunsa yana ta nishi, hannunsa an yanke shi, da ƙafarsa ta hagu, kasancewar da wuta, ya sanya ta ga yadda yake zubar da jini, a gigice ta ƙaraso cikin matsanancin tashin hankali ta ce "Master faɗa ku ka yi da wani? Ya aka yi ka ji ciwo haka?" Yayi shiru yana fesar da iska daga bakinsa.

Da gudu ta shiga É—akinta, ta É—aukko zani ta danne masa na hannunsa da ya fi zubar da jini, ta rikice ta rasa me za ta yi, kawai ta nufi hanyar fita.

Ya ce "Ina zaki?"

Cikin tashin hankali ta ce "Maƙota zan je, a samo abun hawa a kai ka asibiti kar jininka ya ƙare".

"A haka kuma zaki fita?"

Sai a lokacin ta ga, ko hijjabi babu a jikinta, ta koma É—aki, ta É—aukko hijjabinta sai kuka take yi, tana dawowa falon ya ce "Kar ki fita"

"Meyasa? Jini fa ka ke zubarwa"

Ya ce "Ki ƙyale ni, zai daina zuba ne"

Cikin kuka ta ce "Ni dai dan Allah ƙyale ni, sai wani abun ya same ka, idan jininka ya ƙare fa mutuwa zaka yi" ba ta ma jira me zai ce ba, ta kasa da gudu, tayi waje. Ta din ga buga gidan maman halimatu, malam lawan ya buɗe, ya tsaya yana tambayarta menene?".

"Dan Allah baban su halimatu, ka taimaka mini, na ga kana da babur, mijina ne aka sare shi dan Allah a kai shi asibiti, sai zubar da jini yake yi"

Ya waro ido ya ce "A daren nan, haka kurum garin taimakonku, wani abun ya same ni, shi ma idan ya samu wani haka zai yi masa, sai da safe" ya rufe ƙofarsa.

Haka ta din ga buga gidajen layin nan, na ƙarshe ne mai gidan ya biyota, sai dai ba shi da abun hawa, suka zo ya tsaya a ƙofar gidan, ta shiga ciki.

Yana zaune, ya kashingiÉ—a ya lumshe idonsa, yana jin yadda raÉ—aÉ—i yake ratsa wurin saran.

"Master, taso mu je"

Bai buÉ—e idonsa ba ya ce "Ina?".

"Wai meyasa ka ke haka, asibiti mana" tayi maganar hawaye na ta ambaliya a fuskarta.

Ya miƙe yayi waje, ya tarar da maƙwabcin na su a tsaye, suka gaisa Al'amin ya ce "Malam ka rabu da ita dan Allah, ka je ka kwanta, ba wani abu in sha Allah"

Ya ce "A'a ga jini kana ta zubarwa, ni bani da abun hawa, na kira wani ƙanina, a nan titi chemist ɗin sa yake, ko taimakon gaggawa sai a baka"

Tayi farat ta ce "Yauwwa mun gode Allah ya saka da alkhairi"

Haka suka tafi, ya kira ƙanin nasa, ya buɗe chemist ɗin babban wuri ne sosai.

Ya fara yi masa É—inki, saboda raunin na hannunsa yayi zurfi sosai da sosai.

Sai dai shi da ake ɗinkewa kamar ƙwarya ko a jikinsa, ita kuwa sai uban kuka take yi, tana yi masa sannu.

Kawai bin ta yake yi da ido, har mamaki yake yi, yadda take nuna matuƙar damuwarta a kansa.

Mai Chemist É—in ya ce "Dan Allah ki daina kukan nan, ba wani abu, ba ki ga shi jarumi bane?"

"To jininsa ba zai ƙare ba, ya zubar da jini sosai tun a gida"

Ya ce "Ba zai ƙare ba in sha Allah, idan ma ya ƙare sai mu saka masa naki".

"Ki daina yi mini surutu a ka kin cika mini kunne" yayi maganar a ƙule. Haushi ne ya cika masa rai, kamar ya kife mai chemist ɗin da mari.

Ta ce "To na daina sannu" tayi maganar cikin kulawa.

A ka gama É—inki, ya ce zai É—an saka masa ruwa, saboda ya taimaka masa ya zubar da jini sosai, amma fafur ya ce ba ya so.

Ya haÉ—a masa magunguna, ya ce ya din ga zuwa ana wanke ciwon, jauhar ta ce "Sai dai ka bani kayan dressing É—in, ba zai din ga zuwa ba".

Mai chemist É—in yayi dariya, ya haÉ—a ya bata, ta ce "Nawa ne kuÉ—in maganin? Da abun da aka yi masa?".

Maƙwabcin ya ce "A'a kar ki damu, Allah ya bashi lafiya, ni zan biya".

Jauhar sai da ta risuna, ta din ga yi masa godiya, sannan ta ce "Tashi mu tafi" ya miƙe tsam ta bi bayansa.

Suka baro maƙwabcin na su a can, suka nufi gida.

"Sannu, ka na jin jiri ne? Idan kana jin jiri mu tsaya ka huta, ko ka dafa ni" kallonta ya yi ya ga me zai dafa. Ya dai yi shiru bai yi magana ba.

Suka isa gida, ya shiga ɗaki ya zauna, ta fito ta hau aikin wurin da ya ɓata da jini, dan a buɗe su ka bar gidan ma.

Ya zauna ya ci abincin da ya tarar a É—akinsa, ta ga ledar omo ce da sabulu da ta ce ya sayo, su yayi wurgi da su.

Ta dawo É—akinsa, ta tarar ya jingina ya lumshe ido, "Sannu master, yana yi maka zafi ne? Ga magungunan nan ka sha kan ka yi baccin".

Ya girgiza mata kai alamar ta ƙyale shi, gumi ya fara tsatstsafo masa, saboda allurar ta sake shi, zafi ya fara ratsa shi.

Saboda kar ta takura masa da surutu, ya kwanta ya hau baccin ƙarya.

Ta fita ta É—aukko mafici ta dawo, ta zauna a gefensa, ta hau yi masa firfita.

Sai dai lokacin kusan ƙarfe biyu ne na dare, ta din ga zabga hamma, yana kallonta, har bacci ya ci ƙarfinta, ta saki maficin.

Ya buɗe idonsa fes a kanta, har mamaki take bashi, yadda take nuna matuƙar damuwarta a kansa, kuma komai zai yi mata ba ta jin haushi.

Hakazalika bai daina mamakin yadda aka yi, iyayenta suka yarda suka aura masa ita ba.

Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya kira walid, uku sauran nan, ya É—aga.

"Walid"

"Maza, ya aka yi ne?".

"Ka san akuyancin da yaran nan suka yi mini?"

Walid ya ce "Wane yaran, suwaye?".

"Na baro chamber, na shigo cikin unguwa, kawai na ji sara a hannuna, sun kai su bakwai, suka hau ni da sara, kasheni suka so yi"

Walid ya zabga ashar ya ce "Suwaye?".

"Bari na yi wa ɗaya shaida, haryanzu ba su san waye ni ba, na karya biyu, sauran sun gudu, sun yi mini rauni a hannuna da ƙafata".

"Yanzu kana ina?"
Chapter 60 · 0% Book details