← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 95

Sashe 44

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi shiru kamar ba da ita yake ba.

"Baby yangar nan tana yawa fa, dan Allah ki yi mini magana na ji nutsuwa mana" yayi maganar yana dawowa kusa da ita ya tsaya.

"Jauhar ki yi magana mana"

"Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi" ta faɗa a hankali.

Ya ce "Kin amince zaki aureni?"

Ta É—aga masa kai alamar eh.

"Wow, anya ba zan  ce a ɗaura mu tafi chinan tare ba?"

Ta ce "A'a, dan Allah a bari na gama makaranta, mun kusa yin WAEC".

Alhaji mu'azzam ya ce "Na so ace zan iya yi miki hakan, amma ba zan iya jurewa ba, kar wani ya rigani, ko da na tafi ina can, iyayena zasu zo ayi maganar, da na dawo sai maganar bikinmu, i will be with my little baby amarya very soon in sha Allah"

Tayi murmushi cikin jin kunya, tana murmushi.

"Jibi in Allah ya kaimu fa zan tafi, babu tsammani tafiyar ta zo, me zaki gaya mini kafin na tafi, da zan din ga tunawa da ke, kin ƙi yarda na baki waya, balle mu din ga waya ina jin daɗi. Yanzu me zaki ce mini?".

Ta ce "Duk lokacin da ka tuna ni, ka yi mini addu'a"

"In sha Allah amaryar mu'azzam, zan din ga yi mana, daÉ—in auren mace mai addini kenan"

Ya din yi mata hira, har ta É—an sake tana yi masa murmushi.

Ita dai ba ta sani ba tana son sa ko ba ta son sa, duk da ya girme mata, ya iya magana, ya sauke shekarunsa dai-dai da nata, ga ƙamshin turaren sa daɗi yake yi mata, dan a hakan yadda take fama, idan ta samu ƴan kuɗi, baka rabata da turare.

Daga kan Surayya zuwa walida da hafsa, babu wadda ba ta fito ba, da niyyar za su fita yin wani uzurin, kuma babu wadda ba ta gaishe shi ba, sai dai gaba É—aya hankalinsa da nutsuwarsa yana kan Æ´ar bainun gabansa wato Jauhar.

Da zai tafi, sai da ya haɗe rai sosai, sannan ta yarda ta karɓi kuɗin da ya bata.

Sai da ya tabattar ta shiga gida, sannan ya tafi.

ÆŠaki ta je ta bawa baba duk abunda ya bata, kuÉ—i masu yawa, mama ta din ga masifa, kamar ta ari baki, da sunan kula da tarbiyyar Jauhar.

***
Al'amin yana kashingiɗe yana busa wiwi, yana kaɗa ƙafarsa ɗaya, yana jin sa a sama, dai-dai da kowa, sai dai busa hayaƙin yana bashi nishaɗi, yana jin daɗin hakan.

Wuƙar gefensa ya ɗauka ya zauna sosai, ya karta ta a ƙasa, ya gyaɗa kai sannan ya ɗago ya ce  "zan shiga ƙofa, zan tayar da tarzoma, zan je ɗaukar fansa"

"Wurin madakin dai?" Walid yayi maganar yana kallon sa.

"Koma wurin waye, ka manta abun da suka yi mana kafin na je prison?"

Walid ya girgiza kai ya ce "Ban manta ba"

"Zamu É—auki fansa, madaki kuma ban ce kowa ya taya ni ba, faÉ—ana ne nikaÉ—ai wannan".

"Shikenan yaushe zamu shiga?"

"Shammatar su zamu yi, zan yi muku magana"

Ya koma ya kashingiɗa, ya cigaba da zuƙar wiwi.

*****
Tun da Allah ya sa Alhaji mu'azzam ya tafi, Jauhar ta manta da babinsa, sai dai in mutanen gidan sun É—aukko hirarsa, ita da yake zuwa wurinta ma ba ta zancensa kamar yadda suke yi.

Babbar murnarta ita yanzu, ganin yadda kantunta yake ƙarewa da wuri, duk da ana yi mata mugunta a gidan, yaya saifu ya ƙara mata jari, ya bata dubu ɗaya.
Ɗan kuɗin da take juyawa, da na riɗin, da na shirin dutsen, bai fi dubu biyu da ɗari biyar ba, amma murna take yi da hakan, jin kuɗin take da yawa, dan ƴar hamsin ɗarin da take bi na riba, ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, dan nan da nan ta tara kuɗin pad, har ta fara tarin kuɗin makarantar islamiyyarta, kan lokaci yayi ta zo tana nema.

Yau an tashi daga islamiyya, ta sayar da riɗinta tsaf, dama da ɗaurin shirin dustenta, ta fito daga aji, tana lissafin tayi maza ta kai musu, ta karɓo wani.

Ko da ta fito wajen gate É—in makarantar, matasa suka gani suna guje-guje, wai faÉ—an daba ake yi, mai dogon zamani ya shigo É—aukar fansa.

Jauhar ko a jikinta tayi gaba, tun da daga in da ake gudun bayansu ne, dan haka tayi gaba abun ta, ta nufi hanyar gidan da take karɓar shirin.

In da take bin shiru babu mutane ma, tana shiga layin gidan shirin, ta ɗaukko robar riɗinta, ta ciro kuɗin cinikinta, ta hau ƙirgawa murmushi ta saki, tana jin daɗi, ta fara tunanin tambayar kuɗin aya gwangwani biyu, ita ma ta din ga soyawa da gishir tana sayarwa.

Hankalinta ne yayi mummunan tashi, bayan da tayi baƙin ganin da ba ta farga da shi ba sai yanzu.

Hannunsa riƙe da wani mutum, da ba ta da tabbacin yana da rai ko babu, da wuƙa a gefen cikin mutumin, hannunsa duk jini, kuma shi ma da yake riƙe da mutumin da take kyautata zaton kashe shi ya yi ƙafarsa sai zubar da jinin take yi.

Tun da ta shigo layin ta fara lissafa kuÉ—i, ya É—aga kai ya ganta, amma ita sam ba ta ganshi ba, hankalinta yana kan lissafin kuÉ—in da yake hannunta, sai da ta je tsakiyar layin, ta kusa zuwa daf da shi sannan ta farga.

Zuciyarta ce ta fara wani iri razanannen bugu, gashi ta kasa ko da motsa ƙafarta, balle ta cirata ta gudu, ba ta taɓa ganin mummunan tashin hankali ba tun da take a rayuwarta ba sai yanzu, ita ko film ne ta ga ana kashe-kashe, ko harbe-harbe bata kalla, kodayeke ita kallo ma bai dameta ba, amma sai yau gata ga gawa da jini.

Ba tare da ta yi tsammani ba, wani irin ƙarfi ya zo mata, ta taƙarƙare iya ƙarfinta, ta kurma wani irin uban ihu, ta yinƙura da niyyar ta gudu, sai dai tsananin bugun da zuciyar ta take yi, ya sanya numfashinta kasa daidaituwa a ƙirjinta, kuma ta gaza ɗaukar nauyin jikinta, dan haka ta faɗi a wurin a sume, robar da cinikin, da jakar islamiyyar duk suka watse a wurin, gefen kwata.

Duk da wannan uban ihun da tayi, babu wanda yayi ƙoƙarin buɗe ƙofarsa ya ga mai yake faruwa.

Duk da dama, gidaje biyu ne kacal a layin, sauran duk bayan wasu gidajen ne a cikin layin.

Tsaki ya ja, ya mayar da idonsa kan liti, da yake numfashi sama-sama.

Ya kalli ƙafarsa da take ta zubar da jini shi ma, saboda saran da aka yi masa.

Ya kwantar da liti, ya tashi ya tafi kan jauhar, ya kai hannun sa kan hancinta, ya ji tana numfashi.

Ya kamo hannunta, ya riƙe tsintsiyar hannunta, ya ji zuciyarta na wani irin bugu, da saurin gaske.

Kamar ya ɗauki tabarma, haka ya ɗauketa daga kan hanya, ya kwantar da ita a tsallaken kwatar, ya tattaro kayanta ya haɗe mata wuri guda, sai dai uniform ɗin ta, duk sun ɓaci da jinin da yake zubarwa.

Wald ne ya ƙaraso layin da sauri, shi ma hannunsa riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙa tana zubar da jini, ya ƙarasa in da Al'amin yake harya fara ganin jiri, saboda jinin da ya zubar.

"Subhanallah, waye yayi gangancin yankarka?"

"Ƙyaleni, ka kira su baffan?"

"Eh, suna bakin titi da É—an sahun"

Ya miƙe ya saɓa liti da yake zubar da jini a kafaɗarsa.

Walid ya ce "Kawo shi, na ga kamar jiri ka ke yi mu ƙarasa".

Ya ce "A'a bar ni da shi, zan yi wa honorable waya, ya aika mana Æ´an sanda asibiti, waccan yarinyar, ka buga É—aya daga gidajen layin nan, su fito su kaita Asibiti, ta tsorata ne, idan kuma ba haka ba za ta yi musu mushe a wurin, saboda zuciyarta na bugawa da sauri sosai"

Walid ya ce "Wai wa yake ta wata yarinya, kai kaÉ—ai zaku tafi asibitin, kalleku fa jina-jina"

"Mai rai ce fa, idan ba su buÉ—e ba, ka haura gidan kawai, ka saka su buÉ—e, yanzu idan muka tafi da ita zai zama wani abun daban" daga haka yayi gaba, ya nufi barin layin.

Walid ya yamutsa fuska, ya samu ɗaya daga gidajen, ya din ga wani irin bugu, kamar yaƙi.

***
Cikin tsananin hanzari ta yinƙura, za ta diro daga kan gadon da take, tana faɗin"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ku taimake ni, zai kashe ni"

Cikin azama baba ya riƙe ta, ƙoƙarin ture shi take yi, ta saukko daga kan gadon. Baba ya ce "Jauhar, buɗe idonki, ki kalleni ni ne ki nutsu" sannu a hankali ta buɗe idonta, ta kalli baba, ta juya ta kalli su mama da Yaya saifu da suke wurin, sai malam jamilu da malam hamza.

Jikinta ya hau wata irin tsuma, ta dinga fizge-fizge tana ƙoƙarin fizge robar ruwan hammunta.

"Ke ki nutsu mana, meye haka ne ana yi miki magana" mama tayi maganar tana haÉ—e rai.

Ta girgiza kai ta ce "Mama tsoro nake ji, wani ya kashe fa, dan Allah ku ɓoye ni zai kashe ni nima, ganinsa nake yi a idona, dan Allah baba ku tafi da ni tsoro nake ji" tayi maganar tana ƙoƙarin tashi tsaye.

Baba ya ce "Wai shi wa?"

Cikin kuka ta ce "Ban san shi ba, kawai gani nayi dai ya kashe wani yana kallona, nima na san zai biyoni ya kashe ni".

Baba ya ce "To ai babu wani wanda aka gani an kashe, ke kaÉ—ai aka gani a layin a sume".

Anty ta ce "Uban me ma ya kai ki can, in da ba hanyar gida ba?".

"Shiri na je karɓowa"

"To ubanwa ya aike ki?"

Baba ya ce "Dan Allah duk a daina wannan maganar, yanzu a bari ta samu nutsuwa".

Ƙoƙarin kwantar da ita Baba yake yi, ta kalli jikin uniform ɗin ta, ta ga jini, ihu ta sake yi, tana faɗin "Meya same ni, baba kalli jini a jikina, na gaya maka nima kasheni zai yi, kalli jini fa wataƙila ma na mutu ne".

A take wani abu ya É—arsu a zuciyar mama, tayi wani shu'umin murmushi, yaya saifu kuwa likitoci ya kira, aka sake yi wa jauhar allurar bacci, dan gaba É—aya nema take ta zare.
Chapter 44 · 0% Book details