← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 95

Sashe 17

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Madaki ya karta wuƙa a ƙasa, ya kalli tarin matasan da sun fi ashirin a gabansa ya ce "Babu rangwame ko sassauci, babu mace babu namiji, ko babba yaro ko tsoho, duk wanda aka samu idan aka shiga operation ɗin nan a farmasa, ayi ɓarna ayi ta'adi a ɗauki fansar abun da Aminu yayi mana, jini ya din ga gudana ko ta ina, duk shagon wanda aka samu a fasa ku kwashi ganima, na yarje muku.
Haka zalika duk wanda ya gano in da Viper yake, muddin ya kawo mini shi, a mace ko a raye, akwai tukuici mai tsoka"

Suka fara shewa cike da maye, ɗaya daga cikin su ya ce "Aminu fa ƙarfe ne a wuta, duk wannan shewar kama shi ba abu ne mai sauƙi ba, da mai sauƙi ne na san da ka riga mu kama shi"

Madaki ya ce "Rufe mini baki, ko na yi gunduwa-gunduwa da namanka, dole ne a kama shi, kai gobe duk wanda aka gani daga tsallaken unguwar su, ya shigo unguwar nan ma a sara mini shi kawai, a É—auki fansa mafi muni na abun da ya yi mana, zan ga da ni da shi, waye zai sarara waye gaba da wani"

Cikin haɗa baki suka dinga faɗin "An gama oga, gobe akwai ƙaramin yaƙi"

misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe, a sannu take tafiya a cikin unguwar, tana duba kwatancen da barrister Habib ya tura mata.

Kasa ganewa tayi, ta tsaya a wurin wani mai kanti, ta sayi ruwa ta sha, kuma tambaye shi.

Tana tsaye tana duba wayarta a cikin shagon provision ɗin, wani matashi ya shigo, suka gaisa da mai kantin ya ce "Bani ƙulli biyu da ruwa uku"

Mai kantin ya ce "Amma ka san ina binka sauran kuÉ—i ko?"

"Zan biyaka, wannan yawa ne, ka bani na ware mana, caji zan yi kaina gaba É—aya babu network,aljihuna kuma yayi gobara"

"Ba zan bayar ba" mai shagon yayi maganar yana miƙawa Nabila ruwan roba.

Nabila ta din ga satar kallon matashin, yadda bakinsa ya karkace saboda shaye-shaye take kallo, laɓɓansa duk sun zazzago.

Tayi gyaran murya ta ce "Ɗan uwa ka bashi mana, tun da ya haɗaka da Allah, in sha Allah zai kawo maka, tun da ya yi alƙawari"

"Rabu da shi, ba ya biyan bashi"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Nawa ne kuÉ—in nasa?"

Mai kantin ya ce "Dubu biyu nake bin sa"

Ta yi murmushi, tare da ciro kuÉ—i a jakarta ta ce "Dubu biyu ai babu yawa, Ga dubu uku, na biya masa kuÉ—in da ka ke bin sa, ka bashi wani bashin, ni kuma ka É—auki kuÉ—in sayayyata"

Matashin ya kalleta ya ce "Sai kin yi babbar yaya, Allah ya ƙara arziki"

Ta amsa da "Amin É—an uwa na gode sosai".

Wani abu ta ga an bashi a nannaÉ—e a leda, da ruwa ya sake yi mata godiya, ya fice.
Yana fita ta ce "Malam dan Allah menene wannan ya saya?"

Mutumin yayi murmushi ya ce "Ƙanwata wiwi ce" waro ido ta yi ta ce "Wiwi kuma, ka ke sayarwa? Amma na ga kai kamar ba ka sha ko?"

"Ki yi ƙasa da muryarki mana, ya zamu yi sana'a ce, ni ba abun da nake sha. ga canjinki"

Cikin mamaki ta ce "Meyasa ka ke sayar da abun da ba ka sha?"

"Kar ki tsananta bincike malama" yayi maganar yana haÉ—e rai. Ta jinjina kai ta ce "To Allah ya taimaka"

Fitowa ta yi daga shagon, ta hangi matashin yayi nisa, ta rufa masa baya ta bishi da sauri.

"Bawan Allah ɗan tsaya dan Allah" ta ƙarasa tana haki.

Ya tsaya yana kallonta ya ce "Ya dai?"

"Abu zan tambaye ka, amma kafin nan ka san abun da ka saya É—in nan, yana da illa ga lafiyarka?"

Tsayawa yayi yana kallon ta, tayi saurin cewa "Dan Allah taimako nake nema, wani gida nake nema, amma na kasa gane layin, ko zaka taimaka mini?"

"Ina ne?"

Ta gaya masa ya ce "Na san gidan, amma ba hanyar ki ka biyo ba nan"

"Dan Allah kwatanta mini"

"Mu je na kai ki bakin layin"

Ta ce "Yauwa É—an uwa, dan Allah mu yi wata magana mana, ka san wani mutum Aminu Viper?" Wani irin burki ya ci yana kallonta.

"Yi haƙuri idan na ɓata maka rai, ɗan uwana ne shi, tun da Allah ya sa ya bar gidan yari, bamu sake ganinsa ba, kuma na ji an ce yaransa sun tayar da tarzoma a unguwar nan a satin nan, dan har asibitin da aka kai waɗanda aka yi wa rauni na je, na zaci zan ganshi, amma ban tarar da shi ba"

Ya ware mata jajayen idanunsa ya ce "Ki ka ce É—an uwanki ne?"

Cikin ƙarfin hali ta ce "Eh, ina da alaƙa da shi"

Ya ce "Na san shi, na kuma san in da yake"

Da sauri ta ce "Dan Allah ka taimaka mini a ina zan ganshi?"

Ya ƙare mata kallo ya ce, idan kin tashi, ki tambayi ina ne layin iraƙi a unguwar nan, idan ki ka je akwai wata babbar bishiya zaki ga wasu a zazzaune a wurin, ki tambaye su, za su nuna miki shi.

Cikin tsananin farin ciki, ta din ga yi masa addu'a. Amma fa sai dai ta kasa tantance irin kallon da yake yi mata, hakan bai dame ta ba.

Har ƙofar gidan matar ya rakata, ta kuma yi masa godiya, ta ciro kuɗi ta bashi, sannan ta shiga gidan matar.

Matar ta karɓi Nabila hannu bibbiyu, bayan da Nabilan ta yi mata bayanin barrister Habib ne ya turo ta.

Ta bawa Nabila duk wani information da take buƙata, tana gama abun da take yi ta tashi ta ce tafiya za ta yi.

Babu yadda matar ba ta yi da ita ba, a kan ta zauna ta ci abinci ta yi salla, amma taƙi, ta tashi ta tafi.

Babu tunanin komai, tana fita, ta tambayi wasu yara, ina ne layin iraƙi?.

Duk sai da suka kalleta, ganin tana mace tana tambayar wannan layin da Æ´an daba suka mayar mallakinsu, abunka da yara, babu tunanin komai suka sakata a hanya, ta yi musu godiya ta nufi kwatancen.

Tana ta addu'a Allah ya sanya ta dace, duk tana da burin cikar nata muardin, amma za ta yi farinciki sosai idan aka ce Nasir ne yayi nasarar kama Aminu, koba komai likkafarsa za ta sake É—agawa, ta nufi layin ba tare da ta san idan ta ganshin me za ta ce masa ba.

Layin shiru babu kowa, babu gina-ginan kirki, sai kangwaye, sai da ta je tsakiyar layin, ta hango wata ƙatuwar bishiya, da mutane.

Kamar ba mace ba, babu razani ko fargaba ta tunkari bishiyar.

Gaba ɗaya suka zuba mata ido, har ta ƙaraso.

Wiwi kawai suke busawa, ta ɗan tsaya nesa kaɗan da su, saboda hayaƙi.

"Ina wuninku"

Suka amsa mata da lafiya ƙalau, suna mamakin ganin mace a wannan chamber.

"Dan Allah tambaya nake yi, wani nake nema, aka yi mini kwatancen nan aka ce zan sameshi".

ÆŠaya daga cikin su ya ce "Waye shi?"

Ta ce "Amm, sunansa Al'amin, amma ana ce masa Aminu Viper, tun da ya fito daga prison ba mu sake ganinsa ba"

Ɗaya ne ya miƙe tsaye ya ce "Ke, ba ki da hankali, a dabar madaki ki ke naman wannan ɗan iskan? Kai kan taba, sako su mass su rakata, tun kan oga ya zo ya saka ayi gunduwa-gunduwa da namanta"

Sai yanzu ta fuskanci shigo-shigo babu zurfi wanda ya yi mata kwatancen ya yi mata.

Cikin sauri ɗaya ya ce "Meyasa za'a bari ta tafi? Bayan ka san yau zamu fasa ɗaukar fansa, ta kanta ya kamata mu fara" yayi maganar yana ƙoƙarin zare makami.

Sai dai tuni suka sako wa Nabila wasu irin murguza-murguzan karnuka, masu kama da zakuna.

Cikin ihu ta kwasa da gudun tsiya, tana kururwar neman agaji, saboda yadda take ganin kamar karnukan za su cinyeta É—anya, sai dai gudun da suke yi ya wuce hankali, ga takalminta mai tsini ne sosai, dan haka suka kusa cimma ta.

Babu tsammani ta faÉ—i, saboda yadda numfashinta ya fara sama-sama.
Ayshercool.
08081012143
[7/22, 1:49 PM] null:               *ƘARFE A WUTA*

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

P8

Ta saka hannu, ta kare kanta, tana jiran su hauta da cizo.

Wani irin fito ya yi wa karnukan, suka juya suka koma da gudu in da yake.

Matashin nan ne na É—azu, da ta biyawa bashi, ya kalleta ya ce "Kin san meyasa na taimake ki?"

Bai jira amsar da za ta bashi ba ya ce "Ba na tunanin Aminu yana da wata ƴar uwa mace, dan haka ƙarya ki ke yi, akwai wata manufa a ranki da yasa ki ke nemansa. Sannan ya taɓa yi mini alfarma a lokacin da ya samu damar da zai kashe ni, kuma kin kyautata mini, alhalin baki sanni ba.
ÆŠan daba ba mahaukaci bane ba, shaye-shaye ne yake ruÉ—a mana tunani.
Wannan shi ne kaÉ—an daga abun da ka iya samunki, idan ki ka cigaba da neman sa, ko bibiyarsa, wannan dabar babu abun da suke buri da fata, sama da su riga Æ´an sanda kama aminu, mace ce ke ki kiyaye kanki, tashi maza ki tafi gasu can tahowa, idan suka cimmiki babu lallai na iya hana su illata ki"

Da ƙyar ta tashi, ta yi gaba da sauri, tana cigaba da haki, adaidaita sahu ta hau, ta yi masa kwatancen in da zai kai ta.

Kasancewar mai rabon shan duka, baya jin bari, suna tafe tana sauke numfashi, tana tunanin son sanin su kuma waÉ—an nan me yayi musu suke son su riga Æ´an sanda kama shi, suna Æ´an uwansa Æ´an daba.

"Ko wani ya kashe musu?" Ta tambayi kanta.

"Yayi kisan kai, kuma a sake shi?
Aikuwa sai na ga ƙwal uwar daka" ta furta a hankali.

Ta so ta gaya wa Nasir, abun da ya faru yau, amma ta san tsaf zai ce zai zaneta, saboda kasadar da ta yi, dan haka ta bar wa ranta cewa sai ta samu wata gagarumar nasara, sannan za ta sanar da shi.
Chapter 17 · 0% Book details