Sashe 22
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsatstsare fuskar Barrister ta yi da kallo, a ranta ta ce "An zo gaɓar da nake so, hasashena ya tabbata, zan cigaba da matsa ka, har sai ka amayar da abun da ka ke ɓoye mini"
A fusace ya ce "Ba zaki tashi ba, ki ka tsare ni da ido?"
Miƙewa tayi tana zumɓura baki, ta ɗauki file ɗin ta fice.
***
Kaiwa yake ta yi yana komowa, a katafaren office ɗin sa, hannunsa riƙe da waya a kunnesa, yana jiran a ɗauka.
Har fitar da ran za a ɗauka, aka ɗaga. Cikin harshen turanci ya ce "Haba sir, kai fa nake jira kayan nan su iso, almost 2weeks, ayi ta ga kaya nan amma shiru, ni na riga na gama clearing road, a yankinmu na arewa, ka hanzarta na fara jin ƙishin-ƙishin canjin controllers na coustom, bana son a kawo waɗanda za mu yi ta fama"
Daga cikin wayar mutumin ya ce"Sai fa ka yi haƙuri, kayan ne ba a gama loda su ba, kuma nima dole sai na gama da controllers ɗinmu na nan, kuma ka daina ɗaga hankalinka, babu wani wanda ya isa a ƙasar nan, ya sha abun da ba mu muka dama ba, ranar laraba kaya za su shigo, amma sample ce allurar, ba a shigo da ita da yawa ba, sai an ga yanayin aikinta tukuna, har da tablet ma"
"To na ji, amma ka tabattar ranar larabar za su iso?"
"Ko tantama babu"
"To shikenan, godiya nake"ya katse wayar, cikin shauƙin irin ribar da zai mayar idan kayan suka tsira.
Zaune take a ƙasaitaccen ɗakin baccinta, jikinta sanye da riga da wando na nylon, masu sauƙin zafi.
Ta zauna ta nutsu, ta zubawa kayan kan table ɗin gabanta ido, tana ta saƙe-saƙe a kan ta sha ko kuma kar ta sha.
Kwalabe ne na magunguna, da ƙwayoyi haɗi da allurai.
Wata matashiyar mace ce tayi sallama, ta amsa mata, ta ƙaraso hannunta riƙe da cup ta na shan wani abu.
"Sweetheart, ya dai na ga kin saka kayan nan a gaba kina kallo?"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Tunani nake yi da zuciyata, in sha ko kar in sha"
"So you are going to quit abusing drugs?"
Ta girgiza kai ta ce "Is not that easy dear, jikina is resisting it, ba sa É—auka ta sai na sha su in a very high doses, ba na son su huda ni, a fara ganewa. Mun yi magana da honorable a kan sabuwar allurar da suka yi order daga Mexico yana ta yi mini yawo da hankali"
"Haba barrister, ke fa ta hannun daman honorable ce, ba zai yi miki yawo da hankali ba. An samu wani zazzafan malami fa"
Ta É—ago idanunta ta kalleta ta ce "Wow, are you serious?"
"Yes of course, aikinsa tested and trusted ne, amma kafin muje a kan buƙatarki, anya ba zaki duba a manyan mutanen nan, mu kai wani ba, ki yi aure yadda zai zama backup kar abubuwa su zo su taɓarɓare fa, ko ki samu wani kamar tsohon mijinki, ki aura"
Ta taɓe baki ta ce "Ba zan iya aure ba, na riga na saba da rayuwar ƴanci, ba zan yi aure in zauna ƙarƙashin wani yana juya ni yadda yake so ba. Ai tun da na yi joining organization ɗin nan kin san in da na dosa".
Ta ce "Na sani dear, amma duk da haka, religion da tradition yana da tasiri sosai da sosai a arewacin najeriya, ba na son wani ya gano wani lagonki, ayi amfani da shi wurin yaƙarki"
Ta girgiza kai ta ce "Muddin ba zan samu wanda zan gindayawa sharuÉ—a ya bi ba, zan iya zamana a haka, i have so many ways to satisfy my feelings, when i need it, ba dai duk su ake yi wa a auren ba? Kin san komai ai ke.
Ki saka mana time, mu je wurin mutumin, ba na son sunana ya ɓace, har sai na cika burina, na kammala aikin da na karɓo a wurin shugabannina, sai na tabattar da samun daidaituwar jinsi a tsakanin mutanenmu na arewa"
Badi'a ta yi dariya ta ce "Ki huta baby, ki É—an yi caji, sai ki kwanta, ko in fita da ke ne?"
"No, ba na son na yi bacci da yawa, zan sake komawa wurin matar nan, a kan case ɗin ɗan gidan honorable, naga alamar za ta yi taurin kai, idan taƙi yadda kawai mu bi hanyar da muka saba bi"
"Hmm, talaka akwai ƙi faɗi, kuɗin ne ba zata karɓa ba kenan? Sa yi biyu babu kuwa"
"Manta da su, idan ki yi waya da journalist ɗin nan, manta sunasa nake yi, ki tura masa kuɗi, a cigaba da ɓoye wanda ya yi laifin, a sanarwa da duniya na shiga case ɗin, a sassaka a social media ma, a dai yi ƙoƙarin ɗauke hankalin mutane daga kai" ta ƙarasa maganar tana tuttula ruwan maganin da ke cikin wata ƙatuwar kwalba tana lumshe ido.
Yau Abba kamar ya san Nabila so take ta lallaɓa ta fita, ya zauna a gida bai fita ko ina ba.
Tayi iya tunanin ƙaryar da zata sharara masa, ta fita amma ta kasa tunawa, dan idan ya tsitiyeta zai gane ƙarya take yi, gashi weekends ne babu aiki.
Cikin ikon Allah, aka samu tarzomar su madaki da Viper ta É—an lafa, saboda an jibge jami'an tsaro a unguwannin.
Nabila har alla-alla take yi, ranar Monday tayi ta fita aiki, daga nan ta tafi nata wuri.
Ranar Litinin tun sassafe wasu daga cikin iyaye mata, suka fara sintirin karɓar belin ƴaƴan su da aka kama, a ofishin su DSP Nasir.
Nasir yana zuwa ya tarar da su, an ce musu su jira sai ya zo.
Tsakanin iyaye da Æ´aÆ´a sai Allah, amma wannan rashin juriyar yana É—aya daga abun da yake taka rawa, wurin sake sangarta yaran.
Bayan sun gaisa da su, ya ce "Da farko ina mai baku haƙuri, domin kuwa ba za mu bayar da belin yaran nan ba, sai mun kai su gaban alƙali tukuna. Yaran nan ku kanku sun fi ƙarfin ku, ba kwa iya tsawatar musu, suna barazana ga zaman lafiyar al'umma, dan haka ku yi haƙuri a wannan karon babu sabo babu ɗaga ƙafa, sai dai na yi muku alƙawarin duk wanda muka kama ba shi da laifi, zamu sake shi, masu laifi kwai zamu kai gaban hukuma".
Bai tsaya jin mai zasu ce ba, ya wuce office É—in sa.
Koke-koke wasu daga cikinsu suka fara, yayin da wasu suka din ga janyo masa jafa'i kala-kala, wai an zalunce su, an rufe musu Æ´aÆ´a.
A cikin office ɗin sa ya karya, kasancewar ya makara, bayan ya kammala, ya je in da ake tsare da yaran, tare da taimakon wasu daga cikin jami'an tsaro, ya fara tuhumar su, da ƙoƙarin zurfafa bincike akan su gaya masa in da viper yake.
Wanda aka ritsa ɗin ana tuhuma ya ce "Wallahi Yallaɓai, da ne dai kafin ya je prison, na san in da yake, har gidansu na sani, muna yi masa aiki sosai da sosai, amma tun da ya fito bamu sake ganinsa ba, su Walid da tarago ne suka san in da yake, tarago kuma madaki ya kashe shi, walid kuma wallahi shima ba a ganinsa, muna yi masa aiki amma bamu san in da yake ba".
Nasir ya ce "Ta yaya ku ke karɓar order daga wurinsa?"
"Randomly, suke zaɓar mutum ɗaya su kai masa takarda, ko aje a ajiye takardar a in da muke taruwa shikenan"
Nasir zai sake magana, wayarsa ta fara ruri, ya zura hannu a aljihunsa ya É—aukkota, ya É—aga ya saka a kunne, tare da yin sallama.
"Kana ina ne?"
"Na shiga wurin aiki sir"
"Yaran nan da ka kama, ka sake su, kowa ya tafi, kuma ka janye jami'an tsaron da ka jibge a unguwar" cikin tsananin mamaki ya tashi tsaye ya ce "Sir, yarane da suke ɓarna fa, har kisan kai aka yi a ranar, yaya zamu....
"This is an order from higher up Nasir, ka saki yaran nan, nima umarni aka bani daga sama, Aminu Viper muka ce ka kamo mana, ba yaran unguwa ba"
Ya taune lips ɗin sa na ƙasa cikin ɗacin rai ya ce "Amma sir, muna kan binciken wanda suka yi kisan kan ne".
"Ka sake su nace, is an order"
Nasir ya ce "Ok sir, as you wish"ya kashe wayarsa, jikinsa yana wata irin tsuma, ya tuna yadda a garin kamo yaran, sai da suka kusa kashe shi, a artabun da suka yi, ga kisan kai, ga miyagun makamai da suka kama yaran da su, amma an bashi order ya sake su, anya kuwa ana son kawo gyara da matsalar tsaro a ƙasar nan!?
Ƙarfe a wuta paid book ne, few pages zan bayar free, masu buƙata za su iya contacting ɗi na, su fara subscribing, miƙaƙƙiyar tafiya ce, mai cike da sarƙaƙiya da ban al'ajabi.
Ayshercool
08081012143
[7/24, 1:44 PM] null: *ƘARFE A WUTA*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Ku yi following channel É—in nan, domin samun littatafan autar manya.
https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h
Masu son ƙarfe a wuta daga farko, ku bi link ɗin nan ku yi joining channel ɗin
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
10
Gaba É—aya zuciyarsa ta cunkushe, ya rasa me ma Yakamata yayi.
Ya daÉ—e a zaune kafin ya tashi ya fita reception É—in.
Sai dai yana zuwa ya tarar da wani mutum a tsaye, baƙi ƙirin da shi, ya ɗaura ɗan kwali a kansa, ga wasu wulaƙantattun kaya a jikinsa kamar mahaukaci, idanuwansa jawur kamar an rina masa.
Nasir ya ce "Lafiya kuwa? Wannan fa?"
Ya dube shi ya ce "Kai ne Nasir ko?" Yayi maganar yana shagiÉ—e kafaÉ—a irin na cikakkun mashaya.
Nasir ya ce "Ya aka yi?".
"Na san ka samu saƙon ka sakar mini yarana, na zo na tafi da su ne"
Wani irin ƙululun takaici ya tokare zuciyar Nasir, yayi ajiyar zuciya ya ce "Kai ne wa?".