Sashe 38
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ambaton Allah ya ji tana yi, tare da kiran sunan mama ƙasa-ƙasa, sai dai bai ma san sunanta ba balle ya kira sunan.
A hankali ta buɗe idonta a kansa, ta yinƙura za ta tashi, amma ta kasa, duk jikinta ciwo yake yi, mararta ma wani irin ciwo take yi mata.
Ya riƙe hannunta, yana tsareta da idanunsa ya ce "Sannu"
Hawaye ya shiga ziraro mata ta gefen idonta ta ce "Me na yi maka jiya ka dake ni?"
Ya É—an yi shiru sannan ya ce "A buge nake ne ba abun da ki ka yi mini"
Cikin ƙarfin hali ta ce "Allah ya saka mini, na barka da Allah"
Ya amsa da "Tom"
Ta sake yinƙurawa za ta tashi, amma ya riƙeta ya ce "Ina zaki?"
"Salla zan yi"
Abdul ya ce "Ki na zubar da jinin zaki yi salla?"
Ta ɗan gyara kwanciyar ta, cike da takaicin yanayin da take ciki, da kuma kallon da yake yi mata, cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah ka rufe mini jikina, ka daina kallona".
Da idanunsa ya tsatstsareta, yana yi mata wani irin kallo, da ya ƙara ɓata mata rai, ta ɗaga hannunta da kyar, za ta ja zanin gado da ya rufe mata ƙafa, ta rufe jikinta da ko arzikin vest babu, amma ya riƙe hannunta, ya mayar ya ajiye wuri guda.
Ya ce "Idan ruwan nan ya goce, mutuwa zaki yi, dan kin zubar da jini sosai, kuma bana fatan ki mutu yanzu, sai kin samu ciki, kin haifa mini É—a, saboda zuciyata ta so abun da yake cikinki, ya zube".
A hankali ta cigaba da sheshsheƙar kuka, tare da fatan ta mutu ta huta da wannan bayahudiyar rayuwar da ta faɗa, duk a silar talauci da rashin galihu, ta san Allah kaɗai ya san halin da mahaifiyar ta take ciki, na tashin hankalin rashin sanin in da take.
Idonsa ya sauka a kan taruwar jinin da ya kwanta a gefen wuyanta, ya ƙara tabattar da ba ƙaramin duka ya yi mata ba.
A karo na farko da ya ji waji abu mai kama da tausayin wani ya shiga ransa, she look very innocent and calm.
***
Tun da Nabila ta shiga office ɗin Barrister Habib, take murmushi, shi ma murmushin ya yi mata ya ce "Ya ake ciki ke ƴar ƙwalisa"
Ta zauna tare da faɗin "Godiya nake barrister, jiya ai na je, an bani duk abun da na buƙata, na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi"
Barrister Habib ya amsa da "Amin ya rabb, ina fatan babu wani abun?"
Ta ce "Akwai, abubuwan da na gani sun É—aure mini kai, ashe kisan kai yayi"
"Ba abun mamaki bane ba, dan mutum irin wannan ya yi kisan kai ai".
Ta ce "Haka ne, amma shekara biyar ya yi ba a yi masa shari'a, kuma aka sake shi, ba tare da wani cikakken dalili ba, gaba É—aya ma akwai abubuwan da babu a cikin file É—in nasa ma"
Ya ce "Nabila cases irin wannan ai da yawa, sai fatan Allah ya kyauta"
Ta amsa da "Amin, yanzu saura alƙalin da ya yi masa shari'a, na ga an rubuta justice zakariyya, amma babu surname ɗin sa"
Barrister Habib ya yi murmushi ya ce "Shi kuma me zaki yi masa?"
"Kawai so nake na sani"
"Ai an yi masa transfer ma daga kano, bama ya ƙasar ya je ƙaro karatu"
Nabila ta ce "Kuma duk hakan yana da alaƙa da case ɗin viper?"
"A'a ba na ce ba, na dai san shi ne before, bani da tabbacin yanzu"
Ta ce "Na fahimta, na gode sosai da sosai, bari na je zan ga Sumayya, yanzu zan dawo, na yi mata alƙawarin haɗuwa da ita yau"
Ya ce "Ok, Allah ya tsare"
Ta tashi ta fita, dan kuwa yau ba ta da aiki sosai.
Sosai take son ganin sumayya, domin ta ba ta labarin halin da ake ciki, a kan binciken da take yi a kan viper.
Ta kira sumayya ta ce mata za ta shiga gidan radiyonsu, su haÉ—u a can.
Tana fitowa daga gate É—in, ta tarar da wani mai napep a tsaye, ta ce "Malam tafiya zaka yi?"
Ya ce mata "Eh"
"Yauwwa, mu je" ta kama adaidaita sahun ta shiga, tana ƙoƙarin ɗaga kiran da yake shigowa wayarta.
Sai dai ba ta kai ga hakan ba, wasu matasa suka shigo napep É—in, suka zauna a gefe da gefenta, suka rufe mata baki da ido, mai adaidaita sahun ya É—auke kan babbar hanya ya yi wani wurin.
Kusan awanni biyar, ramma ta ɗan samu ƙwarin jikinta, har ta samu ta yi wanka, sai dai ta kasa cin komai, ya sake ba ta wasu kayan a cikin nasa, duk da sun yi mata yawa, ta karɓa ta saka, ya ja hannunta zuwa falo.
Solomon ya kawo abinci, da fruit, Abdul ya kalleta ya ce "Me zaki ci a nan?"
Ta girgiza kai alamar a'a.
"Wallahi ko ki ci abinci, ko na sake yi miki tsinannnen duka a wurin nan, bana son shashanci bar ganin ina lallaɓa ki"
Cikin tsoro ta din ga cakalar abincin, tana ci tana kuka.
"Ke, meye sunanki ne ma?"
Jiki a sanyaye ta ce "Ramma"
Ya yatsine fuska ya ce "Meye wani ramma, ba rahama ba?"
"Eh rahama"ta amsa tana sunkuyar da kai.
"Meye yake yi miki ciwo yanzu?"
Ta ja majinar da take shirin zubo mata, ta goge hawayenta ta ce "Duka jikina"
"Dukan da na yi miki ne, gama mu koma É—aki, sai na yi miki tausa"
Manyan idanunta ta kafa masa, tana kallonsa.
"Ki daina kallona da wannan ƙwala-ƙwalan idanun naki, idan ba haka ba, na fita sai kin ganni".
Ta din ga wasa da doyar, ta kasa ci, ta kuma rasa abun yi.
Shiru-shiru sumayya ta din ga kiran wayar Nabila, ga wayar na shiga, amma ta ƙi ɗagawa har ranta ya fara ɓaci, gefe guda kuma ga mutanen honorable na ta kiranta su ji, yaya suka yi me Nabila ta yi da file ɗin viper da ta je nema.
Nabila ta na ji aka sauko da ita daga cikin adaidaita sahun, bayan shafe lokaci ana tafiya.
Babu bakin magana, an rufe mata baki, an É—aure mata ido, sai addu'a kawai take yi a zuciyarta.
Kwance mata idanu suka yi, ta yi tozali da Walid a gabanta yana yi mata wani irin mugun kallo, sai da hantar cikinta ta kaÉ—a.
Wurin da suke kamar jeji, babu gida gaba babu a baya, sai shi da Æ´an daban da suka kawota, ashe mai napep É—in nan ma duk set up ne.
Jikinta ya hau tsuma, sai dai ta kasa magana, amma duk da haka godewa Allah take yi, da ba wurin Viper suka kaita ba.
"Yanzu abun da ki ka yi kin kyauta kenan?" Walid ya yi maganar yana tsareta da idanunsa.
Ta sunkuyar da kai, ya daka mata tsawa ya ce "Tambayar ki nake yi, da ki ka saka a ka kama liti shi laifin me yayi miki, ina har in da Vipern yake kin sani, kuma kin je, meya hana ki tura kai tsaye a kama shi?
Yanzu gashi ina ta fama da shi, ya ce lallai zai miƙa kansa ga hukuma, saboda a saki liti, ba zai sake bari wani ya wahala saboda laifinsa ba"
Cikin dakiya Nabila ta ce "Dama haka ne ya dace da shi ai, mutumin da yayi kisan kai aka sake shi, kuma yake zubar da jinin mutane ai hakan yakamata yayi, ta haka ne zai wanke nauyin laifukan da ya aikata"
Walid ya ce "Haka ki ka ce? Da ya yi kisan kai wa ya kashe?"
ÆŠaya daga cikin su ya ce "Me gida, ka bari mu cire mata ta yatsu ko za ta dawo hayyacinta, ji fa maganganun da take faÉ—a a kan master".
Ya ɗaga musu hannu, ya dube ta ya ce "Shikenan, kin yi gaskiya yayi kisan kai, zan bar Al'amin ya miƙa kansa ga hukuma, amma ki sani duk hukuncin da aka yi masa, ke zaki ɗauki nauyin alhakinsa, idan ma amfani ake da ke dan cimma wata manufa a kansa, wanda suke amfanin da ke sun bar ki a duhu, amma kafin nan yakamata ki san waye Al'amin, meyafaru da shi, daga nan kuma duk abun da ki ka yanke ya rage naki!!!.
GUNDARIN LABARIN.
Tsaki yake tayi a jejjere, yana kaiwa yana komowa a matsakaicin falon, yana sauke numfashi.
Matar da ke zaune a kan kujera ta kalleshi ta ce "Wai yanzu dan Allah wannan sintirin ne zai baka mafita?"
Kamar mai jiran ƙiris ya ce "To yaya zan yi? Magana fa ake ta makomar siyasata, idan muka faɗi zaɓen nan akwai matsala, kuma malamin nan ya tabattar mini da na cika kowane sharaɗi, sai zubar da jini ranar zaɓe, kuma alamu sun nuna gwamnati da gaske take, za a tsaurara tsaro sosai da sosai a wurin zaɓen nan, kuma idan ba a cika wannan sharaɗin ba, komai fa ya rushe"
Matar ta numfasa ta ce "Duk ina yaranka marasa jin nan ne, da suke yi maka aiki?"
"Bilki duk suna hannu, kuma babu wani cikakken jan wuya da zai iya tarar aradu da kan nan, idan aka kama mutum da tayar da tarzoma a wurin, shekara sha biyar ne a gidan yari".
"To sai me, kai zaka yi, ka biya su su yi aiki kawai".
"To ai ki gane, duk sun tsorata da hukuncin ne"
Bilki tayi murmushi ta ce "Ka fito da mai dogon zamani mana, kai ka san zai iya, Al'amin ba"
Ya kalleta sannan ya nemi wuri ya zauna ya ce "Kuma fa kin kawo shawara, sai dai yaron ne hukuma ne sai da rarrash, ban taɓa ganin ɗan iska mai mulkin tsiya ba sai shi, tsaf zai ƙi yi, saboda kusan watanni shida yana tsare ban fito da shi ba"
Ta ce "Amma ai yana jin maganar ka, zai yi ba ni da wata tantama"
Ya jinjina kai ya ce "Hakan za ayi, zan saka a fito da shi"