← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 95

Sashe 6

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baƙar aƙidar ki, da ta ara ta yafa, ba zan lamunta ba. Kun sani ba na ɗaukar duk wani abu da ya shafi Nabila da sauƙi, yadda na yi mata shamaki, da wanda ya zama katangar rayuwarta, dole na tsaya tsayin daka, na kula da ita kamar yadda na yi alƙawari. Ba zan lamunci a cigaba da wulaƙanta mini ƴa ba, har ta fara iƙirarin za ta yi zaman kanta. Babu wani ɗa da ya fi Nabila a cikin gidan nan, idan ki ka sake ce mata agola, to zaki fita ki bar mini gida ki nemi wani uban".

Cikin takaici mama ta a ce "Amma da kunnenka ka ji ta faÉ—a mata haka? Ka san dai makirci irin na yarinyar nan ko?".

"Kunnena ne ya jiye mini, ko zan yi mata ƙarya ne?"

Suka yi tsur-tsur baki daya.

Ya ja guntun tsaki ya bar falon.

Yana fita sauda ta ce "Mama dan Allah sai yaushe Abba zai daina fifita yarinyar nan a kanmu, tun da aurena ya mutu bai taɓa yi mini gori ba sai yau, saboda ita?"

"Ba ke kaɗai ba, ni kaina yadda ki ka san na yi mata kucciya, duk ita ce matsalar gidan nan, amma zan kawo ƙarshen komai da kaina, ki bar ni da su".

Nabila kuwa na É—akinta, itakaÉ—ai, tana duba document É—in shari'ar da director ya saka aka ba ta, sai dai gaba É—aya ba ta da intrest a kan shari'ar, da ta gaji ma, ajiyewa ta yi ta hau waya da saurayi.

Wata matashiyar budurwa ce ta shigo É—akin ta ce "Wallahi Nabila abun da ki ke yi ba kya kyautawa"

Nabila ta É—an kalli Asiya, ta katse wayar ta ce "Da na yi me?".

"Kin saka Abba ya yi wa mama da Anty sauda kaca-kaca saboda ke, sai da Anty sauda ta yi kuka".

"To ai cewa zaki yi, Abba bai kyauta ba ni meye nawa a ciki?"

"Amma ke ki ka gaya masa ta ce miki Agola, bayan yayi musu mu ma ya iskemu a babban falo, ya yi ta yi mana faÉ—a".

Nabila ta ce "Ashsha, ai kin san ni bana kai ƙara, ko dai na ɗauki mataki, ko kuma Allah ya saka mini da gaggawa"

Asiya ta ce "Ai shikenan, kowa yayi na gari kansa".

Nabila ta ce "Allah ya yaye miki Aisya, ke ma fa matar nan idan ta tashi karta miki wulaƙanci, ba saurara miki take yi ba, daga ke har umman, amma ku yi ta bin ta kamar wata shugaba, ni dai ba mai takani ban ɗaga ƙafar na karya ba"

"A'a ai ke ki ka ce, ke ki na da ma dogara"

Nabila ta yi tsaki, tare da furta "Allah ka aurar da ni na huta da wannan kacaniyar gidan, Ya Allah dogo mai gemu" ta fita daga É—akin tana addu'a.

Bayan kwanaki takwas.

A tsaye yake ƙyam, kamar ƙofa, kasancewar in da yake a tsayen ba a iya ganinsa sosai saboda duhu, sai dai inuwarsa ta nuna dogon mutum, kakkaura.

Ya É—auki É—ankwali, ya É—aure kansa da shi, tare da naÉ—o É—ankwalin ya rufe fuskarsa sai idanunsa kawai ya bari a waje.

Ya laluba hannunsa, ya ɗaukko wata irin doguwar wuƙa, ɓangare ɗaya zarto, ɗaya kuma kaifi, ga ta da uban tsini, a ƙalla za ta yi kamu uku, ya ɗaga rigarsa ya soketa.
Ya sake É—aukar wata ya soke a jikin wandonsa.

Yanayin takun da yake kawai, ya isa ya tabbatar daƙaƙarfa ne, saboda yadda ƙasa ke amsa takun nasa.

Bayan wasu awanni, duhun dare ya ƙara yi, sahu ya ɗauke, sai haushin karnuka ko ina.

A ƙofar wani gida ya tsaya, ya din ga waige-waige, ya tabattar da babu kowa. Tamkar ɗan biri, haka ya cafke katangar gidan ya dira ciki.

Ya saka mukulli, ya buɗe wata ƙofa a cikin gidan da duk ta yi ƙura, ya buɗe ta ya kutsa kai ya shiga ciki.

Tsayawa yayi ya kunna fitilar wayarsa, yana haske ɗakin, take ya ji wani abu mai tsananin ɗaci ya fara kaiwa da komowa a ƙirjinsa, ya ji numfashin sa na barazanar barin ƙirjinsa.

Jikinsa ne ya fara rawa, ya ji tamkar hankalinsa zai gushe, ya durƙusa a wurin yana wani irin haki, cike da wani yanayi na mai shirin fita hayyaci.

Hayaniya ya fara jiyowa a waje, hakan ya saka shi miƙewa tsaye babu shiri.

Cikin sauri ya fito daga ɗakin, ya kama katanga, ya leƙa, sai dai yana leƙawa ya ga ƴan ƙato da gora da miyagun makamai, sun fara taruwa a kewayen gidan, kasancewar akwai hasken farin wata, kuma akwai hasken ƙwayayen solar hakan ya bashi damar ganin makaman da suke hannun su.

Babu tsoron komai, ya haye katangar, ya hau saman roofing gidan, ya dira ta wani ɓangaren, jin sautin dirarsa, ya sanya suka rufa masa baya, ta in da suke jiyo sautin gudunsa har da karnuka su na kururuwar a tare.

Sai dai duk da wannan ƙira da Allah ya yi masa, ta siffar ƙarfi ba ya jin nauyin jikinsa, ya din ga dukan ƙasar da dukkanin nauyin jikinsa,  ba su ankara ba, ya ɓace musu ɓat kamar walƙiya.

A bakin titi suka tsaitsaya suna haki, su na mayar da yadda aka yi.

ÆŠaya daga cikin su ya ce "Anya yaron nan, ba da layar zana yake amfani ba?"

"Ba wata layar zana, tsohon hatsabibi ne kawai, ni na yi mamaki ma da ya gudu ai, da da ne fa, wallahi sai ya illata ku kan ya gudun. Ai kamar yadda na gaya muku ne, da na ji alamun ya zo, zan kira ku a waya na sanar muku, ai ba zan sake sukuni ba sai ya je hannu, na za ta ma zaku kira Æ´an sanda ne"

Ɗaya daga cikin jami'an sintirin, ya ce "Ko zamu kira ƴan sanda, mu yakamata mu fara huɓɓasa mu kama shi, sai mu miƙa musu shi, wannan gudun nasa yaushe muka kira ƴan sanda ma"

"Amma duk da haka, yakamata su san yana zuwa ai"

Shugaban su ya ce"Muddin suka sani, canza taku zai yi, ba zai sake zuwa ba".

Malam lawan da gidan sa ne a jikin gidan da yake zuwa ya ce "In ji wa? Ba zai taɓa iya daina zuwa gidan nan ba, yadda ka san ya binne asiri a ciki, kodayeke sai ta yiwu ma asirin ya binne, wannan hatsabibancin nasa akwai lamarin sihiri a ciki, amma zan cigaba da saka ido, da ya zo zan kuma kiranku"

"To shikenan malam lawan mun gode, yanzu ka koma gida, bari mu koma bakin aiki, ko kuma a raka ka ne?"

"Ahha haba, kamar ba namiji ba, ba wani abu bari na koma, ai ya riga ya gudu" Suka yi sallama ya nufi layinsu.

Sai dai yana daf da ƙarasawa gidansa, kawai ya ji an yi ball da shi, kasancewar sa ɗan ƙaramin mutum, sai jin sa yayi, ya yi sama ya dawo ƙasa kamar wani karmami. Ya tashi a gigice yana zaton ko gamo yayi da aljani, ya hau waige-waige.

Haske shi ya yi da fitila, sannan ya ce "Kwana da yawa malam lawan, tsohon butulu, da na ƙyale ka ban yi maka komai ba, shi ne ka cigaba da yi mini bita da ƙulli?"

Cikin kwakwazo, da tsananin razani ya ce "Na tuba, na bi Allah na kuma bi ka, dan Allah" kan ya ƙarasa, ya karya shi ɓaras, ta hanyar saka ƙafa, ya yi masa wani irin duka a ƙafarsa ɗaya.

Malam lawan ya a kurma ihu, cikin tsananin zafin nama, ya cire hular kan malam lawan,, ya tura masa a baki, sannan ya ciro wuƙar ƙugunsa ya yanke shi a damtsensa, aikuwa jini ya ɓalle.

Ya durƙusa a gaban sa ya ce "Yanzu ai ka ji daɗin bayar da rahoton zuwana, ragon maza kawai" ya tashi tsaye ya ja da baya ya ɓace a cikin duhu, ya bar shi a mawuyacin hali, ga karaya ga yanka, gashi kuma ya toshe masa baki.

Ko da ya koma gidansa da yake zaune, ciro wuƙar da ya yanki malam lawan yayi, yayi jifa da ita. Ya tsaya yana haki, abun da ya yi alƙawarin dainawa, yau ya yi, ya zubarwa da wani jini.

Ya dafe kansa yana huci cikin tsananin damuwa.

**
Yau sumayya ba ta haÉ—a tafiya da Nabila ba, dan da wuri sosai ta fita, za ta shiga asibitin murtala ta duba wata yayar babansu da aka kwantar a emergency, za ta kai musu abinci.

Su na tafe da mai adaidaita sahu, ta hango mutane na ta shiga su na fita a wani layi, duk da lokacin gari bai gama hasken da za ace, mutane suna wannan tururuwar ba.

Da sauri ta tsayar da mai baburin, ta biya shi kuɗinsa, ta  sauka, ta nufi layin da mutane ke shiga su na fita.

Wurin duk babu mata, sai maza, amma hakan bai hanata kutsawa da son gano abun da yake faruwa ba.

Tsayawa ta yi ta tambayi wani magidanci, abun da yake faruwa. Ya sanar da ita, gawar wani yaro aka tsinta, a bayan maƙabartar unguwar, an yanke masa al'aura da wasu sassa na jikinsa.

Jikinta na tsuma ta cigaba da kutsawa tana faÉ—in "Ku matsa, ni Æ´ar jarida ce" tare da nuna musu id card É—in ta.

Ta É—aÉ—É—auki hotunan yaron, sannan ta tsaya tattaunawa da mutanen da suka fara zuwa su ka tarar da abun.

Sai kiranta ake yi a waya, ana jiran ta kai abinci, amma sai da rana ta ɗaga sosai, aka gama komai ƴan sanda suka zo, sannan ta yi shirin tafiya, shi ma sai da ta karɓi lambar wayar wani ɗan sanda, da zimmar zai din ga ba ta update na sakamakon binciken da za su yi, a kan gawar.

Ko da ta je asibiti ta sha faÉ—a,na rashin kai musu abinci da wuri, ko a jikinta, saboda ta samu rahoto, dan haka tana ajiye musu abincin, ta yi waje.

Sai dai ba ta fito daga emergency ba, ta din ga jin ihun wani babban mutum, kamar mara gaskiya, haka ta koma tana leƙawa ta ga abun da yake faruwa.

Magidanci ne, ake yi masa É—inkin wani uban yanka a damtsensa, jikinsa yayi kaca-kaca da jini, duk da ana ta yi masa allaurar kashe zafi, amma sai ihu yake yi.
Chapter 6 · 0% Book details