← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 95

Sashe 65

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayar da idonsa yayi kan Anty Zakiyya, ko ƙiftawa ba ya yi, babu shiri ta juya da sauri ta shige ɗaki.

Jauhar ta fito, da jakarta da ledojinta, ya danƙi hannunta, suka yi waje.

Suna fita Surayya ta ce "Bala'i dama wannan ne mai dogon zamanin? Jaraba jauhara na cikin bala'i".

Hafsa ta ce "Ni kuma abun da na gani daban, kut wallahi na É—auka zan ga wani gardin mummuna, ji mutum hanci har baka, kai amma yayi kalar tsoro da yawa, haka yake yi mata wannan tijara"

Mama ta ce "Dalla ku yi mana shiru, kalli asarar da ya yi mana, abincin ranarmu ya mayar da mu baya" mama tayi maganar a ƙule.

"To mama aikin gama ai ya riga ya gama, ni wallahi na zata dukanta zai yi ma. Anty har an gudu ɗaki, bayan ita ta bayar da saƙon da aka gaya masa"

Daga ɗaki ta ce "Haka kurum in tsaya ya kasheni a banza, kin ga wani huci da yake yi kamar kumurci, gashi sai kallona yake yi, ya ƙara girma fiye da yadda na san shi".

Jauhar kuwa suna fita, walid ya rufa musu baya, Viper ya din ga jan ta, gashi saurinsa ya ninka nata, kamar ta hantsila, Alla-Alla yake yi su ƙarasa titi ya saka ta a abun hawa, sai dai suka yi karo da madaki da yaransa.

Wata irin muguwar dariya madaki yayi, wadda ta ƙara fito da ainihin muninsa, baƙi ne wuluk kuma gabjeje, yana da jajayen idanuwa, wanda yake rambaɗa musu farin kwalli, ga wani ƙaton sara a fuskarsa a kaikaice da ya raba fuskar in to two equal parts.

Sai ta ga Al'amin É—in ta nutsatstse ne mai kyan gani, a kan madaki, ta san gidansu ta san sunansa a unguwar su, amma ba ta sanshi a fuska ba.

Jikinta ya hau tsuma, Al'amin ya sakata a bayansa, ya tsaya yana fuskantar madaki, Walid ya tsaya a gefensa.

"Tun da aka gaya mini matarka ta shigo unguwar nan, na ce bari in auna adadin son da ka ke yi mata. Ka san bikin ma bana nan aka yi, labari na samu ban haɗu da kai na yi maka Allah ya sanya alkhairi ba. Ƙarfin halinka ya kai, tun da ka iya ratso cikin unguwarmu ka auri 'ya. Shiyasa na so ka zama ɗaya daga yarana tun a wancan lokacin amma ka ƙi.

Ya leƙa ya kalli fuskar jauhar ya ce "Ashe 'yar gidan Alhaji faruku ce, rabona da ita tun tana 'yar mitsitsiya, ashe haka ta girma ta ƙara kyau, ka bani kunya ma, wannan ai ba ta wani gama nuna ba, wannan ai ka yi mata girma, kodayeke ba a nan take ba an danne bodari ta ka, bakinta mai kyau ɗan ƙarami zai yi daɗin sha, anya wannan ba....

Wani wawan mari Al'amin ya ɗauke madaki da shi yana huci, Walid ya riƙe shi ya ce "Viper ka san me ka yi kuwa?"

Al'amin ya hankaɗe shi, ya kalli madaki cikin ido ya ce "Ka daɗe da kashe Al'amin ɗin da ka raina, ka mayar abun nishaɗinka, Kar ka sake ka shiga shingena, duk wala-walar da zaka yi, kar ka ƙetare iyaka".

Yaran madaki suka yinƙuro, Madaki ya ɗaga musu hannu, ya ciro wata muguwar wuƙa a jikinsa, ya ce "Bari in nu na wa duniya kai rago ne, a gaban matar taka, da ka yi dan ka burgeta"

Wani irin ihu jauhar ta ƙwala, ta rirriƙe Al'amin tana kuka ta ce "Dan Allah kar ka caka masa, zaka kashe shi idan ka caka masa, dan Allah ka yi haƙuri kar ka kashe shi".

Viper ya ce "Kafin ɗayanmu ya bar duniya, za a ga waye ragon, ƙazamin kare kawai"

Ya sake danƙar hannun jauhar, ya keta ta tsakanin yaran madaki yayi gaba, walid kuma ya tsaya a kan hanyar yana kallonsu, dan kar wani ya bi bayansu ya illata su.
Madaki ya bi bayansu da kallo, ya din ga kallon wuƙar hannunsa yana murmushi, lallai yayi sake ɗan zaki ya girma, ya fara zama barazana a gare shi.
Babban abun da ya ƙular da Al'amin, bai wuce yadda jauhar take ta rusa masa uban kuka ba a cikin a daidaita sahu, bayan koma menene ita ya janyo, kamar ya cillata kan titi ya huce, yana zaman zamansa an ƙaƙaba masa ita, yanzu dole duk in da zai yi sai yana tunanin kar a cutar da ita.

Bai kulata ba har suka je gida,ga wani irin ciwo da kansa yake yi, ga zazzaɓi tun a hanya ya rufe shi.

Suna zuwa gida, ya wuce É—akinsa ya bar ta.

Bin bayansa ta yi, cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Master ka yi haƙuri, ban san haka za ta faru ba, nayi niyyar gaya maka dama idan na dawo, dan Allah ka yi haƙuri"

Banza yayi mata, ya rufe idanunsa, saboda yadda sanyi yake ratsa shi, ga wani abu mai ɗaci da ya tsaya masa, ya ƙi wucewa, saboda yadda abubuwan da suka wakana a rayuwar sa, suke dawo masa cikin kansa a yanzu. Idan ya tuna abun da madaki ya faɗa a kanta, sai ya ji kamar ya kurma ihu, ya gama cutarsa, ko shi jai tsaya ya ƙare mata kallo, ya ga bakin nata ba sai shi.

A marairaice ta ce "Master, Yaya Al'amin dan Allah ka yi mini magana, ka yi haƙuri ka yafe mini dan Allah, na san koma menene ni ce sila".

"Get out from sight, ki tashi ki fita kafin ni na sassaraki a wurin nan" a tsorace ta tashi ta fita, tana waiwayen sa.

Tana fita ya riƙe kansa, saboda yadda ya yi masa nauyi.

Anty Zakiyya kuwa, Rahila ta kira a waya, bayan sun gaisa ta ce 'Ƙawata yau na ga tsiya da wasali"

"Bani na sha meyafaru?"

"Yau É—anki ya zo gidan nan ai"

"Wa kenan"

"Sirikinmu mana, wai ashe yaran madaki É—an dabar nan na unguwarmu sun ce idan ta sake zuwa unguwar nan, sai sun sassarata, ta zo gidan nan bai sani ba, a sukwane ya taho, yau mun ga bala'i, kin ga tijarar da ya yi ya ja hannunta suka tafi?"

Rahila ta ce "Zai aikata fiye da haka ma, in dai Aminu ne É—an banzan bawa kenan ake gaya miki"

"Taɓ amma anya ba son yarinyar nan yake yi ba? Kin ga a yadda ya zo kuwa?".

"To ke ina ruwanki, dama dai ba burinki ita wannan ta bar miki gida ba, shi ya sani ba mace ba ce ba? Luf zai yi ai, ni fa tun da aka yi auren ba mu sa shi a idonmu ba, na ce can ya ƙarata"

Suka kwashe da dariya, Zakiyya ta ce "Taɓ amma ƙato ne, sai ka ce ɗan dambe, kuma wallahi ba wani abun gyara da muka yi mata, yau ne ma da ta zo maƙwabciyarmu ta bata, amma haka nan muka kaita"

"Oho musu, in dai buƙata ta biya, ba shikenan ba, su ƙarata"

Suka kwashe da dariya gaba É—aya.

Jauhar ta kasa zaune ta kasa tsaye, master ya ɗau fushi da ita, gashi ya ƙi fitowa, kuma ya korota daga ɗakinsa.

Da canjin hannunta, ta haɗa ta sayo fulawa, ta kwaɓa alkubus, da wata irin miya ya 'yan dabaru, sai dai har ta yi ta gama bai fito ba.

Sai ta kasa ci, ta sake lallaɓawa ta leƙa ɗakinsa, ta ga yana banɗaki, ta cigaba da tsayuwa ya fito, ta tsaya tana sallama a bakin ƙofa.

"Idan ki ka bari na zo na sameki a wurin nan, sai na ɓata miki rai"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri master, na tuba ba zan sake ba"
Kwanciya ya sake yi, ya juyawa ƙofar baya.
"To in kawo maka abinci?"
Kamar ya ce eh, amma yayi mata shiru.

Abun da ya ɗaure mata kai, bai wuce har dare kwanciya yake yi ba, yaƙi fitowa, cikin tsananin fargaba ta shiga da kwanukan abinci ta ajiye masa.

Ƙamshin miyar da ya cika masa hanci, ya sanya ya buɗe idonsa.

Gwiwoyinta ta saka a ƙasa ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ni ko wani hukuncin ka yi mini dan Allah ka daina yin fushi da ni, bana son na ga na yi laifi dan Allah" hawayenta ne yake ɗiga a kan katifarsa, ya gyara kwanciyar sa ya juya mata baya.

Ya tsani kuka, ba ta san ƙara ƙular da shi take yi ba.

Tashi ta yi ta sake zagayawa kamar mayya, tana yi masa magiya.

Ya buɗe jajayen idanunsa yana kallonta, sai dai yaƙi magana.

Yarrrr haka ta ji tsigar jikinta tana tashi, ba ta san kallon ma yake yi mata ba.

"Ka yi magana Please, ka ce ka haƙura" tayi maganar tana jan majina.

Ƙafarsa ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana kaɗawa, saboda ciwon da kansa yake yi, amma a zahiri abun da yake yin, kamar yana yi ne da gayya da nuna mata iko da izza irin ta ɗa namiji.

"Kin cika mini kunne" yayi maganar a hankali, duk da buÉ—É—aÉ—iyar murya ce da shi irin ta jaruman maza.

"To ka ce ka haƙura mana" tayi maganar cikin shagwaɓar da ba ta san ta yi ba.

"Kai mini ruwa zan yi wanka" cikin sauri ta ce "To"

Tunani yake yi daban-daban a ransa, ya ma rasa wanne zai yi, yana shiga wankan, ta sake gyara shimfiɗar katifarsa, ya yi wanka ya fito yanzu ma jikinsa babu riga, yana ƙoƙarin mayar da kayan da ya cire, da sauri ta ce "Ai kana da wankakkun kaya, na wanke maka ka saka wannan" ta yi maganar tana miƙo masa kayan da ta ciro masa.

"Ɓace zan canza kaya" ta fita da sauri,mintuna goma da ta dawo, tuni ya kusa rabin abincinsa.

Garin ta miƙa hannu ta ɗauki jug ta zuba masa ruwa, hannunta ya taɓa ƙafarsa ta ji zafi sosai, ta kalleshi ta sake kai hannunta ƙafarsa. "Master zazzaɓi ka ke yi?"

Lomarsa ya cigaba da yi, cikin tsoro ta sake kai bayan hannunta ta taɓa hannunsa.

"Na shiga uku ba ka da lafiya ai, duk ni na janyo ko?"

Ya karɓi jug ɗin hannunta, ya cire murfin, ya kafa kai ya sha fiye da rabin ruwan, sai ka ce tsohon raƙumi.

Ya gama ya jingina da jikin bango ya sake lumshe ido.
Chapter 65 · 0% Book details