Sashe 40
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A'a ni fa a ƙoshe nake, ka bari na lashe tukunya, ka san ina son romon indomie"
Yayi murmushi ya ce "Ke ce romon ai"
Ya zuba mata a tukunyar, ya datsar mata ƙwan, jikinta har tsuma yake yi, tana hannu baka hannu ƙwarya, ba tare da ta san tana hakan ba.
Yadda ya lura tana ta suɗar kwanon, ya san babu lallai ta ci abinci yau, dan haka ya sake tura mata ta gabansa ya ce "Ungo na ƙoshi"
Ta É—an yi saroro ta ce "Yaya Saifu ba daÉ—i ne?"
"Ina fa, ke kin san duk duniya, babu wanda ya kai ki iya dahuwar indomie, ƙoshi nayi kawai, ki hanzarta ki gama ki je ki kwanta, dare yayi"
Ta karɓa ta yi masa godiya.
Sai dai tana gama ci, wani matashin da zai girmewa saifu ya fito, ya zube mata kayansa na ƙwallon ƙafa, har da takalmi, sai tsamin rana da warin hammata suke yi, ya ce ta wanke masa kafin ta kwanta. Kamar saifu yayi magana, amma yayi shiru ya fasa.
Ƙarshe ba ta kwanta ba, sai ɗaya da rabi na dare, shi ma ko da ta tuna, kwanaki kaɗan suka rage mata jinin al'ada ya zo mata, gashi ba ta da audugar tare jini, ga kuma kuɗin makarantar islamiyyarta, babu shiri ta fasa kwanciyar, ta ɗaukko kwanon da take zuba dutsen da take shiri da shi, ana biyanta, tana tara ƴan kuɗi, duk da shirin ba wata riba ce da shi ba, amma yana taimaka mata sosai.
Tamkar mai shirin hawan aljanu, haka ta haƙiƙance, tana zuba masa bala'i, "Wallahi ba zai yiwu ba, dole ka zaɓa ko ni ko ɗan ka, idan har zai cigaba da shigowa gidan nan, to wallahi ni zan bar shi, dan ba zai illatani da yarana a banza ba, ko ya lalata mini ƴaƴa ba.
Sanin kanka ɓaras ya karya mini ɗa, Allah ne yayi da sauran rabon Musa ya taka ƙafarsa a duniya, ga ni da yara mata, ya din ga shiga yana fita, ba ma wannan ba, yadda ya yi ƙaurin sunan nan a duniya, tsaf zai hana mini ƴaƴa auruwa, to wa ma zai zo ƙofar gidan nan zance, yana tsoron a raba shi da rayuwarsa, ba zai yiwu ba gaskiya".
Ya numfasa ya ce "Rahila, da wani idon ki ke so duniya ta kalle ni? Idan na kore shi na hana shi zuwa gidan nan, yana da in da ya fi nan ne?"
"Idan ba shi da shi ka nema masa, ni fa ba zan cigaba da rayuwa da tantirin ɗan daba a cikin gida ba, ya sabauta mini rayuwata da ƴaƴana ba, Allah ya mayar da shi kurku ya dauwwama a can kowa ya huta, ina dalili za a hana ni rawar gaban hantsi, mutum ba tarbiyya duk na sangarta shi, an mutu an bar mutane da masifa da bala'i a bayan ƙasa, me ake da ɗa irin wanda zahra'au ta mutu ta bari, Aminu ai cikon asara ne a cikin al'umma, wallahi ta yi asarar haihuwa".
Yana tsaye a bakin ƙofar shiga falon, yadda ta ɗaga murya, ya sanya ya ji komai, zuciyarsa ta din ga wani irin hanƙoro, wani abu mai masifar ɗaci ya din ga taso masa.
Ya saka hannu ya danƙe handle ɗin ƙofar iya ƙarfin sa, saboda muddin ya shiga cikin falon, yadda yake jin sa a saman nan, ya cake da wiwi, babu abun da zai hana shi ɗaga matar nan, ya buga da ƙasa.
Ya kasa gaba ya kasa baya, shi bai shiga ba, kuma bai bar wurin ba, kunnuwansa suka cigbaa da karɓar miyagun maganganun da take faɗa a kansa.
Ƙarar da handle ɗin ya bayar ne, ya sanya su juyowa su kalli bakin ƙofar, ɓaras ya karya handle ɗin nan, duk ƙwarin sa, ya fara yi mata wani irin kallo, da ta kasa gane ma'anarsa.
Ayshercool
08081012143
🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*
Da sauri ta ɓuya a bayan maigidan, hantar cikinta na wani irin kaɗawa.
Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Haihuwata ce asara ko? Ni?"
Cikin tsawa ya ce "Kai aminu, ya isheka haka, kar ka kuskura ka aikata wani rashin mutunci, ko ka ce zaka yi mata wani abu, koma menene ba kai ka janyo ba, ka nustu ka zama mutumin kirki mana, kalli yadda ka yi shuhura a shashanci da harkar sara suka, ni kaina ban so fitowarka ba wallahi, yanzu zaka zo ka cigaba da ɗaga mini hankali, ka hana ni zaman lafiya da iyalina, dan haka ka bar mini gida, kar ka sake shigo mini gida, ba na buƙatar ka".
A hankali ya saki handle ɗin ƙofar da ya karya, ya kalli mahaifinsa ya ce "In daina zuwar maka gida, Abbu ina zani? Wurin wa zan je?"
"Ka je duk in da ya yi maka, ko wurin Æ´an iskan da suka ka ke jin maganar su sama da tawa, amma kar na sake ganinka a gidana"
Yayi murmushi mai ciwo, ya ce "Shikenan, zan tafi zuwa lokacin da huce zan dawo"
"Ba na buƙatar dawowarka, tun da ban isa da kai ba, ka je ka ƙarata"
Tuni idanunsa suka rine, zuwa launin ja jawur "Ba a canza tuwo suna, ba ni da wanda ya kai ka ko ya fika, ba ni da gidan da yafi nan, dan haka ba zan daina zuwa gidan nan ba, amma idan ka matsa zan tafi, idan kuma na tafi na bar shi kenan har abada, wani aiki aka fito da ni na yi, da yiwuwar idan na gama aikin, na koma gidan yari, komawar da ba zan sake fitowa ba, sai ku huta da ganina" ya ƙarasa maganar kafofin gashinsa na mimmiƙewa saboda ɓacin rai.
Rahila ta ce "Allah ya raka taki gona"
Juyawa ya yi ya fice, har da sassarfa, dan yanzu abun da zuciyar sa ke raya masa, ba iya ya bugata da ƙasa bane, ya raba maƙogwaronta da wuƙar ƙugunsa haka yake ji.
Tafiya kawai yake yi, yana tunani barkatai a cikin zuciyarsa, har ya ƙarasa in da yake son zuwa.
Suna ganinsa suka mimmiƙe tsaye, sun risunar da kawunansu, tamkar dai yadda ake yi wa shugabbani, a wurin shugabancinsu, ba tare da ya ce komai ba ya zauna, yayi shiru.
Liti ne yayi gyaran murya ya ce "Allah ya taimaki mai dogon zamani, menene damuwarka ne?"
Al'amin yayi shiru, dan shi bai san me zai ce ba ma.
Ba yadda ba su yi da shi ba, amma yaƙi magana.
Liti ya miƙo masa wani satchet ɗin magani, ya ce "Ga wannan ka sha rabi, yanzu za ka ji ka ɓata, ka manta komai, wasu ƴaƴan matsalarka duk za su sauka, daga hau ka saukko za ka ji komai ya goge"
Ya saka hannu ya karɓa, yana jujjuya satchet ɗin.
"Ka saka ɗaya a ƙasan harshenka, shikenan".
Ya ɓalli ɗayan ya saka a ƙasan harshen sa, ya jingina da bango, zuciyarsa na cigaba da tafasa.
Sai dai bai fi mintuna sha biyar ba, idanunsa suka fara lumshewa.
Yayi gyaran murya ya ce "Liti"
Liti ya ce "Boss".
"Chairman ya fito da ni saboda na yi masa aiki, ya ce na je yana son ganina, zai gaya mini aikin da zan yi masa, sai dai kafin na yi masa aikin zan yi nawa, ko da kuwa zan koma gidan yari ban yi nasa ba"
"Allah ya taimaki maza, wane aikin ne, a shirye muke mu yi maka ko menene"
Ya jinjina kai ya ce "Madaki zan kashe! Sai na kashe madaki!!"
Liti yayi turus ya ce "Maza, duk lokacin da muka yi yinƙurin ɗaukar fansar nan, wahala muke sha madaki fa har tsafi yake yi wallahi, ya gagaremu"
Ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa ya ce "Shhhh, ni bai gagare ni ba, zan kashe shi na koma gidan yari"
Liti ya ƙura masa ido sannan ya ce "Maza ko ƙwayar ta fara yi maka aiki ne?"
Ya buÉ—e idanunsa da suka yi ja, ya kalli liti, sannan ya mayar ya lumshe su a hankali, bacci yayi awon gaba da shi.
***
Rana ta take sosai, ƴan makaranta na ta ɓullowa da ga lungunaa da titunan unguwannin.
Sosai jauhar take sauri, ta je gidan da take yi musu shirin dutse, ta kai wanda ta yi, ta karɓo wani su bata ƴan kuɗaɗenta.
Babban layi ne sosai, ababen hawa na kaiwa suna komowa, ta tabattar babu abun hawa, wata danƙareriyar mota, ta shawo kwana a guje, ba tare da ko yin horn ba.
Gaba ɗaya ta ruɗe, ta kasa gaba ta kasa baya, kawai ta tsaya ta ɗora hannunta a kan ta, tana maimaita lahaula wala ƙuwwata illa billah.
Da ƙyar ya iya cin burki, ya fito a fusace mutumin, babban mutum ne sosai, ya kusa sa'an Baba ma, ya hau ta da faɗa "Ba kya gani ne, wannan wani irin rashin hankali ne?"
Ta kalleshi da fararen idanunta ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi na duba ban ga mota ba, ka yi haƙuri dan Allah"
Mutanen wurin da suka saddaƙar sai ya buge Jauhar, suka taso suna salallami, sai dai aka rasa me nuna masa shi ne yayi kuskure, saboda uwar shaddar da ta bi lafiyar jikinsa ta kwanta.
Sai kuma jikinsa yayi sanyi, ganin yadda take ta bashi haƙuri, duk da shi ne mara gaskiya, pressure da yake ciki da tension ne ya sanya shi hucewa a kanta.
Sai kuma ya kwantar da murya ya ce "Ki yi haƙuri, ai ba ki ji ciwo ba ko?"
Ta ce "Babu abun da ya same ni" daga haka ta tsallaka ta shiga layin da take son shiga.
Kusan dozen biyar tayi na shirin, aka bata naira ɗari da hamsin, ta kuma karɓo wani tana lissafin saura ɗari biyu da hamsin, ta samu kuɗin pad, wanda magana ake ta saura ƴan kwanaki jinin ya zo.
***
Al'amin ne zaune a kan kujera, yana wasa da zoben azurfar hannunsa, Indabo yana ta bayani, amma sam hankalinsa ba a kansa yake ba, dan bai san me ma yake faÉ—a ba.
"Aminu magana nake fa"
Ya É—aga idonsa ya kalle shi ya ce "Ina jinka"