← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 95

Sashe 8

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumayya ta risuna ta ce "Am sorry sir, ban san ku na ciki ba, Arfa mu je ki ga....

"A'a tsaya mana na ga nan ɗin, Nabila ta shiga cikin fara'a ta ce "Yallaɓai ina wuni?"

Shima cikin fara'ar ya ce "Lafiya ƙalau, ya ki ke?"

"Lafiya lau sir, ina fatan ba zan takura muku ba, ina son sanin abubuwan da ban sani ba a rayuwata, mussaman wanda ba field É—ina ba, sister ina wuni?" Tayi maganar tana kallon lawisa da ta yi bala'in haÉ—e rai.

Lawisa ta takurawa Sumayya ne, saboda tana ganin ƴar gayu ce, ga ta baƙa amma baƙinta mai kyau ga ƙwazo, tana gudun ta ƙwace mata matsayin ta, kuma ita bazawara ce, a da a wurin babu wanda ya kaita gayu a wurin, amma yanzu sumayya ta fita.
Yanzu kuma ga Nabila, ita da take da hasken fata ma sosai.

Nabila ba ta san lawisa ta amsa ko ba ta amsa ba, ta ja kujera ta zauna, tana yi wa MD tambayoyi, a kan abubuwan da suke cikin news room É—in.

Lawisa ta ƙulu,ta din ga harar Nabila, amma ko a jikinta, ita kanta sumayya sai da haushi ya kamata abun da Nabilan take yi.

Nabila ta ce "Yallaɓai, ko zaka saka mini lambarka, idan wani abu ya kama na aiki, zan iya taimakawa i am barrister Nabila Yusuf"

Ya ce "Wow, what a very young and beautiful barrister, kin zama lawyer da ƙananan shekaru, ya karɓi wayar Nabila, ya saka mata lambarsa, ta tashi ta yi musu sallama.

Sumayya kamar ta yi bindiga, su na fita ta din ga ɗurawa Nabila ashar, a kan abun da ta yi, tare da gaya mata alaƙar Lawisa da kuma MD.

Nabila ta ce "Sumayya, dan Allah kar ki ɓoye mini, idan yana da kuɗi na ci rabona, na ga zai yi son mata"

Ganin Nabila na neman mayar da ita mahaukaciya, sai ta canza maganar.

"Ke kin san menene? wai ni zan kai rahoto har kashi biyu, sakaryar matar nan ta ce ba za a saka ba, wai ba sa buƙatar irin wannan labarin, MD ya tambayi me nake yi a reception ba na aiki, wai ta ce masa ban iya aiki ba, na rasa uban da na tsare mata ta tsane ni, dama ni na samu damar da ake baki, a wurin aiki, in yi wata shida ina aiki a wurin, wai ban iya aiki ba, da yake kwanan nan ya dawo daga ƙaro karatu, tun da aka ɗaukemu ya tafi".

Maimakon Nabila ta tausaya mata, sai ta hau dariya, "Ai kawai ki fara soyyaya da MD ko ta bala'i, shi ne zaki rama".

Sai da ta ga Sumayya ta yi fushi sannan ta ce "Sorry my sumy, maganar gaskiya babu daɗi, kuma kishi take da ke kuma tana ƙoƙarin kare abun da take so, shikenan"

Idon sumayya ya tara hawaye ta ce "Sai kuma ta din ga daƙile ni a harkar aikina? Ta yi mini adalci kenan?"

Nan ta ba wa Nabila labarin abun da ya faru, daga fitowarta daga gida, zuwa yanzu.

Nabila ta ce "Na shiga uku, sumayya me ƙasarmu ke son zama ne? A zahiri an nunawa mutane ana neman mai laifi, a baɗini kuma hukuma na ɓoye shi? Duk yadda ake fama da ƴan daba da masu ƙwace a garin nan, tirƙashi ana maganin ƙaba kai yana daɗa kumbura, ke ba ki san sunan wanda ya yi laifin ba?".

Sumayya ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, bai faÉ—a ba, korata ma suka yi".

"Mu ƙarasa titi mu tari napep mu je asibitin, mu tattauna da shi mutumin, ni kin san ba na tsoron a mutu ko a yi rai. Sannan zan je na samu Yaya Nasir na yi masa maganar wannan ai abun kunya ne"

Sumayya ta girgiza kai ta ce "A'a, na tsorata da kashedin da aka yi mana, a bar zancen kawai, ban san suwaye mutanen ba".

Nabila ta ce "Wallahi sai mun je, akwai wata shashasha da ta isa ta hana ki cigaba a rayuwa, idan ma ba a saka radiyo ba, sai mu kwatsa a media ina da mabiya sosai a social media, sai ayi duk wadda za ayi.!!!"

Ayshercool
08081012142
[7/18, 2:10 PM] null: ⚔️*ƘARFE A WUTA ⚔️

*AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Page 4

"No Nabila, abun da ki ke yi is too risky, mutanen nan da gaske suke, they mean what they said, kar ki jefamu a matsala"

Nabila ta ce"Karatunki ya tashi a banza kenan sumayya? Idonki har da hawaye saboda takaici. Wasu lokutan kin fiye sokwanci sumayya, da ni ce da tuni na ci buhun ubanta".

Sumayya ta ce "Ni ce sokuwa ko? na gode amma ni ba zan iya kasadar da ki ke yi ba, na rasa aikina, but wait mu je na rakaki in da aka aike ki mana"

Nabila ta ce "Wa? Taɓ tuni na kira MD na bashi uzuri, dama barrister Habib ne ya aike ni, yadda wannan matar ta wurin aikinku take, lawashi ko lotion take, haka yake yi mini, ba ya ƙaunata"

"A'a, naki ya sha banban da nawa Nabila, shi taimakonki yake yi ai"

Nabila ta kwaɓe fuska ta ce "Ke, idan fa kin ga ina zuƙewa a aikin nan, wanda za a kare ba shi da gaskiya ne, MD zan saka ya canza mini team daga na su Barrister Habib, na Barrister Bashir nake so, wata zazzafar shari'a za su kara, shari'ar manya ce, a kan kuɗi, zuwa zan yi na sha kallo, kuma an ce akwai yiwuwar na haɗu da masoyiyyata kwanan nan"

Sunayya ta ce "Wa kenan?"

"Anty Naja'atu Bunkure mana, kin san am die hard fan of that woman, Barrister Naja'atu duniya ce, ga gayu malam, harshenta akwai turanci, kamar wadda aka haifa royal palace É—in Elizabeth"

Sumayya ta yi tsaki ta ce "Aikin banza ƴar wahala, ita ta zama abun da ta zama a harkar aiki, har tana burgeki, ke kuma kina zaune kina shashanci, wallahi ƙarshe ki koma ƴar ɗaukar jakarta"

Nabila ta ce "Kan uba, degree holder in yi dakon jaka, Kin ci mutuncina fa,

Sumayya ta girgiza kai, haryanzu Nabila shirirta da yarinta na damunta.

Ko da Nabila ta je gida, tun a tsakar falo take tambayar magajiya, ina DSP.

"Bai dawo daga aiki ba, na ji É—azu yana cewa ko za su je ringin"

Nabila ta ce "Aikuwa ya yi ya dawo, sun bayar da maza, in mun zauna ya yi ta cewa police ya fi lawyer, yau zai sha kunya idan ya ji me suka yi. Yau zazzafan debate ne tsakanina da shi, har lemo zan yi mana aji daÉ—in yin musu"

Anty ta ce "Ka ji mashirirciya, musun da za ku yi za ki haÉ—awa lemo?".

"Eh mana, É—an sanda sharri, lawyer kuma musu" tayi maganar tana dariya.

Wani mugun kallo mama ta yi mata, yaran gidan nan har take suke yi wa Nasir da discipline master, saboda yadda suke jin tsoron sa, amma tsakaninsa da Nabila sam ba haka bane ba, suna good time sosai da Nasir, kuma duk gidan bayan Abba ba ta da abokin hira ko shawara sai shi.

Nabila ta share mugun kallon da maman ke yi mata, ta tafi É—aki.

Misalin ƙarfe huɗu na yamma, Sumayya ta ga kiran lawisa, kawai ta basar ta cigaba da kallon tv, ta kira ya kai sau huɗu sannan ta ɗaga.

"Ki na ji ina kiran waya ki ka ƙi ɗagawa?"

"A silent take, bacci nayi ne".

"Ki tura mini recodings ɗin nan, su murtala ba su sami wani samo rahotanni masu muhimmanci ba, kuma na ga su Mikiya radiyo duk sun wallafa labarin yaron nan, ki turo mini mu ga wanda za a iya tacewa a saka" Sumayya ta taɓe baki ta ce "To"

Ta kashe wayar, ta ce "Allah ya ƙara, da mu muka fara sanar da labarin, kuma mu ka saka a internet, ai da ya fi, tun da ni ce ƴar jarida ta farko da ta fara zuwa wurin, amma ki ka ƙi"

Ta lalubo lambar Nabila ta kirata, ta gaya mata abun da ya faru. Nabila ta ce "Amma baki da wayo sumy, ke yanzu sai ki tura mata, saboda ba ki da zuciya?"

"To yaya zan yi mata?"

"To amma kin san ko kin tura mata, sunanta za ta faÉ—a a mai rahoton ko wanda ya karanta ba ke ba ko?"

Sumayya ta É—an yi shiru ta ce "Kuma fa haka ne"

"To tun wuri ki ce mata kin goge kawai, gobe ba za ta ƙara yi miki wulaƙanci ba".

Sunayya ta ce "Haka za ayi, na gode sosai" cikin hanzari ta kira Lawisa, ta sanar mata da cewa ba ta ga recordings É—in ba.

Aikuwa ta hau ta da bala'i, Sumayya ta danna recording tana dariya ƙasa-ƙasa da niyyar ta turawa Nabila.

Bayan sun gama wayar, ta turawa Nabila, suka din ga dariya, Nabila na ƙara bata ƙwarin gwiwar, kar ta sake ta ɗauki raini ko wulaƙanci daga wurin lawisa.

Ta kuma cigaba da lallaɓa sumayya, a kan lallai ta koma asibiti, ta sake tattaunawa da mutumin nan, ko iya sunan mai laifin ta samo.

Barrister Habib ne ya shiga office É—in MD, ya zauna suka gaisa, cikin takaici Habib ya fara magana, "Barrister, ni fa na gaji da iskanci yarinyar nan, idan a team É—i na za ta zauna, ta zauna, kuma dole ta yi biyayya ga abun da na sakata, idan wurin Bashir za ta koma, ta koma na gaji da iskanci da rashin mutuncin da take aikatawa, ba ta san aiki ba ko kaÉ—an"

MD ya ce "Calm down Habib, na sani wallahi, na san ku na haƙuri da ita, wallahi nima nauyin mahaifinta nake ji ne, abun da yayi mini a rayuwa idan na kore ta ban yi wa kaina adalci ba, shi ma yana yawan bani haƙuri a kanta, marainiya ce kuma ba ta da cikakkiyar lafiya."

"Mu ma duk marayun ne ai, waye yake iskancin da take yi? Ta zo lokacin da ta ga dama ta tafi lokacin da ta so, she's not serious at all"
Chapter 8 · 0% Book details