Sashe 73
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta je ta É—auko man, ta dawo ta zauna a bayansa, tana shafa masa a hankali.
Ta ce "Juyo" ya gyara kwanciyar sa a hankali, jikinsa wasu wuraren duk shaidar yankan wuƙa, bayan tabon duka.
Haka kurum zuciyarta ke raya mata, kai hannu kan gashin da yake kwance a ƙirjinsa, da sauri ta rintse idanunta ta kawar da wannan tunanin ta kira sunansa.
"Master"
"Mmm?" Ya amsa idonsa a rufe.
Ta ce "Ka na jina?"
"Mmm"
A ɗan shagwaɓe ta ce "To ka kalle ni, magana zamu yi fa"
Ya buÉ—e idanunsa a kanta, take ta sunkuyar da kanta, saboda wani irin nauyi da kwarjinin da idanun nasa suka yi mata, a tunaninta ta daina jin tsoron sa, ashe haryanzu da sauran rina a kaba, yayi mata shiru yana kallonta yana jiran tayi maganar, sai dai ta kasa.
Gaba É—aya sai ta diririce, ta kasa maganar sai cigaba da shafa masa man zafi a wuri É—aya a kafaÉ—arsa.
Hannunsa ya saka ya cire nata, ya karɓi man zafin ya ajiye, ya ce "Ya aka yi?"
"Dama sonake na ce dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, na yi sanadiyar shigarka wahala, duk laifina ne da ban gaya maka an kawo maka saƙo ba, ka yi haƙuri mantawa na yi ka yafe mini dan Allah"
"Idan naƙi fa" yayi maganar very serious.
Cikin damuwa ta ce "Please dan Allah ka yi haƙuri"
"Zan duba, ki je ki yi karatunki saboda exams" ta jinjina kai ta tashi, tsakar gida ta fita ta hau wanke-wanke, ta ɗaukko kayansa da ya cire, da wanda ya dawo da su daga prison, ta jiƙa su dan ta wanke.
Wasila maƙwabciyarta ce tayi sallama, kasancewar ƙofar ba a rufe take ba, jauhar ta ce "Anty wasila sannu da zuwa ga kujera"
"Yauwwa jauhara, ashe mai house ya dawo, jiya na ji halimatu ta ce ta ganku, na zata sharrinta ne ma, na zo ɗazu tun takwas da rabi, na yi ta bugu baki buɗe ba na ce bari na tafi, su jauhar ana can jikin miji an liƙe ba a tashi ba"
Jauhar kawai ta yi murmushi tana fatan Allah ya sa bai jiyo ba, tun da yana falo a kwance.
Ta ce "Jiyan ya fito, ban samu na shigo na gaya muku ba ke da maman halimatu".
"Allah sarki jauhar, kin sha wahala shikenan kuka ya ƙare, ki daina anty wasila ba ki san me nake ji ba, zuciyata kamar ciwo take, Allah dai ya bar wannan ƙauna, zuciyar ya daina ciwo ko?"
Dariya kawai jauhar take yi ta ce "Ta daina"
"To ai da kamata yayi, da ki ka san zai fito, ki yi magana ayi gyare-gyare a gyara masa turaka, ki zo na baki kayan maman nihal Anty maryam, na sanmiki kayanta ki gwada ki ji, ai ba kya yi shiru ki zauna haka ba" (Ga mai buƙatar jarraba kayan maman neehal sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 0706 677 4630).
Wasila ta din ga sakin layi, sai da jauhar ta ce "Anty wasila yana nan fa, yana falo yana jinki"
Tayi ƙasa da muryarta ta ce "Na shiga uku, kuma ki ka bar ni nake ta zuba, amma baki kyauta mini ba".
Ta durƙusa ta kwashi takalmanta cikin sanɗa, ta fice, jauhar ta din ga dariya, ta rufe ƙofarta, sai dai ita ma shiga falon ya gagareta, saboda kunyar abun da wasila ta din ga faɗa, dan ta san halinsa, sai ta sakankance, bacci yake yi, ta ga idonsa biyu.
Ta jima tana raɓe-raɓe kafin ta shiga ɗakin, baccinsa yake yi, sosai take jin tausayinsa, yanayin yadda yake miƙa ma, kawai ya tabbatar mata da zaman gidan kaso bai yi masa daɗi ba.
Tana ta dirzar kayansa, ta ji an yi wani irin fito a waje, sannan aka buga mata gate, ta saka hijjabi ta buÉ—e ta ga su walid.
Ta ce "Yaya walid, ina wuni"
"Madam dama mutumin nan ya fito baki sanar mana ba? Sai yaran da muka saka gadinki ne suka faÉ—a mana".
"Dan Allah ku yi haƙuri, na san zai neme ku, bacci yake yi ne".
Liti ya ce "Ko dai ki ka ɓoye shi ki ka hana shi fitowa"
Ta ce "A'a na isa? Ban hana shi fitowa ba, ina dai roƙon Allah ku bar mini shi, na san dole dai zai zo in da ku ke".
Walid ya sake wani irin fito, tana waiwayawa ta ga har ya zira riga ya fito.
Saroro ta yi ta tsaya tana kallon sa, ya ƙaraso, zai raɓata ya wuce.
Jiki a sanyaye ta ce "Fita zaka yi? Ban gama ganinka ba fa"
Kallonta ya yi, ya raɓa zai wuce ta ce "Dan Allah Master kar ka sha komai, ko ka je in da ake aikata laifi, dan Allah" maganar da tayi, har hawaye ya cika mata ido.
Bai kulata ba ya fita, gaba ɗaya sai ta ji garin yayi mata babu daɗi, duk da tana cikin shauƙi, da farincikin dawowarsa.
Tana jin shewar su walid, da suka ganshi, ta ja jikinta, ta koma É—aki, aikin ma ta kasa cigaba, kawai ta saka kuka, kasancewar shi ne kaÉ—ai abun da take yi, ta rage damuwarta, sai kuma tsananta ambaton Allah.
Tun wannan fitar da yayi, tun tana saka ran dawowarsa, har ta cire rai, dan har magariba ba ta kuma saka shi a idonta ba.
Tayi ta addu'a a ranta, Allah ya sa yana lafiya.
Har bayan goma na dare, ta kasa kwanciya, sai sha ɗaya da wani abu, ta ji yana rufe ƙofa, ta fito falo da sauri, ya shigo yana haska fitilar wayarsa, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi, jikinta yayi sanyi ta kasa yi masa magana, yadda yake tafiya ya tabattar mata da a buge yake, ya wuce ta ya tafi ɗakinsa.
Ta nemi wuri ta zauna a wurin, ta haɗa kai da gwiwa, ta din ga kuka ƙasa-ƙasa, ta tashi ta nufi ƙofar ɗakinsa ta leƙa, ɗakin duhu, sai dai tana hango hasken wutar jikin sigarinsa, ta juya ta koma ɗakinta, ta ji tana neman sarewa, kamar Allah ba zai karɓi addu'arta a kan sa ba, da sauri ta din ga istigfari, ta nemi wuri ta kwanta.
Da safe da ta tashi, ba ta ko nufi ƙofar ɗakinsa ba, sai da ya fito ya tarar da ita a falo, tana shirin dutse.
Cikin girmamawa ta ce "Ina kwana"
"Lafiya ƙalau" ya zauna a kan doguwar kujera, ta ce "Afuwan kar ka ga ban kawo komai ba, wallahi ba kuɗi a hannuna ban girka komai ba"
Bai yi magana ba, sai kamar bayan mintuna goma, ya É—auki wayarsa ya É—an danna ya saka a kunnensa.
"Kawo mini bredi da lipton, kayan tea dai na dubu biyu, kawo mini gida ka karɓi kuɗin". Ya ajiye wayar.
Jin wayar da ya yi ya sanya ta tashi ta É—ora tea, kasancewar da wuta ta É—ora a heater.
Tana cikin kwashe tea ɗin, ya fito ya je ya karɓo kayan shayin, ya ajiye mata a ƙofar kitchen.
Ta ce "To, Allah ya saka da alkhairi"
Ta ɗauka ta dudduba, da yabi ta ita, iya buredi da sugan ya isa, sauran kuɗin ko taliya sa saya, ta ɗauka ta soya ƙwan, ta kawo kayan karin.
ShikaÉ—ai ta haÉ—awa ta koma gefe, ta cigaba da shirinta.
"Wannan shirirtar ta fi ki karya kumallo?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba na jin yunwa ne, zan karya amma".
Gaba ɗaya ba ta walwala, duk surutun nan ma da take yi masa, yau bakinta shiru, ta kunna mp ɗin ta, ta ajiye a gefe, tana saurar radio, ana ta zancen za a tafi yajin aiki, saboda tsadar rayuwa da rashin ingantacciyar rayuwa ga ma'aikata.
"Amm Angela ki ke ko?"
Tayi murmushi ta ce "Ko 'yar madara ba" tayi maganar cikin ƙoƙarin ɓoye damuwar da take ciki.
"Koma dai wanne ne, magana ce da ni"
Ta ce "To" ta ajiye kayan abun da take yi, ta fuskance shi, amma ba ta yadda sun haÉ—a ido ba.
"Kalleni, idan ina magana na fi son ki kalleni, ki daina sunkuyar da kai"
Kallo É—aya tayi masa ta sake sunkuyar da kai ta ce "Ba zan iya ba ne, wani abu nake gani a cikin idon naka da yake bani tsoro"
"Kin kusa daina gani, wata shawara na yanke a kan zamanmu, ni wannan yawan koke-koken da ki ke yi, da wahalar da ki ke sha ba na so, jin sa nake yi kamar wani nauyi a kaina, kuma ni gaskiya ba zan iya daina wasu abubuwan ba, ina saka ki a damuwa da matsala sosai, ga rayuwar ki a cikin hatsari, duk saboda ni.
Kina takura rayuwata sosai da sosai, nima kuma ma san ina takura ki dan haka na yanke shawarar kawai na sauwwaƙe miki, ki koma gida Allah ya baki wani mijin ki yi aure, ni ba na buƙatar mace a cikin rayuwata".
Tun da ya fara maganar, ta ji kamar an jona mata shocking, zuciyarta ta din ga bugawa da wani irin sauri, ta rasa me ma za ta ce.
Sai da ya kammala tsaf, sannan cikin ƙarfin hali ta kalleshi ta kawar da mai ta ce "Wannan ne tukuicina kenan? Baka buƙatar mace a rayuwarka, nima ƙaddara ce ta kawo ni in da ka ke, na zata idan na jure na cigaba da yi wa baba biyayya, na yi biyayyar aure, komai zai wuce, zan ci riba, amma yanzu na fuskanci ni ce mara sa'ar, ko ina ba a buƙata ta, yanzu tozarta maraicina shi ne ka ga ya dace da ni, har ya sanya ka ce ba zaka yafe mini ba jiya? shikenan ka bani a rubuce na kai wa baban, na gode master, amma duniya da ba a yafiya da mu zo i yanzu ba, na san nayi maka kuskure amma na baka haƙuri, amma ka sani idan ka sake ni, ka tozarta maraici" ji tayi numfashinta ya yi wa ƙirjinta nauyi, kawai ta tashi jikinta na rawa.
Tsananin fargaba da tashin hankalin maganar da ya gaya mata, ya sanya period ya zo mata ba shiri, har jikinta ya ɓaci, dama sauran kwana ɗaya ya zo.
Har tayi maganar ta gama, ba ta kalleshi ba ko sau É—aya.