Sashe 21
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni ce barrister da na karɓi case ɗin ƴar ki, na zo mu tattauna ne, in yi magana da ita"
Nan da nan hawaye ya cika idon matar ta ce "Tana banÉ—aki, bari ta fito"
rufe bakinta ke da wuya, yarinyar tayi sallama a ɗakinta, muryarta ƙasa-ƙasa.
Mahaifiyarta ta amsa, barrister kuwa zuba mata ido ta yi, yadda yarinyar take ɗingishi, take tafiya da ƙyar, har ta zo ta zauna.
Ta kalli uwar ta ce "Kun kaita Asibiti ne?"
Ta ce "A'a, tun dai a can an kaita, maigadin gidan ne ya kaita, har aka yi mata ɗinki a goshinta, gashi nan in da aka ya ji mata rauni. Dan Allah baiwar Allah ki taimake mu, kamar yadda Allah ya taimake ki, a karɓar wa yarinyar nan hakkinta. Saura ƴan kwanaki aurenta, ya lalata mata rayuwa, idan zancen nan ya fasu a garin nan yaya zan yi?"
Ta kalli yarinyar sannan ta kalli uwar ta ce "Baiwar Allah kuma hadda halinku, na son abun duniya duk yadda hukumomi ke jan kunne a kan kai yara aikatau meyasa ba kwa ji? Meyasa zaki kaita aikatau, maimakon makaranta?, a ƙa'ida fa kema sai an hukunta ki"
Cikin rauni da damuwa ta ce "Baiwar Allah da ina da yadda zan yi yaushe zan kaita aikatau? An yi garkuwa da mahaifinta an ce mu kai kuɗin fansa, mun tattara dabbobi da gonaki mun sayar, mun bayar a kai a sako shi, sun rike ƙanin mahaifinta da ya kai kuɗin, sun haɗa su su duka sun kashe, gona ɗaya ta rage mana, ita ma wani mutum duk ya tarkata ya ƙwace, wai zai gina kamfani, an ce za a bamu diyya, gonar miliyan uku an bani dubu bakwai, abun da zan girka na basu su ci, ita da ƴan uwanta, bani da shi, nima ba cikakkiyar lafiya ce da ni ba, kuma ita ce babba, makaranta tana zuwa ajinta uku a sakandare, kuɗin da ake biya na makarantar ba ni da su, ya zan yi?" Tayi maganar kuka yana ƙwace mata.
"Shikenan ya isa haka?, Amma kuma irin haka kin yi gaggawa zuwa gidan radiyo ki faÉ—a, ai wurin jami'an tsaro yakamata ki je".
Maman ramma ta ce "Na je, dan da aka kira ni na je can birnin asibiti, da ƙyar aka karɓe ta wai ba ɗan sanda, daga can na je wurin ƴan sanda naga suna nema su cuce ni, wai ƙarya muke yi, babu yadda za ayi a ɗauki ƴa ta aiki a wannan gidan har ayi mata fyaɗe. Ba ki ga sintirin da na yi ba, na rasa abun yi shiyasa na kai wurin masu radiyo ko Allah zai saka a taimake mu"
Ta jinjina kai ta kalli yarinyar ta ce "Ramma ko?" Ta jinjina kai alamar eh.
"Gaya mini yaya aka yi abun ya faru?" Ta É—aga kai ta kalli mahaifiyarta, sai ta fashe da kuka ta kasa magana.
"Hajiya É—an bamu wuri mu yi magana" babu musu, ta tashi ta fita ta bar É—akin.
"Kin ga ki yi shiru ki kwantar da hankalinki, ki yi mini bayanin yadda abun ya faru, in ga ta ina zamu ɓullowa lamarin"
Shiru ta yi tana tuna yadda lamarin ya kasance.
"Ke!" Ya kirata cikin tsawa, bayan sun haɗa ido da ya shigo, ƙara razana ta yi, dan ba ta yi zaton wani zai shigo yanzu ba, a dai-dai wannan lokacin, da ta duƙufa tana ta aiki a falon gidan.
cikin tsuma ta kalleshi ta ce "Na'am".
"Ina masu gidan?" Yayi maganar yana ƙare mata kallo, matashiyar yarinya ce, da ba ta wuce shekara goma sha huɗu ba, irin farkon tashen balagar nan, ƙirjinta ya fara tasawa, wannan ne karo na biyu da yake ganinta a gidan. Tun a ranar farko yake jin wani abu na fuzgar shi a kanta.
Cikin rawar murya ta ce "Ai ba su dawo ba tukuna, gyaran gidan dai muke yi".
"Ke kaÉ—aice a gidan kenan?"
Cikin rashin wayo ta ce "Eh, amma zulai ta je sayo katin waya, zata dawo, tare muke aiki da ita, wai a satin nan za su dawo".
Yayi wata irin ajiyar zuciya ya ce "ÆŠaukko mini ruwa a kitchen zan sha" ta jinjina kai, ta ajiye duster hannunta, ta tafi da sauri har da gudu.
Sai dai tana shiga kitchen ɗin, ya bi bayanta, ya mayar da ƙofa ya rufe.
Turus ta tsaya tana kallonsa, jikinta yana rawa, taga ya fara tunkaro ta.
Ta ja da baya ta miƙa masa ruwan, amma ya haɗa da hannunta ya riƙe.
"Dan Allah ka sakeni, in ƙarasa aikina"
Babu tausayi ko imani, ya ce "Nawa aikin zaki fara yi tukuna, kafin nata"
Ganin akwai alamun ƙarfi a tare da ita, ba zata tsaya ba, ya sanya ya gaura mata wani lafiyayyen mari. A take hancinta ya fara zubar da jini.
Ta ƙwala ihu, ya sake buga kanta da cabinet na kitchen, goshinta ya fashe, nan ma jini ya hau zuba, ga goshi ga hanci, dan haka ta kasa magana, jikinta ya saki.
Haka ya keta mata haddi, ta hanya mai muni da rashin tausayi ya tashi ya fice ya barta.
Idonta biyu, amma ta kasa taɓuka komai, ko ɗaga hannunta ta kasa yi.
Zulai ce ta dawo ta tarar da ita cikin mummunan yanayi, a rikice ta fita ta kira É—aya daga cikin masu gadin gidan, suka É—auke ta suka kaita Asibiti.
Aka ƙi karɓar su, sai da aka kira matar gidan aka sanar mata, suka yi magana da likitoci ta waya.
Sai dai duk abun nan, ramma ba ta san ko sunansa ba, balle ta san É—an waye shi.
Kafin matar gidan ta dawo, ta aiko a bawa ramma kuɗi, a bata haƙuri su koma ƙauye, ko warkewa ba ta yi ba aka sallame su, shi ne mamanta ta ɗauke ta suka tafi gidan radiyo.
Ramma ta bawa barrister labarin komai, tana kuka mai taɓa zuciya, goshinta ga ɗinkin da aka yi mata a asibiti, ga na ƙasanta da yake addabarta da raɗaɗi.
Tayi ajiyar zuciya ta ce wa mahaifiyar ramma ta shigo.
Bayan ta shigo ta zauna, ta kalle su ta ce "Baiwar Allah, dan cuta na san an cutar da ku, amma za ki sake jefa kanki a halaka, gara ku yarda ayi masalaha.
Babu wata kotu, ko wani alƙali, da zai tsaya miki ya ƙwato muku hakkinku, saboda yaron nan ɗan gata ne gaba da baya, ubansa suke da ƙasar.
Dan haka ki yi haƙuri, a baku wani abun, ki samu ku sai abinci, a kuma kaita asibiti, idan ta warware ta koma makaranta.
A take ramma ta fashe da kuka, mahaifiyarta ta ce "Haba baiwar Allah, shikenan bawa dan talaka ne, ba zai samu adalci ba, kuɗi zasu ƙare, mutuncin ƴa ta fa? ni gaskiya so nake a karɓa mata hakkinta".
Barrister tayi shiru tana zancen zuci "Ko yaushe mutumin ƙauye ya wani san ƴancinsa? Da matar nan take zaƙewa?'
"Naira miliyan uku za a baku, kuɗi hannu, ki yi tunani zan sake dawowa. Idan kuma kun ƙi, zan cire hannuna, duk matakin da uban yaron ya ɗauka a kanku babu ruwana, ina sake gargaɗinki, babu ke babu magana da wani ɗan jarida ko makamancin haka, idan kunne ya ji jiki ya tsira" ta ciro kuɗi a jakarta, ta ajiye musu, ta tashi ta fice.
***
Kamar zai tashi sama, saboda tsananin tashin takaici da haushi, ya ce "Madaki, wace irin shiririta ce wannan ku ka yi, ta yaya zaku bari, jami'an tsaro su sake kamaku?"
Cikin muryarsa da ta riga ta fashe irin ta mashaya ya ce "Kai ka san ba laifinmu ba ne ba, wani banzan bakware aka kawo mana, kai zaka tsawatar, ka saka a sake su, dan idan babu su babu aikin nan"
"Shikenan, na ji, ka saurare ni da kyau, zuwa hankali ya riga ya kwanta, mutane sun manta da abun da ya faru watan baya, ina son a cigaba da yi mini aikina, amma a wannan karon yankin yamma da gari zaku je, yaron kar ya wuce ɗan shekaru goma zuwa sha biyar, jininsa nake buƙata, a zuba a babban dam ɗin da yake rarraba ruwa a yankina, tun daga mazaɓata, sai ku kawo mini ƴan marainan yaron, da hanjinsa. Sa'ar aikin ranar laraba ce bayan al'muru. Idan kujerata ta cigaba da tabattuwa kuma zaku mora"
Madaki ya ce "Wannan ba zai yi wahala ba, ka huta kawai, kujerar nan ko an so ko an ƙi, mai hawanta sai bayan ka mutu honorable"
"Eh, amma ba yanzu zan mutun ba ai, sai an kwana biyu tukuna, zan aiko maka kuÉ—i, ayi abun da yakamata larabar tsakiyar wata za ayi, yaranka kuma za a sake su"
"Sai da kai honorable, ka ci dubu sai ceto"
"Yauwa yayi".
Nabila kuwa sannu aka din ga yi mata a wurin aiki, ana tambayarta yaya jiki, ta din ga amsa musu da yauwwa.
Ofishin barrister Habib ta je, ta gaya masa yadda suka yi da matar, da duk abun da ta yi documenting.
Ya karɓa ya duba sannan ya kalleta ya ce "Yayi, amma me ki ke gani a kan case ɗin? Do you have interest on it?"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Wani case na jiyo, na wata yarinya da aka yi wa fyaɗe,amma ana ta ɓoye abun, amma na ji an ce su barrister Naja'atu sun shiga case ɗin, hankalina ya fi karkata a can".
"Wai ke menene haɗinki da wannan naja'atun ne? Ki kiyayi kanki da lamarin matar nan,tun da sun shiga case ɗin, ki ƙyale su, case ɗin wannan hajiyar ki tsaya ki mayar da hankali a kai ki yi"
Ta marairaice ta ce "Amma barrister menene aibun hakan, tun da class mate ɗin ka ce, ka haɗa ni da ita dan Allah, ina son irin aikace-aikacenta na jin ƙai"
Ya cire medical glass ɗin sa ya kalleta ya ce "Wai ke meyasa ki ke da taurin kai ne? Ke ma ki kafa naki harkar jin ƙan marasa gatan mana, dole sai kin zama ita, ke kin san wacece Naja'atu kuwa? Zahirinta ki ka sani, baki san baɗininta ba, go and work on this case now".