← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 95

Sashe 80

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da kuka take yi, ta fara ɗaukarsa a hoto tana murmushi ta ce "Kai zan fara yi wa hoto da wayar nan, haryanzu mamaki nake yi, wai master ne ya saya mini waya, Allah dai ya sanya mini kai a cikin aljanna ya jiƙan mama, ya ja da ran wanda suka rage mana, Allah ya goyi bayanka ya yi maka jagora a cikin lamuranka. Kai master na rasa wace addu'ar ma zan yi maka, na rasa wace irin godiya zan yi maka ma"

Har cikin ransa ya ji daÉ—in Addu'ar da take yi masa.

Ya kuma amsa da Amin.

"To mun gama ki tafi"

"To me na yi maka ka ke korata?"

Ya ce "Sigari zan sha"

Ta ɓata fuska ta ce "Da sassafen nan ba ka ci komai ba, sai ka fara da hayaƙi, haba mai babban suna, idan a baya babu wanda ya damu da lafiyarka, ni ina son ka yi lafiya, ka rayu saboda ka ajiye 'yar madara, yau dai ɗaya ayi haƙuri dan Allah a ɗaga ƙafa kar a sha da sassafen nan" kamar shashasha haka yake bin ta da kallo, ta karɓe lighter da sigarin hannunsa, har da ta gefe ta cikin kwali ta tattaresu.

"Bari na dafa mana shayi, cincin na yi jiya, amma na kasa ci saboda damuwa, ka yi brush sai ka fito ka karya, kuma zan din ga leƙowa saura na ga mutum ya sha wani abu"

Sunkuyar da kai ya yi, yana murmushi da gefen bakinsa.

Jauhar ta samu na yi, lambar baba ta kira, yana É—agawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Baba na yi waya"

Baba ya ce "Masha Allah Alhamdilillah, ina tayaki murna waliyya"

"Ka hau what's app mu yi video call"

Baba ya ce "To shikenan waliyya" Al'amin ya kalleta ya maimaita waliyya a ransa, lallai ta ci sunan da mahaifinta ya kirata da shi.

"Master, nan ne wurin video call É—in ko?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Tana kira baba ya É—aga fuskarsa ta Bayyana a screen É—in wayar.

"Baba wayata touch screen ce mai kyau".

Baba yayi dariya ya ce "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi."

"Amin, ina su yaya saifu su mama da Anty?"

"Duk suna nan lafiya, baba dan Allah kowa da kowa a turo mini lambarsa, duk zan yi musu magana ta what's app, zan din ga kiran su kuma a waya"

"To shikenan, a ina ki ka samu waya ne?"

"Master ne ya saya mini" sai kuma ta ce "Au amm maigidan ne ya sai mini"

Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar baba, ya ce "Allah ya saka masa da alkhairi, ya yi muku albarka baki É—aya"

"Amin baba" ta kaste wayar.

"Master " ya É—ago ya kalleta.

"Na gode sosai" ya É—an tsuke fuska ya ce "Kin faÉ—a kin sake, ya isa haka"

"Bar ni na yi yabon gwani ya zama dole".

Tana cikin maganar hankalinta ya kai kan labarin da ake yi a radio, wata mata ce take kuka, take roƙon gwamna, sarki da kuma jami'an tsaro su kama Aminu mai dogon zamani bisa karya mata ɗa da yayi, ya soke shi da wuƙa, an kai shi asibiti rai a hannun Allah gashi ba ta da ƙarfi, tana neman a bi wa ɗanta hakkinsa.

Cikin tsananin tashin hankali, jauhar ta kalli Al'amin, tamkar bai ji me aka faɗa a radiyon ba, sai tauna cin-cin yake yi ƙururus ƙurus ko a jikinsa an mari dutse.

Ayshercool
08081012143

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

    Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

    Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

    Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

     Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955

Jinjina kai indabo yayi, ya ce "Za ayi ba zai gagara ba, zamu dawo idan an kammala aikin, kuma wa'adin da aka É—ibar mana ya cika".

"Shikenan, nasara tana tare da kai, ba yaƙini muke da shi ba, tabbaci nake bakaz duk da akwai ƙalubale a gaba, sai da ba za su gagara ayi maganin ƙalubalen ba, amma a gaba kaɗan ɗin akwai dutse, da zaka yi karo da shi, na buga na duba, duk babu hanyar maganin dutsen nan, sai dai ayi ragas, ko ka kar dutsen ko ya kar ka"

P.A ya ce "Kuma babu yadda za ayi da dutsen? Ko wata mafitar?"

"A yanzu dai babu,

Suka tashi suka fito, suna tafe a hanya Indabo ya ce "P.A"

"Na'am honorable"

"Bokan nan kullum cikin faɗin ayyuka masu hatsarin gaske yake, ina tsoron tonuwar asirina, kar mu je in sake janyo wa kaina jagwal kana kallon yadda yarinyar nan Naja'atu ta zame mini alaƙaƙai"

"Mu bi komai a sannu sir, zamu yi nasara kuma samo yarinya ba zai gagara ba, ko cikin ƙauyukan nan aka bincika za a samu, ko kuma Naja'atu ta samo a irin mutanen da ke hulɗa da su" yayi ajiyar zuciya ya ce "Ba zan so ce a samo ta ɓangaren ta ba, amma kai na ɗora maka ragamar samowar"

"Za a bincika in sha Allah sir"

"Yayi, ina jiranka, ka ga idan lokaci ya ƙure, aikin da muka yi ya koma baya"

"Haka ne, da yardar Allah ka ci kujerar nan ka gama, mu je injiniyoyin suna can gida suna jiranka, aje ayi lissafi"

"Ok to, Aminu haryanzu ya ƙi zuwa ko?"

"Wallahi yaƙi, Allah da wani wanda zai iya yi mana irin kasadar da yake ɗauka, da mun canza shi, ɗan rainin hankali ne, ko fushi yake saboda wannan karon ba ka fito da shi ba?"

"Da fushi yake yi, ba zai ɗauki wayata ba, kuma ina son aiki da shi, ba ya jin kasada komai zafinta kuma ba shi da mgana ko kisan kai zaka yi a gaban sa, sai ya ga dama zai ɗaga kai, balle ka ji zancen a waje. Sannan babban abun shi ne, bokan nan ya ce nasarata tana tattare da wanda yake zubar mini da jini, na riƙe shi sosai, shiyas nake shanye iskancin sa".

P. A ya ce "haka ne ya na da amana, ba shi da magana sam, amma shi ya san da hakan ne?".

"Haba dai, hauka nake yi na bari ya sani, ba abun da ya sani, kawai aiki yake yi mini"

Misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma, manyan injiniyoyi ne zaune a falon indabo, suna ta lissafin ginin plazarsa.
Ga wanda zai tattauna da su a kan harkar yaƙin neman zaɓensa, suma su na jiransa.

Al'amin yana cikin falon, ana ta lissafi, shikuwa yana hakimce yana kallon tv.

Sai da aka gama lissafi, za ayi total É—in kuÉ—i, Al'amin ya kalli shugaban engeneers É—in ya ce "Kayi plusing da kuÉ—in siminti buhu shida, da tiles carton biyar"

Ya ce "Na menene?"

"Ina ruwanka, ka saka kawai".

Injiniya ya kalli Indabo, Indabo ya ce "Kuɗi ka ke buƙata ne na baka?"

"Gyaran gidana zan yi nima"

Indabo ya ce "Engeneer a rubuta, a bashi"

Al'amin ya sake cewa "Akwai yarana mutum biyar, da nake son a saka mini su a cikin aikin ginin nan, su yi su ma a sallame su"

P.A ya ce "An gama mai dogon zamani"

"Zamu zo tare da su, ni ne cikon na shida, da ni za ayi aikin a biyani"

P.A ya sake cewa "Ba ka da matsala"

Aka gama aka sallami injiniyoyi, 'yan jami'iyya suka shigo, duk yana zaune, aka gama meeting.

Duk sai da suka gama, sannan Indabo ya mayar da hankalinsa da Al'amin ya ce "Mai zamani" ya É—aga ido ya kalli indabo.

"Akwai tafiya da zan yi ƙaddamar da takarata, a yammacin garin nan, ina buƙatar tawagar ka kai da mutanen ka, saboda ban san ya zata kaya a wurin ba, 'yan sandan nan gaibu ne wasu lokutan".

"Yaushe ne?"

"Nan da kwana goma"

"Cikin azumi kenan?"

Indabo ya ce "Eh"

"Allah ya kaimu, baka da matsala"

P.A ya ce "Allah ya ƙara maka nisan zango mahadi mai dogon zamani. Ina matarka kuwa?"

Da sauri ya kalli P.A ya ce "Kamar ya ina matata, meye haÉ—inka da ita?"

"A'a babu komai, lokacin da kana tsare ne, ta zo ita da Walid, ko da yadda za ayi ka fito, lokacin honorable baya nan"
Viper ya yi shiru bai sake cewa komai ba.

Wata ƙatuwar mage ce ta shigo, da matasan 'ya'yanta, fara tas kana ganinta ka san 'yar waje ce.

Al'amin ya tashi ya nufi in da take, ya saka hannu ya É—auki guda É—aya ya ce wa P.A "Wannan mace ne ko namiji?"

"Namiji ne"

"Zan tafi da shi"

P.A ya ve "Ka san kuɗin abun nan kuwa? Ya kai dubu ɗari shida fa, wannan ƙaramin".

"Da gold aka yi shi ne?" Yayi maganar yana nuna É—an muzurun da yake ta ihu saboda ya ji matsa.

Indabo ya ce "A'a É—an Germany ne"

"Tun da ba daga aljanna ya zo ba shikenan, kai kawo leda na saka shi" yayi maganar yana kallon mai goge-goge.

"P.A ya ce wace irin leda kamar zaka É—auki masara, kwando dai za a baka.

Yayi ƙerere, aka kawo masa kwando, ya saka muzurun ƙato da shi fari, jikinsa cunkushe da gashi mai kyau.

Ya kalli Indabo ya ce "Zan tafi"

Indabo ya yi murmushi ya ce "Ga abun kuÉ—i nan ka É—auka a hannunka, ai ba sai an sallameka ba"

"Za a sallame ni ko in tafi?"

"P.A sallame shi"

P.A ya buɗe jaka, ya ɗebo kuɗi ya miƙawa Viper.

Al'amin yayi masa wani mugun kallo, indabo ya ce "Ƙara masa"

"Ya ƙara ɗebowa, ya ƙara masa"

Ya karɓa ya ce "Na karya wani yaro, yana emergency, babar yaron tayi maganar a kamani, a bi wa ɗanta hakkinsa, yana can a emergency asibitin tsakiyar gari, a kashe wutar, ko ta ƙone yiwuwar aikinka, hankakin nan suka yi ram da ni, ba zan yi aikinka ba" daga haka ya fice daga falon.
Chapter 80 · 0% Book details