← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 95

Sashe 93

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta É—aura aniyar, fara É—ora Al'amin a turbar tafiya masallaci kuma, ya din ga salla a cikin jama'a, kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, ya kwaÉ—aitar da al'ummarsa, mussaman da ciwonsa ya kame, dan ya fara saka riga ya fita ma.

Sai dai fa aikin ba na wasa bane ba, dan wasu lokutan idan ta tashe shi sallar, har a idar tana fama da shi bai tashi ba, mussman idan a cake yake, idan ta yi alwala kuwa ta zo tashinsa, ƙarshe sai ta ta alwalar ta karye, shi kuma bai yi ba.

Sai dai ta tsananta addu'a da gaya wa Allah. "Ya Allah ga bawanka Al'amin, kai ka halicce shi, ka shirya wanda suka aikata laifuka fiye da nasa, Ubangiji Allah ka shirya mini shi. Allah ka sa ya shiryu a sanadin zamana da shi, Allah kar ka saka na ƙosa ko na gaji, Allah ka dubi niyyata ta son zama da shi da yin biyayyar aure kamar yadda ka umarta, Allah dan kunfayanunka ka shiryi wannan bawa naka"

Duk in da jauhar ta ji Addu'ar biyan buƙata, irin su salatul haja, salla raka'a biyu, fatiha da sura, idan ta idar ta mayar da goshinta ƙasa, ta karanta la'ila ha illa ant subhanaka inni kunt mina zalimin. Ƙafa arba'in  da ɗaya, ba ta ɗagowa sai ta gaya wa Allah buƙatunta.
Salatul tasbih, da sauran tasbihai haka take yi, tana yi wa Allah magiya da yin tawassuli da su, ta roƙi Allah ya shirya mata mijinta, ya haɗa kan su su zauna lafiya.

Yau ta samu yayi sallar asuba ƙarfe shida saura da ƙyar, ta dawo dan ta saka shi yayi azkar, ta tarar har ya kunna sigari daga idar da sallar.

Bai yi tsammanin za ta dawo É—akin ba, kawai ya ji sallamarta ta shigo. Kamar yadda tayi tsammani, bai daina sha ba, kuma ya tsuke fuska.

Ta ƙarasa gabansa ta zauna, ta zuba masa ido.

"Kin san an hanaki shaƙar hayaƙi ko? Kin san ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba"

"Kai ma bai dace da kai ba, ina gaya maka ina son lafiyarka, su kan su masu kamfanin abar sun yi gargaÉ—i a kan haka, dan Allah ka ajiye magana zamu yi".

Bai ajiye ba, yayi mata shiru yana cigaba da fesar da hayaƙin wani wurin daban.

Tashi tayi ta zagaya, in da yake fesar da hayaƙin tana kallonsa.

"Meye haka ne wai?"

"Dan Allah ka ajiye mu yi magana"

"Ina jinki ai" wani abu mai É—aci ta haÉ—iye, kawai ta tashi ta bar masa É—akin.

Ta koma ɗakinta ta tsaya, kuka ya ƙwace mata, sai ta fara saito abubuwa, sai Al'amin ya sake burkice mata, tun da suka yi aure take yi masa addu'a, amma abun nasa sai a hankali.

"Kul jauhar, kar ki yi saɓo, ko ki yi wa Allah butulci, Allah sami'ul alim ne, idan ka roƙa baka ga tasirin abun ba, lokacin ne bai yi ba, tun da shi ya ce mu roƙa zai amsa, kuma Allah ba ya sabon aiki' wata zuciyar ta gargaɗe ta.

Istigfari ta cigaba da yi, ta nemi wuri ta zauna a tsakiyar gadonta, tana cigaba da tasbihi.

Sai da gari yayi haske sosai, ta fita tana aiki, ya fito cikin takun ƙasaita, ya nemi wuri ya kame a kan kujera.

Sai da ta kai zuciyarta, sanna ta iya ce masa "Ina kwana?"

"Lafiya ƙalau" a ranta ta ce 'Ka yi laifi, kuma ka maze kana hura mini hanci, da ni ka ke zancen'.

Ta ajiye masa karin kumallonsa, ta koma É—akinsa, ta na gyarawa, yanzu ya rage watso mata kaya daga wardrobe, sai dai ya tara mata kayan wanki, a kan katifarsa.

Tsayawa yayi a bakin ƙofa, yana kallonta.

Yayi gyaran murya ya ce "Kin ce zamu yi magana, ta menene?"

Ta kalleshi ta ce "Ka manta kawai" ta ƙarasa maganar tana kwaso kayan wankin za ta fita.

Har ta gota shi, ya janyo ta kamar wata 'yar tsana, ya tsuke fuska ya ce "Gaya mini menene?"

Ta sunkuyar da kanta, hawaye ya fara zubowa daga idonta, wani na bin wani.

"Menene kuma yanzu?"

Cikin rauni ta ce "Kai ne"

"Na yi me?"

"Kusan kullum sai ka sakani kuka mussaman kwanan nan, na ce dan Allah ka daina shan komai ka ƙi dainawa, haba master wane irin uba ka ke son ka zama idan Allah ya bamu zuriya? Ina son in ga ka daina shan komai ka daina abun da ka ke yi. Amma ƙir-ƙiri ɗazu ka ƙi daina sha".

Ya ce "Ke, wai an gaya miki daina shaye-shaye kamar daina cin tuwo ne? Ina ƙoƙartawa fa, duk kin addaba mini, ina ji ina gani, asuba ina shan kara biyar zuwa sama, amma ɗazu uku kawai na sha amma ba kya gani, kuma yaushe na ganki, balle a tara wata zuriya? Shiyasa ma ban bari sun ƙaraso ba tukuna sai na gama abun da nake yi. yayi maganar yana basarwa.

Wata irin kunya ta kama ta, jin abun da ya mayar da maganar.

"Ki daina damuwa, ina ƙoƙari sosai, ba zan iya dainawa ba, sai na cika burina, mutum ɗaya kawai zan kashe, shikenan"

Jauhar ta kalleshi ta ce "Kisa kuma? Ana ga ƙura kana ga yaƙi, idan an yi nan sai ka yi can"

Dogon harshensa ya zaro mata, yayi wani irin murmushi, sai ta ga kamar ya canza gaba ɗaya, ya dafo kafaɗarta kamar ƙawarsa ya ce "Bar wankin, zan yi ki haɗo da naki ma, idan na gama zan yi gyaran kwatar layin nan, duk an bari ta cushe da shara, me zaki dafa mana da rana?"

"Master ba ka da aiki sai zancen abinci ne?"

"To idan ban yi zancen abinci ba zancenki zan yi babyn roba"

"Saura ta katako, rana zata yi mini, ko wankin ka saɓa sai na yi mana ɗauraya"

Al'amin ya ce "A'a ki yi aikin ki zan wanke" yayi maganar yana yi mata wani irin kallo tare da murmushi.

Ita ma murmushin ta yi masa ta ce "Harshenka dogo ne, meyasa ka ke fito da harshe ne?"

Ya ce "Rantsuwa ce, kowane specie É—inmu, akwai irin ta su".

Jauhar ta yi dariya ta ce "Wai specie kamar a biology?"

"To in ce kowane É—an daba?"

Ta yi saurin girgiza kai ta ce "A'a ba na son wannan kalmar, babu daÉ—in ji"

Ba tare da ta gane ba, yayi mata wayo, ta daina fushin da take yi, dan babban burinta ya kula ta, ya sakar mata fuska.

Aka shiga satin bikin Hafsa, Anty Zakiyya ta kira Jauhar ta ce "Jauhar wai yaushe zaki zo ne? Ayyuka sun kacame, ko dai baƙin ciki ki ke yi da lamarin nan ne?"

Jauhar ta ce "Haba Anty, ba haka bane wallahi. Kin ga maigidan ne ba ya jin daÉ—i, idan na taho babu mai kula da shi".

"Kamar yaya? Au mijinki ya fi 'yar uwakki, kamar wani mijin kirki, da waye yake kula da shi idan ba shi da lafiyar?"

"A'a Anty, ai miji duk in da yake miji ne, yana buƙatar kulawa ne, ba dan....

"Dalla yi mini shiru, har wani tinƙaho ki ke yi da wannan abun? Makakken ɗan wiwi.

Ba tare da Anty ta sani ba, tuni ya karɓi wayar daga hannun jauhar, ya saka a kunnensa tana ta masifa "To ki zauna sai yadda yayi da ke, ai mutumin kirki mai kuɗi shi yake saka doka a bi, ba irin mijinki ba da har ki ke gaya mini wai ai miji miji ne ba".

"Makakken É—an wiwi yana godiya, kuma kun san da makakken ne, ku ka aura mata ni. Ni na hanata zuwa matata ba baiwa ba ce, ta zo ta yi muku bauta, ba zata zo ba, idan kun ga dama ku bar bikin kar ku yi" Jauhar tana girgiza masa kai, amma sai da ya gama maganar ya jefar da wayar.

"Master, iyayena fa, ba a haka yakamata a gaya musu ba, da ka bi a hankali, na san yadda zan gaya musu".

Al'amin ya ce "Kin san bani da tarbiyya, ban iya magana da manya ba"

"A'a ba haka nake nufi ba"

"Idan ma dai hakan ki ke nufi, idan kuma ban isa ba, ki shirya ki tafi "

Jauhar ta ce "A'a ka ma isa, ai na fasa zuwan, amma ai ka yi mini alƙawarin zaka kai ni gidanta bayan bikin ko?" Tausayinta ne ya kama shi, ba dan haka ba da gidan hafsan ma ba zai bari ta je ba, amma ya tuna ɗan uwa duk in da yake daɗi ne da shi, kuma bai kamata ya hanata zuwa wurin 'yar uwatta ba, amma kamar ko a jikinsa ya ce "Zan yi shawara"

Anty Zakiyya kuwa, sai da kayan cikinta suka yanutsa, saboda tashin hankali da ta ji muryar Al'amin a waya.

Sai dai jauhar ta sha zagi a gidan, ana cewa baƙin ciki ne da hassada ya sanya ba zata zo ba.

Yaya saifu ya ce 'm"Jauhara ba ta da irin wannan zuciyar, hankalinta na kan mijinta, wannan aure dai, in dai dan cin amana aka yi shi, ba in da zai je zai watse".

A fusace Anty ta ce wa mama "Ki ja wa É—anki kunne, kar ya sake aibata mini auren 'ya"

An kai kwanaki huÉ—u ana events kala-kala na auren Hafsa, jauhar sai kallo da ta din ga yi, tana murmushi tare da jin babu daÉ—i rashin halartar auren yayarta, ga 'yan uwa da abokan arziki duk an taru.
Ita ma ta É—ora hotunan, tana yi wa hafsan fatan alkhairi.

Aka gama biki, aka kai hafsa gidanta, wanda suke haÉ—e da uwar gidansa, kowacce part É—in ta daban.

Aka yi sayen baki aka watse, ya tara su yayi musu nasiha, bayan Uwargidan ta fita, Alhaji mu'azzam ya ce "Bari na je na ɗan ƙara rarrashinta, na san tana cikin damuwa" haushi ya kama hafsa, dan a zatonta yana zumuɗinta, ba zai saurari uwar gidan ba.

Sai dai har É—aya na dare bai dawo ba, ta kira wayarsa a kashe, tun tana saka ran ya dawo, har ta gaji, bacci yayi awon gaba da ita.

Da safe ma, ga yunwa ga gajiya, amma ba ta ganshi ba, sai sha É—aya na safe.

Ya ce "Jauhar am sorry please" ta kalle shi cikin takaici ta ce "Jauhar kuma?"
Chapter 93 · 0% Book details