← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 95

Sashe 31

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba wannan nake son ji ba" yayi maganar yana sunkuyowa daf da fuskarta.

"Wacece ita?"

Sumayya ta ce "Ƴar wani tsohon soja ce, dan Allah idan wani laifin tayi maka ka yi haƙuri, ba zata ƙara ba, idan ma dan ba ta gaisheka bane ranar, dan Allah ka yi haƙuri ba zata sake ba, ba ta da lafiya ne ranar"

Ya girgiza kai ya ce "Ko É—aya, tarko nake son na yi da ita, aiki za ta yi mini"

Jiki na tsuma Sumayya ta ce "Wane irin aiki kuma?"

Ya gyara zamansa ya ce "Kin san wani É—an daba Aminu Viper?"

"A'a ban san shi ba wallahi"

Indabo ya ce "Kina ƴar jarida, ki ce mini ba ki san shi ba, jami'an tsaro na neman sa ruwa a jallo, na yi niyyar shafe tarihinsa, aka samu wani ya yi mini zagon ƙasa, ya rusa mini komai.
Har a yanzu ana ta ƙoƙarin kama shi, kwatsam na ganku, kuma na ga tana da wani abu da zan iya yi masa tarko da shi ya zo hannuna, dan haka ƙawarki za ta yi mini aiki"

Hankali tashe ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, mutumin da yake kashe mutane, tana mace ina ita ina ɗan daba, ba jami'an tsaro suna nemansa ba? Za su kama shi dan Allah ka ƙyale mu"

Yayi wata muguwar dariya ya ce "Kin san waye indabo kuwa? Kama Aminu ya zama gawa ne kaɗai zai samar mini da nutsuwa da kwanciyar hankali, dan haka dole ƙawarki za ta yi mini aiki"

Ta buÉ—e baki za ta yi magana, wayarta ta fara ringing, ta É—auka ta duba, ta ga nabila ce take kiranta.

Ya ƙureta da idonsa ya ce "Ɗaga mana, ɗaga wayarki"

Jiki na rawa ta É—aga, ta kara a kunnenta.

"Sumayya kina ina ne?" Muryar Nabila ta fito raÉ—au a wayar.

Sumayya ta ce "Ina nan ƙalau, lafiya kuwa? Na ji kamar kina numfashi da ƙyar, ciwon ne ya tashi"

"Sumayya na kusa mutuwa yau" tayi maganar tana sauke numfashi.

A rikice sumayya ta ce "Mutuwa kuma, lafiya"

"Na haÉ—u da Viper, ya kusa kashe ni"

Ras gaban sumayya ya faɗi, indabo ya ƙura mata ido, yayi mata alama ta cigaba da wayar.

Jiki a sanyaye Sumayya ta ce "To maƙaryaciya, ni zaki jirga?"

"Wallahi ba ƙarya nake yi ba, ya na ji muryarki kamar wadda aka ritsa, kin je hirar ne? Ko wani abun ya faru ne?"

Sumayya ta ce "A'a, maƙaryaciya, mutumin da ake nema ruwa a jallo ki ka gani bai kashe ki ba?"

"Ban sani ba, tun da kin ƙaryata ni ki je ki ƙarata, ina fatan dai mutumin nan bai yi miki wani abun ba, dan mutumin nan yayi ruwan ƴan iska"

Kallonsa sumayya ta yi, sannan ta ce "Mu haÉ—u a gida"

Nabila ta ce "Ai dole mu haÉ—u yau, akwai magana, zan biya asibiti numfashin zai É—auke, ki kula da kanki dan Allah, jikina yana bani kamar akwai matsala a in da ki ke, idan da wani abu, ki sanar da ni"

"Ke normal ne, sai mun haɗu" ta kashe wayar tare da kallon honorable Indabo ta ce "Wallahi ƙarya take yi, ba wani Viper da ta haɗu da shi, yayanta ne jami'in tsaron da yake bincikensa, amma wallahi ƙarya take yi"

Cikin ko in kula, indabo yayi dariya ya ce  ce "Wato na yi zubin ƴan iska, wato a  rayuwata ni mutum ne mai sa'a, na tsinci dami a kala, yanzu ke zaki yi mini aikin ba ita ba.
Dole ki tabattar idan da gaske take ko akasin haka ki sanar mini, duk wani aiki ko bayanai da nake son samu, ke zaki nemo shi a wurinta, idan ki ka saɓa umarnina kuma, zan saka a kawar mini da ke da ita baki ɗaya!"

Sumayya gabanta ya faɗi, ta rasa abun yi, kamar ta kurma ihu, wannan wace irin ƙaddara ce, ace babban mutum kamar wannan da ake ji da shi a kujerun iko, na ƙasa da jihar nan, ya rasa wanda zai saka a gaba sai su ƴaƴan cikin sa.

Ya ce "Buɗe wayarki ki bani" tamkar shashasha, haka ta cire password ta miƙa masa, yayi ƴan danne danne a jiki.

Wani mutum ne yayi sallama, ya shigo, ya ce "Gani sir"

"Wannan wayar zaka yi wa aiki"

Ya ce "Ok sir" ya karɓi wayar yana daddanawa, sannan ya miƙowa Indabo.

Ya ce masa "You can leave"

Ya miƙa wa Sumayya wayar ya ce
"Daga yanzu za ki din ga karɓar umarnin, abun da ake buƙatar ki yi, idan ki ka saɓa umarnin, zaki yi dana sani mara amfani, dan sai na fara da wulaƙanta rayuwarki, na tozarta ki, kodayeke dama wulaƙantacciyar ce. Dan ku ƴaƴan talakawa baku da wani amfani, kuma babu wani abu da zai faru idan na salwantar da rayuwarki, da kuma ta ta".

Sumayya ta sunkuyar da kanta ƙasa, ƙirjinta na cigaba da bugawa.

"Tashi ki je sakatariyata zata sallame ki"

Sumayya ta tashi jiki babu ƙwari, ta bar ɗakin, tana tunanin wace masifar suke shirin shiga ita da Nabila. Allah wadaran bakin Nabila da bashi da saiti wasu lokutan.
Shi kuma yana babban mutum, menene alaƙarsa da wani Viper, wai shi waye ma wannan vipern, da ya fi kuɗi wahalar samu?

Tana fita sakatariyar ta miƙe tana murmushi ta ce "Har kun gama?"

Sumayya ta ce "Eh"

Ta miƙa mata envelope ta ce "Ga wannan ya ce "A baki"

Sumayya ta karɓa ta duba, kuɗi ne maƙudai a ciki, gabanta ya faɗi, tabbas idan ta karɓi kuɗin nan, ta tabatta sai ta din ga bin umarninsa, gashi ba ta san wane irin umarni za a bata ba.

Ajiye envelope É—in ta yi ta ce "Ba na so"

Ta nufi hanyar fita, tana tuna yadda ya kirata da wulaƙantacciya.

Tana gaggawa ta kai ga ƙofar da zata fitar da ita waje, mutumin da ya karɓi wayarta ɗazu, ya sha gabanta, wanda hakan ya tilasta mata tsayawa.

Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Kamar yadda honorable ya gaya miki, ke zaki yi mana aiki a zahiri, bama buƙatar ta san kina yi mana aiki, dan haka ko kin karɓi kuɗi, ko baki karɓa ba, baki da zaɓi dole sai kin yi komai kasadarsa, ko da kuwa yana nufin sanya rayuwar ƙawarki a siraɗin rasa ranta, zamu yi amfani da ita, idan kuma kin zaɓeta zaki iya rasa taki rayuwar"

Cikin matsananciyar damuwa Sumayya ta ce "Muna mata, menene alaƙarmu da ƴan daba, wannan ba aikin hukuma bane ba?"

Yayi murmushi ya ce "Shi zaki gayawa hakan ai tun a ciki, idan kuma zaki kai wa hukumar ne, ga fili ga mai doki"

Wani abu mai ɗaci, ya tokarewa sumayya a ƙirji.

Cikin ɓacin rai ta ce "Amma dai ba ku yi mana adalci ba, wannan tamkar rusa mana rayuwa ne, tayaya muna ƴaƴa mata zaku yi tarkon kama mutum mai irin wannan hatsarin da mu"

"Ai ba ke aka ce ba, ƙawarki aka ce, dan haka ina kina son lafiyarki, da mutuncinki, kiyi abun da aka umarce ki, ita ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba. Ki yi ta kanki kawai, idan har ki ka yi abun da aka buƙata, babu wata alfarma da zaki nema a ƙasar nan ki kasa samu, zaki zama ɗaya daga cikin yaran honorable, za ki yi kuɗi, zaki ɗaukaka za kuma ki shahara, ki nutsu ki yi tunani da kyau, kar ki yi wawanci, ki je aikinki ya fara daga yanzu"

Shiru ta yi tana kallonsa, har ya gama maganganun da zai yi, sai dai gaba É—aya ta rasa wani tunani ma yakamata ta yi.

Ba ga ce uffan ba, ta raɓa shi ta buɗe ƙofar ta fice.

A cikin mota, direban gidan radiyon, da wanda suka rakota suke tambayarta, yaya program É—in ya kasance?.

Cike da basarwa ta ce musu lafiya ƙalau.

Kafin su ƙarasa gidan radiyon, ta ce su sauketa, tana da uzuri, dan haka ta sauka, ta kira Nabila a waya.

Tana kira Nabila ta É—aga, "Yaya kina ina ne? Kina asibitin ko kin tafi gida?"

Nabila ta ce "Ina can, wai sai bayan 2-5hrs za su sallame ni, idan na zama stable, haryanzu numfashi yana bani wahala"

"Ok to gani nan zuwa"

"To masoyiyya Allah ya kawo ki lafiya"

Sumayya ta sauke wayar, kamar ta fashe da kuka, duk yadda take da Nabila, ace ta ha'inceta, ta saka rayuwarta a hatsari, anya amana ta ce haka kuwa?.

A haka ta ƙarasa Asibitin, ta tambayi ɗakin da Nabilan take, aka nuna mata.

Nabila na ganinta ta ce "Oyoyo sumyna"

Sumayya tayi murmushin yaƙe ta ce "Ya jikin?"

"Alhamdilillah da sauƙi"

"Baki kira kowa a gida ba, na ganki ke kaÉ—ai?"

Nabila ta ce "Rabu da ni, ba wanda na kira, ƙarshe dai walida ko baba magajiya ne za su zo, dama da DSP yana gari ne, to shi ma wai ya tafi workshop ko me oho dai, Abuja ya tafi, dama da zai zo, to sai anty, ni kuma bana son takura musu, sai dai ba yadda na iya, na gaya wa Abba, kar su ji ni shiru. Amma ya na ga kamar kin yi kuka? yaya program ɗin?"

Sumayya ta ce "Wani irin kuka ana zaune ƙalau, program lafiya ƙalau, ga recording ɗin ma ban kai ba, na ce bari na zo na  fara ganinki tukuna".

Nabila ta haɗe fuska ta ce "Ki gaya mini idan wani abun yayi miki, mu san abun yi, na gaya miki ni gaba ɗaya mutumin nan bai yi mini ba, dai-dai nake da shi idan wani abun yayi miki, in yi fito na fito da shi, sai in da ƙarfina ya ƙare."

Sumayya  ta haɗe rai ta ce "Ke da ya yi mini wani abu kya gannin a haka, ba wannan ba, maganar da ki ka gaya mini a waya, da gaske ki ke ko kuwa?"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Baki yadda ba ko?"

"Yaya za ayi na yadda, mutumin da ake ta fafatukar yaya za a kama shi, ki ce mini kin haÉ—u da shi, kawai in yadda ta yaya?"
Chapter 31 · 0% Book details