← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 95

Sashe 46

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ajiye kofin ya ce"swizalan ɗina ta sha jini sosai, wannan yankanma, ban lura yaron ya taho ba ne, yadda nake ji na anya ba wasan dambe zan fara ba walid. Idan na kwana biyu ban motsa ba, idan na tashi motsawar ba na iya riƙe kaina fa".

Walid shi ma yayi murmushi ya ce "Ai ƙarfi ya yi maka yawa aminu, ka shiga dambe abun ba zai yi mana kyau ba, daga karate zuwa dambe, amma da sauƙi jikin ai ko?"

Ya kalli ƙafar ya ce "Alhamdilillah, da sauƙi sosai, jibi za ayi aikin honorable, zai je campaign fa"

Walid ya É—an tsuke fuska ya ce "Akwai hatsari fa a aikin nan".

"Ai ban ce wani ya tayani ba, nikaÉ—ai zan yi abuna"

Walid ya girgiza kai ya ce "Sorry, ba zaka yi kai kaÉ—ai ba, amma da rauni a jikinka, ba ka warke ba".

"Ba ruwanka da ciwona, zan yi abuna a haka" walid ya girgiza kai, dan ya san ko me zai ce, bai isa ya hana Al'amin abun da yayi niyya ba.

***
Kamar zakiyya za ta tashi sama dan sauri ta ƙarasa gida, saboda rahila na bata shawarar nan, ta ji shawarar ta kama zuciyarta, kuma taga hakan ne kawai mafita, ayi ayi jauhar ta bar gidan kafin Allhaji mu'azzam ya dawo, wataƙila ita ke tsokanewa samarin kirkin ido, ba sa ganin nasu ƴaƴan sai ita.

Ko da ta koma gida a can ta tarar da mama, ita har ta dawo tuni.

Ta ja ta É—akinta, ta ce "Na samo mafita fa, amma ban sani ba ko zata yi miki?"

Cikin zaƙuwa mama "Wace mafitar ce, ina jinki"

"Me zai hana mu san duk mai yiwuwa, a aurar da jauhar, kafin Alhaji mu'azzam ya dawo, tun da dama sai ya dawo, za a tsayar da lokacin bikin".

Mama ta ce "To wa za a aurawa kafin ya dawo É—in?".

Anty ta ce "Ba zai gagara ba, sai dai shawo kan Alhaji ne aiki"

"Wane irin aiki kuma? Babu wani aiki, ni a wurina ba aiki bane ba, wa ki ke gani yakamata ta aura".

Zakiyya ta muskuta ta ce "Kin san dai muka bari ta auri wani mai danshi, daga ni har ke babu wanda za ta saurara, tun da bamu muka haifeta ba".

Mama ta ce "Na sani"

"To, kin san yaron nan da yayi suna a ƙofa, mai dogon zamani?"

"Eh ina jin sunansa sosai"

"To mariƙiyarsa, ƙawata ce tare muka yi boarding ai rahila shehu, kwana biyu bamu haɗu ba, kwatsam na je ƙofar na'isa na ga ɗan ta, ya rakani har gidan, to ita ma haka take fama da shi, ta rasa sukuni, kullum cikin tashin hankali take, neman maraba take da shi, uban ya kore shi, amma yaƙi barin gidan, kin ga idan aka aura mata shi, mun huta, a fake da fyaɗe aka yi mata, kuma dai ga tambarin da ki ka yi uwarta na maita, kawai dai ki lallaɓa maganar, kin san yadda zaki yi dai sabgar nan ta yiwu, wallahi muddin ba ta bar gidan nan ba, bana tunanin za a din ga kula namu, kuma wallahi ta auri mai kuɗi, kashinmu ya bushe, ai kin san riƙon da muka yi mata".

Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Maganarki duka gaskiya ne, kar ki damu, wannan shawarar ta yi, kuma na aminta da ita, yadda muka kwashi baƙincikin uwatta, ita ma ba zata ji daɗi ba. Duk da wasu lokutan tana bani tausayi tana da biyayya, amma idan ba haka ba, namu ba zasu auru ga irin wanda muke so ba, ki gayawa ƙawartaki azo a nema masa aurenta, zan ji da komai"

Anty ta washe baki ta ce "Alhamdilillah, magana ta ƙare".

Jauhar kuwa, ba ta san me ake  ƙulla mata ba, ita lissafinta yadda za ta mayar da jarinta, dan tun da ta farka a asibiti, da ta dawo gida sai jakarta babu kuɗin cinikinta, dan ma mai shirin dutse ta yafe mata.

Duk yadda take jin nauyin yin roƙo, haka ta cire kunya, ta tambayi yaya saifu ya taimaka mata da jari, ta cigaba da sana'arta, kuma cikin ikon Allah ya bata, saboda ta hannun daman sa ce sosai da sosai, aiki duk yawansa duk wahalarsa babu ƙyuya take yi masa, gyaran ɗaki, wanki guga idan baya nan tayi girki, ta zuba ta kai masa ɗakinsa, idan ya gama ci ya bar kwanukan a ɗakin, ta kwaso ta gyara masa, dan haka baya jin ƙyashin kyautata mata sam.

***
Abbu yana daga kwance ya kammala azkar, ya juya zai yi bacci, rahila ta shigo É—akin, ta nemi wuri ta zauna a kan gadon ta ce "Tun da idonka biyu tashi mu yi magana"

Ya juyo ya ce "Ina jinki"

"Magana ce mai muhimmanci, a kan Aminu".

"Aminu dai Aminu dai, me kuma ya faru wannan karon?"

"Menene ma bai faru ba, tun da an mutu an bar mini jaraba da masifa, kullum hankalina a tashe, nan aka zo ana bayar da labari, sun je ya tayar da tarzoma, har an yanke shi a ƙafa, rashin mutuncin sa kullum ƙara gaba yake yi"

"To, na ji, maganar kenan ki sake maimaita mini abun da yake aikatawa? Wannan ai wani abu ne da na riga na sani".

"Ba shi ne ba, magana ce a kan mafita game da abun da yake yi"

Ya tashi zaune ya ce "Wace irin mafita?"

Rahila ya gyara zama ta ce "Akwai wata ƴar ƙawata, yarinyar rashin ji take yi, tana neman fanɗarewa, gashi ba ta da wani tsayayye, na ce tun da shi gashi, kuma akwai wannan kangon gidan da ya gada, a gyara masa ka nema masa aurenta, ta je su ƙarata ko zai yi hankali idan ya ajiye iyali".

Abbu ya É—an yi shiru sannan ya ce "Too, ikon Allah, banda abunki wane mai hankalin ne zai bawa Al'amin auren Æ´ar sa, yadda suanansa ya yi shuhura, a kan rashin ji".

"To ai yarinyar na ce maka fitina take yi ita ma"

"Kuma sai ayi gyaran ɓarna da ɓarna? Sai a aura masa wadda ba ta ji?"

Rahila ta ce "To shi ɗin menene? Shi na kirkin ne?ko Jin yake yi? Sai su rufawa juna asiri, amma aka ƙyale shi a haka, nan da shekara ashirin, kana ganin zai yi nutsuwar da zai kula wata mace da sunan zai aura, tsabagin wauta da kayen maye ne kawai a cikin kansa"

Abbu ya numfasa ya ce "Maganarki haka take, amma kamar yayi ƙanƙanta ma da auren shekara ashirin da bakwai, ga ba sana'a yake ba sai ɗaukar magana, da yaya zai riƙe auren? ga faɗa da faɗin rai".

"Idan ya san ya ajiye mace, dole ya nemo ya ba ta ai, tun da morarta zai din ga yi, ko kuma kana tunanin zafin rai da faÉ—in ransa zai hana shi, mu'amala da ita ne namiji ne fa".

Abbu yayi murmushi, har sai da haƙoransa suka fito, ya ce "Na san ɗa na kamar yunwar cikina, ban san meyasa mata ku ke tunanin maza, bamu da wani tunani idan ba wannan ba, Aishikenan".

Ta kwanta ta ce "Aikuwa idan haka ne, da sai an dangana da nema masa magani, idan baya wannan tunanin"

Ya kwanta a kusa da ita ya ce "Zuwa da safe in Allah ya kaimu, sai ki yi mini kwatancen gidan su yarinyar, na samu mahaifinta".

Ta ce "Yauwwa Abbu ko kai fa"

****

Jauhar ta dawo daga makarantar dare, ta tarar da Baba da baƙo a waje, ta durƙusa ta gaishe su, sannan ta shiga cikin gida.

Baba ya nuna wa Abbu ita, ya gaya masa ita ce jauhar É—in da suke maganarta, Abbu sam bai ga alamar rashin ji, a tare da jauhar ba sai ma nutsuwa da kamala, hatta muryarta mai sanyi ce, yayi mamakin da rahila ta ce masa wai ba ta ji, fanÉ—ararriya ce, sai dai bai yi magana ba, suka cigaba da magana da Baba a kan nemawa Al'amin auren jauhar, ya sanar da baban jauhar Al'amin É—in ba ya ji, sai dai bai gaya masa irin rashin jin ba, ya zata Baba ya san komai, saboda yadda rahila tayi masa bayani.

Baba ya ce "Babu damuwa, Allah ya tabbatar musu da alkhairi, na san iyayen nata ba za su zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba".

Suka taɓa hira, ya tambayi Baba ko akwai wani shiri da za su yi? Baba ya ce idan sun shirya kawai su kawo abun da suke da shi, ayi komai a wuce wurin.

Suka gama magana, Abbu ya tafi gida yana farinciki, tare da fatan Allah ya sa ƙarshen matsalar Al'amin ce ta zo, Shi ma Baba ya shiga gida, can ƙasan zuciyarsa yana ta kokwanto da wasi-wasi, amma ya kasa ayyana hakan a zahiri.Sam  bai iya tambayar menene rashin jin da  Aminu yake yi ba, bai tambayi menene sana'arsa ba da sauran su, kawai shi dai ya tsinci kansa da amincewa, bayan da mama tayi ta jaddada masa idan har Alhaji mu'azzam ya dawo, ya ji ƴan daba sun yi mata fyaɗe za ta wulaƙanta, ba zai aureta ba, shi gaba ɗaya ma ya manta da batun ya karɓi kuɗin auren Jauhar.

Abbu na komawa, Rahila ta tare shi, tana tambayarsa yadda suka yi, ya ce "Ya amince zai ba shi ita, amma ni da ya nuna mini yarinyar, ba ta yi kalar marasa ji ba".

"Ban da abunka Abbu, dama a goshi ake gane marasa jin? Kai dai kawai ayi sha'ani".

"Amma anya ban yi ganganci ba kuwa, ban sanar da shi ba na je na nema masa aure, idan ya bujire fa".

"Au sai ma ya yarda? Ashe na kabari zai dawo duniya idan shi ne zai yadda, ka yi iya yinka a matsayin ka na uba, kar ma ka sanar masa, sai ka kai kuÉ—in, kuma ku saka lokaci kaÉ—an, kar ya tafka wata tsiyar, ba akwai gidan da ya gada na wurin babarsa a chiranci ba, aje a É—an gyara masa, ya zauna".

Abbu ya jinjina kai ya ce "Shikenan Allah ya yi mana jagora".

Kwana huÉ—u, Abbu ya kira baba, ya ce za su zo, su kawo dukiyar aure.
Chapter 46 · 0% Book details