← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 95

Sashe 19

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ta girgiza kai ta ce "A'a baki saka da ni ba, Allah ya taimaka".

Sumayya tana ta aiki a news room, Nabila ta yi sallama ta shiga.

Sumayya ta kalleta ta ce "Ina aikin?"

"Ban je ba, ya aikin?"

"Lafiya ƙalau, meyasa ba ki je ba?"

Nabila ta ce "Ke ba wannan ba, yanzu na ga managern ku a waje muka gaisa"

Sumayya ta ce "Good, ya aka yi?"

"Rahotonki na last week, a kan case É—in yarinyar nan da aka yi wa fyaÉ—e, na ji shiru baku sake cewa komai ba"

Sumayya ta ce "Eh ya aka yi?"

Nabila ta ce "ina da intrest a kai ne, ina son shiga lamarin, na ji shiru haryanzu babu wani update, na an É—auki mataki"

Sumayya ta ce "Dalla ware, kamar wata lawyer kirki, you are not even serious about the job"

Nabila ta ce "Ke ban son wulaƙanci fa, am serious, na ji an ce wanda yayi laifin mai lasisi ne a garin nan, ina son sanin waye shi?"

Sumayya ta ce "Nima ban sani ba"

"Kamar yaya ba ki sani ba, am serious fa, da gaske nake sumayya ina son shiga case ɗin, free of charge na taimaka wa yarinyar, na ji tausayin su sosai da sosai, yadda uwar take kuka. Kuma daga ji ƴan karkara ne, masu ƙaramin ƙarfi".

Sumayya ta galla mata harara ta ce "Sannu ambulance uwar taimako, manyan lawyoyi sun riga sun shiga case É—in tuni, sai ki ja gefe"

"Suwaye manyan lawyoyin? Kuma wai waye dan Allah, waye yayi fyaÉ—en?"

"Ke! Nifa a rubuce aka bani, karantawa kawai na yi, hatta recording É—in da aka saka, na muryar uwar da Æ´ar, tararwa na yi an yi, ban ma gansu ba, ban ga suwaye ba, balle na samu wani bayani. Case ma fa lamarin ya kusa zama a gidan nan, saboda saka muryar matar da aka yi, murtala ne dama ya yi recording É—in ya saka, sai da aka kusa korarsu"

Nabila ta ce "To fa, ina murtalan yake?"

Sumayya ta ce "Ba zan nuna ba, kin ganki Nabila"

"Ba wani abu zan yi ba, sonake kawai ya haÉ—ani da matar da yarinyar".

"Babu fa abun da zaki iya yi a kai, shi ma bai san waye wanda yayi fyaɗen ba, yarinyar aiki take a gidan, baƙo ne daga zuwa yayi mata. Dan Allah ki haƙura da case ɗin nan"

A É—an fusace ta ce "Saboda me?"

Sumayya ta yi murmushi ta ce "Na ji an ce mutuniyar ki da jama'arta sun shiga cikin case ɗin, shiyasa na ce ki haƙura"

Nabila ta ce "Wa kenan?"

"Naja bunkure mana, antynki mudubinki, a bar ƙaunarki" Sumayya ta yi maganar tana dariya.

A take annurin fuskar Nabila ya É—auke, haka kurum jikinta ya bata babu gaskiya a lamarin nan.

"Uban mudubin nawa, in dai wannan mudubin ne, Allah ya fasa shi na huta, wallahi sumayya tun daga abun da matar nan ta yi mini, kawai nake ji a jikina fuska biyu ce da ita, wadda take kallon jama'a da ita, da kuma wadda take ɓoyewa"

"To ko ma dai yaya ne, sun shiga case É—in, kin san kuma ba zasu tsaya su saurareki ba, mussaman da ta iya yi miki kallon ke ba komai ba ce ba"

Nabila ta ce "Haka ne, amma rai dai an cire wa fara kai, lokaci ne, yana nan zuwa da zan bawa duniya mamaki, sai na saka ƙafa na bi ta kanta ko da halin ƙaƙa"

"To ki bi a hankali, kar ke duniyar ta baki mamaki"

Nabila ta yi shiru tana tunani.

Sumayya ta ce "Ya dai?"

Tayi guntun tsaki ta ce "Sumy zaman gidanmu babu daÉ—i, kamar in gudu wallahi".

"Wai Nabila ba zaki daina wannan iƙirarin ba?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba zaki gane ba, faɗa muka yi da Siyama, har da Abba ayi mini faɗa, sauƙinta ɗaya ta ci duka da tukunya na din ga dukanta"

"Haba Nabila, wannan ai yawa ne, degree holder da dambe?"

"To yaya ki ke so in yi? In zuba mata ido ta yi mini duka? Ga uwarsu ta addabi rayuwata, ba ta san yadda ta tsane ni, nima haka na tsaneta ba, kawaici kawai nake yi mata ba.
Duk uban ƴan matan gidan nan har da zaurawa, babu wanda duka sanyawa ido sai ni, da na motsa ayi ta janyo mini jafa'in karuwanci" ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido.

Sumayya ta ce "No dear, dan Allah ki ƙara jurewa, lokaci ne da kin yi aure zai wuce"

"Yaushe zan yi auren? Dan Allah ni mummuna ce Sumy? Duk saurayin da ya zo, sai za a fara maganar aure, sai ya gudu kamar wata jaɓa"

"Nabila kina da matsala, Babu wata halittar Ubangiji mummuna. Ga ki fara, ga gayu da ilimin addini da na zamani, kina da kwarjinin da ki ke bawa maza tsoro ne, ai ke kalar manya ce tawan, ba duk kai ba"

Cikin takaici Nabila ta ce "Ba wasu manya, manyan da suka din ga yaudarata Allah ya isa da ba su aure ni ba suka ɓata mini lokaci, ni yanzu kowaye ma zan aura na bar musu gidan, ko ba na son shi. Idan ba haka ba wallahi wataran sai na gudu"

Sumayya ga tausayin Nabila ga dariya, tabbas Nabila akwai farijinin samari, masu kashe mata kuɗi ma kuwa, sai dai Nabila ta fiye zaɓe-zaɓe, kuma ba ta fiye ba wa masu sonta da gaskiya muhimmanci ba.

"Ki gudu ki je gidan uban wa? Gaki ga Abba nan maza ki gudu kar ki fasa"

Sai kuma ta koma rarrashinta, har bayan azahar suna tare, sai da sumayya ta tashi suka fito tare.

A reception suka tarar da wani mutum, ana ta yi masa fadanci, yana hura hanci cikin manyan kaya na alfarma, reception É—in ko ina security.

Sumayya ta risuna ta gaishe shi ya amsa, amma Nabila ko kallonsa ba ta yi ba, ta sunkuyar da kai, kamar alla-alla take yi, ta yi ta bar reception É—in.

Ɗan rikicewa yayi, ya ƙura mata ido, amma ta basar ba ta gaishe shi ba, sai so yake yi ta ɗago su haɗa ido, dan ya tabattar da abun da yake tunani, amma taƙi ta mayar da kanta gefe.

Mamaki ya shiga yi, yana tunanin ko dai gizo idonsa yake yi masa? Sai dai ya rasa abun yi kafin ya yi wani yinƙuri, sun bar reception ɗin.

ÆŠaya daga cikin ma'aikatan ya kalla ya ce "Wannan mai hijjabin ma'aikaciyar ku ce ita ma?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a sir, she's just a guest here"

Ya ce "She looks familiar to me, anyway shikenan dai" yayi gaba.

Cike da takaici Sumayya ta ce "Kina kallon babban mutum ki ka basar ba ki gaishe shi ba, sai kallonki yake yi, ki ka sani ko shi ne mijin a dace a daidaita ko ƙyasawa yayi? Da irin wannan halin naki, ki ke korar samarinki na kirki wallahi".

"Kin fi kowa sanin bani da baƙin hali, wasu lokutan ma cewa ki ke yi na fiye zaƙewa"

"Haka ne, amma baki kyauta ba, ko dan kallon da yake yi miki, ai kya kula shi".

Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban taɓa jin na tsani wata halitta a kallon farko da na yi mata a rayuwata ba, sai wannan mutumin. Gaba ɗaya ya canza mini mood lokaci guda"

Sumayya ta waro ido ta ce "Meyasa kun taɓa haɗuwa ne? Me yayi miki?"

"No, ina ganin shi a poster dai, ba ɗan majalisa bane? Ban taɓa jin komai idan na ganshi a poster ba, sai yau da na ganshi ido da ido, bana fatan Allah ya sa na sake sanya shi a idona. Kin san me? ji nake kamar ya taɓa cutar da ni, cuta mai muni"

"Arfa, kina hayyacinki kuwa? Tayaya mutumin da ki ka fara gani yau kawai, ki ce kin tsane shi, ya cutar da ke how?"

"Ban san tayaya ba, amma haka nake ji a raina, kuma da gaske nake jin hakan"

"Ki daina irin wannan wasan, kar ki saka a din ga yi miki mummunar fassara"

"Forget, ba zaki gane ba" tayi maganar a daidai lokacin da suka ƙaraso titi.

Tun ba ayi sallar magariba ba, walid ya riga ya gama tatara gayyar matasa zauna gari banza, wanda suka yi bankwana da fatan samun ingantacciyar rayuwa, suka kama makamai da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi.

Kasancewar ba a cikakken hankalinsu suke ba, haka suka raraka kowa da kowa gida.

Yaran madaki, na ta shirin shiga É—aya unguwar sare-saren É—aukar fansa. Labari ya iske su cewar, yaran Aminu sun rigasu yin dirar mikiya.

Ba su yi zaton gayya guda, yaran aminun suka É—aukko ba, dan haka suka fita domin su far musu.

Kamar ba jikin É—an Adam ba, haka suka din ga sara da sukar junansu, mutanen unguwa duk suka shiga gida suka rufe.

Aka yi rashin sa'a madaki baya nan, É—aya daga cikin yaransa, ya kira shi ya sanar da shi halin da ake ciki.

Nasir yana zaune ya idar da sallar magariba yana lazumi, so yake ya tambayi ina arfa, ya ga ya jikinta, amma mama na babban falo, ya san da ya yi hakan, za ta yi masa faÉ—a, tare da sake gargaÉ—insa a kan Nabila.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya shafa addu'ar, ya É—aga tare da yin sallama.

Da sauri ya tashi tsaye, yana faÉ—in gashi nan zuwa.

Da sauri ya É—auki mukullin motarsa, ya fito daga sashin mama, zuwa falo.

Mama ta kalleshi ta ce "Ya dai? Ya na ganka a birkice?"

Dai-dai lokacin Nabila ta fito daga ɓangaren ɗakinsu, hannunta riƙe da kofi, hakan ya sanya ya kasa ba ta amsa.

Zuciyar sa ta tsananta bugawa da sauri, doguwar rigar material ce a jikinta, kanta babu É—ankwali, tayi parking É—in gashinta.
Wani irin kyau ta ƙara yi masa.

"DSP yaushe ka dawo?" Tayi maganar tana kallonsa.

"Da magaribar nan, yanzu nake shirin nemanki, in ga ya jikin naki? Wayarki ba ta shiga"

Anty ta ce "Jiki yayi kyau, har fita tayi"

"Fita kuma, ki ka je ina? Kuma da iznin wa?"

"Dan ubanka ina yi maka magana ka shareni, maganarta ta fi tawa muhimmanci ne ko yaya?"
Chapter 19 · 0% Book details