← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 95

Sashe 88

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga matsi ya ƙaru daga gidansu, babu in da zai samu abinci, ya yanke shawarar fara zuwa kasuwa ya duba ko dako ya fara, sai da ya je ya tarar ashe dakon ma sai ka san wani, sai an san da kai, duk sana'ar da yayi tunanin farawa sai ya ga dole sai da jari, gashi Rahila ta cigaba da ziga Abbu, ya ƙara tsanar Al'amin wai shi ne silar mutuwar Sadik.

Al'amin ya fara gajiya da yunwa da take neman tagayyara shi, ya fara zuwa gida ya É—auki duk abincin wanda ya tarar ya cinye, idan ya tafka wannan tsiyar, sai ya gudu ya kwana a kangwaye, gashi ya koma HND tun Sadik na raye, dama shi ne yake ta fafutukar tara school fees É—in sa kan ya rasu, yanzu kuma ga yunwa da rashin kuÉ—in transfort dan haka ya daina zuwa makaranta gaba É—aya.

Gashi ko a maƙwabta aka rasa wanda zai yi wa Abbu nasiha, ko su din ga taimakonsa, saboda ana ganin babansa yana da rufin asiri.

Yana can garin yawonsa, kawai ya hango wanda ya kashe Sadik, a tsallaken titi, da tawagar matasa 'yan daba, da gudun gaske Al'amin ya tsallaka titin, sai dai kan ya ƙarasa sun ɓace masa, cikin tashin hankali ya ƙarasa wurin wani mai ice ya ce "Malam dan Allah wanda ya wuce ɗin nan ina yayi?"

Ya kalli Al'amin ya ce "Meye haÉ—inka da shi?"

"Yayana ya kashe da almakashi, bai yi masa komai ba, 'yan sands suna ta nemansa"

"Taɓ, ka raba kanka da wannan. Madaki kenan gawurtaccen ɗan daba ne, hukuncin kisa ma aka yanke masa a gidan yari, amma muka ga an sake shi, duk ya gallabe mu, ya hanamu sukuni mu ma, sai dai ka bar wa Allah kawai" Ai Al'amin bai tsya jin ƙarshen zancen ba, ya shiga cikin unguwar ya din ga yawo, amma bai ga madaki ba.

Washegari da sassafe, ya koma wurin 'yan sanda ya gaya musu ya ga wanda ya kashe yayansa, su tafi tare da shi a nemo shi, an gaya masa sunansa madaki.

Wani ɗan sanda ya kada baki ya ce "Ka san mutum nawa madaki ya kashe aka ƙyale shi?" al'amin ya ce "Ni ina ruwana da mutum nawa ya kashe, ku kama shi a kai shi kotu ni dai".

"Ko an kai shi ma, za a sake shi, ka je ka yi haƙuri haryanzu bamu tabattar da shi ya kashe shi ba".

Kasancewar Al'amin yana kan tashen balaga, ya sanya ya tsaya yana yi musu rashin kunya, aka saka wani sageant, ya zane shi aka kore shi. Hakan yayi matuƙar tunzura zuciyar Al'amin, ya din ga jin jinin ɗan uwansa ba zai tafi a banza ba.

Ya din ga sintiri a unguwar da madaki yake, kasancewar ba su da nisa sosai, ya samu duk bayanin da yake son samu a kan madaki, da in da yake zama da shi da yaransa.

Ya je gida ya shiga kitchen ya samo, wuƙa sabuwa gal, ya je ya ɓoye, ya saka a ransa shi ma sai ya kashe madaki, ko da kuwa za a kama shi a kashe.

Sai dai aka yi rashin sa'a, Madaki bai fiye zama a unguwar ba, sai idan zai shigo yayi rashin mutunci, Al'amin ya din ga fakonsa, har ya yi wataran sa'a ya tarar yana nan.

Gadan-gadan ya ratsa tarin matasan da suke ɗauke da makamai suna shaye-shaye, ya nufi madaki da wuƙa.

Matasan suka mimmiƙe, amma madaki ya ɗaga musu hannu, a kallo ɗaya madaki ya gane Al'amin.

Kafin ya ƙarasa gaban madaki, sani ya sanya ƙafa ya taɗiye Al'amin dan haka ya faɗi a gaban madaki, suka kwashe da wata irin dariya.

Al'amin ya yinƙura zai tashi, madaki ya saka aka take masa kafaɗun Al'amin da ƙafa, yana ƙoƙarin tashi, amma cikin ƙarfin Al'amin ya tashi, madaki ya tako gaban Al'amin ya shaƙe wuyansa.

Take Al'amin ya ji kamar an shaƙe shi da wata muguwar sarƙa mai nauyin gaske, a take ya ji numfashin sa na neman ƙwace masa. Al'amin ya saki wuƙar ya koma kokowar raba hannun madaki da wuyansa, madaki ya tsare shi da jajayen idanunsa da ya rambaɗa musu farin kwallin tsafi, yana ƙyaƙyata wata uwar dariya, daga bisani kuma ya tsuke rai tamau, ya ƙara tsananta shaƙe Al'amin, sai da ya ga ya daina motsi, sannan ya watsar da shi a wurin, ya kalli wani ya ce "Ku kai shi arear su ku watsar"

"Ba za a saita ma hanya daga duniyar ba ya ci bulus kenan?"

Madaki ya girgiza kai ya ce "Yana cikin tsananin ɗacin rashin ɗan uwansa, idan aka yage shi daga sararin nan, hutawa zai yi, sai ya gane kuskuren da ya aikata na yinƙurin da yayi"

Suka ɗauki Al'amin suka kai shi unguwar su, suka jefar da shi a sume a gaban wani mai kayan miya, suka ce wa mutanen wurin "Gashi nan, ajiyarmu ne, zamu din ga bibiyar sa ku kira tsohonsa ya ɗauke shi idan yan buƙatarsa".

'yan unguwa suka É—auke shu, suka kai shi gida, Abbu yana nan, aka kwantar da shi a tsakar gida, ana shafa masa ruwa, mai kayan miya ya gaya wa Abbu abun da yaran madaki suka ce, aka shawarce shi a kan ya kai maganar wurin jami'an tsaro, amma Abbu ya ce babu ruwansa, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, shi bai aike shi wurin 'yan daba ba.

Tun daga nan madaki ya mayar da Al'amin kamar karen farautarsa, ya saka rayuwarsa a gaba, wataran har cikin unguwar su yake aikawa, a nemo masa Al'amin, a kai masa shi har dabarsa, su casa shi da zalunci kala-kala, wai sa ya saduda ya nemi afuwar abun da ya yi wa madaki, dan ba a taɓa samun wanda ya yi abun da Al'amin yayi ba, ya rasto har dabarsa ya nemi ya kashe shi, yana ƙanin ƙanin bayansa.

Al'amin ya kalli madaki ya ce "Ka yi kaɗan na nemi afuwarka, baƙin kare kuma in sha Allah sai na zubar maka da jini, kamar yadda ka zubar da jinin ɗan uwana da bai yi maka komai ba"

Ya durƙusa ya soka wa Al'amin wata kibiya a cinyarsa, cinyar sa na zubar da jini, amma saboda azabar taurin kai, ya datse haƙoransa ya ƙi ihu.

"Na fuskanci zaka yi mini amfani, na saka ka cikin yarana daga yau, zaka din ga yi mini aiki"

Al'amin ya girgiza kai ya ce "Ni fa kallon kare nake yi maka, da na bika gara na yi mutuwar wulaƙanci"

Ya ce "Shikenan zamu gani, dafin ciwon da nayi maka na fili da na zuciya ya isheka ka saduda".

Al'amin ƙafa taƙi takuwa, sai da kyar, ya din ga tagayyara a gari, yaran madaki suka matsawa unguwar su Al'amin, duk da suma suna da ƙasurguman 'yan daba, amma ba sa shiga harkar faɗan matasan 'yan daba.

Al'amin ya ƙi ya karaya ya saduda, ga ƙafa yana ɗingisawa, ga yawon neman in da zai ci abinci, kullum rahiila cikin gaya wa Abbu take, Al'amin abubuwan da yake da yadda 'yan daba suke kawo masa farmaki, sun tabbatar da cewar shaye-shaye ya fara yi, dan haka lallai ya kori Al'amin daga gidan, ya daina zuwa kan ya kuma janyo musu wata masifar, ta ce a kama masa shago a cikin unguwa ya bar kwana a cikin gidan, duk da dama ba kullum yake kwana a gidan ba.

Wata ranar juma'a da yamma, Al'amin yana tafe yana ɗingisa ƙafarsa, yaran madaki suka shigo, da wasu irin mahaukatan karnuka, kuma kai tsaye suka sakarwa Al'amin su, gashi ba zai iya gudu ba, saboda ƙafarsa, suka dirar masa da cizo, ya din ga danƙar karnukan nan yana jifa da su, manyan karnuka ne sun kai biyar, wannan ya yage shi ta nan, wancan ya kai masa cizo ta nan, sai da suka ga yana neman fara halaka karnukan, ko su yi mutuwar kasko da su, sannan suka nufi Al'amin suka fito da makamai. Dan madaki cewa yayi, su kai masa wani sashe na jikin Al'amin sun cire masa.

Karnuka sun yi masa kaca-kaca da kayansa, da fatarsa da cizo da yakushi, jikinsa duk jini, amma ya yinƙura ya tashi, ganin sun tsaya a kansa da makamai.

Ɗaya ya shammace shi, ya sara masa wuƙa a cinya ta baya, ya hankaɗa shi ya faɗi, yana faɗuwa suka ga ɗaya daga cikinsu ma ya faɗi ƙasa jini na zuba daga jikinsa.

Gaba É—aya suka É—aga kai suna kallon wanda ya yi aikin.

Wani gabjejen mutum ne, baƙi mai jiki sosai, da jajayen ido, a yaran madaki wani ya yinƙuro, amma ya caka masa wuƙa a ciki shi ma, ya faɗi.

Ya durƙusa ya ɗago Al'amin, jikinasa jina-jina, ya kalli wanda suke tare ya ce "Samo abun hawa, a kai yaron nan asibiti" ya kalli sauran yaran madaki ya ce "Ku je ku gaya wa madaki, ya zo dabata ni dodo babban sarki, ina nemansa. Na ji labarin irin ɓarnar da yake shigowa unguwar nan yana yi, kasancewar bana shiga shirgin shirmen ƙananan matasa, ya sanya ban damu ba. Sai dai na wuce a mota, a wancan lokacin na ganku kuna dukan yaron nan, wannan karon ma na ganku kun saka karnuka na cizon sa, kamar ba ɗan adam ba awanni ashirin da huɗu na bashi, ya zo yayi mini bayani, idan ya bari na taka na je in da yake sai dai uwarsa ta haifi wani. Ku ɗauke mini wannan mushen, ku ɓace daga gabana" jiki na tsuma, suka ɗauki wanda aka cakawa wuƙar suka tafi da shi.

A asibiti ɗan wando kawai aka bar Al'amin da shi, jikinsa sai tsatstsafar da jini yake yi, saboda cizon karnuka da yakushi, ga raunin da yake ƙafarsa, sai da aka yi dressing raunukan jikinsa, sannan aka yi masa rigakafin cizon mahaukacin kare, dan ba a san wane irin karnuka ne suka ciji Al'amin ba, aka saka masa ruwa, sannan aka kawo masa lafiyayyen abinci daga restaurant.

Dodo babban sarki, bai sake bi ta kan Al'amin ba, sai bayan magariba, ya je Asibiti da shi da yaransa, aƙalla dodo ya kai shekaru arba'in da biyar, ya girmi madaki sosai, madaki kuma ya girmi Al'amin.
Chapter 88 · 0% Book details