Sashe 55
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ana sallar isha'i sai gashi ya dawo, ya tarar da ita, fitilarta babu batirin kirki, duk tayi duhu, sai kwashe ruwa take a falo.
A ransa ya ce "Iyayenki ne suka ja miki" tayi masa sannu da zuwa, ta cigaba da aikinta, har zai wuce ya dawo ya karɓi kwanon, ya haɗe mata kujerunta wuri guda, ya kunna fitilar ƙaramar wayarsa, ya ƙarasa kwashe ruwan.
Shi kansa ya san gidan nan kango ne, yana buƙatar gyara sosai, bai ci ace har an saka mutum a ciki ba, amma da iyayensa da na ta, ya rasa wannene uban garajen da ya saka aka yi haka.
Ya É—aÉ—É—aga labulayen, saboda É—akin ya sha iska, daga nan ya tafi makwancinsa, ta tafi nata.
Da safe ruwan duk ya tsane, amma sai ƙanƙame jikinta take yi, ƙarnin ruwa da ya kwanta ya din ga damunta.
Haka nan ta daure, ta gyara gidan, ta zuba miya ta yi jallof ɗin macaroni, kasancewar falon a jiƙe yake, da danshi, da sauran Lipton ɗin jiya, ta dafa shayi har da su citta ta yi sallama a ƙofar ɗakinsa, bai amsa ba dama labulen a ɗage yake ta shiga.
Ta ajiye masa ta ce "Ina kwana?" Ba ta jira ya amsa ba, ta haÉ—a masa tea, ta tashi ta fita.
Aka jima ta dawo, ta shiga banÉ—akinsa ta wanke, ta É—auki bokiti ta dawo, ta haÉ—o ruwan zafi na wanka, ta kai masa banÉ—akin ta ce "Master ga ruwan wanka nan na kai maka, mai É—umi ne" idan ta ce mastern nan, sai ya É—aga kai ya kalleta.
Ta ce "Yauwwa, master zan kafa ƙusa a toilet ɗin ka, idan ka gama wanka, ka dinga saƙale soson, idan ba haka ba sabulun narkewa yake yi, sai ka ga ya ƙare da wuri"
Ta zagaye shi, ta fara tattare kayan duk da ya watsar a ɗakin kamar ƙaramin yaro.
Ya gama cin abincin sa, ya fara shan tean, yana jin yadda ƙamshin da yajin citta yake ratsa shi yana yi masa daɗi.
Yana zaune ta gyare ɗakin, ta kukkuna masa turaren wuta, sai dai kafin ta ƙarasa, ya kunna sigari a ɗakin.
Sai da ranta ya sosu, akwai sauran warin ta jiya da daddare ma da ya sha, ta gama aikin É—akin, ta kunna turaren wuta, ya kuma kunna wata sigarin.
Ta maze ta ce masa "Ruwan wankanka, kar ya huce fa, na ga garin da sanyi haryanzu, idan ka yi wanka da na sanyi, zaka yi mura"
A hasale ya ce "Ke, fita ki bar mini É—aki, kin gama tsegumin ai, kin sakani a gaba kin ga abun da nake yi, to fita ki bar min É—aki, ba zan wankan ba"
Ba ta sake cewa komai ba, ta juya ta fice, ta cigaba da ayyukan ta, tana tsaka da wanke-wanke, ya fito da sauri, hannunsa riƙe da waya yana cewa "Kar ku raga musu, gani nan zuwa" ta miƙe tana kallonsa, amma ta kasa yi masa magana.
A haka yana ƙaurin sigarinsa da komai, ga kayan da su ya wuni jiya, ya wayi gari da su, amma bai canza wasu ba, ya fice cikin matsanancin sauri.
Ta koma ta cigaba da aikinta, tana addu'a Allah ya sa ba wani rashin jin zai je yayi ba.
Baba yana gida, aka aiko ana sallama da shi.
Yana fita ya tarar da 'yan uwan Alhaji mu'azzam da suka kawo kuÉ—i.
Suka gaggaisa, ƙanin mahaifin Alhaji mu'azzam ya ce "Gamu mun dawo, ɗanka ne ya dawo da mu, ya ce a bayar da haƙuri, kar a ji mu shiru, ayyka sun yi masa yawa, ba zai samu dawowa nan kusa ba, shi ne ya ce mu zo ayi magana, a ƙarasa shirye-shirye kawai, ayi auren a tura masa ita can".
Gaban Baba ya faÉ—i jikinsa a sanyaye ya ce "Alhaji dama ko da baku zo ba, zan neme ku ni na zo, an sami matsala ne, zan dawo muku da kuÉ—in aurenku".
Suka yi turus gaba É—aya suka ce "Wace irin matsala ce haka?"
"Yarinyar nan, yau ta kusa sati biyu, ina mai baku haƙuri, a bashi haƙuri dan Allah. Zan kawo muku kuɗin aurenku"
"Amma wani abun yayi ne, ko wani laifin shi mu'azzam É—in yayi?".
Baba ya ce "Ko ɗaya, ka san matar mutum kabarinsa, mu'azzam bai yi mini komai ba, dan Allah a bashi haƙuri"
Suka ce "To shikenan, Allah ya tabattar mana da alkhairi".
Suka amsa da "Amin"
Baba ya ce "Ku bani account number, na mayar muku da kuÉ—in auren"
ÆŠaya daga cikin su ya ce "A'a, a bar wannan maganar sai ya dawo tukuna, Allah ya basu zaman lafiya"
Ya amsa da "Amin".
Bayan la'asar yara duk suna islamiyya, babu 'yan aike, ta ce bari ta fita ta sayo maganin sauro, idan ya dawo sai ta gaya masa.
A ƙofar gida suka haɗu da maman su halimatu a waje da wata maƙwabciyar su, suka gaisa ta ce "Maman halimatu, ba ku shigo mini mun gaisa ba haryanzu".
"Wallahi Amarya, ba ƙi muka yi ba, kin sa yanayin mijin naki sai a hankali, abun da tsoro, kar wani abu ya faru".
Ranta bai yi mata daÉ—i ba ta ce "Haba dai, ina ruwansa da ku? Kawai dai a shigo a gaisa, shikenan a gaida su halimatu" tayi gaba zuciyarta babu daÉ—i, a duk lokacin da ta ji an aibata shi, sai ranta ya sosu.
Har dare ba ta sake ganin Al'amin ba, gashi ita ba waya ba, wasa-wasa har dare yayi babu Al'amin babu dalilinsa har garin Allah ya waye, bai kwana a gida ba.
Sai abin ya fara damunta, gashi ba ta san a ina za ta ganshi ba.
Abu kamar wasa, aka sake shafe wuni, aka shiga kwana na biyu, babu shi babu labarinsa, nan fa hankalinta yayi mummunan tashi, gashi ba ta san wa za ta nufa ta gayawa ba.
Maman halimatu ce tayi sallama, Jauhar ta saka hijjabi ta fito tana murmushin yaƙe ta ce "Maman halimatu, sannu da zuwa shigo"
"A'a ba shigowa zan yi ba, abbansu yana nan bai fita ba, bai san ma na shigo ba na ce kin kuwa san an kama mijinki?" Gaban Jauhar ya faÉ—i ta ce "Yaushe? A ina? Waye ya gaya miki?"
"A bakin Abban su halimatu na ji, cune suka yi masa aka kama shi, amma dan Allah kar ki gaya masa wanda suka saka aka kama shi É—in dan Allah, na gaya miki ne na san baki sani ba".
Tuni idon Jauhar ya cika da hawaye ta ce "Eyya, meysa abban su halimatu yayi haka? Wallahi babu abun da zai yi wa wani, ba ruwan shi da kowa idan ba taɓa shi aka yi ba, ina aka kai shi? Dan Allah ki gaya mini, ina gidan ban san ina zan nufa ba ma".
Tayi ƙasa da murya ta ce "Yana anti daba can aka kai shi".
"Menene anti daba kuma? Ina ne?".
"Can in da ake kai 'yan daba, ki shirya ki je ki duba shi".
Ta ce "To na gode" bayan tafiyar maman halimatu, take ta ji haushin malam lawan ya kamata.
Tayi tunanin ko gidansu za ta je, ta faÉ—a, amma sai ta ga idan tayi hakan, kamar ta tozarta kanta ne, dan haka ta fasa ta É—ora girki, ta gama ta shirya, ta zuba a flask, ta bi kwatancen da maman halimatu tayi mata.
Su kansu yanayin jami'an tsaron wurin, tsoro suka bata, ba ta taɓa zuwa police station ba, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta ce "Dan Allah wani nake nema"
"Wa kenan?" Wani ya tambayeta.
"Al'amin sunansa"
ÆŠan sandan ya ce "Anya, babu wani mai irin wannan sunan da muka kama".
Ta ce "Dan Allah nan aka ce mini an kawo shi, dan Allah officer ka duba mini"
Na kusa da shi ya ce "Ko viper take nufi?"
Ta ce "Eh shi, mai dogon zamani"
"Ya aka yi me zaki yi masa?"
"Wurinsa na zo, maƙwabciyata ta ce mini cune aka yi masa aka kama shi, wallahi bai yi komai ba".
"Ke ya aka yi ki ka san bai yi komai ɗin ba? Wacece ɗin sa ke, ni tun da muke kama shi ma, ban taɓa ganin wani ya zo wurinsa ba, idan ba ire-iren sa ba ko yaran ubangidansa ba"
Ta ce "Mijina ne"
Saroro suka yi suna kallon jauhar, kyakywar yarinya ƙarama da ita.
"Ke kuma auren soyayya ku ka yi? Jama'a kun ga matar Viper, yaushe ne kuwa zuwansa na ƙarshe aka fito da shi aka ce aure yayi" waiwayowa suka yi suna kallonta, ta sunkuyar da kai tana fatan Allah ya sa su bar ta ta ganshi.
ÆŠaya daga cikin su ya ce "Ku fito da shi, ta ganshi, amma dai Viper yayi asara, daga aurensa ya saka 'yar mutane fara sintiri saboda shi".
Saroro yayi da ya hangota cikin hijjabi, 'yan sandan suna yi mata tambayoyi.
Tana ganinsa tayi ajiyar zuciya, ya ƙaraso gaban kantar ya kalleta ya ce "Me ya fito da ke?"
"Kwana biyu baka nan, ban san in da ka ke ba, sai yau ban san kama ka aka yi ba"
Ya sake kallonta ya ce "To ware ki koma"
Jauhar ta ce "To in koma, kai fa ba sakinka za su yi mu koma ba?"
Al'amin ya ce "Ki tafi na ce, kuma kar ki sake zuwa wurin nan kina mace, ware" haushi ne ya kamata, yadda yake korarta, shi ba ayi masa abun arziki sai hantara.
Ta É—ora leda É—uake da flask É—in Abinci ta ce "Gashi abinci ne na kawo maka" sai da ya É—an yi shiru yana kallonta.
Tun da ya fara rashin jin sa, babu mai tunawa da shi, ya kawo masa ziyara ko abinci, idan ba su walid ba, sai kuma ita yanzu.
"Ahh yau zamu ci girkin amarya, amma hajiya sai kin fara ci kafin ya ci"
Bai saurari É—an sandan ba, ya É—auki abincinsa ya koma gefe.
Ya buÉ—e, ta yi sauri ta zagaya, ta huda ruwa pure water, ta ce masa "Ka fara wanke hannunka"
Kamar ya shareta, sai kuma ta zuba masa ya wanke, ya saka hannu ya fara cin abincin.
"Akwai sauro ne wurin? Na ga kamar ya cijeka, jikinka duk cizon sauro?"
"Mmm" ya amsa yana cigaba da cin abincin.