← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 95

Sashe 35

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Viper ya tsaya cak, yana jiran ya ji me zai ce.

"Na yi aikin da ka saka ni, ya tafi yadda yakamata "

Ya kaɗa kai tare da yi masa alamar ya ƙaraso.

"Ina labarin malam lawan?"

"Kamar dai yadda ka ce, an kula da komai, sai dai babu wanda ya sake zuwa, gashi yanzu yana yawo a cikin unguwa".

"Madaki fa?"

"Shi ma kamar dai yadda ka sani, Honorable indabo yake yi wa aiki yanzu".

"Ina buƙatar isassun kayan aiki, a kwanakin nan zan dirar masa, mu ɓalla ƙarfe, sai dai mu yi mutuwar kasko, ayi wadda za ayi".

"Ba yanzu ba" suka ji muryar Walid.

Suka mayar da hankalinsu kan sa.

Walid ya ce "Viper da sauran lokaci, kai ka san madaki ba haka kurum yake daba ba, da zai kasu cikin sauƙi, da tuni mun kawar maka da shi, ka ɗan saurara tukuna"

A hasale ya ce "Ba zan saurara É—in ba tukuna"

"Viper!"

Ciki ƙaraji ya ce "Walid ka ƙyale ni"

Walid ya girgiza kai ya ce "Da zan iya, da tuni na yi, mutumin nan ya fi ƙarfinmu ko ta ina, idan ka yi amfani da zuciya wallahi ba zamu yi nasara ba, ka bari mu bi komai a hankali mu lissafa, yadda ko mutuwar kasko ce mu yi"

Cikin ƙaraji ya ce "Ba zan jira ba, na gaji, na gaya maka na gaji. Na so bin komai a hankali, meyasa ka kawo mini yarinyar saboda me? ka san ka ƙara tunzara zuciyata yaya ka ke so na yi, so ka ke sai na haukace tukuna? Kalli yadda na koma walid, kalle ni, abun da nake ta ƙoƙarin dannewa ka fama mini, dan me zaka kawo mini wannan yarinyar sannan ka ce na nutsu how? Ta ɗauki wayata ta tafi, ka na da tabbacin hannun wa wayata za ta shiga? Idan aka tashi kama ni, kana da tabbacin su waye za su kama ni, idan na ƙare a haka ban aikata abun da nake ƙuduri ba fa? Ko dai ka nemo duk in da yarinyar nan take na kasheta, ko kuma a yau ba sai gobe ba, sai na yi gaba da gaba da madaki ko na kashe shi ko ya kashe ni, amma kafin nan sai na fara gaba da gaba da wancan dabban" tuni gumi ya tsatsttsafo masa, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, kafofin gashinsa ya bubbuɗe.

Walid ya taka gabansa a hankali, cike da shirin ko ta kwana, dan ya san ƙarshenta sai ya ba shi gwale-gwale, ko ya mangare shi.

Ya shammace shi, ya soka masa sirinji a damtsensa, kasancewar jikinsa babu riga, ya fara yi masa allura, sannan ya fara yi masa magana.

Walid ya ce "Na san na yi laifi, amma ka bari na gyara laifina da kaina, na san abun da ka ke ji É—an uwa, ba kai kaÉ—ai ka ke ji ba Al'amin"

Viper ya zubawa walid ido, ya rasa me zai yi, yana tsaye ya kashe masa jiki, ba zai iya komai ba, kasa tsayuwar yayi, ya tafi zai faɗi walid ya riƙe shi ya kwantar, ɗan mama kuwa dama tuni ya arce, dan yana tsoron a shaƙe shi.

Barrister Naja'atu ce zaune a katafaren ofishin ta, tamkar na matar gwamna, yana ɗauke da duk wani kayan alatu da ake buƙata.

Sannu a hankali take shafa screen É—in wayarta, daga bisani ta saka wayar a kunnenta.

"Honorable, ka isa Abujan ne?".

Ya amsa da "Eh ma sauka"

"Ok, yaya maganar yarinyar nan da Abdul ya yi raping?"

"Yes, he handle the case himself, yayi maganin abun".

Ta ce "Ok, ina fatan ka ja masa kunne, kar ya je ya aikata wani shirmen da ba zamu iya gyarawa ba".

Ya ce "No, kar ki damu, zai yi abun da ya dace".

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, dama ina tsoron ya yi wani shirmen ne, amma tun da ka ce haka, shikenan"

Ta katse wayar, ta mayar da hankalinta kan sakatariyarta da ta shigo.

Cikin gyatsine ta ce "Ke kuma ya aka yi?"

"Kin yi baƙi ne ma"

"Suwaye?"

"Eh to, da alama dai ƙorafi suka kawo, ke suke.....

"Ke bani da lokaci, ayyuka sun yi mini yawa, su ganki ko wani daban, hutawa nake buƙata, wannan jaraba a uzzurawa rayuwarka, london zan wuce ma ni this week na je na huta. Ki fita ki je ki sallame su" ta juya jiki a sanyaye ta bar office ɗin.

Salim ya kalli Abdul da ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana shan giya a cikin wine cup ya ce "To wai yanzu ya zaka yi da yarinyar nan da ka kawo ka ajiye, Ga abun da aka tsara, kai kuma ga abun da ka yi?"

Ya É—an girgiza giyar a cikin kofin sannan ya ce "Gani na yi za ta ci bulus idan ta tafi a haka, sai na gama moreta zan aikata kawai"

"Amma ba ka ganin, hakan zai iya kawo matsala, yanzu ko a nan gaba?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba wata matsala, na É—an lokaci ne, zan gama abun da zan yi da ita, zaka iya tafiya ma kawai"

Ya jinjina kai ya ce "To shikenan"

Sannu a hankali ta buɗe idonta, ta din ga gani dishi-dishi, ta kasa tantance a ina take, dan ba ta taɓa ganin wurin ba.

Ji ta yi an rufe ƙofa, ta ɗaga kai ta kalli mai shigowar, take gabanta yayi mummunar faɗuwa, duk da idonta bai gama washewa ba, amma sarai ta gane shi.

"Kin tashi kenan? abun da aka shaƙa miki bai taka kara ya karya ba, amma ki ka yi wannan dogon zangon" yayi maganar lokacin da ya tsuguna a gabanta yana kallon idonta.

Ƙirjinta ya din ga bugawa da sauri da sauri.

Ganin ba ta ce komai ba, ya sanya ya tashi ya fita, babu jimawa ya dawo da plate a hannunsa, É—auke da indomie da kifi a ciki, sai ruwan roba, hannunsa É—aya kuma ledar magunguna ce.

Ya tura mata plate É—in gabanta, sannan ya fara haÉ—a alluran.

Tayi shiru ta zuba masa ido, har sai da ya ce "Ki ci mana, allura zan yi miki"

Cikin kuka ta ce "Dan Allah kar ka kashe ni"

Abdul ya yi wani murmushi ya ce "Saboda me?"

"Ni dai kar ka kashe ni, dan Allah ka mayar da ni wurin babata"

Ya kalleta ya ce "Kashe ki fa sai na yi, ba dai ke taurin kai ba ke da babar taki, zan nuna muku cewa talaka ba komai bane illa bawa kuma takalmi ga masu kuÉ—i da dukiya, ba yanzu zan kashe ki ba, sai kin gama yi mini amfani tukuna.
Yanzu ki ci abincin nan, zan yi miki allurai na zazzaɓin da yake jikinki".

"Ni ba zan ci ba" ta yi maganar za ta tashi tsaye, amma ya daka mata tsawa ya ce "Wallahi idan ba ki ci ba, a yanzu zan kashe ki, ko gawarki babarki ba zata gani ba".

Babu shiri ta fara cin abincin, sai dai a loma ta uku, ta hau amai, ta amayar da duk abun da ta ci.

Cikin tsananin takaici ya ce "Ke mahaukaciyar ina ce zaki yi mini amai a nan? Nan yayi miki kama da wurin juye ƙazanta?.

Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

"Tashi mu je in nuna miki in da duster da mopper suke ki gyara"

Cikin tsoro ta tashi, tana jiri tana bin bango, haka ya saka ta gyara wurin da ta yi aman.

Bayan ta gyara, ta shiga banÉ—akin tayi alwala, ta fito ta tayar da salla, ba tare da ta san ina ne gabas ba, da kuma adadin sallolin da ake bin ta ba, dan ba ta san adadin lokacin da ta shafe, ba a hayyacinta ba.

Ya dawo ya tarar da ita a zaune, a takure wuri guda, bai kulata ba, ya ƙarasa ya sanya hannun sa a goshinta, ya ji shi da zafi rai. ɗaga ta ya ja ta ya dungurar da ita a kan gadon.

Ya kama hannunta, ya saka sirinji, ya fara É—aukar jininta.

Bayan ya gama É—aukar jininta, ya yi mata wasu allaurai duk a jijiyar hannunta.

Ta zubawa saurautar Allah ido, dan kasa magana ta yi, tun yana allurar ta fara jiran jin alamar ciwonta ya ƙaru, dan ta sallama kashetan zai yi kamar yadda ya faɗa, amma bayan ya gama yi mata ya tashi ya fice, ya kulleta a ɗakin, ba tare da ta ji yanayinta ya sauya ba.

***
Abun duniya fa ya ishi Nabila, wayar Viper ta zame mata wahala, dan kuwa kashe ta tayi gabaki É—aya, sai dai duk in da ta zauna, musamman da daddare, idan ta shiga cikin duhu, Viper ne yake yi mata gizo, har abun ya fara tasiri a yanayin mu'amalarta.

Tana toilet tana wanka, wayarta ta din ga ringing babu ƙaƙƙautawa, ta kammala wankan ta fito, ta ɗauki wayar tana dubawa.

Lambar Nasir ta fara kira, ta nemi wuri ta zauna a gefen gado, tana jiran ya É—aga.

"Ina ki ka shiga ne? Ko kina wurin aiki ne?"

Ta ce "A'a, yanzun nan na dawo gida"

"Baki da lafiya ne?"

"No, gajiyar aiki ce kawai"

"To, aikin ki yayi kyau arfa, na yi waya da mu'azzam, gayen nan da ki ka faɗa mun kama shi, tare da tabar wiwi da ƙwayoyi"

Sassanyar ajiyar zuciya ta yi ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah shi ne abun godiya, what next?"

Ya É—an yi shiru sannan ya ce "Na saka lallai su fara tuhumarsa, ya faÉ—i in da Viper yake".

Zuciyarta ta din ga raya mata ko ta sanar masa kai tsaye, abubuwan da suke gudana, ta bashi wayar hankalinta ya kwanta, amma zuciyarta ta gargaÉ—e ta a kan aikata hakan.

***
In da ya bar ta a kan gadon, nan ya je ya sake tarar da ita, ta tashi ta zauna ta dunƙule jikinta a wuri ɗaya tana bacci, sai ajiyar zuciya take yi.

Wani irin murmushi ya yi, yayi miƙa lokaci guda, ya fara rage kayan jikinsa.

Motsinsa ya sanya ta farka, fes ta buɗe idanunta, sai dai hankalinta ya yi mummunan tashi, ta ja da baya, ba ta ƙaunar ganinsa ko kaɗan.
Chapter 35 · 0% Book details