← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 95

Sashe 79

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jauhar kuwa tun da tayi tozali da takardar nan ta kasa nutsuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuma taƙi buɗe takardar, da ta leƙa ta hangota ma, sai ta yi sauri ta fito daga ɗakin, ta din ga lissafa irin halin da za ta shiga idan ta koma gida, da irin dariyar da za su yi mata.

Kuma yaƙi dawowa, har dare ba ta ganshi ba, hakan ya ƙara sanyata cikin tashin hankali, ba irin tunanin da ba ta yi ba, har ta fara tunanin ko da ya saketa, barin gidan yayi gaba ɗaya, sai dai kayansa suna nan, dan ita ta gyara ɗakin ya watso da komai ya bar mata a wurin.

Sai sha biyu saura ya dawo, idonta biyu ya dawo ba ta yi bacci ba, sai da ta tabattar ya shiga É—akinsa, sannan ta É—auki takardar ta bishi É—akinsa.

Yana kwance a kan katifarsa, ya cika É—akin da warin taba.

Yanayinsa ya nuna a buge yake, saboda fitilar ɗakinsa a kunne take, ya haye katifa ya mimmiƙe idanunsa sun yi ƙanana da ƙyar yake ɗaga su, kallo ɗaya ya yi mata ya mayar da idonsa ya lumshe.

"Master sai da ka rubuta takardar nan hankalinka ya kwanta ko?"

Bai buÉ—e idonsa ba ya ce "Ke ki ka ce na rubuta"

"Kuma sai ka rubuta É—in ko? Saboda ina fargabar kar ka sake ni, bakomai maraici ne ya janyo mini, Allah ya gani na yi iya yi na, na yi biyayyar aure, amma kullum kallona ka ke yi wadda ta takura rayuwarka, ga takardarka nan, ban ma buÉ—e ba balle na san meye a ciki, kuma wallahi ban saku ba" ta dire masa takardar a jikinsa, ya ziro harshensa tare da naÉ—e shi ya mayar, ya gyara kwanciyar sa, har ta gama surutanta, bai kuma motsawa ba.

Kasa bacci tayi, ta ɗaura alwala ta tayar da salla, ta din ga addu'a Allah ya sa ya fasa sakinta, saboda ita a ganinta gara ƙalubalen gidan Al'amin a kan na gidansu.

Duk rintsi ba zai daketa ko ya ci mutuncin ta ba, ko yi mata sharri ba, sai dai miskilancinsa da gaya mata baƙar magana wasu lokutan da har daɗi take ji ya kulata, ciyar da su kuma da take yi mafi yawan lokuta baya damunta, sai ma yi wa Allah godiya da take yi da ko yaya ba ya hanata abun da zata sarrafa su ci, ko yaya ta kasa abun sayarwa za a saya dan ma ana yi mata mugunta.

Bayan sallar asuba tayi shiru tana tunani, ta ga sam ba ta kyauta ba, wasu abubuwan da ta yi masa, tun daga jifansa da kwanuka, har zuwa tsiwar da ta yi masa, ita tayi mamaki ma da ya ƙyaleta.

Yau ba ta iya komawa bacci ba, ta fito aikace-aikacen ta, tana yi tana leƙawa ko ta gani ko ya tashi.

Tana falo ta jiyo motsinsa, ta tashi ta shiga É—akin da sallama.

Ya amsa mata, ba tare da ya kalleta ba.

Jiki a sanyaye ta durƙusa ta ce "Master ina kwana?"

"Lafiya ƙalau"

"Ka tashi lafiya, ya ciwonka?" Sai a wannan karon ya kalleta sai dai bai ce komai ba.

"Master dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri ka yafe mini, abubuwan da na yi maka kwanan nan ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba, wallahi ni ba mara kunya ba ce, kawai na rasa ya zan yi da wasu abubuwan ne, damuwa tayi mini yawa, dan Allah ka yi haƙuri idan ka sakenin ma, ka yi haƙuri ka mayar da ni" tayi maganar cikin rauni.

Ya lumshe idanunsa ya ce "Bani wuri zan kunna hayaƙi"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri master, ka yafe wa 'yar madara ɓacin rai ne ba zan sake ba, na san ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri"

"Sai fa kin tafi, kin isheni ne kawai takura mini ki ke yi"

"Dan Allah ka yi haƙuri, na daina takura maka, har cincin na yi maka jiya, in kawo maka?"

"Eh ki kawo mini, sai fa kintafi"

"Da ka san abun da hakan ka iya haifar wa rayuwata, da baka sake ni ba, dan ka ga ina ta roƙonka shikenan, duk ranar da ka bari na bar rayuwarka na bar ta har abada lokacin da zaka so ka ganni da kuɗi ba zaka ganni ba".

"Eh na ji, kafin ki fara ɗaukar makami, gara mu rabu, ungo takardarki tafi da ita" yayi maganar yana danƙa mata takardar da ya warware. Ta rintse idanunta, tuni ta fara kuka, ta buɗe idanunta ta sauke a kan kyakkyawan rubutunsa, dan ganin saki nawa ya yi mata.

*Ba zan dawo da wuri ba, na bar kuÉ—i a kan katifata ki sai wani abun ki ci*

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, ta ce "Shi ne ka yi ta wahalar da ni? Dama ba sakina ka yi ba, ka sakani kuka?"

Hamma yayi, yayi shiru ta ce "A'uzibillah" duk gurbin da ya yi wani abu, yakamata ya yi addu'a bai yi ba, sai tayi masa.

Ta ce "Aishikenan amma dan Allah ka yi haƙuri abubuwan da na yi maka ka yafe mini"

"To, ki bani wuri zan sha abu"

Ta ce "To bani wayar da ka bani jiya" gefen katifarsa ya nuna mata, ta tashi ta É—aukkota a kwali.

Ta kalleshi ta ce "Yanzu dan Allah wannan ta wa ce master? To kai ina taka?" Ya nuna mata keypad É—in sa.

"Wallahi ko a mafarki ban taɓa tunanin riƙe waya ba, yaya saifu ya taɓa bani keypad mama ta ƙwace, Allah ya saka maka da alkhairi ya saka ka a aljanna, Allah ya nuna mini ranar da zaka daina shan komai, ka zama limami saboda salihancinka, Na gode master na gode sosai da sosai" tayi maganar tana tattaɓa wayar.

"To excuse me, ina son yin caji"

"To yi mana"

Ya ce "Ki fita ki bani wuri dai, kar ki sume mini yau bani da kuÉ—in zuwa asibiti"

Maƙale kafaɗa tayi, ta ce "Master, wai yaushe zaka kai ni na gaida mama ne? Da wurin hajiya ma?".

"Wace maman?"

"Mamanka mana, bamu taɓa zuwa ba, na san wadda na gani a gidanku ba ita ce mamanka ba"

"In ji wa?"

Jauhar ta ce "Babu uwar da zata zauna hankalinta a kwance, alhali an yi wa É—anta sharri an tsare shi".

"Mama ta mutu" ji tayi kamar ya soka mata mashi, ta kalleshi ta ce "Kai ma ka san pain É—in master? Ka girma da ita ka santa?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Jiki a sanyaye ta ce "Ni ban ma santa ba, ina yawan takura ƙwaƙwalwata, dan na tunota, da rayuwar da muka yi tare, amma bana iyawa, baba ne yake da hotonta, nayi-nayi ya bani, ya hanani, idan na shiga ɗakinsa zan gyara masa, sai na ɗauki hoton in yi ta kallo ina jin daɗi, duk da ina jin kewarta, ina son in san yaya take ya halinta yake, yadda su mama suke faɗa ne ko akasin haka? Kawai saboda Baba ya saka hoton a cikin wallet ɗin sa, ya ce zai kai a wanko wani ya saka a yi enlarging ɗin sa ya bani, mama ta ɗauki hoton ta yayyaga, ta watsar wallahi ji na yi kamar ta yaga zuciyata, bana riƙo idan an yi mini laifi mantawa nake yi, ana yawan cewa bani da zuciya amma haryanzu a raina, na kasa jin cewa na yafe wa mama abun da ta yi mini.
Da farko da na taso, na zata mama ce ta haife ni, daga baya na gane ba ita haife ni ba, sai na fara tunanin ko kawai faɗowa na yi ko tsinto ni aka yi, kowa yana da uwa ban da ni, wataƙila a haka aka haifeni, daga baya na yi tunanin ko kawai 'yar aiki ce ni, na zata 'yan aiki duk ba su da iyaye. Daga baya na gane baba ne babana, uwa ce bani da ita, sannu a hankali kuma na gane ina da uwa amma bata duniyar.
Sai dai ba na jin daɗin irin yadda su mama ke aibata mamana, duk da ba ta raye ban san ta ba, har suna cewa mayya ce ta taɓa kama su ma, amma baba yana faɗar cewa mamana mutuniyar kirki ce, irin halina ɗaya da ita, haka yaya saifu ma yana faɗa.
Mama ce mariƙiyata, na so in tashi kamar ita ce wadda ta haife ni, amma ƙiriƙiri sai ta nuna mini banbanci ba ita ta haife ni ba. Ta saka aka cire ni daga makarantar kuɗi, aka mayar da ni ta gwamnati wai ba na gane karatu ni daƙiƙiya ce, kuma ni babu mai kula da ni, ko koya mini assignment komai ni nake yi wa kaina gashi baba ba ya iya magana a kan abun da ake yi mini.
Ita kuma anty Zakiyya cin zali na zahiri, na daku a wurinta, duk ba wannan ba ni ya riga ya wuce, kawai haryanzu ina jin zafin yaga mini hoton uwata da mama tayi, da ƙazafin nan da suka yi mini, na fanɗarewa, na san zan yafe musu wataran amma ba yanzu ba.
Ina son in ga mutum yana hira da mamansa, ko suna wasa irin na ɗa da uwa, abun yana burgeni, ko mutum ya din ga gaya wa mamansa damuwarsa da daɗi master, wataƙila kai ka samu wannan damar ni kuwa ban samu ba, maybe da mamanka ta yi tsawon rai wannan rayuwar za ta zo maka da sauƙi". Tana gaya masa raɗaɗin abun da take ji a zuciyarta yana raguwa, duk da kuka take yi.

Ya ce "You are missing her?" Yayi maganar yana kallonta.

Ta jinjina masa kai ta ce "So badly"

"Ki yi mata addu'a" ta jinjina masa kai tana goge hawayenta, a take shi kuma ya tuna irin tasa rayuwar, duk da lokuta da dama idan ka haɗu da wanda ku ke da irin matsala ɗaya ku ka yi sharing ana samun releif, amma yanzu shi ba ya son doguwar magana idan ya fara ma gajiya zai yi, duk da kwanan nan jauhar na isarsa da saka shi magana, kuma muddin ya gaya mata shi nasa labarin, zata shiga damuwa dan haka ya ƙyaleta.
Chapter 79 · 0% Book details