Sashe 67
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai ka ce takaba take yi, duk ta fita hayyacinta, ba ta san wurin wa za ta nufa da maganar nan ba, kuma ba ta san ina hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin take ba ma, balle ta je, ba kuma ta san ta tambaya a gano wani abun, gashi ko gidan su Al'amin ɗin ma ba ta sani ba, balle ta je ta gaya musu, ko da wani abu da za ayi a kai.
Ta dudduba ta tattara ɗan kuɗin da take da shi, ta fita, ta samu mai napep ta tambaye shi idan ya san ina ne hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Ya ce mata ya sani, ya É—auke ta ya tafi da ita.
Ta din ga yawo a cikin hukumar, aka ce mata ba ya wurin, ba a kai shi ba, sai da ƙyar aka ce mata yana nan, amma ba zata ganshi ba, babu irin magiyar da ba ta yi ba, amma suka hanata ganinsa, ƙarshe sai gida ta koma a matuƙar galabaice.
Ta rama salollin da suke kanta, ta din ga addu'a da fatan Ubangiji Allah ya fitar da shi lafiya, da ta san abun da zai faru kenan, da ba ta karɓi abun da ba ta san ko menene ba ta ajiye masa.
Ɗaya maƙwabciyar ta ta wasila, wadda mijinta ya taɓa raka su wurin mai chemist ta shigo gidan.
Ta ce "Jauhar yaya ake ciki, kin same shi kuwa, kin je wurin 'yan sandan?"
Ta ce "Eh na je, ba su bari na ganshi ba"
"Kuma ba su gaya miki abun da yayi suka kama shi ba?" Ta jinjina mata kai alamar eh, wasu hawaye masu ciwo suna zubo mata.
"Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki jauhar, in sha Allah komai zai wuce kamar ba ayi ba, kuma in sha Allah zai fito"
Ta ce "To Allah ya sa".
Yau ma haka ta kwana salloli, da kai wa Allah kukanta, da fatan Allah ya saka mijinta yana lafiya ya kuɓutar da shi.
Da safe ta sai ƙosai da buredi, ta dafa tea, ta kuma wanke ƙafa ta koma wurin nan, amma suka sake ce mata ba za ta ganshi ba, tayi magiyar har ta gaji, ta basu abincin ta ce su bashi.
Ta koma harabar wurin, ta nemi wuri ta zauna, ta rasa abun da yake yi mata daÉ—i, rabonta da abinci tun a jiya, gaba É—aya tunanin halin da Al'amin yake ciki, da wanda zai shiga a nan gaba ya dame ta, ta gaji da zama ta tashi ta nufi gida.
ÆŠakinsa da suka shiga duk suka watsar da kaya ta shiga, dan damuwa ba ta bari ta shiga ta gyara ba.
Duk sun watsar da komai na É—akin, ta tattare masa kayan, tana cikin gyarawa ta gano wayarsa, ta É—auka tana duddubawa sai ta ga tarin kiran walid da liti, cikin hanzari ta kira lambar walid.
"Ya ne maza? Tun shekaranjiya ban sake jin ɗuriyarka ba, na zo gidanka ba kowa ka kuma ƙi ɗaga waya".
"Assalamu alaikum" tayi masa sallama.
Ya ce "Ahh madam ke ce ashe? Ya ake ciki yana ina?"
Muryarta na rawa ta ce "Shekaranjiya da daddare jami'an tsaro sun zo sun tafi da shi"
"Kamar yaya? Me yayi?".
"Abu aka kawo aka ce na ajiye masa, su kuma suka zo da daddare suka ga kayan a leda, suka tafi da shi na je sun hanani ganinsa" tayi maganar cikin kuka.
Walid ya ce "Ya isa haka yi shiru, bari na zo gidan gani nan"
Sai ta É—an ji sanyi a ranta, tamkar yana zuwa zai fito mata da Al'amin É—in.
Kusan awa É—aya da rabi, ta ji ana knocking gate.
Da sauri ta tashi ta je ta buɗe, liti ta gani da Walid, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe su.
Walid ya amsa ya ce "Ya aka yi, meyafaru?"
"Yadda dai na gaya maka, wani ne ya kawo wata leda ya ce a ajiye masa, na manta ban nuna masa ba, kawai suka zo cikin dare suka tafi da shi, naje na je hukumar sun hana ni ganinsa"
Liti ya ce "Ki yi haƙuri, ki daina kukan haka, kuma kin tabattar bai yi wani laifin ba?"
"Ni dai a iya sanina bana tunanin yayi wani abun, duk da ba tare muke yawo da shi ba, amma dai sun ce a kan kayan da suka gani a gidan nan ne"
Walid ya ce "Ki kwantar da hankalinki, in dai Viper ne, mutum ne mai sa'a koma menene zai fito, amma ki kwantar da hankalinki, yanzu idan muka je babu lallai su sauraremu, amma in sha Allah gobe in Allah ya kaimu da wuri zamu je mu ga yadda za ayi".
Ta ce "To shikenan na gode sosai, bari na kawo muku ruwa"
"Kar ki damu a ƙoshe muke, ki kwantar da hankalinki idan da wani abu ki kira lambata"
Ta ce "To na gode"
Ta rufe ƙofa suka tafi, liti ya ce "Ikon Allah"
"Menene?"
"Kawai rayuwar Mai zamani nake kalla, yadda yake gararambarsa da kamar babu mai so, idan muka faÉ—a cakwakiyarmu, iya mu muke warware kayarmu, babu wanda ya damu da mu, shi kalli Allah ya kawo masa mai kula da shi".
"Haka ne, amma tausayi ta bani wallahi, yarinya ce sosai. Yana ta buyagi da rashin mutunci an yi masa aure, amma sai da ya mari madaki saboda ya tankata".
Liti ya kwashe da dariya ya ce "Kai mace fa aka ce maka, na raba ka"
Walid ya kwashe da dariya ya ce "A ƙi faɗinsa, da madaki ya ce ya kashe ta, mazewa yayi ba zai motsa ba, wai ba shi ya aiketa ba, amma ka ga wasu jijiyoyi da suka tashi a goshinsa, ga wani gumi da yake a iya karan hancinsa, bai san yana wasu abubuwan ba" suka sake kwashewa da dariya.
Liti ya saka su guduma É—an gidan mai unguwa, su din ga kaiwa sun komowa, suna É—an zagaywa a layin gidan viper, idan suka ga wani abu da ba su yadda da shi ba, su sanar masa.
Suka cigaba da kaiwa suna komowa a hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, amma su ma ba su samu ganin Viper ba, suka ce sai dai idan sun kai shi wurin jami'an tsaro su je can su ganshi.
Hankalin Jauhar ya ƙara mummunan tashi, ta rasa in da za ta saka ranta ta ji daɗi.
Ta sake amfani da wayarta, ta kira walid a waya, da yake sun ce kar ta sake zuwa hukumar, ta bari za su din ga zuwa su.
Ta duba wayar kaf, babu sunan wani mutumin kirki a ciki, balle tayi tunanin akwai lambar wani ɗan gidansu, ta kira duk sai sunayen su Liti da ire-iren su.
Sai kuma ta fara tunanin ko ba shi da kowa ne? Amma da ba shi da kowa ai ba zata ga kakarsa ba, kuma an nuna mata Rahila ranar da aka yi bikinsu Anty Zakiyya ta ce mata wai babarsa ce, amma tana tantama tun da aka yi auren, bai taɓa kai ta gidansu ba, kuma babu wani wanda ya zo daga gidan.
Walid suka Kuma dawowa suna rarrashin ta, a kan suna ta ƙoƙarin ganin ya fito, ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah to ina ne gidansu, yakamata ace sun sani"
Walid ya ce "Taɓ ke 'yan gidan na su da suna ta tashi, da baki gansu ba, ki manta da maganar su kawai ki cigaba da addu'a".
Ta ce "Amma kamar yakamata a gaya musu halin da yake ciki, ko ba za su yi komai a kai ba".
Walid zai yi magana, liti ya ce "Bari na kwatanta miki gidan na su" yayi mata kwatance sannan suka yi mata sallama suka tafi.
Liti ya ce "A irin wannan yanayin da take ciki, idan ba ka kwatanta ba sai ta tsaneka ai, idan ta je ta ganewa idonta shikenan"
"Haka ne, amma ka san wannan matsiyaciyar matar gidan na su ba mutunci gareta ba, kar ta ƙara mata zafi". Suka cigaba da tattaunawa.
Kusan kwanaki bakwai da kama Al'amin, idan ka ga jauhar sai ka ce tayi jinyar shekaru, duk ta ƙare ta fita hayyacinta.
'yan sana'oin ma ba ta iyawa, saboda tunani da damuwa.
Liti ya zo da safe, tana falo tana karatun Alkur'ani, ta ga kiran waya a wayar Viper, ta tashi ta fita ya ce "Sako hijjabinki mu je, sun bawa 'yan sanda shi, idan Allah ya taimake mu, wataƙila mu ganshi" cikin tsananin zumuɗi, ta yafo mayafinta, ta rufe gidan suka tafi.
Sai dai da suka je ɗin ma, tsugono ba ta ƙare ba, dan sun fi ƙarfin awa biyu, walid da liti suna safa da marwa, da faɗi tashin su ga Al'amin, Jauhar addu'a kawai take yi, tun da ta ga haka ta san lamarin ba ƙarami ba ne.
Da ƙyar aka ce za su ganshi, aka tafi da wasu wani wuri, suka jira a reception ɗin sashen.
Babu tsammani ta ɗaga kai ta ga yana tahowa, yana ɗingisa ƙafa, cikin hanzari ta miƙe tsaye ta zuba masa ido, kansa a ƙasa jami'an tsaro sun taso shi a gaba, su liti ma miƙewa suka yi tsaye, da ya kusantota sai ta ga jikinsa duk alamar duka, gefen fuskarsa a kumbure, haka wuyansa, shirt ɗin jikinsa tayi datti, duk busasshshen jini, take jikinta ya hau tsuma cikin tashin hankali.
Ya zo ya nemi wuri ya zauna kamar basarake, gabansa ta ƙarasa cikin tashin hankali muryarta na rawa ta ce "Master, dukanka suke yi haka?"
"Maza wai meyafaru ne? Me ka yi haka aka kawo ka nan?" Walid ya tambaye shi cikin damuwa.
Jauhar ta ce 'Yallaɓai, dan Allah ku sake shi, dan Allah ku yi haƙuri ba zai ƙara ba, wallahi kayan da ku ka gani a gidan lafina ne, bai san da su ba, dan Allah ku yi haƙuri ku sake shi"
Ɗaya daga cikin 'yan sandan ya kalleta ya ce "Yarinya yayanki ba ya ji, ba zamu sake shi ba, wanda aka kama da cocaine ki ke cewa a saki ba shi da laifi? For more than 7days ya amsa laifinsa yaƙi, ga kaya an kama shi da shi, yayi magana yaƙi kamar dutse"
Gaba É—aya sak suka yi suna kallon É—an sandan.