Sashe 48
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malam jamilu ya shiga matsananciyar damuwa, da samun labarin auren jauhar, dan har ga Allah yana matuƙar sonta, tsoron kar ta daina ganin mutuncinsa, ya sanya ya ɓoye mata.
Gidan jauhar da aka je jere, yana da girma, sai dai tsakar gidan tsurar ƙasa ce, cikin ɗakuna babu floor, sai dai an yi plasta a ɗakunan, falo ɗaya da ɗakuna uku a ciki, kowanne da banɗaki, sai kitchen a tsakar gida da tsakar gida mai girma.
An yi wearing É—in wutar lantarki, a gidan.
Sai buhunhuna, aka shimfiɗa a ƙasa, sannan cikin ɗakunan aka saka leda, falo kuma aka shimfiɗa carfet, saboda duk turɓaya ne.
Tagogin duk babu na kirki, sai kame-kame da faci.
Sai kujerunta, ƴan gida masu kyau, ɗaki ɗaya an saka furnitures, ɗaya kuma sai aka saka ƙatuwar katifa da wardrobe mai biyu, abun saka takalma. Duk da haka gidan ya yi kyau.
Amarya ta din ga fargaba da tunanin, waye mijin nan, da haryanzu za ace, bai taɓa ganinta ba, kuma ba ta taɓa ganinsa ba? Kuma ya amince da zai aureta.
Dogon gashinta baƙi, aka gyara mata shi, aka yi mata lalle ja da baƙi.
Haka kurum take tuna Alhaji mu'azzam, a haÉ—uwarsu biyu, yadda yake nuna yana sonta, ba ta son ya zai ji ba, idan aka ce masa an yi mata aure.
Kodayeke ita ba ta san dalilin fasawa da shi ba.
Su liti suka lura da shirun Al'amin ya ƙara yawa, duk da ba mai yawan magana ba ne dama, sai ya zauna yayi shiru yana zancen zuci.
Walid ya ce "Baaba, wai dan Allah kwanan nan meyake faruwa ne? Kamar ka na cikin damuwa" tabbas ba dan Walid ya tambaye shi yanzu ba, ba zai gaya masa ba.
Ya karkace ya ɗaukko invitation a aljihunsa, ya miƙa wa walid.
Wani irin ihu walid yayi, haɗi da kururwa, yayi katantanwa a ƙasa ya kuza uwar ashariya.
Sannan ya ce "Allah dai ya biya maza, dama zaka afkawa sabgar nan, ka yi mana shiru haka? Ba ka gaya mana ba, balle mu shirya saura kwana uku fa".
Sauran matasan da ke wurin suka miƙe suna tambayar Walid ko lafiya?.
Ya miƙa musu invitation ɗin, take suka hau shewa suma, suna dara.
Kawai ya dafe kansa, yayi shiru.
Walid ya ce "Wai tsaya, auren dole za ayi maka ne? Na ga baka murna, kuma shi ne ba ka taɓa kai mu ehhh, mun gaisa da antyn namu ba, iya wuya mun samu mai dafa mana abinci"
"Walid, Abbu ne ya shirya komai, ni ko ganinta ban taɓa yi ba, kuma ba na fatan na ganta, kuma ba kowa ne ya shirya wannan abun ba, sai wannan shaiɗaniyar matar ƴar haramun, ya ce umarni yake bani ba shawara ba, ni kuma na yanke guduwa zan yi, ba abun da zai haɗani rayuwa da wata mace, ba za a mayar da ni nusari ba, kalli yadda mace ta yi silar rushewar farincikin rayuwata gaba ɗaya"
Walid ya zauna kusa da shi ya ce "A'a maza, duk lalacewar naka naka ne, kai ka san albarkar dattijan ke riƙe da mu, ka daina kallon abun da yake yi maka na rashin jin daɗi, idan yayi maka baki ƙara watsewa zaka yi.
Duk da lokaci ya ƙure, dole ayi celebration, zamu gayyaci gayu a sha shayi a babbaka hayaƙi, abun farin ciki ya same mu" ya ƙarasa maganar suna shewa, ban da Al'amin da zuciyarsa kamar ta yi bindiga.
Hatta kayan da Al'amin zai saka na aure, sai da Abbu ya saya wa Al'amin, dan ko ganinsa bai sake yi ba, sai dai ya fita yawon neman sa.
Ƙarfe goma na dare, su Walid suka shirya party, aka dafa shayi aka raba lemuka, da kayan shaye-shaye.
Gogan yana gefe, yana zancen zuci, har ga Allah so yake ya gudu, amma ya san ya gudu alaƙarsa da Abbu za ta ƙara tsami. Kuma ya san ko ya gudu sai ya dawo, ba zai iya barin Abbun ba.
Tunani yake kowace mai tsautsayin da ba a so, ce haka, aka zaɓi a aura masa oho.
Ana tsaka da walimar hayaƙin, faɗan daba ya kaure, Al'amin kuma ya koma gefe ya ƙi magana, ƴan sanda suka yi wa wurin dirar mikiya, saboda rahoton da ƴan unguwar suka kai wa jami'an tsaro, ai kuwa suka kame su har da shi suka tafi da su ana gobe ɗaurin auren da bai san wacece matar ba.
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Abbu kuwa hatta É—inkin da Al'amin zai saka, ya yi masa, sai dai tun ranar da ya gaya masa, bai sake saka shi a idonsa ba.
Yana zaune yana ta mitar rashin ganinsa rahila ta ce "Ba fa zama zaka yi ba, tashi zaka yi ka je ka nemo shi duk in da yake, kar ya kunyataka a idon duniya.
Kana kallo yanzu na sauke mayafina daga gidansu amaryar, sun yi walima, duk sun gama shiri, na kai musu mukullin gida, har jere sun yi, fita zaka yi ka nemo shi ai"
Haka Abbu ya shuri takalama ya bazama, aka sanar da shi, su na can wata unguwar, suna walimar aurensa.
Ya bazama ya tafi, yana zuwa ya tarar da labarin Æ´an sanda sun kama su duk sun tafi da su.
Hankalin Abbu ya tashi, ya tafi division É—in nan unguwar aka masa a station É—in ma artabu aka yi da su, an kwashe su an kai su anti daba, ya ce wallahi ba za shi anti daba a daren nan ba saboda shi.
Da ya koma gida kuwa, rahila kamar ta ari baki saboda mitar, meyasa bai je ba a sake shi, kar ya basu kunya, ya ce idan za ta iya, ta tafi.
Jauhar kuwa su mama suka sakata a ɗaki, suna yi mata nasiha, fuskokinsu ɗauke da fara'a da jin daɗi, da nanata mata ba zasu zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba.
Ita dai ta damu sosai ta ga waye wannan mijin, da har suka ga ya dace da ita? Har a ranar idonta da kwanciyar jinin jifan da mama ta yi mata da takalmi.
Washegari ranar juma'a, za a É—aura aure a babban masallacin juma'a, amma Al'amin yana tsare.
Sha ɗayan rana, sai ga P.A ɗin Honorable indabo a anti daba da kansa, ya je belin Al'amin, wanda ya yi hakan ne, saboda aikinsa da yake son ya ƙarasa masa.
Suka din ga sara masa, suka gaisa ya gaya musu wurin wanda ya zo, yake son ya yi beli, da wanda ya aiko shi"
"Gaskiya malam yaron nan ba zai ci bulus ba, state CID zamu kai shi"
P.Aya ce "Ayi haƙuri, in anjima za a ɗaura masa aure, ko dan albarkacin wannan a sake shi mana"
"Wai ka san me ya yi kuwa?"
"Eh, an ce sun yi shaye-shaye sun tayar da tarzoma ko?".
"Ai da wannan ne da sauƙi, ya saba zuwa wurin nan a kan haka, jiya ƴan sandanmu sun kamo su, saboda sun sha tana gaya musu gaibu, a tsakiyar harabar station ya ɗaga ɗan sanda ya buga da ƙasa, saboda yana ganin ya isa, ya na ji da ƙarfi. Kuma ya din ga yi wa mutane wani shegen kallo kamar kumurci, zai gane kurensa, CID zamu kai shi"
Ana haka shugaban kula da sashen ya shigo da shi da wani matashin ɗan sanda, suka ƙame suna sara masa, ya kalli P.A ya ce "Lafiya kuwa?".
Suka gaisa sannan ya ce "Honorable ne dai ya kuma aikoni ayi ban baki, a saki Mai dogon zamani "
"Ba su gaya maka laifin da yayi ba? Jami'inmu fa ya daka, ba ya ji yaron nan ko kaÉ—an"
"Sun gaya mini, amma kamar yadda aka saba, honorable ya bayar da saƙo"
Ya numfasa ya ce "A fito da shi da sauran yaran da ku ka kama" aka buɗe Al'amin, da yaransa, ya fito yana ɗan jirga ƙafarsa a hankali, saboda taron dangin da suka yi masa jiya, suka yi masa dukan tsiya, daga jami'in ya tankaɗa ƙeyarsa, ya waiwayo a fusace ya saka ƙafa ya kwashe shi a wurin.
Daga shugaban, har PA É—in babu wanda ya kalla, ya kama hanyar ficewa daga cikin station É—in.
Ya girgiza kai ya ce "VIPER kenan, Allah ya shirya".
PA ya ce "Viper kuma?"
"Eh sunansa kenan a gidan nan, sunan da suka saka masa kenan, ban san sau adadin da muka kama shi ba, ban taɓa ganin mutum mai bala'in taurin kansa ba, mu daka mu daka wallahi ko gezau ba ya yi, ga wani sheɗanin kallo da yake yi wa mutane, kai ka ce kumurci ne zai kai sara, shiyasa nake yi masa sha'awar hakar tsaro, yana da girma da kwarjini na gaske, amma shi ba a saka shi ba a hana shi".
P.A yayi murmushi ya ce "Ai tun da ka ga honorable ya riƙe masa wuta, ba ya wasa da lamarin sa, kai ka san ba ƙaramin mara ji ba ne".
"Eh ai ku ne ke goya musu baya"
"Ai sabgar tamu ce dole sai da su".
Kafin PA ya gama sallamar su ya fito, tuni su Viper sun ɓace.
Har gida walid ya je ya sanar da Abbu, an sako su, amma yayi yayi da shi, ya taho gida yayi shirin ɗaurin auren yaƙi.
Abbu ya bi walid, har in da Al'amin yake, ya mimmiƙe yana bacci, jikinsa duk shaidar dukan da ya sha a station.
Maganar duniya Abbu yayi, amma yayi burus ya ƙi tashi, sai da ya cire takalmi ya hau ƙwala masa, sannan ya tashi da ƙyar yana muzurai, Abbu ya tasa shi a gaba zuwa gida.
Ba ƙaramin kyau manyan kayan suka yi masa ba, yayi wani irin kyau na mussaman, kwarjinin da Allah ya yi masa ya fito sosai da sosai.
Bayan sallar juma'a aka É—aura masa aure, bayan an saukko daga masallaci, babu wanda ya sake ganinsa.
Jauhar kuwa gabanta sai tsananta faɗuwa yake yi, ƴan ƙawayenta na makaranta, suna ta tsokanarta, suna yi mata raha, amma ta kasa sakewa.