Sashe 91
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk wani sirri na dodo, babu wanda Al'amin bai sani ba, kallon abu dodo yayi Al'amin ya san me yake nufi.
Kai tsaye ya kan tura Al'amin wurin indabo, a lokacin yana fafutukar neman kujerar ɗan majalisa, sai dai wasu lokutan baya son dodo ya aika masa Al'amin, dan idan yayi masa abun da bai yi masa ba, tafiyar sa yake ya ƙyale shi, ba ya jure cin zarafi ko wulaƙanci, komai ƙanƙantarsa, ya yaɓawa indabo baƙar magana ya ƙara gaba, duk ba abu ne mai wahala a wurin Al'amin ba, Indabo ya kai wa dodo ƙarar Al'amin.
Amma ya ce "Ina nema masa afuwa, ka riƙe Al'amin yaro ne mai amana, kuma duk cikin yarana babu wanda zai iya yi maka aikin da ka ke so bayan shi, yaro ne mai amana sosai da sosai, kuma ba shi da surutu, hakazalika yayi hannun riga da tsoro.
Dodo ne ya nuna masa makamai kala-kala samfurin wuƙaƙe, da in da in ka sakawa mutum zaka kashe shi, da wanda za ka yi masa illa.
Dodo yana yawan faɗar, Son da yake yi wa Al'amin daga Allah ne, bai taɓa son abu sosai da yake jin sa a ransa kamar shi ba. Ya san son da yake yi masa, ba zai kai na ɗa da uba ba, dan haka ya din ga mamakin yadda aka yi, mahaifin Al'amin ya wofantar da shi, duk da soyayya irin ta ɗa da uba.
Ba yadda bai yi da Al'amin ya ɗora karatu ba ya ƙi.
Ya ce "Aminullahi, harakar daba da shaye-shaye ba abune da nake yi maka fatan ka É—ore a kai ba, yakamata ka koma makaranta.
Al'amin ya ce "Ni ma ba na fatan na É—ore, ina É—aukar fansar abun da madaki yayi mini zan bar daba".
Ya dafa kafaɗarsa ya ce "Ina maka fatan hakan, sai dai haryanzu ba ka kai ƙarfin da zaka tunkari yaron nan ba, dan kuwa shi har da tsafi yake yi, kai kuma na san komai za a yi maka, ba zaka yi tsafi ba, amma ba a shiga dawa dan ƙarya, ko na kare kai, zan nema maka".
Duk da an É—auki lokaci, yaran madaki ba su shiga unguwar su Al'amin ba, sai rana tsaka, suka shigo unguwar neman faÉ—a, a karon farko Al'amin ya É—auki makami, jikinsa na wata irin tsuma, zuciyarsa na tafasa, wanda hakan ya faru ne a sakamakon abubuwan da yake ta'amalli da su.
Dan shaye-shaye nasa, kala-kala ne, kowanne akwai lokacin amfaninsa. Idan wani aiki yake son yi, ba ya son gajiya da wuri, sai ya banki wiwi sai ya daɗe yana abun da yake so, ba tare da ya gaji ba. Idan kuwa rashin mutunci yake son yi, haka zai yi mata haɗe-haɗe na mussaman, haka ma idan so yake ya bugu. Bai fiye ta'amalli da ƙwaya sosai ba, ya fi ƙarfi ga wiwin.
Ya je ya samu yaran, kan mai uwa da wabi, yayi musu ɓarna, sannan ya taka har dabar madakin, ya yi masa warning, "Ka gargaɗai karnukanka, a kan shigar mini area su nemi faɗa, idan ba haka ba, kan babban karen zan zo, na yi masa takunkumi, yadda haushi ma sai ya gagare shi"
Madaki tun da dodo ya sanya ya bawa Al'amin haƙuri, ba su sake arangama ba, kusan shekara biyu, sai a wannan lokacin, sai da gabansa ya faɗi, saboda yadda kamannin Al'amin suka juye, ƙarara alamun shaye-shaye suka bayyana a tare da shi, yadda ya sake zuwar masa kai tsaye ba tsoro ko fargaba, ya sanya shi gane kuskuren da ya yi na barin Al'amin a raye.
Tun da Al'amin yake tare da dodo, bai taɓa rashin kuɗi ba, kuɗi yake kamawa manya da ƙanana, kuma bai taɓa ci wa dodo amana ba.
Har a cikin ma'aikata, ana samun ɓata gari waɗanda suke sayar wa dodo kayan maye, idan sun kama, duk wani salo na yadda ake sayar da kayan, ba tare da an gane ba, Al'amin ya goge, haka idan kana ta'amalli da su, kallo ɗaya zai yi maka ya gane.
Yan kwamutin unguwa, suka kai ƙarar Al'amin wurin hukuma, a kan yana tayar musu da tarzoma, ba tare da la'akari da yaran da suke rashin jin tun kafin ya fara ba.
Dodo ya je ya samu shugaban 'yan vigilant, ya ce masa "Wallahi duk wanda ya sake ɗaukar ƙafa, ya kai ƙarar Aminullahi sai ya ci ubansa, lokacin da aka kashe ɗan uwansa ku nawa ku ka tashi ku ka je wurin jami'an tsaro domin ganin an ƙwatarwa yaron hakkinsa, saboda ba yaranku aka kashe ba. Lokacin da yake ragaita ba shi da sana'a, mutum nawa ne suka mayar da shi makaranta? Ko suka bashi sana'a, dan mahaifinsa ya wofantar da shi, kuna 'yan unguwa ba ku ga dacewar ku nusar da shi kuskuren sa ba? Ai duk society da suka yi watsi da yaran su irin su Aminullahi muna nan muna jiran su, mu zamu karɓe su, mu mayar da su abun da ya dace. Gargaɗi nake yi, ni dai an san ba zan kamu ba, to haka Al'amin ma, ko bayan raina, ina da masu fito mini da shi idan ya shiga cakwakiya. Ku shirya Al'amin bai fara yi muku rashin ji ba tukuna"
Ƴan unguwa suka rasa abun yi, yaransu da suke ƙanan rashin ji, suka fara bin Al'amin, yana ba su kayan wiwi suna sayarwa, yana ba su kuɗi, dama gashi da kyauta kuma ba shi da baƙin ciki.
Duk yaran dodo, suna shakkar Al'amin, ko dan saboda masifar dodo idan aka taɓa shi, dama Al'amin ya fi yin faɗa da Walid, dodo ya kan ce masa Mai laya, ka kiyayi mai zamanin nan, idan ka ƙure shi, ba zan saka baki ba, idan ya tashi yi maka ɓarna ba. Su yi faɗa su yi daɗi.
Tafiyar gaggawa ta kama dodo, zuwa kudancin Najeriya, sai dai ya ce wa Al'amin ya zauna, ya kula masa da harƙallarsa ta kano, ba zai tafi da shi ba.
Abun da Al'amin bai taɓa yi ba, sai a wannan karon ya ce "Meyasa ba zaka tafi da ni ba?"
"Aminullahi, tafiya ce mai hatsari, ka kula mana da harƙallarmu, sannan kar ka manta rules ɗin, a tafiyarmu babu BODMAS, idan ka ji wuta, ka wargaza komai ka ɓace"
Al'amin ya jinjina kai ya ce "Allah ya taimaki sarki babban dodo"
"Na gode, Allah ya ja zamaninka, zuwa in da ba ka zata ba, a cigaba da riƙe amana Aminullahi" haka nan Al'amin ya ji baya son dodo ya tafi.
Kwana uku da tafiyar Dodo, suna zazzaune, suna shan sigari, aka jefo wata jaka ta katanga.
Walid ya É—aukko jakar, wasu daga cikin yaran wurin, suka fita da gudun tsiya, suna neman wanda ya jefo jakar, ba su ga wanda ya jefo ba.
Al'amin ya ja jakar ya buÉ—e, kawai yayi tozali da kayan dodo a ciki, face-face da jini, har da takalminsa.
Cikin ƙaraji Al'amin ya ce "Nooooo" ya tashi jikinsa yana tsuma ya girgiza kai ya ce "Impossible, ba zai yiwu ba, sarki yana raye, raina mana hankali kawai ake yi"
Walid ya riƙe Al'amin ya ce "Al'amin ka nutsu mana, musulmai ne mu, idan ba a kashe sarki ba, babu yadda za ayi a ciro kayans jina-jina a kawo mana".
Al'amin ya fara neman ya fita hayyacinsa, Walid suka danne shi, suka shaƙa masa wani abu, jikinsa ya saki ya hau bacci.
Al'amin ya razana, ya shiga tashin hankali, ya É—imauce sosai da sosai, da mutuwar dodo, ba zai manta gudunmuwar da ya bashi ba, duk da ba ta arziki ba ce ba, Al'amin kamar zai zare.
Duk wata hanya da zai bi ya gano wanda ya kashe dodo, ya rasa, damuwa ta ƙara yi masa yawa.
Ya ɗaukko makaman da ya saka aka ƙera masa, sweazland, Russia da kuma iraƙi, ya zuba musu ido, bai taɓa zaton ya shaƙu da shi haka ba.
Mussman madaki ya zo ya sami Al'amin, yana ƙyaƙyata masa dariya, wai garkuwar da fake a bayanta, an samu wani gwanin saitin ya rusata, yanzu zai koma Al'amin ɗin sa matsoraci na ainihi.
Sai dai cikin sa'a, Al'amin yana tare da sweazland, dan haka madaki ya fara yi wa rauni da ita ya ce "Dan an fasa garkuwata, ba ya nufin zaka cim mini, *Ƙarfen cikin wuta nake* na fi ƙarfin ɗauka da hannu, ko da mariƙin roba, daga yau ka rubuta ka ajiye, ɗaya ya riski ajalinsa ne kawai zai kawo ƙarshen gabata da kai".
Madaki ya kalli cinyarsa da ke jini ya ce "Meyasa ba ka kawo ƙarshen gabar yanzu ba, ka kashe ni?"
"Saboda na fika sanin waye kai, akwai lokacin da ya dace da hakan".
Yaran dodo, sun so Al'amin ya gaji harƙallar dodo, ba ita ba har manyan hada-hadarsa da manyan mutane. Amma Al'amin yaƙi, ya ce baya buƙatar duk wani abu da zai din ga tuna masa da dodo, kuma zai yi abun da zai Allah zai gafarta masa, ba ɗorar da laifukansa a bayan ƙasa ba.
Da yawa sun so su ya basu sirrikan dodo, su cigaba da sana'arsa, amma Al'amin ya ƙi, ƙarshe ma suka bar wannan gidan gaba ɗaya, ya je ya kafa masa sansanin.
Walid suna zuwa da Al'amin duba mahaifiyarsa, da ciwon Cancer ya kama, aka kwantar da ita a asibiti, kullum cikin neman jini ake, duk wani kuɗi na Al'amin, sai da ya ƙare a wurin kula da mahaifiyar Walid.
Liti dama shi isaknci ne da abokai, suka saka ya lalace, dan har waje babansa ya kai shi yin karatu, bai koyo komai ba sai shashanci ya dawo.
Kasancewar jinin Al'amin da na babar Walid iri É—aya ne, ya bayar da jininsa sosai an saka mata, kullum cikin Kwantar wa da Walid hankali yake, tare da bashi tabbacin zata warke.
Har zariya suke kaita Asibiti gashi, amma cikin ikon Allah ta koma ga Allah, abun nan da Al'amin ya yi wa walid, ya sanya ya sanya duk abun da zai yi masa baya fushi da shi, ko yayi sai ya huce.
Suka koma ƙaramar harƙallar sayar da wiwi, idan kuma aikin ƙarfi ya samu su yi.