← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 95

Sashe 57

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ai ba zamu iya baki belinsa ba, kin ga mace ce ke, kuma yarinya, Allah ya sa ya daina abun da yake ko dan saboda ke, karɓi kuɗinki, ba zamu sake shi a kan wannan ɗan kuɗin ba, kotu ma zamu kai shi"

Kawai ta saka kuka, "Dan Allah ku yi haƙuri, ba zai ƙara ba dan Allah kar ku saka a kai shi prison"

Ɗaya daga 'yan sandan ya ce mata "Yi haƙuri ki daina kuka, da wasa yake yi miki, an zo belinsa ma, ke ki ke tayar da hankalinki, ko mun kama shi zamu sake shi"

Kasa daina kukan tayi, hannunta riƙe da kuɗin, wani ɗan sanda ne ya fito, da alama babba ne, bayansa kuma walid ne da Al'amin da wani mutum.

Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta zubawa fuskarsa ido, da take a É—aure babu walwala.

Walid ya ce "Kai Viper, wannan ce yarinyar da na tarar a gidanka, tayi mini rashin mutunci"

"Wannan fa me aka yi mata take kuka?"

"Sir, matar Viper ce" ya kalleta ya ce "Hajiya me aka yi miki ki ke kuka?".

"Ce mini suka yi na kawo dubu hamsin za a sake shi, na kawo kuma suka ce mini wai kotu za su kai shi" ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka cike da yarinta.

Ya kalli 'yan sandan ya ce "Waye ya ce ta kawo dubu hamsin"

"Sorry sir, dan ta daina zuwa aka gaya mata haka"

Nan ya hau yi musu faɗa, suka din ga bayar da haƙuri, Al'amin kamar bai santa ba, yayi gaba. Da sauri ta bi bayansa, tana ta yi masa magana yayi shiru.

Walid ya ce "Haba mai dogon zamani, ka tsaya ka saurareta mana"

A fusace ya waiwayo ya hau ta da masifa "Ban ce miki kar ki sake zuwa wurin nan ba? Kin san suwaye ake kawowa wurin nan? Mutuncinki ne a ganki a nan?" Sai da ta ja da baya a tsorace ta rufe fuskarta, saboda razana da masifar da yake yi mata.

"Wai Aminu meyasa ka ke yin haka? Da uban waye ya damu da kai, yake ta taka? Macen kenan haka zuciyarsu take, ko dan matar gidanku ba ta da kirki kowa ma haka yake?" Tsaki ya yi yayi gaba.

Walid ya ce "Yi haƙuri mu je, rabu da shi ya ƙarata, kar ki sake tayar da hankalinki saboda shi" suka tari a daidaita sahu suka tafi gida.

Da suka je gida, ta shiga gidan ta bar shi da Walid.

"Aminu, dan girman Allah ka rage jaraba, kalli yadda duk ta rikice saboda kai, kar ka yi wasa da damar da ka samu, ka saka ta tsaneka dan Allah"

Ya tsaya ya ƙarewa ƙofar gidan malam lawan kallo, yayi ƙwafa ya shiga gidan, ba tare da ya tanka Walid ba.

Jiki na rawa ba tare da ta yi fushi ba, ta kawo masa tea da buredi.

Ya gama baccinsa ya tashi, ya yi wanka, ya gama ya ga ta kafa masa ƙusar rataye soso a banɗakin, har zai rataye yayi tsaki ya yar da soson a kan sabulun ya fito.

Ya canza kayansa ya fito falo, Satar kallonsa take yi, kamar ya ƙara kyau, kwana biyun da ya yi a tsare ba ya shan komai, kamar ya yi kyau sosai. Sai murna take yi ya dawo gida.

"Ke!" Ta É—ago ta kalleshi.

"Meye sunanki ne?"

"Jauhar"

Ya kalleta ya ce "Me? Angela?"

Murmushi ta yi ta ce "Angela kamar wata mage,  sunana Jauhar"

Guntun tsaki ya yi ya ce "A saka muku normal suna, sai dai a saka ƙaƙale-ƙaƙale da iyayi, ni ba zan iya ba"

"To ka kirani da fatimata fatima zahra" wani irin zirrrr ya ji a jikinsa, fatima zahra, sunan mace mai girma da daraja a idonsa, Ummansa abar ƙaunarsa, duk da ba ta duniyar, amma idan ya ji sunan har wata tsuma yake yi.

Ya maze ya ƙarewa falon kallo, ya fita tsakar har zai wuce ya kalli kitchen ɗin ta sannna ya ce "Zo nan"

Ta fito ta ce "Gani"

"Wa ki ka sayar wa carfet É—inki da kwanukanki?"

Gabanta ya yi wata irin mummunar faÉ—uwa, yaya aka yi ya gane ko ya sani? Sai ka ce aljani?

Ya ƙare mata kallo ya ce "Ina jinki, ya aka yi ki ka samu wannan kuɗin da ki ka kai? Ina kuma abubuwam da na tambayeki? Ki ka yi mini ƙarya kuma jikinki ya gaya miki"

Kamar munafuka, haka ta zayyane masa komai.

Bai ce mata komai ba, ya fita.

Sahura na tsakar gida, tana hira ita da wasu coustomominta, kawai ta ga wasu irin zaratan matasa su uku, a tsakiyar tsakar gida da manyan gorori kamar za su farauta.

Ta tashi ta ce "Lafiya malam? Me ku ka zo yi mini a gida. Wannan ai.... Haɗiye maganar tayi, da ya sako ƙafarsa cikin isa tsakar gidan.

Yana shigowa idonsa ya sauka a kan carfet É—in, a shimfiÉ—e a falonta.

Ya ce "Liti, ku naÉ—o mini carfet É—in nan"

Ta waro ido ta ce "Malam lafiya?" Walid ya zaro wuƙa ya ce "Ki ka kuma magana, sai kin ɗaware daga sararin nan yanzun nan" daga ita har sauran matan, suka hau tsuma.

Kamar abun banza, suka din ga yi mata cilli da kujeru, suka naÉ—o carfet.

Viper ya ce "Dubu sha biyu ki ka saya ko?" Ta jinjina masa kai.

Ya ce "Ɗaukko mini sauran kayan da ki ka karɓa a wurinta" jiki na tsuma ta shiga ta kwaso su.

Ta ajiye masa a tsakar gidan, ya ce "Ɓarauniyar zaune, daga yanzu ki san abun da zaki din ga saya, ban da a nutse na zo miki, sai na saka an zana miki awarwaro a hannu, yadda gobe ba zaki sake zalunci ba. Liti ba ta kuɗinta".

Liti ya zaro kuÉ—i zai bata, Al'amin ya ce "Wait, ta riga ta shimfiÉ—a a É—akinta, ka cire dubu uku a kai, sannan ka sake cire dubu biyu zan cika ku wanke mini carfet É—in ku kai mini gida.

Haka kuwa aka yi, suka cilla mata kuÉ—i, suka kwashe kaya suka tafi.

Jauhar ta na yi wa wasu stone work, dan kuwa matar ta fara kawo mata kayan tana yi, hakan yana É—ebe mata kewa.

Ba ta yi aune ba, ta ganshi a tsakiyar falo, hannunsa da kaya, ya dungurar mata da su a tsakiyar wurin ya ce "Daga yau, ko cokali ki ka kuma sayarwa, saboda ni sai na ɓata miki rai, fiye da yadda ki ke tunani"

Baki buɗe ta ce "Master, karɓowa ka yi, kuɗinta suna wurina fa, Allah zai kaman..."

"Na ba ta kuɗinta, ko tsintsiya ki ka sake sayarwa, zan gane kuma ranki sai ya ɓaci".

A hankali ta ce "Na shiga uku".

***
Matasa ne a ƙalla su biyar, dukkanin su, babu wanda ya gaza ko ya wuce shekaru ashirin da biyu, suna sanye da tufafi masu nuna datti, gashin kansu da yanayin fuskarsu kuwa, babu tambaya sun bayyanar da tsantsar rashin ji a tattare da su, sai bushe-bushe suke yi, suna shewa.

Wani matashin ne ya diro ta saman katanga, gaba É—aya suka nutsu, suna yi masa sannu da zuwa.

"Kai gayu akwai matsala wallahi" gaba É—aya suka tattara masa hankalinsu suna sauraren sa.

Ya ce "Kaii, wai ashe mai zamani ne ya tare a unguwar nan kusan sati biyu bamu sani ba?"

Ɗaya daga cikin su ya miƙe ya ce "Ƙarya ne wallahi, me yake yi mana a unguwa".

"Nustu, ni ma ban sani ba sai É—azu, mai unguwa na ji yana maganar, sai za su je police station, ko a sasanta ayi zaman lafiya da shi, ko ya bar unguwar nan".

ÆŠayan ya yada sigarin hannunsa ya tashi ya ce "Guduma gaskiya kar dagus É—in ka ya janyo mana matsala, ya san waye mai dogon zamani kuwa?".

"Guys mafita É—aya ce wallahi, kun san ba a sarki biyu a zamani É—aya ko?"

"Me ka ke nufi?"

Guduma ya ce "Dole É—aya ya bi É—aya"

"To waye zai bi wani?"

"Kwanciyar hankalinmu da nustuwarmu, shi ne mu yi mubayi'a, samunsa ma a unguwar nan wani security ne, zai sa a din ga jin tsoranmu"

Wani matashi ya ce "Ƙarya ne wallahi, babu wanda ya isa ya zo unguwarmu mu yi masa mubayi'a ba a isa ba".

"Kai Kwano, bari na yi maka wani lissafi, duk sarkin da ya zo garinka ba da ziyara ba, ya shafe awanni arba'in da takwas, a irin harƙallarmu, to ɗayan biyu, ko dai ɗaya ya bi ɗaya, ko kuma a yaƙi juna, a kama sarki ɗaya da mutanensa a matsayin ganimar yaƙi, mu rayu a matsayin bayinsa, harƙalar da Mai zamani yake yi, ta ci uban tamu, ba sa'anmu bane ba, mu yi abun da ya dace, idan kuma mu ka bari rigima ta ɓalle, wallahi a unguwar tamu, zamu rayu kamar bayi ne amma ku yi tunani".

Can Al'amin kuwa yana zaune a station, ga mai unguwar da yake da sauran mutanen unguwa.

Yana zaune yana kallonsu, suna ta ɓaɓatun gaskiya ya tashi ya bar musu unguwa, saboda bad record ɗin da suka samu, a kansa daga in da ya baro, kuma nan ma ya zo yana yi musu shaye-shaye kar ya ɓata musu yaran unguwa.

Suka yi suka gama, yayi shiru kamar mai zancen zuci, suka yi suka gama, D.P.O ya ce "Malam Aminu, ka ji abun da mutanen unguwar da ka tare suka ce, me za ka ce?" Sai da ya ja wasu seconds, sannan ya ɗaga kai, ya kalle su da jajayen idanunsa masu matuƙar kwarjini, duk suka yi shiru, suna sauraren sa, ya ce "Haryanzu ban ji an ce ga abun da na yi ba ai. Ba zan ce komai yanzu ba, gobe in Allah ya kaimu, mu haɗu a nan ƙarfe huɗu na yamma, zan faɗi abun da na yanke".

D.P.O ya ce "Ina fatan ba wata ɓarnar zaka yi ba?"

"Ba na sara sai an zo ramina" daga haka bai kuma cewa komai ba, ya tashi ya fice, ba tare da ya jira iznin hakan ba.
Chapter 57 · 0% Book details