← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 95

Sashe 50

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shiga yana ƙarewa gidan kallo, shi dai ya san gidan kango ne, amma yadda aka jera masa kaya, yayi kyau.

Yana shiga falon, bai bi ta kan ina amaryar take ba, ya tuntsurar da ƙullin kayansa ya haye kujera ya mimmiƙe kamar gawar sababi.

An fara kiraye-kirayen sallar asuba, ta shiga banÉ—akin cikin É—akin, tayi alwala ta din ga nafilfili, har aka yi sallar asuba.

Bayan ta idar tana cikin azkar, wani irin nannauyan bacci, ya kwashe ta a wurin.

Sai da gari ya yi haske, sannan ta farka, ta tashi tana salati, ta tashi tana ƙarewa ɗakin kallo. Yayi kyau sosai da sosai, duk ko fenti babu amma furnitures ɗin sun yi kyau.

Ta fita falon gabanta na faɗuwa, domin gaida mai gidan da no nemanta bai yi ba, sai dai ba ta gan shi ba, ta leƙa ɗaya ɗakin, amma baya nan, sai ghana must go a falo.

Ta fito tana ta lelleƙa gidan, abun ya burgeta, duk da ba ƙerarren gida bane, amma ta ji daɗin cewar gidanta ne ita ke da iko da shi, amma da ta tuna haryanzu ba ta yi ido huɗu da angon ba, sai gabanta ya faɗi, ta fara tunanin ko shi ma auren dolen aka yi masa da ita.

Tunawa ta yi, da 'yan dabar Unguwar su, sun ce idan suka kuma ganinta a unguwar su, sai sun sassarata. Gaba ɗaya ranta ya ƙara dugunzuma.

Ta zauna shiru a falo, tana ta jira, ko wani zai zo mata daga gida, amma shiru babu wanda ta gani, ga yunwa tana ji, dan wunin jiya ba abun da ta ci, gashi ta kwana ta wayi gari ba ta saka komai a cikinta ba.

Can kuwa, Rahila kuwa kamar ta taka rawa, ta rabu da ƙaya, Aminu ya bar mata gida, ta ƙara sakewa da ita da yaranta yadda take so, fargabar ta zata ragu sosai da sosai, ta san yanzu dole zai tattara ya bar unguwar ya ƙara gaba.

Dangin mahaifiyar Aminu da suka zo, daga can ƙauyen tofa, ta din ga wulaƙanta su, dan sai da ta yi wa Abbu masifar dan me za a gayyato su, sai dai a hakan gudunmuwar dubu ɗari biyu suka bawa Abbu na auren.
Ban da uban kayan abinci da suka taho da shi, suka ce a ƙara a kan na biki. Sai dai har suka yi kwana biyun, ko sau ɗaya ba su ga Al'amin ba, sai kwasar takaicin rahila, yadda take wulaƙanta su, tare da aibata shi, tana an mutu an bar mata riƙon masifa da tsiya.

Washegari da safe, waÉ—anda ba su je ganin gidan ba, suka ce za su je su ga gidansa, daga nan za su wuce su koma tofa. Da Abbu suka yi sallama, Rahila kuwa ko kallo ba su isheta ba.

Har wajen sha ɗaya da rabi na safe, jauhar na zaune na rarraba ido,  ta ji sallma a tsakar gidan.

Amsawa tayi, tana jiran ƙarasowar masu sallamar.

Mata ne wasu 'yan dattijai, da matasan 'yan mata.

Jauhar ta karɓe su hannu bibbiyu, suka shigo falon suka zazzauna, hannunsu da kaya.

Suka gaisa da jauhar, É—aya daga cikinsu ta ce "Tubarkallah, Aminullahi ya mori 'yar kyakykyawar yarinya Tubarkallah, ya sunanki?"

Jin abun da suka ce, ya sanya ta gane 'yan uwansa ne, ta ce "Jauhar"

Suka din ga maimaita sunan nata, suna cewa sunanta na 'yan birni.

"Ina Aminullahin ne? Tun da mu ka zo, bamu ganshi ba, gashi daga nan can gida zamu koma" cewat wata dattijuwar.

Jauhar ta ce "Ya fita"

"Ohh, ji soko, daga kawo masa amaryar jiya, har ya saka ƙafa ya fice, to Allah ya kyauta. Kin ganni ni kakarsa ce, ga yayar gyatuma tasa, nan duk 'yan uwan mahaifiyarsa ne, amma ba ya zuwa in da muke. Dan Allah kya ɗan din ga saita shi a hanya, ki yi ta haƙuri kin ji, Allah ya baku zaman lafiya"

Kunya ta saka jauhar kasa amsa musu.

Suka yi ta yi mata hira, amma ta kasa amsa musu, saboda nauyinsu da ta din ga ji, sai dai kakartasa mace ce mai barkwanci, suka ba ta kayan da suka zo da su, su tsintsiyar laushi da ta kwakwa, kaskon turaren wuta, kayan miya har da kuÉ—i.

Jauhar ta yi tayi musu godiya, sai dai ranta duk babu daɗi, ga baƙi amma babu abun da za ta basu.

Zuwa azahar, suka yi mata sallama suka tafi.

Har la'asar babu wanda ya sake zuwa, ta ji babu daÉ—i sosai, rashin ganin wani daga gidansu ko mutum É—aya.

Yaran maƙwabta suka ɗan shisshigo mata, shigowar ta su tayi mata daɗi, ta basu kuɗi, ta ce su sayo musu buredi.

Suka sayo, suka zauna, suka ci tare da su, ta ajiye wani da niyyar idan mai gidan ya zo ta bashi.

Mama kuwa bayan sun koma gida daga kai jauhar, duk 'yan biki sun watse, kowa tayi ta kanta.

Suka ƙule a ɗaki ita da zakiyya ta ce "Zakiyya duk da gidan yarinyar nan babu gyara, amma yayi kyau sosai da sosai"

"Eh ai hakan yayi, ma rage wani surutun, har ku ka taho kuwa kun ganshi ya je gidan shi angon?"

Mama ta ce "Ina fa, itakaɗai muka baro, sai wasu 'yan uwan babarsa, su ma na san ba zasu jima ba zasu tafi ba. Nifa sunansa kawai nake ji, ban taɓa ganin sa ba".

"Zaki ganshi ne, ba dai ya zama sirikinku ba? Ni na san shi, amma lokacin yana yaro, ai kin san daga baya suka dawo ƙofar na'isa da ba a nan suke ba, ni tsoro nake ji ma kar yaran nan su cigaba da kawo mana farmaki"

Mama ta ce "Babu abun da za su dawo su yi mana, mun yada ƙwallon mangwaro mun huta da ƙuda, yanzu menene abun yi?"

"Abun yi, shi ne mu jira dawowar wannan Alhajin, mu ga yadda za a ɓullowa lamarin ya haƙura gaba ɗaya da batun ta"
"Haka ne, to Allah ya dawo da shi lafiya, sai ayi ta ta ƙare, jauhar dai an aurar da ita, sai mu jira mu ga yaya zai kasance da namu 'ya'yan.

Gidan jauhar magariba na yi, yara suka watse suka bar ta itakaÉ—ai kamar tsohuwar mayya. Sai fitila ta kunna, ta saka mayafinta ta din ga korra sauro daga É—akunan, saboda yadda suke ambaliya kamar a barikin su.

Ta rurrufe ko ina, tana jiran ta ga ta ina ango zai shigo, amma shiru.

Har bacci ya kuma cin ƙarfinta ya kwashe ta.

Wunin ranar kuwa, Al'amin zarya ya din ga yi, sai da aka sakar masa yaransa da aka kama a unguwar su madaki, har suka sanar masa iƙrarin da 'yan unguwar da suka yi, na idan suka kuma ganinta a unguwar sai sun sassarata.

A ransa ya ce Allah ya ƙara, maganinsu kenan, da suka ga babu wanda ya dace su bawa 'yar su sai shi.

Tare da su ya wuni yana shaye-shaye, Walid ya na son ya yi masa magana, amma ya san yana yi za su yi faɗa, dan haka sai dare ya sake lallaɓa shi, daga can unguwar ya goya shi a babur ya kai shi gidansa na ɗorayi chiranci.

Sai dai kamar jiya, kafin gari ya yi haske, ya sake barin gidan, gashi ko brush ba ta da shi, ba ta da kayan girki, haka ta kuskure baki ta cinye biredin jiya, gashi ba ta son cigaba da taɓa kuɗin da aka bata, yakamata ta nuna masa kayan da aka bata, saboda 'yan uwan sa ne suka bata.

Ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan tudu ta zauna, tana tunanin yanzu haka za ta rayu, wanda ya ajiye ta baya ko ƙaunar ganinta, kwana na biyu kenan haryanzu ba ta ga kalarsa ba ma.
Tana son yin wanka da sauran buƙatu, amma ba hali, babu ruwa, ga rijiya a gidan amma babu guga, babu sauran kayan masarufi.

Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ya dawo da ita hayyacinta, ta tashi ta ɗaukko mayafi ta saka, ta buɗe a hankali.

Saifu ta gani a tsaye, hannunsa riƙe da kaya.

Ta washe baki ta ce "Yaya saifu" yayi murmushi ya ce "Na'am Waliyiyya"

Ta bashi hanya ta ce ya shigo, ta karɓi kayan hannunsa, suka shiga har falo.

Ya kalleta ya ce "Yaya babu wata matsala dai ko?"

Ta girgiza kai ta ce "Babu"

"Ina mijin naki yake?"

"Baya nan, ya su baba? Ya su mama?"

"Suna nan ƙalau, gida yaƙi kyau ba kya nan, duk 'yan matan nan an rasa wadda za ta yi aikin da ki ke yi" tayi shiru tana murmushi.

"Ga sauran kayanki na kawo miki, na harhaÉ—o da na É—akinki duk na kawo miki, muddin ki ga ya yi miki wani abu da baki gamsu ba, ki gudo gida kin ji ko?" Ta jinjina masa kai alamar to.

Ya ce "Kina buƙatar wani abun ne?"

Ta ce "A'a"

Ya miƙe ya ce "Na san ba zaki faɗa ba ai" ya shiga kitchen ɗin ta yana dubawa, babu alamar an dafa wani abu.

Ya É—auki gas É—in ta, ya fita da shi, ya yo mata refilling, ya yi mata sayayyar kayan shayi da 'yan kayan abinci, ya dawo ya kawo mata.

Ya ce "Ki yi haƙuri jauhar, bani da kuɗi, amma zan sake dawowa in sha Allah, kar ki yadda da wani haƙuri, na san zaman aure haƙuri ne, amma kar ki zauna ana zaluntarki, ko ya ce zai dake ki, zan sake dawowa in sha Allah kin ji ko" ta ɗaga masa kai alamar eh, ya sayo mata guga, ya janyo mata ruwa ya tara mata, ta din ga yi masa godiya suka yi sallama.

Bayan tafiyar sa, tayi wanka ta canza kaya, yaran maƙwabtanta da suka shgo, ta dafa musu taliya, suka ci ba ta gaza ba, ta ɗebarwa maigidan nasa ta ajiye.

Sai dai yaran da wuri suka tafi yau, ta samu wuri tana wanke-wanke, ta ji kamar an wuce ta bayanta.

Tashi ta yi a firgice, tana addu'a da tunanin ko gane-gane ta fara yi.

Sai dai ta ga takalmi a ƙofar falon, kasancewar gidan akwai gate, kuma akwai ƙaramar ƙofa, ƙofar a buɗe take.

Ta lallaɓa ta leƙa, ba ta ga kowa ba, ta shiga falon tana tambayar waye?.
Chapter 50 · 0% Book details