← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 95

Sashe 36

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya hawo kan gadon ya nufota, ta din ga ihu tana kiran sunan Allah, ta na yi masa magiyar ya ƙyaleta, ya mayar da ita gida.

Amma kamar ya kamo ƴar kaza, haka ya danƙota zai yi mata rashin mutunci, sai dai yana haɗa ta da jikinsa, ya ji kamar ana hura wuta a Jikinta, saboda zafin zazzaɓi, gashi sai wani irin ƙarni take yi, da warin man kaɗanya da take shafawa ya haɗe da ƙarnin koren sabulun da take wanka da wanki da shi.
Ba wannan ya fi damunsa ba, rashin saukar zazzaɓin jikinta ne bai so ba, dan ko a yanzu a galabaice take.

A ɓangaren ramma ma, warin giyar da yake yi, da ƙamshin turaren sa ya sanya ta fara yinƙurin amai, ba shiri ya cikata, ta sauka da gudu, ta tafi banɗakin da yake cikin ɗakin, ta din ga kwara aman, sai dai ruwa kawai take amayarwa, bayan shi babu komai a cikinta.

Ta gama aman tana ta sauke numfashi, ta lallaɓa ta fito, tana bin bango, sai dai ta tsaya cak tana kallon sa yadda ya zuba mata ido.

Cikin kuka ta haɗa hannayenta ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, ka mayar da ni in da ka ɗauko ni, hankalin mamana na san yana can a tashe, dan Allah ka yi mini rai ka yi haƙuri" ta ƙarasa maganar tana zubewa a kan gwiwoyinta tana bashi haƙuri".

Strip ɗin gwajin ciki ya ɗago da yake hannunsa, wanda ya gwada da jininta da ya ɗiba ɗazu ya ce "Ke ce mace ta farko da ta fara ɗaukar cikina, kin kafa tarihi, tun da ki ka ce ba za a zubar ba, nima na ji ya shiga raina, ina son abuna, zaki haife shi kafin na kashe ki, kuma ba zan kashe ki ba sai bayan kin haihu" ta yi shiru tana cigaba da zubar da hawaye, wai ita ce ɗauke da ɗan shege a cikinta, a wani keɓantaccen wuri tare da ɗan iska, saboda kawai ba su da kuɗi, sai yau ta ƙara tabattar da illar talauci.

Ya miƙe tsam daga kan gadon ya fice ya bar ta a ɗakin, ba tare da sanin makama ko abun yi ba.

Sumayya ce a office É—in manager, fuskarta É—auke da matsananciyar damuwa.
Ya kalleta ya ce "Sumayya yaya aka yi ne? Ko yayi miki wani abun ranar da ku ka yi program É—in?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"To menene? Na ga kin yi editing ma kin tura mini, komai yayi normal, na ce a saka idan lokaci yayi kin yi ƙoƙari sosai, ina ga program ɗin hannunki zai dawo gaba ɗaya"

Ta sauke numfashi ta ce "Sir"

Ya amsa da "Yes ma"

Sai kuma ta yi shiru.

"Ki gaya mini mana idan da wani abu" ta girgiza kai ta tashi ta fita.

Addu'a ya din ga yi a zuciyarsa, tare da fatan Allah ya sa ba wani abun indabo yayi mata ba, dan ya san halinsa sarai.

Nabila tana office É—in ta, tana aiki, barrister Habib ya buÉ—e ya shiga da sallama.

Miƙewa tayi tsaye ta ce "Sannu da zuwa, da ka kirawo ni ai"

Ya ƙarasa gaban teburinta ya ce "Babu damuwa, aikin da ki ka ba ni ne na yi"

Tayi murmushi ta ce "Taimakon da na nema dai aka yi mini"

Shi ma murmushin ya yi ya ce "Zan tura miki court ɗin da aka fara yi masa shari'a, da sunan wurin wanda za ki je ya binciko miki file ɗin, akwai dai wani abu a ɓoye".

Cikin sauri ta ce "Ok, ai daga nan ma kana tura mini sai na tafi"

Ya ce "Wait, ki tafi yanzu ba ki da aiki ne?"

"Ai na kusa kammalawa saura kaÉ—an ne"

Ya ce "shikenan, zan tura miki ta what's app, amma ki bi a hankali, fa kar ki je ki yi abun da ba shikenan ba"

"In sha Allah, na gode sosai"

Yana fita ta fara lissafi a ranta, tun kan viper ya je hannu, za ta bibiyi cases ɗin sa na baya, domin a shirye take da ta ƙalubalanci hukumar shari'a ciki har da alƙall da kuma hukumar gidan yari, kan sakin Viper ba tare da ƙa'ida ba, ta san ko ba ta yi nasara ba, za ta yi suna sosai.

Tattara jakarta ta yi, ta fita bayan da saƙon barrister Habib ya shiga wayarta.

Ba ta wani sha wahala ba zuwa kotun da ya bata adress É—in, tun da dama sananniyar magistrate court ce a kano.

Ofishin rijistra ta je, suka gaisa da mutanen wurin, sannan ta tambayi office É—in mutumin da barrister Habib ya gaya mata.

Aka yi mata iso, sannan ta gabatarwa da mutumin kanta, da wanda ya turo ta.

Ya karɓeta da mutuntawa sannan ya ce "Baiwar Allah, gaskiya ta in da ki ka biyo, babu yadda za ayi na kasa yi miki alfarma, amma riƙe file ɗin nan, tamkar saka hannu ne ki ɗaukko ƙarfen da yake cikin wuta ne, dan Allah kar ki je ki yi wani abu da bai kamata ba, tun kan ki zo aka yi waya, aka ce a baki idan kin zo"

Nabila ta ce "In sha Allah, babu wani abu da zan yi, ina É—an yi wani bincike ne kawai".

Ya ja ta suka tafi wani wuri a cikin kotun, suka shiga can wani office, da ba zaka ce akwai mutane a wurin ba, sai da suka shiga can ciki, suka iske wani mutum yana ta aiki a computer.

Suka gaisa, wanda ya rakota ya ce "Oga, ga baƙuwa mun yi, Barrister Habib ne ya aikota, shi kuma daga top oga, ya ce a kawo ta file ɗin Al'amin viper zaka ɗaukko mata"

Shiru mutumin yayi yana kallon ta sannan ya ce "Ya sunanki?"

"Nabila yusuf maitama"

"Me za ki yi da file É—in?"

Ta É—an rausayar da kai ta ce "Wani bincike nake yi ne"

Ya mayar da hankalin sa kan mutumin da ya rakota ya ce "Ka gaya mata illar da ke cikin hakan?"

"Na gaya mata, ko ma dai menene na gaya maka wanda ya ce a ba ta ai"

Yayi ajiyar zuciya yana cigaba da yi wa Nabila kallon tuhuma, ya tashi ya shiga wani wuri.

Ta kalli mutumin da ya rakota ta ce "Yallaɓai, meyasa file ɗin yake da hatsari har haka?"

Yayi murmushi ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Yana da alaƙa da rashin gaskiya"

Mutumin ya fito ɗauke da file ɗin, duk ya yi ƙura, hannu na rawa ta karɓa ta ja kujera ta zauna, ta fara dubawa.

Sannu a hankali ta din ga bin bayanan ciki, da binciken rahoton Æ´an sanda a kai, sai dai komai ba straight forward aka yi shi ba, gaba É—aya kanta ya kulle, ba ta fuskanci wani abun kirki a ciki ba.

"Amma sir, ina ƙarshen shari'ar, ai wannan ba a yanke hukunci ba, ranar ƙarshe da aka ɗaga shari'ar an ce sati uku za a sake zama, yanzu kusan shekara biyar, ba a sake rubuta komai ba"

Mutumin ya ce "Eh yadda ki ka gani a haka yake"

Cike da mamaki ta ce "Dan Allah wane alƙalin ne ya yi masa shari'ar?"

"Yana abuja" suka bata amsa a taƙaice.

"Wannan documentation É—in, sam ba a yi shi ma yadda za a fahimta ba, amma dan Allah....

Wanda ya É—auko mata File É—in ya ce "Mu fa babu abun da za mu iya sake gaya miki, ba wanda yake da damar zuwa wurin nan sai staff É—inmu, dan haka ki tashi ki tafi".

Ta miƙe tsaye ta ce "Na gode sosai"

Ta fito daga office ɗin tana mamaki, ta ja ta tsaya tana kallon office ɗin, a abun da ta fuskanta wuri ne da ake ɓoye files na musamman.

"Yayi kisan kai!" Ta faÉ—a a fili.

"Ba abun mamaki bane ba, da gani zai aikata abun da ya fi kisan kai, amma menene dalilin ajiye shi shekara biyar, ba ayi masa shari'a ba, an ɓoye file ɗin sa a wuri na musamman, ya shekara biyar a prison, kuma kwatsam an sake shi, babu document na wanke shi aka yi daga laifin ko kuwa, duk da an rubuta ya amsa laifin, amma wane hukuncin aka yanke masa? Wayyo Allah kaina zai fashe" ta yi maganar tana dafe kanta, da ya yi mata nauyi.

***
A tsaye yake a kanta yana ƙare mata kallo, yanayin yadda take a kwance ya tabbatar masa da salla ta yi.

Ruwan robar hannunsa ya fara zuba mata a Jikinta, hakan ya razanata ta tashi a gigice.
Ya watsa mata sabulu da soso a jiki ya ce "Ki tashi ki je ki yi wanka, ba na son ƙazanta, kar ki haifar mini ɗa mai dauɗa"

Ta yinƙura ta tashi da kyar, tana jiri, ga yunwa ga zazzaɓi ga kwana da ta yi amai, ta din ga bin bango, har ta isa banɗaki.

Ta daÉ—e a banÉ—akin tana kuka, sannan ta yi wankan ta fito, ta tarar da shi a kan gado a zaune yana danna waya.

Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Dalla cire wannan kayan, ƙazamar banza da wofi, har amai ki ka yi a jikin kayan amma ki ka mayar da su jikinki" kallonsa take yi, to tsirara yake son ta zauna?

Ya buÉ—e wardrobe É—in da ke É—akin, duk kayansa ne a ciki, ya jefa mata wata shirt, ya ce ta É—auka ta saka.

Banza ta yi masa, ta kawar da kanta gefe, wanda hakan ya hasala shi, yana zuwa gabanta ya kwasheta da mari, abunka da jiki babu ƙwari, take ta faɗi ƙasa, ta riƙe fuskarta.

"Ke kin isa ina magana ki yi mini banza, Æ´ar wahala mara amfani, É—auki ki saka kan na tattakaki"

Ramma ba ta ƙaunar duk da abun da zai taɓa lafiyar jikinta, haka ta zura rigar nan, ta zo mata har gwiwa, sai rufe jikinta take yi.

Ya danƙota, ya fita falo da ita.

A falon ya haɗa mata baƙin shayi, sai soyayyen dankali da ketchup ya ce ta ci.

Gaba É—aya a tsorace take, saboda kar ya kuma dukanta, haka ta din ga tsakura tana ci tana hawaye.

Ta gama ci, ya ɗaukko alluran zazzaɓi da yake yi mata yayi mata.
Chapter 36 · 0% Book details