Sashe 84
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saura sati guda salla, gidan jauhar mutane ne kawai ke shiga suna fita, masu mayafai, masu ɗinkuna da zata yi wa stone work, masu kitso da lalle, a haka kuma tana kasa kayanta, na shirin dutse, sarƙa abun hannu, jigida, ga kayan lemo, masu zuwa kitso suna yi mata ciniki. Ta zama very busy, idan yamma ta gabato, ga aikin abinci, sai dai garin Allah yana wayewa, ya fice ya bar gidan, saboda mutane.
Sai dai ana shan ruwa take sallamar kowa, ta ce sai gobe, za ta kula da mijinta.
Yana falo a zaune, ya gama shan ruwa ya kasa tashi, wata mata tayi sallama, tayi ta yi wa jauhar magiya, wai tana son ta turo yaran, ta wanke musu kai, tayi musu kitso, kowace yarinya É—ari da hamsin, su huÉ—u.
Jauhar ta ce "Haba Maman Nana, ki bani É—ari bibbiyu mana, ga wanke musu kai, ga kitso?"
"Taimakawa zaki yi jauhar, idan ki na son gobe mu kawo miki coustomers, kin san yadda garin yake, ubansu bai bani ko sisi ba, ni nake wahalata dan yaran su fito fes, ko hankici bai yi mana ba"
Jauhar ta ce "To shikenan, bari na sallami master, gobe in Allah ya kaimu akwai mutane sosai, turo su yanzu a wanke musu kan, in dafa ruwa a heater tun da da wuta, gobe in Allah ya kaimu da sassafe sai ayi kitson"
"Ke, na hana kitson, kwashi yaranki ki tafi wani wurin ayi miki" ta ji muryarsa a ƙofar falo.
Jauhar ta ce "Master meyasa?".
"Na hana kitson, duk wannan wahalar da ki ke wuni kina yi a ɗari da hamsin? Dama wuni ki ke wahalar banza, saboda aikin yi yayi miki ƙaranci? Get out malama kwashe yaranki ki fita, iyayen son banza".
Kamar jauhar ta yi kuka ta ce "Master dan Allah...
"Shhh" yayi maganar yana ɗora yatsansa a kan laɓɓansa.
Matar ta fita ta kalleshi kamar za ta yi kuka ya ce "Na ga aiki ne yayi miki ƙaranci, mu je ina da aikin da zan baki ni, ki zauna ki wuni kina wahala, a ɗari da hamsin, ina zaki kai kuɗi ne wai? Duk kin rame saboda kin saka azabar son kuɗi a ranki" Yayi maganar yana kallon ta, tana tsaye tana tura baki.
Ya fizgota gabansa ya ce ya kai hannunsa wuyanta ya ce "Wannan ƙashin na wuya da ki na shi? Duk kin yi wuri-wuri ga azumi ga wahala" da sauri ta ɗan kama jikinta, saboda unexpected ya saka hannunsa a wuyanta.
Maimakon ya sauke hannunsa, sai ya miƙar da hannunsa zuwa kan maƙogwaronta, ya fito da dogon harshen sa har wurin haɓarsa, ya lanƙwasa shi, sannan ya mayar cikin bakinsa ya ce "Na ga kina motsa baki, me zaki ce?"
Jauhar ta ce "Ai shikenan ka korar mini coustomer, kuma ka shaƙeni zaka kasheni ka huta. Kuma sai ka biyani kuɗin wanda ka korar mini, ɗari shida"
"Bana son ganin wannan ƙashin, kwana uku kawai na baki ya koma" yayi maganar yana sake shafa wuyanta. Riƙe hannunsa tayi, tana kallon idonsa, da abun da yake yi matan ko a jikinsa.
Ɗan muzurunta ne, ya yo tsalle yana yakushin ƙafar Al'amin, saboda riƙe wuyan jauhar da ya yi, yana kuka.
Al'amin ya kalli muzurun, yayi cilli da shi, ya ce "Na kusa mayar da abun nan in da na ɗauko shi, ya fiye zaƙewa, zo ki yi mini aikina"
Ta biyo shi tana mitar ya korar mata coustomer's , ya nuna mata kujera 3seater ya ce ta zauna.
Ta nemi wuri ta zauna, ya kwanta ya miƙe ƙafafuwan sa a kan cinyarta ya kaɗa mata yatsunsa, alamar tayi masa tausa.
Ta ji haushin yi mata asarar ɗari shidan da yayi, shi kuwa ko a jikinsa, sai dai ƙasan zuciyarta mamaki take yi, ashe yana kallonta har haka da ya gane ta rame.
Iya ƙarfinta ta saka tana jan yatsun ƙafarsa, tana son yayi magana, amma ko a jikinsa.
Tun tana yi da marmari, har ta fara gajiya, dama gashi wuni tayi aiki, tun tsakiyar azumi rabonta da baccin kirki.
A take ta fara gyangyaɗi, bacci mai ɗan nauyi ya yi gaba da ita, kamar a mafarki ta ji abu yana taɓa cikinta, ta buɗe idonta ta ga menene, babban yatsansa ya saka yana taɓa cikinta.
Da sauri ta ɗame cikinta, ta kalle shi, ya rufe idonsa kamar mai bacci. Ta riƙe ƙafarsa, ta sake kallonsa, amma ya saka ɗayar ya cigaba.
Ta saka duka hannunta biyu, ta rirriƙe ƙafafunsa, tana ajiyar zuciya kamar mara gaskiya.
A hankali ya buÉ—e idonsa, yana kallonta, ta sake É—aga kai ta kalleshi, suka haÉ—a ido, tayi saurin kawar da kanta.
"Dambe zamu yi ne ki ka rirriƙe mini ƙafa? Tausa fa na ce ki yi mini".
Kamar ta yi kuka ta ce "Na gaji bacci nake ji"
"Eh da aikin banzanki ne, ba zaki gaji ba ai, kin ga yanzu kya samu lada sama da ɗari shidan da ki ke yi mini ƙunƙuni a kanta"
A shagwaɓe ta ce "Ni ba ƙunƙuni nake yi ba fa, ka yi haƙuri to" ya janye ƙafafuwan sa daga kan cinyarta, ta tashi da sauri, muzurunta ya bi bayanta, ta saka hannu ta ɗauke shi ta nufi ɗaki.
Baba ya ji daÉ—in abun da ya tarar jauhar ta kai masa, ya din ga murna da sanya mata albarka, tare da yi mata addu'a iri-iri.
Ganin hankalin Jauhar yana kan 'yan kuɗaɗen da take samu, na sana'ointa, ya sanya ya ƙyaleta, baya son yawan takura mata.
A goman ƙarshen nan, haka ta din ga damunsa, a kan yawaita ibada, dan azumin kawai yake yi, ba sauran ibadu. Da ƙyar take saka shi yayi salla cikin dare ko raka'a biyu ce.
Dama idan aka sha ruwa, ya ƙoshi sai ya je dabar su, sun yi shaye-shaye tukuna ya dawo gida.
Ana jibi salla, ta saka shi a gaba da naci, da magiya, su je ayi masa aski saboda gabatowar bikin salla ƙarama.
Ya ce na za shi ba, ƙarshe ita ta zauna, ta wanke masa kan, ta rage masa sumar da almakashi, tayi masa gyaran fuska da shaver, tamkar ɗa da uwa.
Ana gobe salla, ta yi masa list dai-dai na talaka, ta ce ya sayo, za ta yi abincin salla, dan abubuwa da dama idan ba ta ce masa yayi ba, ba zai yi ba, idan kuwa ta ce ya sayo zai sayo, idan ba shi da hali kuma zai gaya mata ba yanzu ba.
Da sassafe ƙarfe bakwai, ta shigo ɗakinsa da mp ɗin ta, an sako kabarbari da ake yi yayin tafiya idi, tana maimaitawa.
*Allahu Akbar, Allahu Akbar la'ilahaillala*
*Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamd*
*Allahu Akbar kabiran*
*Walhamdilillahi kathiran*
*Wa subhanallah bukratan wa asila*
"Master, kar mu makara sallar idi fa, ka tashi" ya motsa a hankali yana yamutsa fuska.
Ta miƙa masa hannu ta ce "Barka da salla? Ina fatan ka yi sallar idi lafiya"
Yayi miƙa tare da hamma, ta ce "A'uzibillah, Alhamdilillahilazi ahyana, ba'ada ma amanatana wa ilaihil nushur. Ga ruwa mai zafi can, ka zo ka karya mu shirya"
"Sai na karya tukuna"
"To taso ka yi brush, ko sai na ɗauke ka ne, sai ƙara maƙalewa ka ke yi a katifa"
Kukan É—an muzurun nan ne ya sanya Al'amin shi tashi zaune ba shiri, ya biyo jauhar yana yi mata É—an kuka.
Ta kalli muzurun ta ce "Sweetheart, mu je na baka abinci" Al'amin ya tashi ya bar ta da muzurunta, saboda zaƙewar muzurun ta fara yawa a kan matarsa.
Ya fito daga wanka, ta shigo ɗakin da wata leda, ta saka dogon hijjabi light blue, sai zuba ƙamshi take.
"Master yi sauri zamu makara"
Ya shafa mai, ta buÉ—e ledar ta fito da É—inkakkiyar shadda light blue, da hula, ga agogo sai takalmi soso na ta da nasa, iri É—aya na ta na mata na sa kuma na maza.
Turus yayi yana kallonta, cikin tsananin mamaki.
"Ungo saka, bari na je na rufe É—akina kan ka gama"
Kamar soko ya kasa karɓar kayan.
"Ko ba ka so ne?" Tayi maganar a sanyaye.
"A ina ki ka samo wannan kayan?"
Ta ce "Dama ana samo kaya ne? Neman kuÉ—in da ka ke cewa na saka a gaba ne, ka san wata nayi ina yi mana tarin nan? Hmm saka kayanka ina zuwa bari na É—aukko wayata da darduma" ta ajiye masa ta fice.
Kallon kayan ya din ga yi yana jujjuya su, har da aiki a jikin kayan, shi bai yi mata kayan salla ba tayi masa?.
Ya saka wandon, ya tsaya yayi shiru yana kallon rigar, har ta dawo É—akin.
"Master saka mana" ta karɓi rigar tana ɓalle botiran jiki, ya karɓa yana sakawa ta ce "Alhamdilillahilazi kasani haza saub, waraƙatani min gairi haulin minni wala ƙuwwa"
Ta saka masa hula, ta saka masa lence É—in hannun rigar, ta É—aura masa agogo, tare da saka masa farin glass na maza.
Tayi wani irin murmushi ta ce "Tubli wa yuklifllahu ta'ala. Wallahi kana da kyau master, ka ga yadda ka yi kyau kuwa? Subhanallah saka takalmin mu ke falo na yi maka hotuna" gaba É—aya jikinsa yayi sanyi, ashe matan ma sunan suka tara? Wace irin mace ce jauhar.
"Master ka yi dariya mana, sai hoton ya fi kyau"
Ta gama yi masa hotunan, ta riƙo hannunsa, ita ma ta saka nata gilashin fari, suka fita sallar idi.
Musulunci mai daɗi, al'ummar musulmi na ta ɓarkowa ta kowane angle zuwa masallacin idi.
Shi rabonsa da zuwa sallar idi ma, har ya manta lokacin, amma yau albarkacin auren mace ta gari, ta saka shi a gaba har zuwa masallaci.
Aka idar da sallar idi, suka haÉ—u a wani gate É—in daban, bisa koyi ga sunna, jauhar ta bawa wata wayarta, ta ce dan Allah tayi mata hoton first eid with habinbi.
Ta ɗauka zai ce baya so, bisa ga mamakinta, sai ta ga ya saka hannu, ya dafo kafaɗarta jikinsa, yana kallonta, ta saka hannu ta zagaya a ƙugunsa kasancewar da kaɗan ta wuce ƙugunsa, ta kalleshi ita ma tana murmushi. Hotunan sun yi kyau sosai, banda wanda ya yi wa Al'amin kyakkyawan sani, ba zai gane shi ba, sai ya zama very decent and calm.