Sashe 68
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wace irin cocaine kuma? Ka ga malam ba ma son rainin wayo, haba kai tare fa muke sabgar nan da shi, a gidan uwar wa zamu ga cocaine ɗin?" Walid ya yi maganar a matuƙar fusace.
Cikin tsawa wani ya ce "Kai ka san a ina ka ke?"
"Na sani mana, ai ba lahira ba ce, balle ace mutum ta sa ta ƙare, ƙarshen abun dai ku kashe mutum, kai da muna harka da cocaine zaku ganmu a haka ne?"
Jauhar ta yadda sai hali ya zo É—aya ake abota, daga Al'amin har abokansa ba su da tsoro.
Fashewa ta yi da kuka ta ce "Wallahi Yallaɓai zan iya rantsewa ba ya ta'amalli da cocaine, bai san ma in da zai same ta ba".
"Yayi bayani da bakinsa mana"
Cikin hanzari ta koma wurinsa, ta ce "Dan Allah Master ka yi musu magana ko zasu ƙyale ka mu tafi, ka gaya musu ba taka ba ce ba, laifina ne"
Yadda ginin wurin ba ya motsi, balle yayi magana haka Al'amin yayi kirim a wurin.
"Dalla malam ka yi musu bayani, ka gaya musu ba ka ta'amalli da ita kar su yi ta tila maka na jaki a banza su nakasa ka" Walid yayi maganar cikin ƙunar rai, dan ya san ƙage kawai aka yi wa Al'amin.
Liti ya ce "Kai ma ka san ba zai yi ba, wasu lokutan zuciya in dai irin ta shi ce ba ta yi ba"
Jauhar ta riƙe hannunsa za ta yi magana, sai dai jikinsa kamar wuta Saboda zafi, sai yanzu ta tuna bai gama warkewa ba aka kama shi, durƙushewa tayi a gabansa ta cigaba da kuka.
"Lokacinku yayi, zaku iya tafiya"
Liti ya ce "Ko ba ku ce ba zamu tafi, kowa yayi na gari dai kansa ya yi wa"
Al'amin ya miƙe tsaye, ya saka hannu ɗaya ya ɗagata daga durƙushen da take, ya juya zai koma, ta saka ƙarfinta ta rirriƙe shi tana kuka.
"Ke wai meye haka, da ki ka samu aka bari ki ka ganshi" É—an sandan ya daka mata tsawa.
"Wallahi sai dai ku rufe mu tare, ni ba zan tafi ba, wai ya ake so na yi ne? Ya zan yi ko ina babu daɗi, ni komai nawa ba sa'a. Na gaya muku ba shi da laifi, amma dukansa ku ke yi, tayaya hankalina zai kwanta idan na tafi? Ba laifinsa ba ne wallahi, laifina ne na karɓi abu daga hannun wanda ban sani ba dan Allah ku ƙyale shi"
Matsanancin tausayin da jauhar ta bawa liti, ya sanya ya fice ya bar wurin, kuka take iya ƙarfinta, Al'amin har mamaki yake yi, tsakaninsa da ita ba wata shaƙuwa ko kulawa ta musamman amma idan abu ya same shi, gaba ɗaya sai ta rikice.
Walid tsayawa yayi ya ga viper zai rarrasheta ko kuma ƙasaitar zai tsaya ya cigaba, da kuwa ko 'yan sandan za su rufe shi, sai ya zage shi.
Ɗaya daga jami'an tsaron yayo kan jauhar, da nufin ya ɓanɓareta ta ƙarfin tsiya, su mayar da Viper, cikin hanzari ya ja baya da ita a jikinsa, ya ɗaga masa hannu yana ƙara tsuke fuska.
Ya saka hannu, ya ɓanɓareta daga jikinsa, ya riƙe hannayenta, gaba ɗaya kammnin fuskarta sun canza saboda idanunta sun kumbura sosai ta koma pink saboda kuka.
Ya sunkuyo dai-dai fuskarta ya ce "Kin kusa fara exam, ki yi karatu sosai, kar ki zauna zaman shiriritar nan, ki yi ƙoƙari ki yi karatu ki zama lawyer ko likita, ko dan saboda fitinannen mijinki, ki gaida mini da kwaɗinki da ƙadangaru idan kin koma gida" tana jin yadda jikinsa yake fitar da hucin zafi da warin datti, kwana bakwan nan babu alamar wanka ko wadataccen abinci a tare da shi.
Ya kama kafaÉ—arta, ya saita ta hanyar fita ya ce "Kar ki sake zuwa wurin nan saboda ni" ya kalli walid ya nuna masa Jauhar, ya yi masa wata inkiya, ya juya suka mayar da shi.
Suka fito tana kuka, liti ya girgiza kai ya ce "Wallahi Mutanen nan 'yan wuta ne"
Walid ya ce "Kai wannan hurumin Ubangiji ne, amma ko dan hakkin yarinyar nan Allah sai ya kama su, a gidan uwasu zai ga cocaine ɗin, wallahi ƙila su suka zo da abar su suka saka masa"
"Zasu aikata ai ba tsoron Allah suke yi ba" sun yi gaba suna ta surutu suna zage-zage da tsine-tsine.
Suka nemi jauhar suka rasa, suka waiwaya, tana bakin ƙofar in da suka baro, ta zauna dirshan tana matsar hawaye.
Liti ya ce "Taɓ lallai sabga da mata sai haƙuri, wannan ko mutuwa yayi abun da za ta yi kenan"
Walid ya ce "Sai an yi mata uzuri, ba ta saba ganin wannan tashin hankalin ba, ina zuwa".
Ya koma da baya wurinta, ya zauna ya din ga rarrashinta, tare da ba ta tabbacin Aminu zai fita.
Cikin kuka ta ce "Ba ma fa shi da lafiya, zazzaɓi ne a jikinsa"
"Ki yi haƙuri, Allah zai bashi lafiya"
Ta sake cewa "To yanzu daga nan me za su yi masa?"
"Wallahi ba mu sani ba, amma zamu cigaba da bibiya in sha Allah, sai mun ga abun da ya ture wa buzu naɗi" da ƙyar ta taso, suka kaita har gida, Walid ya ba ta kuɗi, ta ce ba zata karɓa ba, sai da ya ce mata Al'amin ne ya ce ya bata sannan ta karɓa.
Har ta shiga falo, aka buga mata ƙofa, ta dawo ta buɗe, ta ga Malam lawan baban su halimatu a tsaye.
Ta durƙusa ta gaishe shi, ya ce "Wato duk na san ke da mijinki, kuna jin haushina, amma ni duk in da gaskiya take sai na faɗa. Ke yanzu ki ji da halin da mijinki yake ciki, amma kin zo kina tara mana maza a layi, kusan kullum sai sun zo, shi fa aure abu ne mai daraja da muhimmanci".
Jiki a sanyaye ta ce "Tara maza kuma?"
"Eh mana, wannan da ku ke fita tare da su ku dawo, muharraminki ne?"
Kalmar ta yi mata nauyi sosai, amma ta dake ta ce "Aboknsa ne, su ne suke taimaka mini a kan case É—in sa"
"To ke me yayi miko zafi? Ki koma gidanku mana, idan ya fito kya dawo, ko ma ki haƙura da auren, da kyanki da ƙuruciyarki nan da nan wani zai aureki, shi kuma ya cigaba da shashancinsa".
Ta ce "To na gode sosai"
"Ai gara dai ki san abun yi, ni Allah ya sa ma ba iyayenki ki ka bujirewa a kansa ba, Allah yake jarabatarki ba" gaba É—aya sai ta ji kimarsa ta zube a idonta.
Jauhar ta kama Alƙur'ani da da carbi, tayi ta Addu'a tana gaya wa Allah.
Aka sake shafe kwana biyar, su liti suna yi mata yawo da hankali, suka kuma hanata komawa wurinsa, sai su ce mata sun je yana lafiya yana gaisheta.
Haka kurum ta ji a ranta ƙarya suke yi mata, ba tare da sun sani ba, ta sake ɗaukar ƙafa ta tafi wurin 'yan sanda, har da abincinta ta tafi da shi, sai dai suka tabbatar mata sun kai shi kotu, har alƙali ya aike da shi gidan gyaran hali, zuwa lokacin da za a cigaba da shari'a.
Cikin tashin hankali ta tambaye su, zuwa yaushe zai fito.
Suka ce mata ta tafi kotun ta tambaya, suka din ga yi mata wasa da hankali, har da wanda suka biyota da maganar lalata.
A ƙofar gida, ta tarar da su walid, sai jan ƙafa take da ƙyar, ta ƙarasa.
Walid ya ce "Madam ina ki ka tafi ne, mun zo ba kya nan?"
Ta kalleshi cike da karaya ta ce "Dama an kai shi prison ba ku gaya mini ba?"
Liti ya ce "Komawa ki ka yi kenan, ke ana ta ɓoye miki, dan kar ki tayar da hankalinki, shi muka zo gaya miki, sai da muka tsara yadda zamu gaya miki, yadda ba zaki damu ba, amma kin tashi kin tafi kin jiyo wa kanki damuwa"
Ta ce "To ya zan yi, na kasa jurewa".
Walid ya ce "Yanzu dai tun da kin riga kin je kin ji da kanki, shikenan amma ki yi haƙuri zamu nemo wata hanyar mijinki zai fito in sha Allah"
Jinjina musu kai kawai tayi, ta shiga gida. tuna da liti yayi mata kwatancen gidan su Al'amin, kamar korarriya, ta sake É—aukar hanya, ta tafi unguwar su Al'amin tare da fatan Allah ya sa idan ta je gidan su Allah ya sa a dace a samu hanyar fitar da shi.
Sai da ta haɗa da tambaya, sai dai gidan na su ba ɓoyayye bane ba, mussaman ma sunansa da ya riga ya shahara sosai.
Sau biyu tana sallama aka amsa, mata wata matashiyar budurwa, da zata girme mata ta leƙo ta amsa.
Ta ce "Ya aka yi?"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Baƙuwa ce"
Amira ta ce "Baƙuwa daga ina?"
Rahila ta ce "Amira ki bari ta shigo mana"
Ta bawa jauhar hanya, ta ƙarasa ta shiga falon da sallama.
Rahila na ganinta ta washe baki, cike da duniyanci ta ce "Amrya ba kya laifi, ko kin kashe ɗan masu gida" jauhar ta zube har ƙasa ta gaisheta.
"Lafiya ƙalau, zauna a kan kujera mana jauhar" ta sunkuyar da kai tare da girgizawa ta ce "Nan ma ya isa"
"Amira matar Aminu ce fa, kawo mata ruwa dan Allah" kallon banza ta yi wa jauhar, ta gyara zamanta ta cigaba da danna waya.
Rahila ta ce "Ke fa 'yar wulaƙanci ce amira".
Jauhar ta ce "Ai a ƙoshe ma nake"
"Allah sarki, ya mijin naki, tun da aka yi auren ba ki zo mana ba" tayi shiru tare da sunkuyar da kai tana murmushi.
"Bari yanzu babansu zai shigo, sai ku gaisa".
Amira ta saci kallon jauhar, kyakywar bafulatanar yarinya, daga muryarta kawai zaka san ba ta da hayaniya, ita aka aurawa Al'amin.
Abbu ne yayi sallama suka amsa masa gaba ɗaya, ko da ya shigo sau ɗaya jauhar ta kalle shi ta mayar da kanta ƙasa, babu in da Al'amin ya bar kamanin mahaifinsa.
"Abbu ga 'yar ka fa, sirikarka matar Aminu"