← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 95

Sashe 72

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ta samu kuɗi, take yin sayayya, ta ari waya ta kira walid, ya zo ya karɓa ya kai masa.

Sana'a tuƙuru jauhar kamar tayi ƙwace, dama ga azumi yana gabatowa, ana samun ɗinkuna, dan haka tana samun aikin stone da beads, sai dai ba ta iya sakin jiki ta kashe kuɗin, saboda akwai abun da take son yi.

Ita ce mayafai, har da su kantu da aya,  haka take saya ta soya ta ɗaura a leda yara na saya.

Har guga take karɓar kayan maman halimatu, ta ta da ta yara tayi mata, ta biyata.

Sana'oi kamar zata yi ƙwace, duk da ana yi mata mugunta a kan wasu abubuwan, mussman gidan mai ɗinki, da take yi mata aikin stone ta fara yi mata mugunta.

Ta ƙara tsananta addu'a, da roƙon Allah, a kan Allah ya kuɓutar mata da mijinta, ya shirya mata shi.

Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, saura kwanaki biyu Al'amin ya fito, jauhar ta yi ta gyaran gida, ta ƙara gyara masa ɗakinsa.

Ranar da zai fito ɗin, ta yi girki, sai dai kuɗin hannunta ba su da yawa, duk mutane sun riƙe mata kuɗi, dan muɗin hannunta ba za su ishe su kuɗin mota ba ita da shi.

Ta dafa ruwa ta zuba a flask, ta shirya tun ƙarfe tara, ta tafi prison ɗin, gashi damuna ta ja baya, an fara wani irin sanyi mai ratsa jiki.

Ta nemi shiga cikin prsion É—in, aka ce mata a waje za ta jira, idan yau za a sake shi, za ta ganshi ya fito.

Tana nan zaune, wasu suna ta fitowa, 'yan uwansu suna ta murna, sai dai shiru-shiru ba ta ganshi ba.

Nan hankalinta ya tashi, ta sake nufar wurin masu gadin ta ce "Wai haryanzu ban ganshi ba, kuma yau aka ce mini za a sake shi"

"Waye ya ce miki za a sake shi?" Wani gandiroba ya tambayeta.

"Yayana ne"

"Yayan naki alƙali ne? Ko shi ya kawo shi nan ɗin, wanda zamu saki kenan yau sun gama fitowa"

"Innalillahi na shiga uku" ta faÉ—a a raunane.

Ayshercool
08081012143

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955

Da kallo suka bi jauhar, ganin yadda take yi musu kuka wiwi, wani gandiroba ya ce "Koma tsallake, idan ki ka gama kukan, sai ki tafi".

Ta juya ta kama hanyar tafiya, tana ji a ranta kamar duk duniya, babu wanda ya kaita rashin sa'a.

Sannu a hankali yake tunkaro gate É—in fitowar, zuciyarsa cike da mamakin yadda aka sake shi, dan bai san ma zai fita ba, sai yau É—in.

Tsayawa yayi bayan ya fito daga cikin gate ɗin, ya lumshe idanunsa sakamakon hasken ranar da ya ji ya yi wa idanuwansa yawa, sannu a hankali ya cigaba da buɗe su, har ya ji hasken yayi dai dai da abun da idon nasa yake buƙata.

Kamar an kira sunanta ta waiwayo, ta hangoshi a tsaye, shi ma ita yake kallo da mamaki, ba ƙaramin kashedi ya yi wa su liti ba, a kan kar su kuma ɗaukarta su kaita in da yake.

Da sauri ta nufo shi, ta kasa tsayar da hawayenta ta na wata irin ajiyar zuciya ta ce "Har na ji daÉ—i, da suka ce mini, ba za su sake ka yau ba"

Yayi shiru yana kallon ta.

Ƙare masa kallo take yi, an yi masa aski an aske masa sajensa da gemunsa, sai ɗan kaɗan da ya fara fitowa, idanunsa sun washe yayi haske, saboda babu kayan shaye-shaye a nan, sai dai ya rame sosai.

Kallonta kawai yake yi, kamar wata baƙuwar halitta, sai dai bai yi mata magana ba.

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Mu tafi?" Ya jinjina mata kai yayi gaba.

Ta ɗaga ƙafarta kenan takalminta ya tsinke, ta durƙusa ta cire takalmin ta ce "Takalmina ya tsinke" ya kalli ƙafarta sannan ya dubeta, ƙafarta busu-busu, duk yadda ya santa da gayu, ko ba ta gaya masa ba, ya san tafiyar ƙafa ta yi.

Ta tsayar musu da abun hawa suka hau, sai dai har suka je in da za su sauka, duk surutun da take yi, ko sau É—aya bai tanka mata ba.

A titi suka sauka, saboda kuɗin motar ba zai isa a shiga da su har ƙofar layin ba, har ta yi gaba, ya janyota ya cire mata takalmansa ba tare da ya ce komai ba.

Ta ce "A'a ka saka kar ka taka wani abun".

Kallon da yayi mata, ya sanya ta yin shiru, ta saka takalman kamar zata tashi sama a kansu suka shiga layinsu, kamar ta taka rawa, master ya fito.

A falo ya zauna, ya kashingiÉ—a ya lumshe idanunsa, ta shiga banÉ—akinsa, ta haÉ—a masa ruwa mai zafi, ta ce "Master ga ruwan wanka na kai maka" bai yi mata musu ba, ya tashi ya tafi, kafin ya fito ta jera abinci a falo, ya yi wankan ya fito falo, ya tarar da abinci, yanayin yadda yake cin abincin ya tabattar mata da yana jin yunwa sosai duk da dama can acici ne.

Yana so yayi mata magana, amma ya rasa me zai ce mata ma, ya gama ci ya tafi É—akinsa ya kwanta, dan surutunta ya fara takura shi, duk da yayi kewar abubuwa da yawa a tare da ita, sai dai yadda yake jin zuciyarsa a cunkushe babu daÉ—i, ya sanya shi jin surutunta ya gundure shi.

Allah ya taimaketa, ya wuni a É—aki, bai fita ko ina ba, tun da ya dawo.

Hafsa kuwa ta samu abun yi, dan tun da Allah ya sa ta mallaki lambar wayar Alhaji mu'azzam, take kiransa a waya, da sunan rarrashin sa a kan rashin jauhar, tare da ƙoƙarin sake ɓata jauhar ɗin a wurinsa.
Mahaifiyarta ta sake miƙewa wurin shige-shige a kan Allah ya tabattar da lamarin aure tsakanin hafsa da Alhaji mu'azzam.
Cikin ikon Allah, idan ta kira shi, yana amsawa ba ya yi mata wulaƙanci ko makamancin haka, hakan ya sa ta cigaba da ƙoƙarin cusa kanta cikin hikima da kissa.
Sannan suka yi ƙoƙarin rufe wa mama duk wani abu da yake faruwa, ba ta san halin da ake ciki ba.

Kasancewar Al'amin ya fito ya dawo gida, ya sanya jauhar yin isashshen baccin da rabonta da shi, tun kan a rufe shi, dan bayan sallar asuba da ta kwanta, ba ta farka ba sai goma saura.

Ta fito tsakar gida da sauri, ta fara aikace-aikace, ta dafa tea ta soya dankalin hausa.

Ta dafawa Al'amin ruwa a heater, ta je ƙofar ɗakin ta tsaya tana sallama.

Ƙasa-ƙasa ya amsa, ban da yana da buɗaɗɗiyar murya ma ba za ta ji ba, ta shiga tana sake yin wata ta ce "Ina kwana master"

"Lafiya ƙalau"

"Ban san ka tashi ba, yau na makara da na fara kawo maka ruwan wankan ai, bari na haÉ—a maka" ta haÉ—a masa, yanzu ma bai yi musun yin wankan ba, ya tashi ya shiga banÉ—akin.

ÆŠakin fes yake, amma ta din da karkaÉ—e karkaÉ—e, da goge-goge, ta kunna turaren wuta, ta fito masa da kaya ta saka musu turare.

Ya gama ya fito, jikinsa yana É—igar da ruwan wanka, ya É—auki dogon wando ya saka, ya zube mata wanda ya cire a kan katifa ya fito.

Kallo É—aya tayi masa ta kawar da kanta gefe ta ce "Ba ka saka rigar ba, na fito maka da ita ma".

"Ba na buƙata, wandon ya isheni".

Jauhar ta ce "To ai kar ayi sallama, a ganka a haka".

"Ki koma É—aki idan ba zaki iya kallona a haka ba" yayi maganar yana zama.

Ya kalleta ita ma yau ba hijjabi a jikinta, doguwar rigar material ta saka, mamaki yake yi, yadda ta yi duhu, ga wani uban ƙashin wuya da ya fito mata, tayi rama sosai da sosai, ashe jiya dan ya ganta a cikin hijjabi ne ya sanya bai gane ba, sai ya ji ransa babu daɗi.

Ta haɗa masa abincin ta miƙa masa, ya ɗauka zai kai baki ta ce "Bisimillah" a zuciyarsa ya maimaita sannan ya fara ci.

"Askin nan da aka yi maka, ka yi kyau, sai dai ban so aka aske gemun ba gaba É—aya"
Idan ba gizo idanunta suka so yi mata ba, da murmushi zai yi ya shanye abun sa.

Ta tanƙwashe ƙafarta ta sake cewa "Sannu master, a prison ɗin ma duka ake yi, na ga bayanka duk shaidar duka. Wallahi ba zan taɓa yafewa wanda suka yi maka sharri ba, ban taɓa shiga tashin hankalin da na shiga ba, na san baka ta'mali da wannan abar, sauran ma zaka daina wataran in sha Allah" tayi maganar hawaye na cika mata ido.

"Kun kusa gama exams ko?"

Jin yayi magana ya sanya ta saurin ce wa "Eh, cikin azumi zamu gama in sha Allah"

"Allah ya taimaka"

"Amin na gode, baka tambayeni kwaɗinka da ƙadangaru ba?"

Ya rausayar da kai ya ce "Ai naki ne ba nawa ba" hakan yayi da kammala cin abincin.

Ta ce "Alhamdilillahilazi aɗa'amana haza, warazaƙatana min gairi haulin minni wala ƙuwwa, Ubangiji Allah ya ciyar da mu na anjima" tayi maganar tana tattare kwanukan.

Kafin ta dawo ya É—auki pillown kujera ya kwanta.

Ta je gabansa, ta durƙusa ta kai hannunta goshinsa ta ce "Wai haryanzu kana zazzaɓin ne?"

Ya girgiza kai alamar a'a.

"Master duk ka yi wani iri kamar an canza mini kai" duk lokacin da ta danganta shi da ita, sai ya ji wani abu a ransa da bai san Menene ba.

Yana daga kwance ya din ga miƙa, yana ɗan banƙare kafaɗunsa zuwa bayansa.

"Ciwo bayanka yake yi ne?"

Ya gyaÉ—a mata kai alamar eh.

"Bari na É—aukko man zafi na shafa maka zaka ji daÉ—i, naga wani raunin bai gama warkewa ba". Ya jinjina mata kai, sai dai bai buÉ—e idonsa ba.
Chapter 72 · 0% Book details