← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 95

Sashe 14

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhamdilillah sir, an yi clearing matsalar jiya, duk da an kusa samun akasi, yaron ba ya ji ko kaɗan, idan aka cigaba da tafiya a haka, kar asirinmu ya tonu fa, dan hakan tamkar yi wa doka karan tsaye ne, mu na saɓa ƙa'idar aiki"

Yayi murmushi ya ce "Kar ka damu, doka ce ta fara yi wa yaron karan tsaye, shiyasa nake amfani da dokar, wurin bi da komai"

"Haka ne sir, amma fa police suna neman shi ne ruwa a jallo, mu kuma muna kare shi, muna taka doka da yawa"

"ASC, ko sun kama Al'amin, ba zasu bari doka ta yi aiki a kansa yadda yakamata ba, za su bar shi da masu son zuciya ne, su yi abun da suka ga dama da shi, ba wai hukumar ce kawai take nemansa ba, akwai lauje cikin naÉ—i ne a neman da ake yi masa"

ASC ya numfasa ya ce "Shikenan, amma laifukansa sun yi yawa, duk wani ta'addanci da za'ayi a garin nan sai ka ji yaransa ne, slide mistake za'a iya kama shi, duk da wani abun kuma idan muka bincika, sai mu tarar ba shi É—in ba ne ba"

"Haka ne, amma idan an kama shi ma, sunana na ko naka, babu wanda zai fito, haryanzu bai san ko ni waye ba, kuma ba zan bari ya sani ba, kuma yana aikata wasu laifuka ne dan ya tilasta na ƙyale shi, ko kuma na bayyana kai na a gare shi, amma ka rabu da shi, komai cikin tsari nake yin sa, ka bar police su cigaba da neman sa, hukumarka kuma ta cigaba da aikinta, kamar yadda na ce maka"

Ya amsa da "Shikenan sir, am always loyal to you, na gode"

"Yauwwa ASC, duk halin da ake ciki dai, ina buƙatar ka sanar da ni"

"No problem, sai an jima" bayan sun yi sallama, yayi wata irin dariya, da shikaÉ—ai ya san ma'anarta ya ce "Wannan shi ne jifan tsuntsu biyu da dutse É—aya" yayi maganar yana kallon yaronsa da yake tsaye yana kallon sa.

Ya ce "Lallai, amma zan so in ji wani irin shiri ne haka ka ke yi sir"

"Za ka gani a aikace, kai dai ka cigaba da biyayya ga abun da duk na umarce ka, nima zan yi amfani da ƙarfin iko da kujerata, na yi abun da ya dace".

"Ok sir, in sha Allah".

***
Misalin ƙarfe takwas na dare, wasu daga cikin manya na ƙungiyar ƙato da gora na unguwar suka tattaru suka zauna meeting a cikin ɗan madaidaicin office ɗin su. Duba da abun da ya faru, na faɗan daba da aka yi da yaran Aminu da na Madaki a waccan unguwa, sanin ya na shigowa unguwar lokaci zuwa lokaci, sannan kuma akwai yaransa a unguwar, ya sanya su zaman yin meeting, dan ƙara ƙarfafa tsaro a cikin unguwar su, kar su gama da can su dawo nan.

Suna tsaka da tattaunawar, wasu zaratan matasa suka yi sallama, suka amsa suna bin su da kallo.

Suka shiga cikin office É—in, suka kewaye su, duk suka tsaya suna kallon su.
A hankali ya sauke face mask É—in fuskarsa, a take suka shaida shi.

Kafin su yi magana ya ce "Awa ɗaya rak nake buƙata, zan gama abun da ya kawo ni na fita, muddin na kuma shigowa unguwar nan, ku ka sako ni a gaba, kamar kare za ku kama ni, wallahi sai na yi muku abun da na yi wa malam lawan".

Shugaban ƴan sintirin ya ce "Dan meyasa zaka din ga shigo mana unguwa? Kai da hukuma take nema ruwa a jallo, ka san kai tauraruwa mai wutsiya ne, duk in da ka je sai ka yi fitina, tun da yaranka suka yi ɓarna jiya, na san cewa nan ma zaka shigo. Duk ka lalata mana yara ka tafi ka barmu da masifa, kuma yanzu ka dawo kana cigaba da bibiyarmu"

Cikin tsawa Walid ya ce "Kai, ka iya bakinka, wallahi ko na ɓare maka shi har ƙeyarka".

Cikin tamkakiyar fuskarsa Viper ya ciro zungureriyar wuƙar da take ƙugunsa, ya karta ta a ƙasa tayi wata irin ƙara, sannan ya ɗora ta a gefen wuyan mutumin ya ce "Ƴaƴanku za su cigaba da yi mini biyayya, sai na mayar da unguwar nan mafi munin sansanin ta'adancci da zubar jini, komai ya faru ai ku kuka so, yanzu dan Allah kai ba ka ji kunyar faɗar abun da ka faɗa ba? Duk in da zan je zuciyata na tsakiyar unguwar nan, kuma zan cigaba da shiga da fita yadda nake so, har sai na yi maganin azababbiyar ƙishirwar da ta addabi ruhina. Duk abun da na aikata muku na ɓarna, ku kuka so, mutanen banza masu butulci, kun taki sa'a da nake dakon alƙawari mai nauyi a kaina, ban da haka tun a fitowa ta, ɗaya bayan ɗaya zan yi muku kisan gilla. Idan na sake shigowa unguwar nan, kai da wannan mutanen, ku ka yi yinƙurin yi mini wani abu, duk wanda na kama, zai zama mutum na farko da zan yi wa yankan rago!" Gaba ɗaya suka zuba masa ido, suka kasa ko motsin kirki, saboda yadda suka zagaye su da miyagun makamai.

"Ku karɓe wayoyinsu, ku rufe mini su, ku saurari order da zan bayar. Duk wanda yayi muku gardama ku karya mini ƙafarsa, ko ku tsarge masa cinya".

"Angama boss"

Yana fita daga office ɗin, suka mayar suka rufe, suka ƙwace musu wayoyi, sannan suka tsaya a kansu da wasu irin zabga-zabgan wuƙaƙe, kamar a abba tuwa.

Babu wanda ya iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi, dan a yadda matasan suke muzurai, kuma shaye-shaye ya huda su, duk umarnin da ya ba su za su bi.

Sannu a hankali yake tafiya, har ya kawo cikin layin, ya tsaya a ƙofar wani gida, ya shafe tsawon lokaci kawai ya zubawa gidan ido, yana zancen zuci, daga bisani ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa na kusa da shi, ya ja mask ɗin sa, ya rufe fuskar shi.

Yaro ne ya fito ya ce "Waye?", ya cewa yaron "Ka je ka cewa babanka an zo duba shi"

Mintuna kaÉ—an yaron ya dawo, ya ce ya shiga.

Bai yi sallama ba, haka ya kunna kai cikin gidan, har tsakiyar falon maigidan, ba tare da an yi masa iznin hakan ba.

Daga maigidan har matar gidan, da Æ´an matan yaran, tsuma suka hau yi, ganin wanda ya shigo har cikin gidansu.

Ya zaro wuƙarsa ya ajiye a gaban malam lawan, sannan ya ɗaga wani mukulli ya ce "Na rufe gidan nan da kwaɗo ta ciki, kuma duk wanda ya yi wani ƙwaƙwƙwaran motsi, zan zaunar da shi kamar yadda na zaunar da kai" yayi maganar yana kallon malam lawan.

Ya durƙusa kama ƙafar malam lawan, da aka naɗe da bandeji, ya dudduba sannan ya ce "Ɗori yayi kyau, sai dai na yi mamakin yadda aka dawo da kai gida, maimakon ka yi jinya a asibiti"

ya saita tsinin wuƙarsa a cinyar malam lawan ya ce "Waye ya ɗauko ka daga asibiti?"

Cikin tashin hankali matarsa ta fara kuka ta ce "Dan girman Allah Aminu kar ka yi masa wan....

"Wallahi ki ka sake magana, sai na karya ɗaya ƙafar, ka gaya mini kafin na huda cinyarka" yayi maganar cikin razananiyar muryarsa.

Cikin matsanancin tashin hankali ya ce "Wallahi wasu mutane ne, ban san su ba, su ne suka sauya mini asibiti, lokaci zuwa lokaci, suke zuwa da likitansu ya duba ƙafata, kuma sun gargaɗeni a kan muddin wani ya ji kaine ka yi mini haka, sai sun kashe ni"

"Waye ya kai ka asibiti ranar da abun ya faru?"

Cikin kyarma da rawar murya malam lawan ya ce "Wallahi kana barin wurin, ina wannan kakarin, wani ya zo yayi mini kashedin muddin na ce kai ne zai kashe ni, ya watsa mini wani abu, ban sake sanin in da kaina yake ba, sai da safe maƙwabta suka tsince ni, na ce masu masu ƙwacen waya ne suka yi mini"

Aminu ya ware masa jajayen idanunsa sosai ya ce "Idan na samu labari  akasin abun da ka gaya mini, kar ka manta take na, maciji nake mai mugun dafi, sai na maka karayar da ba zaka sake taka ƙafarka ba a doron duniya. Zan cigaba da zagayowa zan kuma cigaba da sanya maka ido. Kar ka manta ka yi mini ganganci daban-daban, na kawar da kai, na riƙe biyu a raina idan ka yi na uku kasheka zan yi har lahira".

Malam lawan ya jinjina kai, yana jin yadda mararsa ta cika fam da fitsarin tsoro.

Viper ya a miƙe ya juya ya bi hanyar fita.

Sai da suka tabattar da tafiyarsa, sannan matar malam lawan ta ce "Na shiga uku, baban su Amir dan Allah meya aike ka sake shiga sabgar mutumin nan? Daga ƴan sandan har ƴan ƙato da goran kar wanda ya ƙara tambayarka abu a kansa ka ce ka sani, kalli bala'in da ka jefa mu a ciki?"

"Ke dalla rufe mini baki, tun da yanzu na tsira da raina shikenan, ina ga sayar da gidan nan zan yi na bar unguwar, idan ba haka ba wataran kasheni zai yi "

"Ai koma menene Allah ya ƙara wallahi, abun da ka yi wa bawan Allah nan ka yi butulci da yawa"

"Au so ki ke na rufawa mutumin banza asiri Haule? Ni ki ke gaya wa haka?"

"Oho ai gaskiya ce" haka suka cigaba da faÉ—a, tana mita da É—ora masa alhakin janyowa kansa ko ma menene.

Aminu kuwa, ta waya ya ce wa su É—an mama, su baro Æ´an vigilante É—in, su bi shi gida.

A gidan suka tarar da shi, ya dubi Walid ya ce "Ka yawaita survey a cikin unguwar nan, mutumin nan ya tabattar mini da cewa, wanda suka canza masa asibiti, suna zuwa da likta har gida yana duba shi".

"To shikenan Oga, in sha Allah za ayi yadda ka ce"

"Kuma na san mutanen nan ne, da mutumin yake kirana a waya, ya zama dole na san waye, da kuma manufarsa a kaina, da yake bibiyata har haka".

Walid ya ce "An gama maigida"

Nabila kuwa tun da ta shiga aiki tana office É—in ta, suna communicating da Yaya Nasir.
Chapter 14 · 0% Book details