← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 95

Sashe 81

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

P.A ya ce "Kai, honorable Mai zamani yana hawa kanmu da yawa wallahi, wai sai abun da yake so za a din ga yi yayi ta yi wa mutane tunƙaho?"

Indabo yayi murmushi ya ce "Rabu da shi lokaci ne, bari a ci zaɓen, ai ka ga mutumin can ya ce akwai nasarar mu a tattare da shi, yanzu abun da za ayi, ka koma ka yi waya, ka saka a haɗa wata tawagar ta 'yan daba, da zasu far mana a wurin taron, yadda za a samu a zubar da jinin shi ma a can. Sannan ka tara mana 'yan media, idan hakan ta faru a ce abokan adawa ne suka yo hayar 'yan daba suka far mana".

"An gama honorable, yanzu kuwa zan je na tara su na sanar musu tun yanzu"

"Yauwwa, idan ka gama da su, a hanzarta ko aike ka yi wurin wanda ya karya É—in, a rufe bakin babarsa"

"Ok sir"

***
Al'amin ya koma gida, ya tarar da Jauhar da maƙwabta, tana yi musu kitso.
Yana shigowa hannunsa riƙe da ledoji, ta tashi tana murmushi, suka gaishe shi, babu wanda ya amsa sai sannu zuwan da tayi masa ya amsa.

Ta miƙe hannu za ta karɓi kwandon, ya ce "Banda wannan" ya shiga falo da shi.

Ta dudduba kayan, kayan abinci ne wata irin ajiyar zuciya ta sauke, tare da yi wa Allah godiya.

Allah ya sa ta gama kitson, ta sallame su suka tafi, ta shiga falon hannunta riƙe da cup ta risuna ta miƙa masa. Ya karɓa ya ga zoɓo mai sanyi, sai ƙamshi yake yi. Ya kafa kai ya zuƙe ya miƙa mata kofin ta ce "Ba ka ce ba"

Ya ce "Alhamdilillah" tayi murmushi ta ce "Sannu da zuwa" ya jinjina kai ta ajiye kofin, ya jefo mata muzurun nan a jiki, ta saki ihu tana tsalle, ta ce "Meye wannan?"

"Shi ma wannan É—in tsoronsa ki ke ji?"

"Kamar kare fa?"

"Mage ne, saboda ƙadangarun da suke damunki, ko shi ma tsoronsa ki ke ji?"

Ta ce "Laaa, to ai bai yi kama da mage ba, masha Allah so cute" ta durƙusa ta ɗauke shi.

"Master ina ka samo shi dan Allah, kamar ba ɗan nan ƙasar ba. Kai amma na ji daɗi sosai, wani sunan zamu saka masa"

Ya ce "Muzuru"

Ta kwaɓe fuska ta ce "Muzuru kuma? Sunan gayu za a saka masa, wane irin muzuru?".

"Ba sunansa kenan ba?"

"A'a, na saka masa suna mai zamani"

"Ki ka kuma ko?" Yayi maganar yana kallonta.

Tayi murmushi tana shafa kyakkyawan jikin muzurun.

Ya ve "Da gaske kin je wurin P.A É—in Honorable lokacin da aka rufe ni?"

Ta kalleshi ta sunkuyar da kai. "Ki bani amsa"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Ko wani irin hali zan shiga, kar ki sake zuwa wurin wani, mussman gidanmu da wurin 'yan siyasar da nake mu'amala da su, dan su fito da ni"

Ta ce "In sha Allah, ba zan sake ba, amma dan Allah ka daina zuwa wurin da zaka cutu, kaga idan aka rufe ka, nikaÉ—ai nake damuwa ba wanda yake taimaka mini, ni kuma ba zan iya jurewa ba ganinka a tsare" tayi maganar jikinta a sanyaye.

Ya saka hannu a aljihunsa ya ciro kuÉ—i, ya ce "Ungo"

Ta saka hannu ta karɓa ta ce "Na menene master?"

"Ana zubar da kuÉ—i ne?"

"Wai bani ka yi? Duka nawa ne?"

"Mmm ki sha madara"

Ta washe baki ta ce "Allah ya saka da alkhairi, Allah ya yi maka jagora, ya ƙara jan dogon zamanin nan"

Ya ce "Za ki ga zamani, idan na kamaki"

Tayi murmushi ta ce "Wannan kuɗin ya fi ƙarfin shan madara ai"

Ta din ga kwarara masa addu'a, tare da nuna tsantsar farincikinta a kan abun da ya yi matan.

A daren ya kira guduma a waya, ya sanar masa da batun aikin ginin da za ayi, ya kira Walid da su liti, da wasu daga cikin yaransa, sai dai sai da suka sha wiwi, suka yi bushe-bushen su, domin samun ƙarfi wurin gabatar da aikin.

Sai dai tun da Allah ya sa Al'amin ya kawo É—an muzurun nan, jauhar ta samu nayi, ta tattara nutuswarta da hankalinta a kansa.

Duk ranar da babu aiki, sai guduma ya zo gidan Viper, ya tambayi jauhar ko ta na da aike ta kawo ya kai mata, tun ranar da ya ga zata kai markaɗe, ya karɓa ya kai mata, Anty sama Anty ƙasa, kasancewar ta mai kyauta, ya sanya take farinjini a wurin mutane, dan idan yayi mata aike, idan tana da Abinci ta na bashi, ba da abincin nan ba ƙaramin kankaro mata kima yake yi a.
Sai guduma ya mayar da Al'amin kamar yayansa, bashi kaÉ—ai ba, har 'yan sauran yaran da suke rashin jin, jama'ar guduma, idan suka ga Al'amin, tsakaninsu da shi girmamawa, idan da kuÉ—i a jikinsa, haka zai bi su mai É—ari biyar mai dubu, hakan ya sa suke yi masa biyaya sosai da sosai.
Hatta layin gidansa, idan kwata ta cika, ko ciyayi suka fito, haka za su zo da kayan aikin su, su gyara tsaf.

Sannu a hankali, Al'amin ya fara janye matasan, shi dai ba zai hana su shaye-shaye ba, sai dai akwai abubuwan da ya yi musu iyaka da sha.

Da sharuÉ—an da ya gindaya musu, a kan in dai za su zauna da shi, sai sun kiyaye su.

Jauhar tana makaranta jarrabawa, biyu suka yi ranar, ta dawo ta tarar an yi plasta a gidan gaba É—aya, da shi da su Walid da guduma, sun yi kaca-kaca da gidan.

Tana tsaka da mamakin ya dawo, ya tarar da ita ta ce "Master, aiki ku ka sha haka? Baka gaya mini ba, balle na kwashe kayan kuma ayi wa masu aikin girkin?".

"Da su mai laya muka yi, ba wani abu".

"Master wai a ina ka samu kuɗi haka? Amma ka yi haƙuri idan tambayar da na yi tayi tsauri".

"Bana sata" amsar da ya bata kenan ya fita.

Zata iya shaidar hakan, amma yakamata ace ta san in da ya samu kuÉ—i, tana tsoron ya É—aukko musu rigima, sai dai gidan yayi kyau sosai.

Da daddare ya dawo, sai dai sai wani share ta yake yi, dan ya ji haushin tambayar da tayi masa.

"Master, dan Allah ka yi haƙuri, na san tambayar da nayi maka tayi tsauri, amma ka yi haƙuri dan Allah, Allah Ya ƙara maka arziki da wadata, ya tsare mini kai a duk in da ka ke" yayi mata shiru yaƙi amsawa.

"Tuba nake, tare da dukkanin girmamawa kaina bisa wuyana, nake roƙon ayi mini afuwa, ayi haƙuri a yafe wa ƴar madara ranka ya daɗe, Allah ya ƙarawa zamaninka tsayi, ya kare ka ko a gida ko dawa ayi haƙuri ina ƙara bada haƙuri namijin mazaje"

Ba ƙaramin fasa masa kai kalamanta suka yi ba, duk da ba yau aka fara yi masa kirari ba, amma sai ya ji nata ya zama na musamman, har cikin kansa ya ji kirarin.
Amma kamar wani basaraken zaki, haka yayi shiru ya cigaba da kaɗa ƙafa.

"To in dafa ruwan wanka na kai toilet É—in tsakar gida? Na san an gaji da yawa yau.

Ya kalleta ya ce "Ba na so"

Ta sakar masa wani ƙasaitaccen murmushi ta ce "Ai na ce ayi haƙuri, manya ba sa fushi fa" ta yi maganar cikin shagwaɓa.

A taƙaice ya ce "Kai mini"

Bayan yayi wanka, suka zauna a falo, suka ci abincin dare, dama tun a hanya ta sayo wa magenta kifi, ta nutsu tana bashi, tana yi wa master hira.

Kasancewar É—akunan an yi sabuwar plasta, ya sanya suka kwana a falo, sai da ya tabattar ta yi bacci, sannan ya fice tsakar gida yayi shaye-shayensa.

Gaba ɗaya washegari jauhar a gidan mai ɗinki ta wuni, ta tayata aikin ɗinki, saboda gidanta su Al'amin suna aiki, hatta ƙofar gidan sai da aka yi wa plasta, gyara ko yaya yake kyau ne da shi, sai ga gida yayi kyau sosai da sosai.

***
Yau É—aya ga azumi, ranar jauhar tana da exams, Al'amin ya ce ta zo ta hau babur É—in sa ya kaita, babu abun da ta tsana irin yadda yake yawo da babur É—in babu salansa, ga babur É—in kamar na 'yan gwangwani,saman babur É—in nan duk a ragargaje, kana kallon wayoyin da aka yi wearing É—in nan da su.
Amma dan kar ta watsa masa ƙasa a ido, haka ya karkato babur ɗin, ta rirriƙe shi ta hau, suka tafi.

Ko da ta dawo a gida ta tarar da shi, duk idonsa yayi ja, wanda idan ba da ƙwaƙwƙwaran dalili ba, ba za ka ganshi a gidan ba.

Ta kalleshi ta ce "Master na dawo"

Ya É—aga mata hannu kawai.

Ta shiga ta canza uniform, ta dawo yana kwance yayi wujiga-wujiga.

Ta fito ta shiga kitchen, dan ta É—ora musu abun buÉ—a baki da wuri.

"Master wai duk azumin ne, ko magana ta gagara" yayi mata shiru. Kawai ta hau dariya "Wallahi master ranar da babu abinci ban san yaya zaka yi ba, wato ba ka ko azumin nafila, yau É—aya duk ka fita hayyacinka har haka?" Hararta yayi, yayi mata banza.

Ta din ga yi masa dariya, ƙarshe ya koma tsakar gida ya shimfiɗa tabarma, yayi shame-shame kamar gawar sababi.

Ko da aka sha ruwa, ba yadda ba ta yi da shi ya tafi masallaci ba, ya ƙi ya shanye lemo jug guda, da uban ruwa kamar amale, kuma ya fara da cin shinkafa, maimakon ya fara da abu mai ɗumi yaƙi.

Ta ce "Ohh ni matar master, ya Allah kar ka hanamu abun da zamu ci a kowane hali, ranar da babu abinci akwai matsala master magana ma ta gagara yau azumi ɗaya kamar zaka rasu?" Yayi mata shiru yaƙi kulata.

A É—an tarin da take yi, da kuÉ—in da ya bata daf da azumi, tayi musu sayyayar kayan tea saboda tanadin azumi.

Sai da aka yi azumi biyar, sannan Al'amin yake iya fita idan yana azumi, ya je ya É—an yi neman kuÉ—insa, gefe ga black market É—in su ta sayar da kayan maye.

Yau ya dawo da la'asar ya sheme a falo, sai sauke numfashi yake yi.
Chapter 81 · 0% Book details