← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 95

Sashe 41

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaƙin neman zaɓe da zan je, ina son a zubar da jini ne, a tayar da tarzoma ayi hatsaniya sosai da sosai, sai kuma ranar zaɓe"

Ba tare da ya kalle shi ba ya ce "Shiyasa ka fito da ni, saboda zan yi maka aiki shi ne ka fito da ni ko?"

"Eh saboda haka ne, kai ne ba ka ji, ka fiye rigima, na yi na yi ka fita sabgar madakin nan, ka haƙura, amma kamar annabi da kafiri, kullum cikin harin juna ku ke, kai ne faɗa a nan kai ne a can, wai fa har sayen rigima ka ke yi"

Ya katse shi da cewa "Nawa zaka biyani?"

"Zan baka dubu hamsin kai da yaranka".

"ÆŠaurin shekara biyar a gidan yari, shi zan yi a dubu hamsin ni da yarana, ka duba babbar kasada ce"

Indabo ya yi murmushi ya ce "Baka da matsala in dai kuÉ—i ne"

Ya tashi tsaye ya ce "Kamar yadda ka yi a wannan karon, ka neme ni kai tsaye, haka nake son ya cigaba da kasancewa, ba na buƙatar sanya wani P.A ɗinka ya neme ni, ya sanar mini da saƙonka"

"Na fahimta, ka san mu ƴan siyasa dole sai muna yi, muna ɓad da sahu, baka da matsala".

Al'amin ya jinjina kai, ya sa kai ya bar falon, cikin takun ƙasaita.

*****
Saifu ne ya shigo gida, wajen ƙarfe uku da rabi, ya tarar da Jauhar tana wanki a tsakar gida, gidan babu kowa, yaran duk sun tafi makaranta.

Ta É—ago ta ce "Yaya sannu da zuwa"

Ya amsa da Yauwwa "Ina makarantar islamiyyar?"

Shiru ta yi ta sunkuyar da kai, ba ta amsa masa ba.

"Da ne nake fa"

"Amm..dama ban biya kuÉ—in makaranta bane, sun ce kar na sake zuwa sai na biya"

"Kuna kin gaya wa Baba?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

Cikin takaici ya ce "To saboda me?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Saifu ya ce "Ke dai sokuwa ce wasu lokutan, dubu uku ne ko? Tashi ki saka uniform ki tafi" yayi maganar yana ciro kuɗi daga aljihunsa, ya miƙa mata dubu uku.

Fuskarta ta faɗaɗa da murmushi, ta saka gwiwoyinta a ƙasa, ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai yaya, Allah ya ƙara arziki".

Ya ce "Amin, bar wankin, tashi maza"

Ta ce "To kar maman su Hafsa ta dawo ban gama ba, labulayenta ne"

"Ajiye, su hafsa idan sun dawo su wanke mata, maza ki tafi".

Cikin murna ta tashi, ta tattare kayan wankin, ta shirya cikin uniform É—in ta, ta tafi islamiyya.

Duk da yau ma sai da aka zane ta, sannan ta shiga ta kai kuɗin makarantar tana ta kuka, dan ba ta ƙaunar duka sam.

Sai dai duk da kukan da tayi, hakan bai hanata farincikin ganin ta koma makaranta ba.

Sai dai bayan ta koma gida, Anty ta rufeta da bala'in ta tafi ta bar mata bedsheets É—in da ta saka ta wanke mata.

Jakarta kawai ta ajiye, ta hau wankin da aka sakata, bayan ta sha uban zagin tsamar nama, ita duk hakan bai dameta ba, ta kammala wankin sauran bedsheet É—in, ta wanke kwanuka ta mayar da abincin dare.

Duk ƴan matan gidan suna zaune, itakaɗai take aikinta a tsakar gidan, idan baƙo ya zo sai ya yi zaton mai aiki ce.

***

Yau tun a makarantar boko, Jauhar ta ji period ya zo mata, gashi kuɗin pad ɗin nata saura ɗari da hamsin ba su gama cika ba, sai kame jikinta take yi, saboda tsoron kar jini ya ɓata ta.

Da ƙyar ta isa gida, tana ta lissafin yadda za ta yi, gashi idan ta yi amfani da tsumma, lalata mata fata yake yi, ƙuraje duk su feso mata, ta rasa in da zata saka ranta.

Haka ta wuni tana fama, ga uban ciwon mara, kamar tayi hauka, dan ma ta samu paracetamol a wurin Yaya saifu ta sha, ga uban aiki dan babu mai ɗaga mata ƙafa, haka nan ta saka tsumman, take amfani da shi, idan ba haka ba ta san haka za ta yi ta staining.

Da magariba, tana zaune a tsakar gida, ta cinye ɗan abun da ta samu ta ci, wanda sam ba ta ƙoshi ba, duk da ita ta girka, sai lashe hannu take yi, Baba yayi sallama.

Aka din ga jera masa sannu da zuwa, yana amsawa.

Ya kalli Jauhar ya ce "Waliyiyya ya na ga kina suɗe hannu, ba ki ƙoshi bane?" Tayi murmushi ta girgiza masa kai ta ce "Alhamdilillah, na ƙoshi baba".

Ya ce "To madalla, Allah shi ne abun godiya, akwai wani mutum da ya zo wurina yayi mini maganarki, ban sani ba, ko ke ki ka turo shi" Gaban juahar ya faɗi, ta kalli in da mama ke zaune a kan tabarma, ita ma tana cin nata abincin. Sau ɗaya saurayi ya taɓa biyota gida, mama ta ce idan wani ya kuma zuwa wurinta, ko ta bawa wani damar ya zo wurinta, sai ta kusa halakata, yayyenta ba su auru ba, ba za ta fara kawo musu maza ba, duk da dama shekarun nata ba yawa ne da su ba, haryanzu a SS2 take shekara goma sha shida, sai dai hasken fatarta ke ɗaukar idon samari ƴan bana bakwai, su biyota wai suna so, saboda kashedin mama ta koma saka niƙab.

But Anty, babar su hafsa ta fito daga ɗakin ta, tana jiran ta ji ƙarashen maganar.

Mama ta ce "Ba magana ake yi miki ba?"

Jauhar ta girgiza kai ta ce "A'a Abba, wallahi ban san kowa ba, ban turo kowa wurinka ba"

"Ƙarya ki ke yi, zaki aikata, ba abun mamaki bane ba kina halin kule-kule a waje, dan a zahiri kina da fuskar tsoron Allah, amma a baɗini ba kya ji" Anty ta ara ta yafa ta ƙarar da zancen.

Baba ya ce "No, shi ma ya gaya mini, bai yi mata magana ba, ya zo ya fara samuna ne, na dai tambayeta ne kawai dan na tabattar, zan bashi dama ya fara zuwa wurinta, dan naga da gaske yake yi."

Dumm ƙirjin Jauhar ya buga, ta fara zance yanzu, makarantar kuma fa, ga burinta na son yin karatu, duk da aure ba ya hana karatu, to amma idan wanda zata aura ɗin ba zai bari ba fa?.

Da sauri mama ta tashi ta bishi É—aki, tana yi masa magana "Yanzu aurar da jauhar É—in zaka yi, ga yayenta duk a jibge, su kusan biyar babu wadda ka aurar?"

Ya tsaya ya kalleta ya ce "To laÉ—ifa, tara su zamu yi tayi ba zamu aurar ba? Tun da ita Allah ya fara kawowa sai mu fara da ita, ita ma ta huta"

A take ta haɗe rai ta ce "Ban gane ita ma ta huta ba, na fuskanci duk lokacin da magana irin wannan ta tashi, sai ka nuna kamar bana ƙoƙari a kan riƙonta, kamar zaluntar ta nake ko?"

Kamar yaronta ya ce "A'a bance ba"

"To wallahi ba za ayi wa jauhar aure ba, ga su Sajida ba, wannan ai cin mutunci ne".

Yayi mata shiru, bai sake cewa komai ba, ya ƙuduri aniyar, aurar da jauhar ko ba ta so.

***
A tsakar gida ta tsaya tana ta kwaÉ—a sallama, daga cikin falon aka amsa mata, wata matashiyar mata ta fito.

Suna ganin juna suka rungume juna, suna murna.

"Zakiyya Bala, yau ke ce a gari?"

"Wallahi kuwa Rahila".

"Ya aka yi ki ka gane gidan nan? Kin san lambarki na rasa".

Zakiyya ta ce "Ke wayata aka sace mini, tun da na canza layi na rasa lambarki nima, ai da Abba na haÉ—u a bakin titi, ya ce mini ai kun jima da dawowa unguwar nan, bamu da wani nisa bamu sani ba".

Rahila ta ce "Allah sarki, shigo daga ciki, shegiyar ƙawata, na yi missing ɗinki fa" suka shiga suna dariya.

Ta kawo mata ruwa da lemo ta ajiye, Zakiyya ta kalli gidan ta ce "Ikon Allah, nan ku ka dawo kenan?"

"Wallahi kuwa, ai yanzu ba abun, tun da aka damfare shi É—in nan, lamuran sai godiyar Allah, amma a hakan ma ai bamu tagayyara ba"

Zakiyya ta ce "Gasakiya ne, Allah ya ƙara rufa asiri, ina su kursum?"

"Duk suna makaranta, kin san tana level 3 ita yanzu, ina su hafsa, haryanzu babu labarin aure ko?"

"Haba Rahila, yaushe za ayi auren su Hafsa ba ki ji labari ba, wallahi babu shiru, abu kamar saka hannu, har na fara zargin uwargidana, sai na ga ita ma ga nata nan biyu, Sajida da surayya, suma babu ana ta shige-shige shiru, dan ma ni da ita kar ta san kar ce, an daÉ—e ana gogawa taga babu riba, na sha gabanta shi ne ta sarara mini".

Rahila ta ce "Subhanallah, kin ga nima ana ta fama, duk wanda ya zo kamar walƙiyya sai ya tafi, ni kuma ba zan bawa talaka aure ba wallahi"

"Ba ke kaÉ—ai ba Rahila, kin ga yaran nan, har mai suka shafa, sun yi É—as sun zama farare, kwalliyar nan, supplements É—in nan, na gyara dai, amma ba tsayayye duk sai shirmanmu"

"Ki daina damuwa fa, lokaci ne"

"Wallahi haka ne, ba ki san wani abun takaici ba, wai sai yarinyar nan, ƙanwar bayansu, jauhar ƴar bafulatanar nan da ya taɓa aura kwanaki, aka rabu tsiya-tsiya ƴar da ta mutu ta bari, wai ita wani ya ce yana so da aure, yarinyar nan sai da Laɗifa ta shiga ta fita, ko suturar kirki ba ta sakawa, wai amma a haka wani ya gani yake so, kin san ita ya bawa riƙonta"

Rahila ta kwashe da dariya ta ce "Ai wasu lokutan maza ƴan wahala ne, ga in da ya dace su je, amma wani wurin suke kai kan su. Ni kaina ga nawa ɗan riƙon ya sani a gaba, ɗan gidan zahra'u tsinannen yaron da asiri baya cin sa, babu irin kurciyar dan ban saka ayi masa ba, amma abu ya gagara".

Zakiyya ta gyara zama ta ce "Ke haba? Al'amin ko"

"Shi, ai ya zame mini bala'i Zakiyya, ya zama riƙaƙƙen ɗan daba da shaye-shaye, za ki ji matasa suna mai dogon zamani shi ne fa"
Chapter 41 · 0% Book details