← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 95

Sashe 90

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dodo ya din ga dariya, ya ce "Kuma zamanin Aminullahi dogo ne a wurin dodo ba, bana tunanin akwai wanda zai ture gwamantin sa a wurina, dan mai dogon zamani dan haka mai laya" yayi maganar yana kallon Walid.

Aka haÉ—a baki aka ce "Ka kiyayi mai zamani" suka yi abun da sigar raha.

Al'amin ya je gida, domin ganin Abbu, amma ya tarar baya nan, Rahila kuma tayi baƙi, ya shiga kitchen ya ga an yi uban abinci, ya kwaso fulasan yayi gareji da su, ya zauna ya hau ci, duk da ya san na baƙin ne.

Yana cikin ci, sai ga wata 'yar yarinya ba ta fi shekaru biyu ba, ta zo in da yake tana kallonsa, ta tsuguna ta saka hannu a kwanon, tana tsintar abincin tana ci.

Ya kalleta, sai ya tuna jaririyar ummi da ta rasu, yanzu ga shi duk su ukun babu su.

Sai ya din ga bata abincin a baki, amma hakan bai hanata saka hannu a kwanon miya ba, haushi ya kama shi, kamar ya kwaÉ—e ta, ya kama rigarta yana goge mata hannun, kawai ya ji salatin Rahila.

Ya É—aga kai ya kalleta ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku jama'a ku taimake ni, zai lalata 'yar mutane, Allah ya sa ba yi mata komai ba"

Sai yayi saroro yana kallonta, ya rasa gane mai take nufi, wanda ta yi hakan ne, dan huce takaicin tozarcin da yayi mata, na cinye abincin baƙi.

Shahida ta ce "Mama wanke wanke nake yi, ina hango su ba abun da yayi mata, abinci kawai yake bata"

"Ƙarya ne rufe mini baki dan ubanki, ke kin taɓa ganinsa yana ɗaukar yara ne, balle ba da abinci a baki, ni na ga abun da na gani" dama 'yar ta maƙwabta ce, uwatta ta kawota ta fita.

Ta tara wa Al'amin jama'a, wai ya saka wa yarinyar hannu a wando, da idonta abun da ta gani kenan.

Duk dakiya da dauriyar Al'amin, jikinsa ya hau rawa, ya kasa ko motsi daga wurin, mutane suka taru a garejin gidan, Abbu dama sallar la'asar ya fita, a masallacin yana lazumi aka je aka kirawo shi.

Cikin tashin hankali ya danƙo Al'amin, ya kwaɗa masa mari ya ce "Me ka yi wa 'yar mutane? Al'amin lalacewar taka har ta kai ga haka? Ni zaka zubarwa mutunci a idon duniya"

Shahida tana kuka za ta yi magana, Rahila ta hanata, wata mata ta cire pampers ɗin yarinyar ta duba ta, ta ce "Wannan yarinyar fa babu abun da aka yi mata, lafiyarta ƙalau da ya taɓata ma, ba za a ganta a haka ba"

Al'amin ya ƙwace rigarsa daga hannun Abbu, ya fice, yana jin zuciyarsa zata tarwatse, bai zarce ko ina ba, sai gidan dodo, suna ganin sa suka din ga tambayar sa, menene saboda yadda idonsa ya yi jawur, amma ya yi shiru ya ƙi kula kowa.

Walid ya kira dodo a waya, ya sanar masa ga mai zamani ya zo, cikin ɓacin rai da tashin hankali.

Ba a ɗauki lokaci ba, sai gashi, ya ce "Waye ya taɓa zuciyar magajin dodo, wa ya taɓa mini Aminullahi?"

"Al'amin ya ƙi magana sai huci da ajiyar zuciya, ga wani gumi da yake yi"

Dodo ya ce "Walid"

"Allah ya taimaki babban sarki"

"Narka jan tablet, ka bani" Walid ya narka ya bashi, ya miƙa wa Al'amin.

Ba tunanin komai, ya karɓa ya shanye ya ajiye kofin, wani zuuuuu ya fara ji a kansa, ya fara ganin hazo-hazo, a hankali ya fara ganinsu bibbiyu, daga haka bai sake sanin abun da ya faru ba, sai sha biyun dare ya farka.

Yayi sallolinsa, ya ci abinci, dodo ya ce "Magajin dodo, ba zan takuraka na ji menene ba, amma ya ka ke ji yanzu damuwar ta tafi gaba É—aya?"

Al'amin ya girgiza kai alamar a'a.

"Duk wannan dogon zangon da ka yi? Bari na baka wani haÉ—in"

Ya naɗa masa wiwi, ya kunna ya bashi, sai dai zuƙa ɗaya Al'amin ya hau tari, kamar zai shiɗe ya ce "Ƙara gwadawa, ba zaka yi ba" ya din ga zuƙa a hankali, tun yana tarin har ya daina.

Ayshercool
08081012143

A din ga yi, ana sauke hakki ₦500
0009450228
Aisha Adam jaiz bank

🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

    Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

    Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

    Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

     Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955

Tun daga lokacin, Al'amin ya fara shaye-shaye. Shiga layinsu ya gagare shi, saboda tsananin kunyar abun da Rahila ta yi masa na sharri.
Sai da ya shafe wata guda bai sake takawa gidan su ba, sai dai kewar Abbu ta din ga damunsa, da asuba ya tafi masallacin da Abbu yake salla, ya yi sallar asuba a waje, ya jira ya fito, Abbu yana tafe ya ji kamar ana bin sa a baya, ya tsaya ya waiwaya, duk da gari bai gama yin haske ba, da sauran duhu, amma hakan bai hana abbu gane Al'amin ba.

Ya tsaya, jiki a sanyaye ya ƙaraso, Al'amin ya risuna ya ce "Ina kwana"

"Kai daga ina? Ina ka tafi tsawon kwanakin nan? Duk yawonka ba ka wuce kwanaki kaÉ—an, amma ban sake saka ka a idona ba" kallon Abbu yayi, yana tunanin da ma yana jin wani abu idan bai saka shi a idonsa ba?.

"Ina nan"

Abbu ya ce "Kana can kana shashanci, gaishe ni ma ba zaka iya zuwa ka yi ba ko?"

Ya ce "Korata ka ke idan na zo"

"Ba dole in kore ka ba? Tun da kai a rayuwarka ba ka gaya wa kanka gaskiya, kuma duk in da ka zauna sai an yi faÉ—a da kai. Ka yi salla ne?" Al'amin ya jinjina kai.

"To wuce mu tafi" yayi maganar yana nuna masa hanya, sai Al'amin yayi ajiyar zuciya, tare da tuna masa baya, da yake É—ora shi a wuyansa idan suka dawo daga masallaci, har tsere suke yi da Abbu, duk yadda Abbu yake ji da shi, yanzu ya zama tarihi.
Yana tuna abun da ya faru ƙarshe, sharrin da Rahila ta yi masa, sai ransa ya ɓaci, ya ƙi shiga layin ya tsaya.

Abbu ya waiwayo ya ce "Ya ka tsaya kuma?"

"Tafiya zan yi"

"Zuwa gidan uban wa?"

Al'amin ya ce "Da wani idon zan kalli sauran mutanen layin, bayan ga sharrin da aka yi mini, idan na ga matar nan, zan iya kasheta, sai anjima kawai na tafi, dama ganinka nake son na yi, tun da kana lafiya Allah ya ƙara lafiya" ya juya ya tafi, Abbu ya tsaya yana kallon Al'amin har ya ɓace wa ganinsa.

Ko da ya koma gidan da suke, walid ya fuskanci Al'amin yana cikin damuwa, yayi masa tayin sigari, ya girgiza masa kai, can ya ce "Walid"

Ya amsa da "Na'am"

"Dan Allah ya aka yi ka fara Shaye-shaye?"

Walid ya É—an yi shiru sannan ya ce "Wan babana ne ya cinye mini gado, nake ta wahala ina fama da rayuwa, matsin rayuwa ya isheni, kuma shi ba tallafa mini yake yi ba, kawai na fara dafar kan kayan mutane, kuma da nasa na fara, aka kama ni aka kulle, rodi ma na sata lokacin, aka É—aure ni watanni shida, da aka kai ni prison ban saba ba, nake ta kuka saboda wahala, a can na haÉ—u da mai gida, sarki dodo, ya din ga kula da ni, bayan ya fita ya dawo ya biya mini tarar aka yanke mini, sake ni, kawai ya cigaba da kula da ni"

"Ina mamanka?"

Walid ya ce "Taɓ tana can tana fama da rayuwarta, kinko ya kanannaɗe rayuwarta, wannan tsohon auran wan baban namu, ya tattare gadonmu ya cinye, Sakandire kawai nayi, ita ma ba ganewa nake yi ba da kyar na kai. Tana fama da kula da ƙannena, ga bata da cikakkiyar lafiya, ni kuma bana iya tallafa mata, har gara yanzu mai gida ya kan bani kuɗi ya ce na je na gaishe ta"

Al'amin ya jinjina kai ya ce "Ka cigaba da kula da ita, dan duk ranar da ka rasata, za ka yi kuka, kuma kar ka bari ta san irin rayuwar da ka ke yi"

"Na nawa kuma, ai wancan tsohon munafukin tuni ya gaya mata, tana yi mini nasiha sosai da addu'a, ba ta taɓa fushi da ni ba"

Daga haka Al'amin yayi shiru, yana cigaba da tunani.

Da sannu Al'amin ya zama gawurtaccen mashayi, duk in da dodo za shi, da Al'amin. Ta kai ta kawo har kudancin Najeriya yake tafiya da Al'amin, ba fatauci ba, har wuraren sarrafa miyagun ƙwayoyi Al'amin ya sani, har manyan mutane a ƙasar nan da suke ta'amalli da su da kasuwancin su ya sani.

Ya haɗa Al'amin da wani inyamuri, ya ƙara gogar da shi a kan harkar na'ura mai ƙwaƙwalwa, yadda ake amfani da ita a aikata laifuka daban-daban, suka sake danganawa da wani bature, ya ƙara koyar da Al'amin sarrafa computer wurin yin laifuka.

Ya zamana kasuwancin miyagun ƙwayoyi, na ƙasashen da suke maƙwabtaka da Nigeria, Al'amin ke tafiyar da kasuwancin su ta online.

Bai tsaya a nan ba, har cikin manyan 'yan fashi, dodo yake shiga da Al'amin.

Dodo ba ya fashi da makami, amma zama a gidajen gyaran hali daban-daban ya sanya ya san masu laifuka kala-kala da yadda ake aikata su, bai fiye harkar daba ba, yafi gane wa safarar ƙwayoyi da makamai.

Idan aka cewa Al'amin magajin dodo, sai dodo ya ce "Wannan dodon, da sauran imani a ransa, ɗan ƙaramin dodo ne, ba zai iya zama kamar ni ba, sonake ya horu, yadda zai iya tunkarar kowane ƙalubale, ciki har da babban burinsa na son ganin bayan madaki, dan kuwa madakin ma ya ƙwafe shi a rai, na cewar sai ya ga bayansa, tun da na saka ya sanya gwiwar sa a ƙasa wurin bashi haƙuri".
Chapter 90 · 0% Book details