← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 95

Sashe 86

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ta ƙara kula shi ba wunin ranar, dama kuma ficewa yayi ya bar gidan, ta rasa sai zuwa yaushe Al'amin zai yadda ya karɓeta su yi rayuwa, kullum ba shi da magana, sai maganar da zata tayar mata da hankali na zai rabu da ita, gaba Al'amin yayi hannun riga da duk tausayi.
Abun da zuciyarsa ta raya masa kawai yake yi, ko ya yi maka daÉ—i, ko akasin haka ba damuwarsa bane ba.
'yan yaran da suka din ga shigo mata yawon salla, su ne suka din ga É—ebe mata kewa da rage mata damuwa.

Sai bayan sallar magariba sannan ta sake ganinsa, tun da ta yi masa sannu da zuwa, ta ajiye masa abinci, ta koma gefe ta na danna wayarta.

Sai da ya ci ya ƙoshi, ya samu wuri a kusa da ita ya zauna, ya ce "Abun wasan, ya dai?"

Ta ɗaga kai ta kalleshi ta sunkuyar, ta hau wasa da yastun ƙafarta.

Hannunsa ya saka shi ma a yatsun ƙafarta yana tayata wasan da take yi da su.

"Master"

"Mmm"

"Meyasa ka ke son lallai sai ka sake ni ne? Saboda ka ga bani da makoma ko? Ban taɓa burgeka, duk ƙoƙarin da nake yi, ba ka appreciating kullum cikin tsorata ni ka ke, kana gaya mini abun da zai ɗaga mini hankali, me nayi maka ne?"

"Baki dace da ni ba, da salihin mutum nagari ki ka dace. Da zan iya samun mutum mai amana da zai riƙe ki, zan iya rabuwa da ke ya aura, you  have an innocent soul, that doesn't deserve someone like me, shiyasa nake yawan gaya miki haka. Ko jiya a fusace nake, na yi miki tsawa sai da ki ka yi kuka, ina ɗaukar hakkinki"

"To ni na ce maka bana son zama da kai ne? Ina yi maka addu'a, wataran zaka daina ai ko?" Tayi maganar tana kallonsa.
Yayi shiru bai yi magana ba, "Dan Allah ka yi magana, zamu iya rayuwa tare, irin damuwar É—aya, matsalar iyalan da muka tashi a tsakanin su, ba sai mu zama familyn junanmu ba, mu rayu cikin aminci da walwala. Amma master meyasa ka ke shaye-shaye bayan ka san yana da illa ga lafiyarka? Yana saka aikata abubuwan da bai kamata ba, kayi faÉ—a da mutane a zubar maka da jini, ko ka zubarwa wani, har kisan kai fa yake saka".

"Wa na kashe?"

Ta ce "Ranar da na fara ganinka, a unguwarmu, gawar wani na ganka da ita ka soka masa wuƙa"

Yayi murmushi, ya haÉ—iyi wani abu mai É—acin gaske.

"Ban taɓa kisan kai ba, ranar ce haɗuwarmu ta farko ko? Ban kashe kowa ba"

Cikin damuwa ta ce "Amma wuƙa fa na gani a gefen cikinsa, kuma meyasa ka ke shaye-shaye?"

"Bana son silly question, rabu da ni" ta gyaɗa kai kawai ta ƙyale shi.

Ranar hawan salla kuwa,  Jauhar ba ta san me ake yi ba, Al'amin ya haɗa yaransa, da miyagun makamai, da sunan tsaro kar wasu daga wani wurin su zo su fake da kallon hawan salla, su kawo musu farmaki su cutar da wani.

Sai dai sun yi ba ta kashi da wasu marasa jin sosai da sosai, ciki kuwa har da yaran madaki.

Sai da 'yan sanda suka yi kame sosai da sosai, daga wurin hawan Al'amin bai koma gida ba, ya wuce cikin gari, saboda kar jauhar ta ganshi da makami, da jini.

A cikin garin ma, sai da suka yi wata fitinar, aka yi sare-sare da faÉ—ace-faÉ—ace.

Sai bayan kwana biyu, jauhar take jin labarin abun da ya faru a wurin hawa, ganin Al'amin lafiya ƙalau ya sanya ta kwantar da hankalinta, tare da bawa kanta yaƙinin cewar babu shi a rigimar.

Kwana na huÉ—u, tana kitchen tana girki, tana shirin kaÉ—a miyar cin tuwo, maman halimatu ta shigo gidan a gigice.

Jauhar ta ce "Maman halimatu lafiya kuwa?"

"Ke kina nan baki san abun da yake faruwa ba?"

Cikin rashin fahimta ta ce "A ina?"

"Wani ɗan daba ne wai madaki, daga can unguwar ku ya zo unguwar nan wai neman mijinki, wai ya illata masa yara, sai tarwatsa mutane suke yi, suna sara kan mai uwa da wabi a guje na ƙaraso"

Cikin tashin hankali ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" take kanta ya sara, jikinta ya hau rawa, ta É—auki wayarta ta kira lambar sa, sai dai tayi ta ringing baya É—agawa.

Hijjabinta ta É—auka, maman halimatu ta ce "Ina zaki? Saran mutane fa suke yi, duk wanda suka samu duka ko sara".

Ai ba ta ko tsaya bata amsa ba, ta fita cikin matsanancin sauri da tashin hankali.

Ba ta san in da za ta nufa ba, addu'a kawai take yi da roƙon Allah, Allah ya tsare mata mijinta.

Mutane na guje-guje ita kuwa kutsawa take tana duba ina zata ganshi tana kuka.

A wani layi ta hango shi, ya riƙe wani matashi, idon Al'amin kawai ta kalla ta san a buge yake, babu alamar mutunci a idonsa, idanun sun yi jawur sai gumi yake yi, yanayin sa ya tabattar mata da ha tafka ɓarna, kafin ta ƙarasa, ya fito da harshen sa waje, kamar yadda yake yi, idan ya ƙudirci aniyar yin wani abu, ya ɗaga sweazland ɗin sa, babu tsammani ya ganta a gabansa, ta riƙe rigarsa tana girgiza masa kai cikin tsananin tashin hankali.

"Idan ka kashe shi, rufe mini kai za ayi, ba lallai na sake ganinka, ka yi haƙuri kar ka yi kisan kai dan Allah"

Jikinsa tsuma kawai yake yi, ya aiwatar da abun da zuciyar sa take raya masa, saboda yadda haÉ—in da yayi amfani da shi, yake fizgar kansa yake jin sa tamkar jinjirin doki, zuciyarsa kuma kamar an kunna wuta.
Ta rirriƙe hannun da ya riƙe wuƙar da shi, da hannu ɗaya ya yi jifa da matashin gefe, shi kuma ya saki wuƙar, sai tangaɗi yake yi, ya kasa tsayuwa, sai gumi da yake tsatsafo masa ya furta "Madaki" kawai ya yanke jiki ya faɗi, sai a lokacin ta ga uban saran da yake gadon bayansa, ashe duk abun nan an sare shi a baya, rigarsa ta rine da jini.

Wani irin gigitaccen kuka ta saki, ta ce "Na shiga uku, dan Allah ku taimaka mini a kai shi asibiti" tayi maganar tana girgiza shi. Ya kalleta da idanunsa, suka yi jawur, jikinsa ya fara rawa ga gumi ya jiƙa masa fuska.

Ragowar mutanen da suke wurin, suka dare suka bar ta da shi, a wurin.

"Master dan Allah kar ka rufe idonka, yanzu zamu tafi asibiti, Allah ka kawo mini É—auki, Allah ka duba lamarin nan".

Guduma ne ya shigo cikin layin da gudu, ya jefar da makamin hannunsa ya ƙaraso, wata irin ajiyar zuciya ta saki, yana zuwa ya jijjiga Al'amin ya ce "Master" sai dai idanunsa sun lumshe, saboda jinin da ya zubar.

Yayi ƙoƙarin ɗaga Al'amin, ya saɓa shi a kafaɗarsa, amma abu ya gagara, ba ƙiba ce da shi ba, sai dai akwai nauyi.

Ya kalli Jauhar da ta rikice, take ta kuka ya ce "Anty ki kwantar da hankalinki, in sha Allah yanzu zamu kai shi asibiti".

Ya din ga wani irin fito, kan ka ce kwabo, wasu matasa suka din ga ɓullowa da ɗaya ɗaya, su ma suna fiton wasu suna fitowa.

Suna zuwa suka yi tara-tara suka sunkuci Al'amin, guduma ya saɓa shi da ƙyar, da ƙarfin tsiya suka ƙwaci 'yar ƙurƙura a titi, suka ce mai ita ya bi si Asibiti su karɓa.

Sai dai da suka je, ma'aikatan lafiya, suka ce ba za su karɓe shi su duba shi ba, sai da jami'an tsaro.

Cikin kuka ta ce "Dan girman Allah kar ku yi mini haka, ku ceto ransa kar ya rasa ransa, dan Allah ku fara duba shi, kan a kawo 'yan sandan" ma'aikatan suka ƙeƙashe ƙasa suka ce, sai fa jami'an tsaro sun zo".

Ta din ga rusa kuka a cikin emergency, guduma sai bata haƙuri yake yi.

Ta kasa jurewa, ta tashi ta bi wani likita, ta riƙe rigarsa tana kuka ya ce "Dan girman Allah ka ceto rayuwar mijina, kar a rasa ransa dan Allah"

Ya ce "Ba laifina bane ba, dole mu san meyafaru kafin mu taɓa shi".

Kan kace kwabo, sashen emergency ya cika da 'yan daba, saboda an kawo al'amin.

Babu tsammani ta ga shigowar liti tare da Walid, da wasu tawagar marsa jin suna take musu baya.

Suka ƙaraso, in da jauhar ke zaune, da Al'amin a gabanta.

Walid ya ce "Madam, ya aka yi haka ta same shi?"

Ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, kawai ce mini aka yi ana faɗa, na je na tarar da shi, da zai cakawa wani wuƙa amma ya fasa, kawai dai ya ce madaki ya faɗi ashe an sare shi, kuma sun ƙi duba shi wai sai ƴan sanda sun zo, dan Allah ka saka baki yaya Walid.

Ya kalli liti ya ce "Zan ɓallo ruwa, a toshe magudanan daga waje" liti ya jinjina kai, ya ja guduma suka fita.

Wasu daga cikin matasan suka shigo, suka koro wasu daga majinyata waje, suka ritsa likitoci da makamai, sai sun duba Al'amin.

Aka ce su kai shi kan gado, Walid ne ya ɗauke shi, suka kai shi kan gado, saran da aka yi masa ba ƙarami bane, yayi zurfi, hakan ya ƙara razana Jauhar.

Liti ya ce "Wannan yankan madaki ne yayi masa shi, wannan shegiyar wuƙar da aka ce ta tsafi ce, da ita yayi masa saran".

Jauhar ta ce "Na shiga uku, ba zai tashi ba kenan?"

Walid ya ce "Zai tashi ki kwantar da hankalinki"

Aka yi wa Al'amin ɗinki, kamar ƙwarya aks ɗinke bayansa, sai dai walid ba su bari an yi a gaban jauhar ba, aka ɗibi jininsa, dan dubawa idan sai an ƙara masa jini, sai dai baya buƙatar ƙarin jini, sai dai an saka masa ruwa saboda jirin da yake yi ya hana shi tashi.

Sai dai ana tsaka da duba shin, jami'an tsaro suka iso, Walid ya ce kar matasan nan su bar su su shigo, sai an gama yi masa komai.

Aka din ga artabu da 'yan sanda da dandazon, yaran da suka yi wa harbar emergency ƙawanya, da kyar 'yan sandan suka shiga.
Chapter 86 · 0% Book details