← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 95

Sashe 26

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannu a hankali barrister Naja'atu take bin titin ƙauyen, sai tsaki take yi saboda yadda garin yake babu kyakkyawar hanyar shiga. Sai uwar ƙura da kwazazzabai a hanyar.
A hankali ta cigaba da tuƙin har ta ƙarasa in da take son zuwa.

Sai da ta shiga tsakiyar tsakar gidan, sannan ta yi sallama.

Daga cikin É—aki a ka amsa sallamar.

Daga baya matar ta fito daga É—akin, ta ce "Waye?" Ganin barrister Naja'atu ya sanya ta É—an saki fuska, ta bata damar shiga É—akin.

Shame-shame taga rammaa a kwance a kan katifa, ta nemi wuri ta zauna a gefe.

Ta kalli in da ramma take, sannan ta mayar da idonta kan maman ta ce "Na dawo ne na ji me kuka tsayar, kuma na ga haryanzu ba ta da lafiya, anya ramma ba shagwaɓa a wannan lamarin? ya ci ace kin ware ai, da auren ma aka yi miki ai da kina gidan miji, ko shi ma hakan zaki yi ta yi masa".

Fashewa da kuka ramma tayi, cikin tsananin baƙin ciki da takaici.

"Meye kuma na kuka? Wannan abun da ki ke yi, sai mutane sun san halin da ki ke ciki?"

Cikin sanyin jiki da damuwa, maman ramma ta ce "Tun da abun nan ya faru, take rashin lafiya, jiya mun je asibitin sha ka tafi, na garin nan, an ce ciki ne da ita" tayi maganar tana fashewa kuka mai taɓa zuciya.

Sak Naja'atu tayi, tana kallon su.

Ta numfasa ta ce "Wai wannan kukan na menene ku ke yi haka, kukan zai yi muku magani ne? Ai wannan ba abun É—aga hankali bane ba"

Cikin tsananin mamaki, maman rahama take kallon barrister Naja'atu.

"Baiwar Allah, ce miki na yi fa, an ce mini ciki ne da ita, wanda ya dubatan ɗan garin nan ne, na san dole maganar nan ta fita, auren yarinyar nan ba zai yiwu ba, amma kina nuna bakomai bane ba, dan girman Allah a karɓowa yarinyar nan hakkinta".

Naja'atu ta ce "Baiwar Allah, ko fa an kai yaron nan kotu yayi prison, abun da zai faru ya riga faru, ba kuma zai goge ba, ɓacin suna kuma ya riga ya ɓaci.
Matsalar mutanen mu na Arewa, kuna giramama al'ada da addini a kan Æ´ancinku. Da in da aka cigaba ne, zata iya haife abun da ke cikinta, idan tana so, and rise him as a single mother, har ta iya neman ya din ga biyanta wani abu a kotu, shikenan. But for now, za a iya zubar da cikin ta cigaba da harkokinta sai me? Is an adolescent crises kowa ma zai iya faruwa da shi".

Cikin mamaki maman ramma ta ce "Baiwar Allah kuma ke musulma ce?"

"Ƙwarai kuwa, muslma ce ni gaba da baya, mafita nake baku da shawara. Zan je na yi booking a saka rana a can cikin gari, private hospital, a cire cikin lafiya ƙalau za a cire shi, yanzu an cigaba nesa ba kusa ba, ku karɓi kuɗin ku ku rage zafi".

Rma ta fashe da kuka ta ce "Ni mama tsoro nake ji, an ce mutuwa ake yi, dan Allah ni dai a kai shi wurin alƙali, an ce kina taimako dan Allah ki taimaka mini, ji nake kamar na mutu na huta, ba a taɓa cikin shege a garin nan ba sai a kaina, dan Allah ki taimaki rayuwata, wallahi wanda zan aura ya ji labari ba zai aure ni ba, babu kuma wanda zai ce zai aure ni, cewa za ayi na zama ƴar iska" ta ƙarasa maganar kamar ta shiɗe.

Barrister Naja'atu ta ce "And so what dan an fasa aurenki? Zaki iya zama duk abun da ki ke so a rayuwa ko da aure ko babu, waye ya ce muku aure shi ne limit na rayuwar Æ´a mace ne? dan Allah ku fuskanci rayuwarku, ku daina bari ana cutar ku da addini da al'ada".

Cikin baƙin ciki maman ramma ta ce "Kin ga ya isa baiwar Allah, idan bawa bai riƙe addini ba haka zai ta rayuwa kamar dabba a gari, babu ƙa'ida babu hukunci? Wannan ai salon bawa yaro damar ya je yayi zina ne, ko ni da nake jahila a cikin ƙauyen nan, sam maganarki ba ta da tushe balle makama a wurina, dan haka ki tashi ki tafi kawai, bana buƙatar taimakon naki, cuta ce an cuce mu Allah ya isa kawai"

Naja'atu tayi wani irin murmushi ta ce "Ƙarshen abun fa kenan, ki yi Allah ya isa, na biyo miki da masalaha amma kin ƙi, shikenan idan kin ƙi ji ai ba kya ƙi gani ba, duk abun da ya biyo baya wannan shi ne abun da ki ka zaɓa. Sai dai ina sake yi miki gargaɗi da babbar murya, kar ki kuskura ki sake shiga kafafen watsa labarai ki yi magana, idan kuma ki ka sake, ba ruwana"

Ta tashi ta sake ajiye musu kuÉ—i, da complementary card É—in ta, ta ce "Akwai lambar wayata a jiki, na san zai iya yi muku amfani, idan ku ka ga babu sarki sai Allah, domin kuwa barin cikin nan, dai-dai yake da zama da ajalinta, dan kome zai É—auka, uban wanda ya aikata laifin, ba zai bari ba"

Gaba ɗaya bin ta suka yi da kallo, har ta tashi ta fita, ramma ta fashe da wani irin kuka, tare da jin ƙarshen rayuwarta ya zo.

Mahaifiyarta ta kalleta ta ce "Ki yi haƙuri ramma, ina tare da ke in sha Allah, na san ko menene ya faru, ni ce sila, da ban tura ki aikatau ba, da haka ba ta faru ba, amma babu yadda zan yi ne, ki yafe mini dan Allah" tayi maganar tana kuka ita ma.

Sumayya na ta aiki a kan computer, sai dai hankalinta baya kan aikin sam, kawai dai tana yi ne, amma ƙasan zuciyarta tsoro da fargabar dalilin da ya sanya, aka ce ta je gidan honorable Indabo ta yi hira da shi take ji, idan a kan laifin da ta yi wancan karon ne, ai ta bayar da haƙuri, kuma lokacin tana farkon zuwa ne.

Sallamar murtala ce, ta dawo da ita hayyacinta, tayi murmushin yaƙe ta ce "Uncle murtala, saukar yaushe?"

Ya nemi wuri ya zauna ya ce "Agogo sarkin aiki, yakamata a ƙara miki matsayi a gidan nan fa"

Ta waro ido ta ce "Ni a wa?"

"Ke a ma'aikaciya jajirtacciya mana, wai ya aka yi mutuniyar take ɗaga miki ƙafa yanzu, lawisa?"

Sumayya ta ce "Hmm, Arfa ce ta ce na daina jin tsoronta, nima na nuna mata bani da kirki idan ta takura mini, shi ne fa ta sarara mini".

"Ai matar nan Æ´ar bala'i ce lamba É—aya"

Sumayya ta sake tattara nutsuwar sa a kan sa ta ce "Yauwwa ncle murtala, akwai matar da ka yi recording, ta zo an yi raping Æ´ar ta, an ce Barrister Naja'atu ta shiga case É—in, ina aka tsaya ne?"

Da sauri ya ce "Rufa mini asiri, ni da aka kusa korata a kan case É—in, kuma lawyoyi da masu kare hakkin É—an adam, sun yi casa a kan case É—in, sai dai tun da ta shiga cikin lamarin, kowa ya ja da baya"

Sumayya ta ce "Ikon Allah, to ai haryanzu ban ji a ina aka tsaya ba, wai É—an waye ne yayi?"

"Taɓ ba zaki ji mutuwar sarki a bakina ba, nima ba ta faɗa mini ba matar, wai dai yaron ɗan masu kuɗi ne, wai ɗa ne ga wani ɗan majalisa, ba ta san sunansa ba, a gidan ƙanwar ɗan majalisar yarinyar take aiki, sun je gidan ta bi ba'asi, an hana su shiga, masu gadin da suka kai yarinyar asibiti ma duk an canza su"

Cikin tausayawa Sumayya take girgiza kai ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shikenan akwai Allah, amma kana ganin ita Bunkuren za ta yi wani abun kirki a kai? Meyasa ba za a bibiyeta ba, a ji a ina aka tsaya a case É—in ba, atleast a gurfanar da shi a kotu mana"

Ya miƙe tsaye ya ce "Lallai ƙanwata baki san ƙasar nan ba, ai dokar ƙasar nan a kan talaka kawai take aiki, ko ɗan kansila ne, ba za su hukunta shi ba, ita kanta barrister nan akwai ayar tambaya a kan ta, duk da a zahiri ta Allah ce, amma yadda ake tsoronta komai tayi, babu wani mai challenging ɗin ta, akwai wata a ƙasa".

"Gaskiya dai, Allah ya sa mu dace "

Ya amsa mata da Amin.

Nasir yana ta yi wa Nabila bayanin, irin cigaban da yake samu a neman viper, amma hankalinta ba ya kansa, jin sa kawai take yi, kawai ji take kamar ta gaya masa halin da ake ciki, amma ta fasa, dan ta san faÉ—a zai yi mata.
Hankalinta bai dawo jikinta ba, sai da ta ji ya ce zai je Abuja.

Ta kalle shi ta ce "Abuja kuma? Me zaka yi?"

"Harkar aiki mana, a ƙalla sati zuwa wasu kwanaki"

Ta kwaɓe fuska ta ce "Har sati?"

"Eh mana, ko in tafi da ke ne?"

Tayi murmushi ta ce "Wace ni, Allah ya bada sa'a"

Kafin ya amsa, wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗaga ya saka a kunnensa, "To" kawai ya ce, ya ajiye wayar ya miƙe ya ce "Bari na shiga sashen mama, tana nemana"

Nabila ta ce "To"

Agogon hannunta take kallo, yau ko Abba zai jajjagata idan ya dawo bata nan sai ta fita, dan tuni ta ɓoye takalminta da hijjabinta a harabar gidan, za ta lallaɓa ta fice, yadda take ji a ranta, ko zata rasa rayuwarta, ba ta da wani burin da ya wuce ta ga an kama Aminu Viper, domin kuwa shi ne ƙashin bayan matsalar aikin daba da dillancin miyagun ƙwayoyi, gefe guda kuma ga dakon burin da take yi.

"Nasiru sau nawa nake gargaÉ—inka a kan yarinyar nan? Ban isa in gaya maka magana ka ji ba ko?"

Cikin son kare kai ya ce "Wallahi mama ba abun da ki ke tunani bane ba, magana muke yi kawai a kan harkar aiki"

"Ni ka yi maganar harkar aikin da ni mana. Wai ma yaya muka yi da kai, ina alƙawarin mu?"

"Mama dan Allah ki ƙara mini lokaci, sonake na kammala aikin nan na nutsu, kin san komai lokaci ne"
Chapter 26 · 0% Book details