Sashe 43
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Al'amin ya ɗaga idanunsa, da suka yi ja fiye da lokacin da ya shigo, ya ƙara matsawa kusa da mahaifiyar, ya zuba masa ido sannan ya ce "Na san ina wari, na san kullum a buge nake, a kowane lokaci zan iya ɗaukar makami na hallaka duk wanda ya yi gaba da gaba da ni, ko wanda bai ji ba bai gani ba. Wasu lokutan ma banbancina da mara hankali kaɗan ne, na san ba na jin magana ko kaɗan, bana tsoro ko shakkae aikata duk wani abu da zuciyata ta raya mini, amma idan ban zo wurinka ba wurin wa zan je? Da haka nake? haryanzu ban san laifina a wurinka ba Abbu, zan yi ƙoƙarin daina zuwa gidan nan kamar yadda ka buƙata, ko aka ce maka ana buƙata, amma idan na daina na daina kenan har abada wallahi! Ka huta lafiya" yayi maganar yana shafar saman hannun mahaifinsa.
Yana miƙewa zai wuce, yayi ball da flask ɗin ruwan zafin da yake tsakiyar wurin, da kwanukan. Gaba sai da suka razana.
Ta ce "Ka gani ko?"
Shiru mahaifin Al'amin yayi, ya tashi da sauri ya bi bayansa, sai dai yana fitowa daga falon, ya ga an jefo Abba, babban ɗan Rahil, ƙaton saurayi amma kamar an watso shara.
Ko ba a gaya masa waye ba, ya san aikin Al'amin ne, Abba kuwa bajewa yayi, ko shurawa ba ya yi, rahila ta fito tana kururwa.
Abbu ya leƙa waje da sauri, a can ƙarshen layi, ya hango Al'amin, ya zare wuƙa yana ta zuba sauri.
Ya rufa masa baya, yana ƙwala masa kira, amma ya ƙara sauri har da gudu, ya bar layin.
Ayshercool
08081012143
🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*
Ganin Aminu ya ɓace masa, ya sanya ya koma gida da sauri, rahila sai kururwa take yi, tana jijjiga Abba.
Ƙannensa mata su azima, suka kewaye shi suka hau kuka.
Abbu ya É—ebo ruwa, ya din ga zubawa Abba, har Allah ya sa ya buÉ—e ido.
Cikin kuka take cewa "Ka gani ko? Ba zaka taɓa yadda da ta'addancin ɗanka ba, har sai ranar da ya kashe mini ƴaƴa, me yayi masa zai yi masa wannan ɗibar karan mahaukaciyar ya watsar? Wallahi na gaji, ina ga tafiya zan yi na bar maka gidan nan kai da ɗanka, na rasa uban me yaron nan yayi masa, ko dan ba kai ka haifi abba ba, ya tsane shi daga shi har nazifi ni ban sani ba. Ni ba abun na kai shi ƙara wurin hukuma ba, ba sa yi masa komai sai dai a sako shi, ni na gaji".
Abbu ya ce "Dan Allah ki daina wannan maganganun, bari na samo mota, mu kai shi asibiti"
Abba kuwa ko magana ya kasa, Nazifi ne ya taimaka aka fita da Abba zuwa mota.
Al'amin kuwa da ya tabattar da ya tserewa Abbu, ya samu wani lungu, ya jefar da wuƙar hannunsa, ya samu wuri ya zauna, yana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai tsananin ɗaci da zafi a maƙogwaronsa, ji yake kamar numfashin sa zai ɗauke, babu abun da zuciyar sa ke raya masa, banda ya kashe matar Abbu wato rahila ya huta.
***
Gidan babu kowa, duk yaran sun tafi makaranta, mama tayi sallama a falon zakiyya.
Ta amsa tare da fitowa daga bedroom ɗin, tayi miƙa ta ce "Lafiya kuwa?"
"Au bacci ma ki ke yi? Lallai kam, to magana na zo mu yi"
Zakiyya ta ce "Ok, bisimillah zauna mana"
Ta nemi wuri ta zauna, ita ma ta zauna.
Mama ta kalleta ta ce "Kin san waye yake son Jauhar kuwa?"
"A'a sai kin faÉ—a".
"ÆŠan familyn mai atamfa ne"
Waro ido Zakiyya ta yi, har tana neman faÉ—owa daga kan kujera, ta ce "Wani mai atamfar?"
"Waɗanda dai ki ka sani,ba ma wannan ba shi zai tsaya takarar majalissar tarayya a yankinsu, jiya na tutsuye shi, yake gaya mini, ga kasuwancin atamfofi da lesuna da yake sayarwa, daga ƙasashe daban-daban yake order kaya, na din ga bugun cikinsa yana gaya mini, wai zata yi karatu idan tana so, idan business take so zai ba ta jari, idan ma zaman gida take so, ayi din ga yi mata komai, duk zai iya kuma nan kusa yake son ayi auren".
"Bantan uba, namu Æ´aÆ´an suna zaune za ayi hakan, muna me?"
Mama ta ce "Hmm, ni fa na daÉ—e ina hana faruwar wasu abubuwan, rannan daga aikenta gidan Hajiyar lamin, wai É—an wan maigidan ya ganta, ya ce ayi masa hanyar aurenta, uban yaron fa sanata ne a Adamawa, hauka nake? Na toshe na hana, na din ga aika su surayya, da walida amma ko kare a familyn babu wanda ya sinsuna su.
Lokacin da suka yi sauka ma, babu kunya wai chairman yana son ta, tun ba ta kai haka ba ma, na ce ba za a lalata mata tunani ba, karatu take yarinya ce, na rasa wannan masifar".
"Mun shiga uku, meyasa kowa sai ita? Kuma duk masu kuÉ—i, namu yaran fa?".
Mama ta ce "Wannan shegiyar farar fatar suke yi wa ai"
"Wace farar fatar? Su ma duk ba suna shafa mai ba, manyan zaratan Æ´an mata, sun sha mai da kwalliya amma ace su duk shiru sai ita?"
"Shiyasa tun jiya ban yi bacci ba wallahi, na saƙa wannan na kwance wancan, dole fa a rusa wannan maganar ma"
Zakiyya ta ce "To yanzu menene shawara? Wallahi na rasa abun cewa, ko malamai zamu shiga ne?".
"Babu lallai yayi tasiri, na fuskanci ƙashin masu arziki ne da ita, amma mu cigaba da shawara kafin faruwar abun".
Zakiyya ta ce "In sha Allah "
Mama ta miƙe ta ce "Sai na ji ki".
***
Cikin ikon Allah Abba ya warware, babu abun da ya same shi, sai dai ya bugu, ya yi ta fama da jiri, sai da ya kwana uku a asibiti, aka sallame shi.
Rahila ta cigaba da É—agawa Abbu hankali a kan Al'amin, a kan lallai ya kai shi wurin hukuma, a san yadda za ayi da shi, kafin ya yi mata kisan gilla ita da yaranta.
Gaba ɗaya maganganun Al'amin sun yi tasiri a zuciyarsa, amma kuma wani ɓangaren, Rahila tana da gaskiya, al'amin barazana ne a gare su, saboda yadda sunan mai dogon zamani, yayi ƙaurin suna a bakin mutanen unguwa, ba iya unguwar ba, har gidajen radiyo, duk wani faɗan daba da zai tashi a arear rukunin unguwannin to sai an ambaci mai dogon zamani wato Al'amin.
Ƴan sanda har sun gaji da kama shi, idan an kama shi ma, ƴan siyasa sai sun saka an sako shi, daɗinta ɗaya ba ruwansa da taɓa kowa ko kayan kowa, sai ƴan daba da jami'an tsaro da su yake faɗansa.
Bayan Jauhar ta dawo daga makaranta, mama da Anty suka sakata a gaba, suna sake yi mata tambayoyi a kan Alhaji mu'azzam, Jauhar ta rasa me za ta ce musu, dan ita ba komai ta sani a kansa ba, dan tun da ya zo sau É—aya, bai sake zuwa ba, dan haka ta din ga ce musu ba ta sani ba.
Aikuwa suka din ga zaginta, tare da kiranta munafuka.
Suka gama zaginta, ta cigaba da sabgoginta.
Yaya tijjani ya shigo, wanda shi ne babba a gidan, ya shiga wurin mama, jauhar ba ta san hawa ba, ba ta san sauka ba, ya kamata ya zane a yammacin nan, wai an ce masa kule-kulen maza take yi.
Ihun jauhar ne ya sanya yaya saifu shigowa, ya tarar TJ yana mata bala'i, wai tana kula maza.
"Haba yaya TJ, idan ba ta kula maza ba, kai za ta kula? Ko za a jiƙata a ruwa a sha ne? Da iznin baba fa ya zo wurinta idan ma a kan wannan mutumin nan"
Mama ta ce "Rufe mini baki, kai da ba ka san me duniyar take ciki ba, yadda maza ke lalata yaran mutane yanzu, idan aka sake lalata ta kawai zai yi ya gudu, kuma fuska ya gani shiyasa ya biyota har gida, da ba ta bashi fuska ba ba zai zo ba. Idan da gaske yake auren zai yi, duk ga mata nan da suka fita komai sai ita.
Saifu kawai ya girgiza kai ya fice, ransa ba ya yi masa daɗi, da irin riƙon da ake yi wa ƙanwarsa a gidan nan, shikenan maraici sai ha zama makamin cutar da bawa?.
Har jauhar ta gama girkin dare, kuka take yi, dan ta daku sosai da sosai, fatarta duk tayi ja.
Baba da ya dawo, bai san me aka yi ba, na dukan Jauhar.
ÆŠan autansu ne wato amir, ya shigo ya ce "Jauhar ana kiranki a waje, in ji wannan mai motar, kin ga har ya bani kuÉ—i dubu biyu".
Anty ta ce "Ba zata je ba, je ka ce ba ta nan, ki mayar da kai ki gama sauran aikace-aikacen ki, idan kuma baki da abun yi, ki zo ina da shi ki yi mini".
Baba ya fito da kansa ya ce "Amir, je ka ka ce tana zuwa, Waliyiyya, ajiye duk abun da ki ke yi, ki je ki sallami baƙonki".
"Amma Alhaji.....
"Amma me? A kan me zaku hana yarinya zance, maganar aurensu fa za a fara kwanan nan, da yaya za su fahimci juna?".
Jauhar kamar ta ce wa Baba ba zata je ba, dan tana tsoron a sake saka yaya TJ ya dake ta.
Amma ta kasa magana, ta zura hijjabinta, ta fita.
Tun kan ta fita ta fara jiyo ƙamshin turaren sa, kamar wancan karon ta durƙusa tana gaishe shi.
Sai dai bai amsa ba, ya ce "Na yi missing É—inki Jauhar, sai dai na baki lokaci ne, dan kar na dame ki. Yaya ake ciki kin yi mana addu'ar? Kin fara so na?"
Maimakon ta bashi amsa, sai ƙifta ido take yi, tana waiwaye kar TJ ya zo ya ce zai sake dukanta, tun da ta tsaya da wani ne ba sa so.
Ya É—ora da cewa "Dama baba ne ya ce na É—an baki lokaci, to kuma ga tafiya ta kamani babu cikkaken shiri, na ce a kawo mini kuÉ—in aure, kafin na tafi, amma na ga bari na ji ta bakinki, kar na yi miki shigar sauri"