Sashe 39
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***
Sanye take da dogon hijjabi launin maroon, har ƙafarta hijjabin ya ɗauki guga, ƙafarta sanye da safa baƙa, sai sauri take yi tana ratsa lunguna har ta iso ƙofar gate ɗin makarantar islamiyyar. Sai dai duk wannan saurin da take yi, an riga an fara tarar makara, wanda idan da abun da ta tsana, shi ne a taɓa lafiyar jikinta.
Kusan mintuna goma ya ƙara, bai shiga ajin ba domin yi musu ƙari, yana jira ya ga ta ina za ta ɓullo, yana ofishin malamai, yake hango yadda malam hamza ya zage ƙarfin sa, yana shimfiɗa mata murtukekiyar dorina a jikinta, sai kuka take tana bashi haƙuri.
Sam bai ga fa'idar duka a cikin ladabtar da É—alibai ba, mussaman mata, macen ma mai rauni kamar wannan baiwar Allah.
Litattafan sa ya kwasa, ya tafi ajin nasu, malam Jamil kenan, ba ya duka ba ya zagi da cin mutuncin É—alibi, amma É—alibai na ganin girmansa da mutuntashi.
Ana tsaka da tilawa ta shigo ajin, ta nemi wuri ta rakuɓe a gefe, ɗaya bayan ɗaya ɗaliban suke tasowa, suna zuwa gabansa da littafi, suna bayar da haddar Alqur'ani mai girma, idan ya kammala ji, ya rubuta maka making haddarka, sauran ɗalibai kuma na cigaba da tilawa, sai dai fiye da rabin hankalinsa yana kanta.
A haka har aka zo kanta, ta tashi jiki babu ƙwari, ta je gabansa ta zauna, ta miƙa masa littafinta, ya karɓa yana dubawa, ba bu in da take da maki ƙasa da casa'in da biyar.
Tayi bisimillah, ta fara karanto wurin haddarta, sai dai ba aje ko ina ba, muryarta ta fara rawa, kuka ya ƙwace mata, bai ce mata uffan ba, ya cigaba da kallon ɗaliban, tamkar haddarta yake ji.
Sai da tayi sosai, sannan ta cigaba da karatun, tana yi tana share hawaye.
"Ba kya son duka meyasa ki ka makara?" Maimakon ta bashi amsa, sai ta sake fashewa da kuka.
"Kin ci abinci ne?"
Ta É—aga masa kai alamar eh.
"Wani abun suka yi miki a gidan" ta girgiza kai alamar a'a.
"To ni wannan haddar taki, ban ji ta sosai ba, dan haka sai kin sake wata, je ki zauna, kuma ki daina wannan kukan" ta jinjina masa kai, ta share hawayenta.
Sai dai zamanta ke da wuya, sai ga malam hamza ya shigo da dogon littafi, yana muzurai.
Yayi wa malam Jamil magana sannan ya ce "Duk wanda ya ji sunansa, ya tashi ya je gida, kar ya sake zuwa sai ya biya kuÉ—in term, tun da ba da yawun bakinmu zamu biya malamai ba, tun da iyayenku ba sanin darajar malaman addini suka yi ba, da dai na boko ne.
Sunan farko sunanta ya fara kira, ya ce "Ke waliyiyya, duk term sai an kore ki, sai an yi ta artabu kan ki biya kuɗin term, duk wannan uban shirgegen gidan naku, dubu uku a wata uku sai an yi ta fama, tafi gida idan kin karɓo kuɗin kya dawo".
Ba wannan ne karon farko da aka koreta saboda kuÉ—in makaranta ba, sai dai a duk lokacin da aka koretan, ta kan ji ta muzanta ainun.
Haka nan ta É—auki jakarta ta tafi gida, tana zuwa gidan ta tarar da wata babbar mace ta shirya za ta fita unguwa, ita da wata budurwa.
"Me kuma ki ka dawo yi, an tashi ne?"
"A'a mama, wai kuɗin makaranta aka turo ni na karɓa"
Matar ta kwaɓe baki ta ce "Uban naki bayanan ai, tun da kin dawo dama unguwa zan je, maza ki ɗora girkin dare, bana son yin daren girkin nan" ta amsa da to.
Budurwar ta ce "Yauwwa Jauhar, akwai kayana a kan gado, dama jibi zan koma school, tun safe nake jiran mai wanki, ya zo ashe ya tafi gida, kya wanke mini, har bedsheets ɗi na, bargona kuma na jiƙa shi, yana baya, idan ya so kan mu dawo idan sun bushe, ko gugar kya rage mini ki goge su".
Ta sake amsawa da "To, sai kun dawo"
Ta ƙarasa ɗakin da take kwana, ta hau cire uniform, ranta babu daɗi, duk ƴan gidan suna makarantun islamiyyar su, ita kuwa an korota daga ta su, kullum sai an kai ruwa rana kan a biya mata kuɗin makaranta, alhalin sauran har na term uku ana biya musu.
Ta canza kayanta zuwa na gida, ta shiga kitchen ta kunna gas, ta tarar ya ƙare, ba ta jira komai ba ta ɗebi itace, ta fita garejin gidan, ta tayar da wuta ta ɗora girki.
Ba ta fi shekara goma sha shida ba, amma yadda take sarrafa jikinta tana aiki, kamar wata babba.
Tana girki tana wanki, a haka ƴan islamiyya suka dawo, kowa ya watsar da jakarsa, da uniform ɗin sa, masu ball suka tafi, masu wasa suka fita, duk suka sake ɓata gidan, ta bi ta sake tattarewa, ta haɗo kan kayan da suka watsar su ma ta zuba ruwa za ta wanke.
***
Fuskarsa murtuk, kamar bai taɓa dariya ba, haka ya tunkari ƙofar gidan, yana wata irin tafiya, mai kama da ta ƙasaita, maimakon ya saka hannu ya buɗe ƙofar gidan, wani irin duka ya yi mata da ƙafarsa, ya shiga ba tare da ko sallama ba.
"Wane mara hankalin ne yake dukar mana ƙofa haka, sai ya karya..... Shiru ta yi ta haɗiye sauran maganar, ganin wanda yake tsaye ƙerere a gabanta.
"Yaushe ka fito? Ko in ce waye ya fito da kai?" Ko kallonta bai yi ba, ya cigaba da takun ƙasaita, ya je ya tura ƙofar wani ɗaki, ya shiga sai dai babu kowa a ciki, dan haka ya fito ya nufi kitchen.
"Al'amin kar ka shigar mini kitchen, ban dafa komai da kai ba, na ga lokacin fitowarka daga prison ma bai yi ba, wannan jaraba da masifa Allah ya yi mini maganinka" ba ta gama maganar ba, ya fito daga kitchen É—in, da kulolin abinci.
Shan gabansa tayi ta ce "Kar ka taɓa mini abinci, abincin ƴaƴana ne da na mijina, bana son tashin hankali Aminu, ka je ka ajiye mini"
Take ya juya idanunsa yayi mata wani irin kallo, a take ta ja da baya ta koma gefe, tana bin fulasan hannunsa da kallo.
Wani irin fito ya yi, wani daga waje ya amsa masa da fiton, ya fita da fulasan abincin ba tare da ya amsa ko É—aya daga maganganun da matar ke ta yi masa ba.
Jauhar kuwa, kafin magariba ta kammala girkin nan, ta kawwame a flask, sai gyara gidan take yaran suna ɓatawa, da masu hankalik cikinsu da marasa hankalin duk babu mai taimakawa a gyara. Ta ɗauki abincin maigidan ta kai masa ɗakinsa.
Tana idar da sallar magariba, ta shirya ta É—auki jakarta, dan tafiya makarantar dare.
Tana fita maigidan yana dawowa, yayi parking ya sauke glashin motar ya ce "Waliyiyya an fito?"
Murmushi ta yi, sai da fararen haƙoranta suka bayyana ta ce "Baba kai ma waliyiyyar zaka ce mini?"
"Eh mana, ba haka malamanku suke ce miki ba, za a tafi makarantar ne?"
Ji tayi kamar tayi masa maganar kuÉ—in term É—in ta na islamiyya, amma ta kasa, mussaman da tuna gargaÉ—in mama da tayi mata.
Ta ce "Eh baba, sannu da zuwa, na kai maka abincinka É—aki ma, kana zuwa sai dai ka ci"
Yayi murmushi ya ce "To Allah ya yi albarka, a kula sosai ayi karatu da kyau"
Ta ce "In sha Allah" ta wuce makaranta shi kuma ya gyara parking.
Gudun kar ta makara a makarantar dare, ya sanya ta fita ba ta ci abinci ba, duk da yunwar da take ji, ta ce idan ta dawo sai ta ci.
Sai dai bayan dawowartata, ta tarar da an cinye komai.
Cikin girmamawa ta ce "Mama an cinye abinci ne?"
Mama ta kalleta ta ce "Au ba ki ci ba dama?".
"Eh, na rana ma ban samu ba, na rufe nawa saboda kar na makara na tafi makarantar dare".
"Eh to ai yayi kyau, al huda huda ina da littafi, to an cinye ki zuba ki ci kan ki tafi ba zaki iya ba, duk salon ace zaluntarki ake yi ba a baki abinci, kin wa kanki ai, ni ki hanzarta ki yi wa yara gugar uniform, tun da ga wuta, kar a É—auke"
Ran jauhar ya sosu rashin samun abincin nan, dan har ga Allah tana jin yunwa sosai da sosai, sai dai babu yadda ta iya, dole ta shiga ta kwaso tulin guga ta hau yi.
Tana gugar nan zabga-zabgan ƴan matan gidan suna kawo mata karon nasu, har wurin sha biyu na dare tana abu ɗaya, ga cikinta sai ƙara yake yi tana hamma, ga bacci da gajiya, ga kuma yunwa.
Bayan ta kammala guga, ta bi manyan ɗakunansu ta ba su, ta kai na sauran yaran ɗakin iyayensu, sannan ta koma ɗakinta, ta yi alwala tayi sallar isha'i, ta yi shafa'i da wuturi, ta nemi ta kwanta. Ba ta yi mintuna goma sha biyu da kwanciyar ba, ta jiyo ana ƙwala mata kira a tsakar gida.
Haka ta sake yinƙurawa, ta fito matashin saurayi ne, tsaye hannunsa riƙe da leda ya kalleta ya ce "Kin fara bacci ne?"
Ta ce "A'a yaya, idona biyu"
"To ga indomie nan, faka-faka dafa mini dahuwar nan taki, mai muslmin daɗi, akwai gasashshiyar hanta a ciki da ƙwai, na san akwai attaruhu da alabasa a gidan, tayi yaji fa sosai"
Ta karɓa ta ce "amma yaya da daddare nan ka ci yaji ka kwanta, ulcer fa"
Zare mata ido yayi ya ce "Sai kin saka an yi mini faɗa ko, maza dafota ƙwan nan fa ya soyu shi ma"
Tayi murmushi ta koma ta sake gangamin haɗa wutar da ƙanan itace, dan kuwa, ta riga ta kashe murhun, kuma ba ayi refilling ba.
Kasancewar a gareji take girkin, sauro yayi mata rubdugu da cizo, sai da wutar ta kama sosai, hayaƙi ya kore su.
Sai da ta gama tana juye masa, sai gashi ya shigo, hannunsa da leda É—auke da lemon roba mai sanyin gaske.
"Yauwwa waliyiyya, Allah dai ya tuttula miki albarka, ya baki miji nagari" ta sunkuyar da kai cikin jin kunya.
Ya samu wuri ya zauna, ya ce "Samo plate ki É—iba, sai ki jiye mini sauran"