← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 95

Sashe 9

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na sani, kuma nima ina gani, ka rabu da ita, duk wani abu da za ku yi ku daina sakata a ciki, ƙyaleta da bashir ɗin, shi ne daidai da ita, ku yi haƙuri dan Allah" MD ya din ga lallaɓa Habib, dan ba zai so rasa gogaggen lawyer kamar Habib a law firm ɗin sa ba, a kan Nabila da ba aikin ne a gabanta ba.

Yau weekends ne, gaba É—aya iyalan major na babbn falo, kowa ya ja nasa wuri yana karyawa, Nabila ce kawai babu a wurin.

Tun yana jurewa ya kasa, yayi gyaran murya ya ce "Ina arfa ne?"

Anty ta ce "Bacci take yi"

Ya kalli walida ya ce "Tasota, ta fito ta karya, sai an cinye an bar ta, ta cikawa mutane kunne da kuka"

Kusan mintuna goma da taso ta, sannan ta fito, kayan bacci ne a jikinta, dogon wando da rigarsa har gwiwa, kanta babu É—an kwali.

Nasir ya tsura mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi.

Abba ya ce "Ina kallabinki? Ki ka fito da wannan gashin ba kyan gani, kamar totuwar masara?"

Ta saka hular hannunta ta ce "Haba Abba, dan daga bacci na tashi ne fa"

"Tafi can ƙazama, kullum kai babu kitso, ba za a rasa kwarkwata a wannan gashin ba" dariya aka hau yi mata.

Ko a jikinta, ta zauna kusa da Abba, ta kalli Nasir ta ce "DSP, yaushe ka dawo ba labari, ya hanya?"

Ya jinjina kai ya ce "Alhamdilillah"

Major da kansa, ya taya Nabila haÉ—a shayi, ga soyayyen dankali, ga bredin ta, amma tana buÉ—e bredin ta ce ba za ta ci ba, kwantai ne.

Major ya miƙa mata nasa ya ce "Duba zaki iya cin wannan? Dankali kawai ba zai riƙe miki ciki ba" ta duba buredin Abban ta ce "Eh wannan sabo ne, Abba ka ƙara mini ƙwan, ni ba na son dankalin ma"

Ya ce "To shikenan, ɗauki nawa da ma ni yanzu ƙwai bai dace da ni ba, a shekaruna"
Idan da sabo, sun saba da ganin irin wannan fifikon da major yake nunawa, duk da mutum ne mai ƙaunar yaransa sosai da sosai, amma son da yake yi wa Nabila na musamman ne, amma fa hakan ba ya hana idan suka yi laifi, ya hukunta su kamar ba ƴaƴan cikin sa ba.

Anty ta ce "Arfa ba zaki bari Major yayi ƙiba ba, kalli yadda ki ke tara mazaunai, saboda ci"

Yayi murmushi ya ce "Tafi kowa girma a gidan nan"

Nabila ta ce "Abba, Allah ya ƙara arziki, ka yi ta sayowa mu na ci"

"Amin arfan Abba"

Nasir ma ya juye mata nasa ƙwan, ta tattare tana dariya, dan ta na son ƙwai sosai.

Mama kuwa kamar za ta yi bindiga, saboda baƙin ciki.

Bayan an kammala cin abinci, su walida ne suka kwashe kwanukan da aka ci, Nabila kuma ta hau labartawa Nasir, abun da ya faru da sumayya da ta je Asibiti.

Fafur Nasir ya ce ƙarya take yi.

Ta haɗe rai ta ce "Yaya, wai meyasa a duniya jami'an tsaro ba kwa yadda kun yi laifi, ko wani ne daga cikinku yayi, sai kun ƙaryata, kun kare mutum"

"Wa ya gaya miki hukuma tana laifi?"

"Ba mutane ne hukunar ba? Ai mutane na laifi, kuma hukuma ma suna yi, wallahi da gaske nake, ka bincika ka ji kuma, koma na kira maka sumayyan"

Ya ce "A'a ai ƙarya ki ke yi, ni zaki zauna kawai dan ki ƙure"

Duk yadda ta so, ta fahimtar da shi, amma ya ƙi fafur.

Abba dai kallonsu kawai yake yi yana dariya, ganin ba zai yarda ba, ya sanya ta ƙyale shi, ta koma wurin Abba.

"Abbana" tayi maganar tana É—an murmushi.

Abba ya ce "KuÉ—i zaki tambaya kenan?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a Abba, abu zan tambaye ka"

"Ina jin ki"

"Abba dama, wata amarya ce, suka kira ni a waya, zan je gida na yi musu make up, ita da ƙannenta na biki, za su biyani, VIP ne har gida"

HaÉ—e rai yayi sosai sannan ya ce "Me na gaya miki a kan wannan sheÉ—ancin? Kin san na hana ki sabgar banzar nan, ban da kalen sheÉ—anu jikinku, me wannan shashancin zai amafana miki, na fuskanci kin fi fifita wannan kwalliyar a kan aikinki, to babu in da za ki je".

"Dan Allah Abba, wallahi zan samu kuÉ—i fiye da salaryna, dan Allah"

"Ba in da zaki, tun da babu abun da ki ka rasa a gidan ubanki, ba matar da zaki bi gida ki na shafawa hoda, idan ta matsu tayi da kanta mana, banda shashanci ace mace ta zauna sai an bita gida shafa mata hoda da gazar"

"Abba!"

"Shut up" yayi mata tsawa, hakan ya tilasata mata yin shiru.

Walida kuwa faÉ—an Abban dariya ya bata, wai idan sun matsu su yi da kansu, ba wadda za aje gida shafawa hoda.

Nabila ta din ga jin ko a ɓoye sai ta je, tana son sana'arta ta kwalliya, Abba kuma ba ya so, wai shashanci ne da fatan aljanu, ita kanta idan tayi a fuskarta wasu lokutan, ya din ga faɗa kenan.

Akwai ranar da za ta je biki, ta yi kwalliya ta saka eyelashes, ya kirata dan ya ga meya samu idonta, gashin idonta yayi tsawo haka, tun da ta ce masa sawa tayi, ba ta ankara ba, ya saka hannu, ya fige shi sai da ya haÉ—a da gashin idonta, ya ce ya kuma ganinta da shi sai ya zaneta.

Har a gaban saurayi, ya taɓa korata gida, wai ta je ta wanke fuskarta, ba za ta cuci ɗan mutane ba, duk ta damalmala fuska da hauka, ta zama kamar wata bebin roba.

Ta rasa meyasa Abba yake adawa da sana'ar nan tata.

Nabila tun a weekend, take cigaba da zuzutawa Sumayya trial ɗin da za su je, kotu ranar laraba, farincikin ta ya kasa ɓoyuwa, wanda hakan ya samo asali ne, da yadda ta ga Barrister Habib ya ƙyale ta, ta koma team ɗin Bashir, kuma ta samu labarin barrister Naja'atu ma tana da shari'a ranar a kotun, dan haka za ta haɗu da ita.

Nabila uniform ɗin ta, tamkar su yi magana, saboda ɗaukar guga, ita kanta a bar kallo ce a cikin kayan, ba fara ce tas ba, amma haskenta mai kyau ne da ɗaukar hankali, domin kuwa jikinta kamar ƙwai, dan tana kashewa Jikinta kuɗi ba kaɗan ba, ba ta da wata damuwa, ba abun da take yi da kuɗi, ban da sayen kayan gyaran jiki, ta samu kuɗi a aikinta, major ya bata, Nasir ma ya bata, ga wanda take tatsar samari, ga ƴan sana'ointa, dan haka kuɗi sam ba matsalarta bane ba.

Barrister Naja'atu Bunkure matashiyar lawyer, mai dakawa maza gumba a hannu, karo da ita sai lawyern da yake jin kansa ya isa, dan abu ne mawuyaci case ya shiga hannunta ba ta yi wining ba. Ana yawan sanar da ayyukan alkhairin ta, a gidajen rediyo na taimako da tsayawa marasa galihu a kan shario'i daban-daban.

Bakin Nabila ya ƙi rufuwa, ganin yau ga ta ga Barrister Naja bunkure, wata ƴar gayu da ita, yadda ta gabatarwa da kotu kanta kawai, ya isa ka tabattar da ta san me take yi, ga yaren nasara a harshenta wato turanci.

Gaba É—aya hankalin Nabila ba ya kan shari'ar, yana kan bunkure, da yadda take magana.

Murna kamar nabila ta taka rawa, yau ga ta ga mentor É—in ta.

Sumayya ta samu damar editing news yau da kanta, kasancewar MD yana ta mitar, ta daina ware kanta, ta din ga shiga ana aiki da ita a haka za ta goge.

Kiran Nabila ta gani, dan haka ta É—aga ta ce "Kiran me ki ke yi mini ina aiki?"

Sama-sama ta din ga jiyo numfashin Nabila, muryarta ƙasa-ƙasa ta ce "Kin tashi daga aiki ne?"

"A'a menene meyafaru?"

A galabaice ta ce "Na dawo chamber ne, na É—auki kayana, ina hanyar komawa gida, ji nake kamar ciwona ne zai tashi, ina titi dan Allah Sumy ki zo"

"Subhanallah, gani nan zuwa amma babu wani a wurin da zai kai ki gida?"

"Ni ba na son damun kowa, dan Allah besty ki zo, kar na mutu a titi"

Ganin ta gama abun da take yi, ya sanya a gurguje ta É—auki jakarta, ta fita, ba ta tsaya ko ina ba, sai hanyar wurin aikin su Nabila, tana ta rarraba ido a titi tana kiran wayarta.

A kan wani tudu ta hango Nabila, idanunta sun yi jawur, da alama tayi kuka sosai da sosai.

Ta ce "Mai napep, bari na ɗauketa ka kaimu gadon ƙaya dan Allah, ba ta da lafiya"

Ya ce "To shikenan" ta sauka ta rungumo Nabila, ta taimaka mata, ta shiga napep É—in, sai dai babu baki, sai numfashi take sama-sama.

"Arfa, meyafaru an ɓata miki rai ne?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"To menene? Haka kurum ciwon ya tashi" buɗe baki ta yi, da nufin yi wa sumayya masifar ta ƙyaleta, amma ta ji numfashin ta, zai gudu ya bar huhunta, hakan ya sakata yin shiru.

Can kuma a hankali ta ce "Sumayya mu je gidanku, wurin umma"

Sumayya ta jinjina mata kai, haka aka yi.

umman sumayya na ganinsu hankalinta ya tashi, Nabila ta samu wuri ta kwanta.

Umma ta ce "Sumayya, me aka yi mata ne?"

"Wallahi umma ban sani ba, kawai kirana ta yi a waya, ciwonta ya tashi"

Cikin kuka Nabila ta ce "Umma dan Allah ki yi mini addu'a, ki ƙyale sumayya"

Umma ta ce "To shikenan" ta din ga tofa mata addu'a, har aka samu ta yi bacci.

Bayan awa É—aya da rabi, ta farka, har ta samu ta ci abinci ta yi salla, umma ta din ga tambayarta, ko wani abun aka yi mata, amma ta ce a'a.

Ganin ta ware, ya sanya umman basu wuri, Sumayya ta sake kallonta ta ce "Ke, wallahi wani abu aka yi miki, yanayinki ya nuna mini, kin ga idonki kuwa, ki gaya mini menene?"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Sumy, ashe haka ake ji, idan aka wulaƙanta mutum mussman a gaban jama'a, a dizaga ka"

"Menene? Waye ya wulaƙanta ki?"

Ta É—an yi shiru sannan ta ce "Kin san Naja'atu Bunkure?"
Chapter 9 · 0% Book details