← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 95

Sashe 76

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta amsa tare da bayar da izinin a shigo, 'yan mata ne da zasu girme mata su biyu, suka shigo falon.

Jauhar ta faÉ—aÉ—a fara'arta tayi musu maraba.

Suka gaisa da É—ayar, É—ayar kuwa sai hura hanci take yi.

Shahida ta ce "Kin gane mu kuwa?"

Jauhar ta ce "Na gane wannan ranar da na je gidan, mun haɗu da ita ai, ƙannensa ne ko?"

Shahida tayi murmushi ta ce "Kin canka"

"Sannunku da zuwa, baku taɓa zuwar mana ko sau ɗaya ba"

Shahida ta ce "Ai da yake ba ma zama a gari saboda school, shekaranjiya ya je gida ya ce baki da lafiya, Abbu ya ce lallai mu zo duba ki kafin ya zo shi ma. Ya jikin?"

"Jiki Alhamdilillah na warware"

"To Allah ya ƙara afuwa, ko mu ce Allah ya raba lafiya, ya kawo mana baby lafiya" Shahida tayi maganar tana murmushi.

BuÉ—e baki Jauhar tayi ta tashi da sauri ta ce "Bari na kawo muku ruwa"

Ta kawo musu ruwa, lokacin ta hura gawayi, ta É—ora girki.

"Wancan ba tea flask É—in mu bane?" Amira tayi maganar tana nuna flask É—in.

Jauhar ta ce "Ina ga naku ne, shi ne ya zo da shi, ina ta so nayi masa maganar na waye, yanayin jikina ya hana, amma tun da Allah ya kawo ku shikenan".

Suka cigaba da hira da shahida, yayin da Amira ke ta harare-harare itakaÉ—ai.

Shahida ta ce "Yaya muka ji da abun da ya faru da yaya na rufe shi da aka yi, Ubangiji Allah ya tsare gaba"
Jauhar ta ce "Amin ya Allah, sharri ne ma aka yi masa, amma duk da haka a tayamu da addu'a dan Allah, duk zai daina wataran sai labari. Ina mama?"

"Haka ne, ana nan ana yi, mama tana nan ƙalau, tana gaishe ki"

Shahida ta sake cewa "Nikam wai dan Allah ya aka yi kuka haÉ—u da yaya ku ka yi aure, har ya taka ya je gida, sha biyu fa ta wuce, ya ce na yi masa girki matarsa ce ba lafiya na ce wace 'yar baiwa ce haka? Kin san a rayuwarsa ta duniya mata ba sa gabansa mu kanmu yadda ki ka san dodo haka yake a wurinmu".
Jauhar za ta yi magana, Amira ta ce "Kin jiki da wata magana shahida, a ina kuwa za su haɗu?, Tallarta fa aka kawo masa ba ta ji, ta fanɗare a gida an rasa yadda za ayi da ita, aka haɗa su, aka jogana masa, da yake shi ma ba sanin ciwon kansa yayi ba, ko ke baki san zancen ba? Kin zauna kina ta zuba ni ina da wurin zuwa" ta ƙarasa maganar tana tashi tsaye ta ɗauki jakarta tayi waje.

Gaba É—aya jauhar ta yi sak, jikinta yayi shock, yayi wani irin sanyi da mamakin maganganun Amira.

Cikin dirircewa shahida ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, wallahi ƙarya take yi, ina zuwa" ta lallaɓa ta ɗauki takalmanta cikin tsananin jin kunya ta bi bayan Amira.

Biri yayi kama da mutum, duba da yadda aka yi auren cikin gaggawa ko wata guda ba a rufa ba, ashe abun da aka gaya musu kenan a kanta?

A take ta ji ciwon kanta ya tsananta, ta fara tunanin wace irin muguwar ƙiyayya ce tsakaninta da 'yan gidansu har haka.

Gidan su jauhar, Hafsa ta shigo daga zance, ta zauna a tsakar gida, Yaya saifu ya shigo, ya kalleta ya ce "Daga ina ki ke?"

"Zance" ta bashi amsa kai tsaye.

"Wurin wa?" Tayi shiru tana kallonsa.

Ya ce "Wallahi kun yi asara, yanzu dama Saboda hafsa ta auri mutumin nan, da yake son jauhar shiyasa ku ka aurar da ita ga mutumin banza, wallahi ba ku kyautawa kanku ba, kuma da ikon Allah sai Allah ya saka mata".

Mama ta ce "Saifu maganar me ka ke yi ne ban fahimta ba?" Ji yayi kamar ya gayawa mama baƙar magana, sa'arta ɗaya mahaifiyarsa ce, babu yadda zai yi da ita, kawai ya fice.

Mama ta ce "Zakiyya, da gaske mutumin nan ne yake zuwa wurin Hafsa?"

Ta haÉ—a rai ta ce "Ni ma ban san zancen ba sai yanzu"

Mama ta ce "To meye abun ɓoyewa ban da abunki, ai abun farinciki ne a gare mu baki ɗaya. Dama ai jauhar ɗin ce ba ma son ya aura, wallahi nayi murna haƙanmu t cimma ruwa".

Sai kuma ta É—an saki ranta ta ce "Wallahi ina ta son na gaya miki, abubuwa ne sun sha mini kai, kuma ba gama daidaitawa suka yi ba"

"Ai bakomai, Allah ya tabattar mana da alkhairi" suka gama maganar ta shiga É—akinta, ta jinjina kai ta ce "Hmm zakiyya kenan, baki da wayo da ni ki ke zancen, duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, zaki gane kuskurenki".

Yau tun la'asar ya dawo, kwana biyu ba ya yin dare, saboda rashin lafiyarta sai dai fa ba zai ce mata sannu ba.

Ya kasa gane kan yanayinta, ta zuba masa abinci, ta koma gefe ta yi shiru.

Ya gama ya tashi ya tafi É—aki, zai É—an kwanta ya huta, kasa jurewa ta yi ta tashi ta bi bayansa.

Ta ssme shi, yana ta watso kayan wardrobe ɗin sa da ta gyara da ƙyar.

"Master"

"Yeah" ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

"Ƙanneka sun zo ɗazu baka nan"

"Ok" kawai ya ce, amma ƙasan zuciyarsa mamaki yake yi, tun da ƙannensa ta ce, da ƙanwa ta ce ya san shahida ce kawai.

"Dan Allah abu nake son tambayarka, na san kai ba ma'abocin ƙarya bane ba, na san ba zaka fara a wannan karon ba" bai amsa ba, dama ba tayi tsammanin hakan ba, ta ce "Da gaske tallata aka kawo maka, wai ba na ji na fanɗarewa iyayena shi ne aka aura maka ni?"

Ya É—aga rigar hannunsa yana kallo kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Eh, haka na ji"

Cikin rauni ta ce "Kuma ka yarda?"

"Kusan haka, dan na san ba yadda za ayi a aureni haka kurum babu dalili, a abun da bai wuce sati biyu ba"

Yayi maganar yana ajiye rigar, ya ɗauki wata, sautin da tayi na ƙwacewar kuka ne, ya sanya shi ɗagowa a tsorace yana kallonta.

Cikin kuka ta ce "Wallahi ni ba lalatacciya ba ce, ban fanɗarewa iyayena ba, dama kallon da ka ke yi mini kenan, kallon da 'yan uwanka da sauran mutane suke yi mini kenan" da ƙyar maganarta take fita, saboda numfashinta da ya fara sama.

Ya ƙaraso gabanta ya ce "Wai ke ba kya gajiya da kuka ne? Komai kuka?"

Hannunta take fifitawa kusa da hancinta, alamar numfashi yana bata wahala, da sauri ya ɗauketa ya fita da ita tsakar gida, ta lumshe idonta hawaye na bin gefen fuskarta, sai dai ƙirjinta sai ɗagawa yake yi yana sauka, alamar numfashin da ƙyar take yi.

"Ko mu koma asibiti? dama sati É—aya suka bamu mu koma"
Ta girgiza masa kai.

"Ba zaki daina kukan ba?" Maimakon ta daina, sai ma wata sheshsheƙa da ta zo mata, ga numfashinta yayi nauyi.

Ya ciro wayarsa a aljihun wandonsa, ya kira liti.

"Maza ya ne?"

Viper ya ce "Kana ina?".

"Na shiga area raba kaya".

"Samo adaidaita sahu, ka zo gidana zan mayar da 'yar madara asibiti"

"An gama mazaje"

Zai ajiye wayar, ta fara vibrating, ya É—aga bai yi magana ba.

"Honorable ya dawo, akwai taron gaggawa da zai yi, yana son ganinka"

"Na ji"

"Dan Allah kar ka ɓata lokaci sosai, ka san zaɓe yana ƙara gabatowa"

Ras jauhar ta gane muryar waye, muryar P.A ce, a take ta jinjina rashin kunya irin na É—an siyasa.

"Dan Allah kar ka je, idan ka tafi mutuwa zan yi"

"Allah ya jiƙanki"

A sanyaye ta ce "Amin, amma dan Allah ko na mutu kar ka je ba na son ka din ga zuwa wurin 'yan siyasa"

"Ki yi mini shiru, idan ba haka ba zan tashi na bar ki"

"Yi haƙuri" ta faɗa tana haki.

A hankali take iya takawa, saboda numfashinta, ya sakata a napep É—in da liti ya zo da ita, sannan ya shiga, liti ya zauna a gefe suka tafi Asibiti.

File É—in ta aka kai wa likita, shi da ita suka shiga, liti kuma yana can waje.

Likita ya ce "Ka ƙi yadda ayi mata gwajin ciki, gashi tana ta fama da an duba dai"

Ya ce "To duba"

Jauhar ta ce "Ni bani da komai".

"Shikenan, ki na da athma ne dama, wannan hakin da ki ke yi?" Ta jinjina masa kai ta ce "A'a allergy ne, shi ma kuma tun ina yarinya ne"

Al'amin ya kalleta, likitan ya sake cewa "Akwai magani da ki ke sha ne? Ai kusan duk abu É—aya ne, allergy É—in da athma"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ai na daɗe ba na shan magani, addu'a nayi ta yi, ya  daina tashi, tun ina ƙarama sosai ban kum jin alamun sa ba"

Likitan yayi murmushi ya ce "Masha Allah, ka ga 'yar baiwa, to a din ga sakamu a addu'ar mu ma, amma dai yanzu zan rubuta miki magani, sai ki kiyayi hayaƙi, ko kin shaƙi wani abun ne?"

Ta ce "A'a kuka na yi kawai na ji na kasa numfashi sosai"

Likitan ya jinjina kai, ya ce "Bari na duba bp naki na gani".

Shi dai gogan bai ce komai ba, likitan ya duba bp É—in ta sannan ya ce "Zahra kina shan magungunan da na baki kuwa?"

"Ta jinjina kai alamar eh".

"A iyayenki akwai mai hawan jini?"

Ta ce "A'a"

Ya kalli Al'amin ya kalli jauhar ya ce "Akwai abun da yake damunki ko?" Tayi yaƙe ta girgiza kai.

"Zahra, ita rayuwar duniya haƙuri ake yi. Malam ka zauna da matarka ku tattauna idan a cikin aurenku matsalar take, a magance ta, idan ba haka ba, hawan jinin nan zai iya taɓa mata zuciya, idan wani abu ka ke yi mata da ba ta jin daɗin sa, ku tattauna dan Allah ku fahimci juna, amma tayi ƙanƙanta da wannan ciwon"

"Zahra" likita ya kuma kiran sunanta, kamar yadda ya gani a jikin file.
Chapter 76 · 0% Book details