Sashe 85
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har suka dawo gida, hannunta na cikin nasa, cike da shauƙi da nishaɗi.
Ya karɓi mukulli ya buɗe musu gida suka shiga, jauhar baba ta fara kira, ta yi masa barka da salla, ya ce mata idan mijinta na da account, ta tura masa ya saka mata barka da salla.
Ta kira yaya saifu ma, haka ta din ga bin family tana yi musu barka da salla.
Ta kalli Al'amin ta miƙa masa wayarta ta ce "Saka mini lambar baba, mu yi masa barka da salla"
"Bani da ita" ya bata amsa.
Ta marairaice ta ce "Dan Allah master"
Ya ce "Sai kuma ki yi"
Haka ta haƙura ta tashi ta ƙyale shi, ta tafi ɗakinta, ya din ga kallon kayan jikinsa, yana sake jinjina ƙoƙari da ƙarfin hali irin na jauhar, wai shi ta yi wa kayan salla.
A status ɗin ta, ta yi posting "Alhamdilillah first eid with my amazing Habibi, Allah ya ƙara wa zamaninka tsayi, ya maimaita mana"
Surayya ce ta fara ganin status ɗin, ta din dariya tana nuna wa 'yan gidan, suka din ga cewa pretending ne, na lallai sai ta nuna wa mutane tana cikin kwanciyar hankali, sai dai suna tsaka da gulmar, ta sake saka hotonsu riƙe da dadduma a filin idi, wanda hakan ba ƙaramin girgiza su yayi ba da ba su mamaki.
Master ya kai mintuna goma sha biyar yana zaune, ta fito sanye da leshinta da ta saka ranar É—aurin aure, ta shafa powder da jambaki, ta saka kwalli, ta kwantar da gashin gaban kanta, da gel, ta yi É—auri mai kyan gaske, gashi ta kaiwa Suwaiba tela ta gyara mata É—inkin, dai-dai jikinta.
Har ya tashi zai shiga ɗakinsa, ya waiwayo ya ganta ta fito, mp ce a hannunta, tana bin waƙar da aka saka, a cikin nishaɗin barka da salla.
Cikin waƙar m sharif *Farin gani kai ne tauraro, ko a cikin samari, mai ji da ni ba ka yin ƙwauro ka sa na wuce gori, na ɗau takarda na riƙe biro, kai na saka a fari, kai zan ba dawakai, kowanne da silkai, matsayinka ya kai ba zan yi ma kishiya ba.......
Da haka ta ƙaraso gabansa tana rawa, tana yi masa fari da ido.
Tsayawa yayi yana kallonta yana murmushi, sai dai bai tsinke da lamarin na ta ba, sai da ta ƙaraso gabansa ta riƙe hannunsa wai sai ya yi rawa.
Karo na farko da ya buɗe haƙoransa talatin da shida yayi dariya.
"Ba dariya zaka yi ba, ka yi mini liƙi ko ka yi mini rawa" ya buɗe baki ya ce "You are not serious"
"Am serious mana, rawa ko liƙi, biyani ɗari shida ta ma da ka korar mini coustomer's" ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu da ɗari uku ya ce "Suke nan nake da su, uwar son kuɗi"
"Ungo dubu ɗaya, sauran bari na bayar da ayata a markaɗo mini, na haɗa da snacks da tuwon salla na raba. Ba ka ce ma na yi kyau ba, ka taɓa ganin mace da tayi kwalliya tayi kyau kamar yadda na yi yau?"
Yayi murmushi ya ce "Ni da ba kallon mata nake yi ba, ya za ayi na sani, ni dai ba ki yi mini kyau ba, kamar babyn roba haka ki ka zama" yayi maganar yana matsa kumatunta.
"Daga Angela zuwa 'yar madara, yanzu kuma babyn roba?"
"Eh, irin na wasan nan ba"
Jauhar ta ce "Kyau nayi maka ne"
Ta fice tsakat gida, tabbas tayi kyau kam, tayi fresh farar fatarta ta karɓi baƙin leshin sosai da sosai, kwalliyar ta yi mata kyau.
Tana tsakar gida, wasila ta shigo ta kawo mata tuwon salla, suka gaisa tare da yi wa juna barka da salla.
Wasila ta ce "Jauhar iyayen soyayya, mu matan layin nan, tare muka haɗa kai muka tafi idi, a hanya muka hango ku, an maƙalƙale hannun master ana yashe baki, kai jauhar a ji tsoron Allah"
Jauhar ta ce "Anty wasila kina saka mini ido wallahi, ki sa ka in ta jin kunya"
"Ke ba wata kunya, riƙe abunki wallahi, abunku gwanin sha'awa, kafin lokacin ya wuce, ba kowane namiji ne yake jure ayi ta soyayya ba".
Al'amin ne ya fito, Wasila tayi tsit dan ba ta san yana nan ba, ta gaishe shi ya amsa ciki-ciki.
"Master ina zaka? Kunun aya ka san baya daÉ—ewa"
"Nura ne a waje ya kirani, ba nisa zan yi ba"
Ta ce "Ok to"
Daga jikin gate guduma ya ce "Antynmu barka da salla".
Jauhar ta ce "Yauwwa malam nura, ina fatan ka je idi?"
"Eh na je, na biyo mu gaisa sannan ki bani tuwon salla".
Jauhar ta ce "Aikuwa ka samu, amma sai ka kai mini markaɗen aya, ka sayo ƙanƙara sai na haɗa maka da tuwon"
Ya ce "Ba case matar babban yaya"
Al'amin bai sani ba, har gidansu jauhar ta aika da abincin salla, guduma ne ya kai ya kai na gidan su ita ma.
Ta zuba wa Al'amin, ya tafi da shi, tun da ya shiga wurin na su, Liti da sauran yaran suke bin sa da kallo.
Liti ya ce "Maza, wannan shuÉ—iyar audugar ruwan sararin samaniya fa, waye ya sayeka cikinta?"
"Ban sani ba"
Walid ya ce "Abun a tambaya ne, ni fa tun da na sanka sau É—aya na ga ka saka manyan kaya, ranar da aka zarga maka uku, ina nufin igiyar sunnar ma'aiki da bint laban É—in ka, wato madam 'yar madara"
Ya tsuke fuska ya ce "Mai laya"
Walid ya É—aga masa hannu ya ce "Tuba nake, na kiyaya wannan ma'adanar abincin fa?"
Al'amin ya ajiye musu kwanuka, suka dirarwa abincin nan da ci babu ji babu gani.
Baba kuwa yaya saifu ya aiko, aka kawo mata fulasanta, da kuÉ—i dubu goma, kasancewar ba ta tura account number da ya ce ba a matsayin barka da sallar ta.
Da daddare da ya dawo, yana shigowa ta ji warin sigari, dan da alama ma a cake yake, bai kulata ba, ya tafi ɗakinsa ya baje a kan katifa, ta bi bayansa har cikin ɗakin, cikin matsananciyar damuwa ta ce "Haba master, shi ne ka je ka sha da yawa, kalli a yadda ka dawo fa, gaba ɗaya ka ɓata mini ɗan farincikin da na tsinci kaina a ciki yau" yayi shiru yana sauke numfashi.
Ta ƙaras ta ce "Tashi a cire kayan to, sai ka saka wasu"
"Get out"
"Ai zan tafi amma......
"I said get out" yayi maganar cikin tsawa.
Ta tashi a razane, ta bar masa É—akin, cikin azumi dai Allah ya taimaketa ya É—an nutsu, saboda baki a rufe yake, ba ya shaye-shaye sosai, yau da ga sallacewa ya koma ruwa.
Saboda tsabar takaici, ko baccin kirki ba ta yi ba.
Da safe kamar ba shi ba, ya tashi ya fito abun sa, ya sayo abun karyawa, sai share shi take yi, amma ya nuna ko a jikinsa. Kasancewarta mai matukar raunin zuciya, sai kuma ta sake.
Suna karyawa, Hafsa ta kira ta a waya, jauhar ta É—aga tayi mata sallama ta ce "Amarya ba kya laifi"
"Mhmm, dama anko ne mama ta ce sai an nuna miki, shi 'yan gida za su yi da bikina, zan turo miki ta what's app lace ne dubu goma sha biyar sai atamfar kamu dubu tara, na san ba lallai ma ki yi"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Anty hafsa kenan, aikam dai kun san mijina talaka ne, zan sako dai abun da Allah ya hore mini na zo, in sha Allah"
"Dama na sani ai, mama ce ta takura a turo miki kar abun ya zama surutu, a ga kin fita daban. Allah ya sauwwaƙe tisya"
"Ba tsiya ba ce anty hafsa, idan ruwanka bai isa alwala bane sai ka yi taimama Allah ya kaimu bikin lafiya" ba shi aka gaya wa ba, amma sai ya ji maganganun hafsan tamkar direct da shi take, wani irin haushi da takaici ya kama shi. Sai dai ya basar ya cigaba da karyawa abun sa.
Ya kammala ci, ta tashi ta yi aikace-aikacenta, yau ma wata kwaliyyar ta yi da abun da Allah ya yassare mata.
Ya ce "Babyn roba"
Ba ta kalle shi ba ta ce "Saura ta rodi"
"Zaki gama kumbure-kumburen naki ki sace"
Ta share shi, tana shafa muzurunta d take cewa boti.
"Ina magana ki ka share ni, kina wasa da wannan abun da nake dana sanin kawo shi?"
"To me zan ce maka? Kawai ka je ka sha abun da ka sha, daga yi maka magana ka hantare ni" tayi maganar idonta na cika da hawaye, saboda takaici.
Maimakon ya damu, sai yayi murmushi ya saka hannu ya matsa kumatunta a hankali ya ce "Abun wasa na, you are like a toy to me, wani abu mai É—an bani nishaÉ—i wasu lokutan"
Galala take bin sa da kallo, ita ce ma abun wasan.
"Kin daÉ—e kina yi mini abubuwa, abun da ki ka yi mini jiya ya tsaya mini a rai, ki ka É—inka sutura sukutum ki ka bani, Allah ya suturtaki ranar da bayi za su tsaya a gabansa babu sutura. Na gode Allah ya baki miji nagari"
Da sauri ta sake kallonsa, sakamon abun da ya faÉ—a na Allah ya ba ta miji nagari.
"I still mean it, haryanzu ina kan bakana na rabuwa da ke a duk lokacin da ya dace, kina takura mini da yawa"
A fusace ta saka hannu, ta buge hannunsa da ya riƙe kumatunta, ta waiwaya tana kallon gefenta.
Ya ce "Idan ki ka kuskura ki ka jefe ni, yau ni da ke ne" tashi ta yi tana kuka, ta nufi É—akinta.
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
  Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
  Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
  Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
   Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃ðŸ¾ðŸ’ƒðŸ¾
Ko kimin mgn ta👇ðŸ½ðŸ‘‡ðŸ½
08093932955