← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 95

Sashe 78

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shi ya ce ku je ku gaya mata cewar kangarewa ce ta sanya aka yi aurena da ita? Ku je ku ci zarafinta?"
Cikin tashin hankali shahida ta ce "Ba ni na faÉ—a ba Amira ce wallahi".

Rahila kuwa hankalinta ya dugunzuma, ta ce "Ka yi wa Allah da ma'aikinsa ka yi haƙuri, dan Allah kar ka yi musu wani abu"

Ai kamar ta tunzura shi, ya saka wuƙa a wuyan Amira, "Ya zama na farko ya zama na ƙarshe, ayi duk cin kashin da za ayi a kaina, ban da 'yar mutane da ki ka haɗa kai ku ka cutar, idan aka kuma zan yi ɓarna, wallahi sai na saka wa mutum ƙarfe"

Shahida ce ta iya cewa "In sha Allah ba za a sake ba" yayi ƙwafa ya fita.

"Amira kin ga abun da ki ka ja mana ko? Da ya illatamu, da kin cuce mu"

Amira kam kasa magana tayi, sai dafe ƙirji tana hakin tsoro.

Al'amin wuni yayi ranar, yana partrol da yaransa a unguwar, saboda kar yaran madaki su zo su afkawa wanda bai ji ba bai gani ba.

Cikin ikon Allah, har dare yaran madakin ba su sake shiga unguwar su Al'amin ba, duk da sun yi artabu sosai da wasu, dan sai da aka yi masa rauni a cikinsa, ya kama hanyar tafiya gida.

Jauhar na falo tana karatun exam, duk da sun kusa kammala jarrabawa.

Ta katangar ya diro kamar ɓarawo,s an samu cigaba, yanzu idan ya ga dama ya kan yi salama.
Sallamarsa kawai ta amsa, ba ta sake kula shi ba, ya wuce É—akinsa, mintuna goma amma ba ta biyo shi ba, ya fito ya ce "A kawo mini ruwan zafi zan yi wanka"

Ta tashi ba ta ce komai ba, ta ɗaukki flask, aurensa da ita ta saba masa da wanka da ruwan ɗumi, saɓanin da da har a kuddudufi wankansa yake yi ya ƙara gaba.
Yanzu kuwa kusan kullum, da an kawo wuta, take dafa ruwan a heater, ta saka a flask.

Ta zo ta haɗa masa ruwan, sai dai ta ga kamar yana ɓoye wani abu.

Kawai ta leƙa ta ga me yake ɓoyewa, yanka ne a gefen cikinsa, ya saka rigarsa yana ƙara goge jinin kasancewar ba mai zurfi bane ba.

"Ka gani ko? Sai da ka je aka yanko ka ko? Abun da nake ta gudu, sai da ka zubar da jini ko, ba za kai daina zuwa wurin da za a cutar da kai ba ko master? Kodayake ma ni abun yake damu, kai ko a jikinka".

"Na ce ya dame ki ne? Ba jikina bane?" Idan ba gizo idonsa yayi masa ba, hararsa ta yi ta fice.

Shi mamaki ma take bashi, tun da ta yi rashin lafiyar nan, take rigima kuma kamar ta rage tsoron sa.

Ya shiga ya yi wanka, ya fito ya tarar da ita da ɗan ƙaramin kwanon abinci, sai kuma kayan dressing, tun na lokacin da aka yi masa wancan raunin.

Bai kulata ba, ya ja kwanon abincinsa ya cinye, awara ce da miya, ya sha ruwa.

Ita ma ba ta kula shin ba, ta saka auduga da spirit tana goge, kan ciwon, tana gogewa tsigar jikinta na tashi, kamar jikinta take gogewa, shi kuwa kamar dutse latsa wayarsa ma yake yi.

Haushi ya isheta, ta kalleshi ta ce "Wai ba zafi ne?"

"Eh babu, idan ma dirzawa ki ke da ƙarfi, dan na ji zafi, ba na ji" ta tashi ta fice fuuu, tana yi masa fatan shiriya a ranta.
Kusan awa É—aya da rabi, ya shigo mata É—aki, ta yi sauri ta tashi zaune, saboda ta san tsiyar da ta aikata masa.

Ya kunna fitila ya hau yi mata bincike a É—aki.

"Me ka ke nema?"

Ya tashi ya nufo ta, ya miƙa mata hannu ya ce "Bani kayana da ki ka sace mini yanzu"

"Ni ba na sata"

Ya ce "To baki nayi ki ka É—auka? Ko kema kin fara sha ne ban sani ba? Kodayeke biri yayi kama da mutum, da ki ka iya kallona ki ka din ga jifana nan gaba ina ga swizaland zaki saka mini ina ga"

"Ni ba na shan komai, kuma ban É—au komai ba".

"Ba ki É—auka ba ya aka yi ki ka san a kan me nake magana?" Tayi shiru ba ta ce komai ba.

HankaÉ—ata yayi, ya janyo ledar kayan shaye-shayen sa a cikin bargonta.

"Na gaya miki idan kin gaji ba zaki iya zama ba, ban ɗaure ki ba, ki ƙara gaba"

A ƙule ta ce "Ka ɗaure ni mana, zan tafi ba ka sallame ni bane, ka rubuta ka gani idan ban tafi ba. Tun da baka da tausayi idan ba mutuwa na yi ba hankalinka ba zai kwanta ba" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Ya kalleta, gaba ɗaya ko faɗan ba ta iya ba, voice ɗin ta sam ba na masu faɗa bane, shagwaɓa kawai take yi.

Ya ce "Kin yanke hukunci kenan? Ai da kin gaya mini da duk ba a zo nan ba, zan rubuta na baki, dama na gaji".

"Kuma wallahi idan ka yi shaye-shaye kai da Allah"

Bai kulata ba, ya jefo mata kwalin sabuwar waya gal, ya ce "Gashi nan, akwai layi a ciki na yi rijista, idan kuma na yi wani laifin na gudu ke za a kama".

"Bana so" ta faɗa tana kwanciya, duk da ƙasan zuciyarta tayi mamakin wayar.

Ya saka hannu ya É—auka ya ce "To kin huta" ya fice ya bar É—akin.

Ta kwanta ta yi shiru, sai ta fara tunanin ya aka yi ya ɗaga mata ƙafa ya ƙyaleta, sai kuma ta ga rashin kyautuwar abubuwan da ta yi masa.

Bayan sallar asuba bacci ta koma, ƙarfe takwas da rabi ta farka, tana ƙoƙarin saukkowa daga kan gadon, tayi tozali da farar takarda da biro. Gabanta ya faɗi ta ce "Na shiga uku sakin nawa ya yi?" Ba ta taɓa takardar ba, ta saukko a sukwane ta tafi ɗakinsa sai dai baya nan ya fice.

Gaba daya jikinta yayi sanyi, sai yanzu ta ƙara jinjina girman wauta da aikata.

Yau rahila har gidan su jauhar ta je, suka ƙule a ɗaka ita da Anty Zakiyya suna ta surutu da shewa.

"Zakiyya ina ga 'yar ku fa an gamu laulayi take yi"

"Kai haba dan Allah"

"Wallahi da gaske, ke 'ya mace shu'uma komai ƙanƙantarta, kin san yaron nan har gida ya zo da wuƙa ya gama ta'addancin sa tana zubar da jini, zai yi mini hauka a gida wai su Amira sun je masa gida sun yi matarsa ko me oho musu, na ga tashin hankali na ce iyee yanzu har ta samu wannan matsayin. Wallahi mamaki nake yadda ta iya zama da yaron nan"

Zakiyya ta ce "Ba ki ganta ba kamar sokuwa, kafin ki ga ta yi fushi, ko tayi zuciya da abu za a jima, ko kuma kawai tsabar ƙarfin hali ne da ƙi faɗi ba"

Rahila ta ce "Sai ta yiwu, ya ake ciki da maganar hafsa?"

"Mu na nan ana ta murginawa, ana shirin kawo kuɗin aure, na ce lallai ta ce masa a haɗo da kayan lefe, ana sallacewa ayi auren, duk da wannan matar ta nuna bakomai na san tsohuwar muguwa ce, wataƙila wani abun zata kitsa, dan haka kan tayi wani yinƙuri ayi a wuce wurin".

"Yauwwa kar ki kuskura ki sakankance ko ki yadda da ita, ni ban zaci lamarin ma zai zo da sauƙi haka ba, ku cigaba da tatsarsa kuna tarin kayan aure"

Zakiyya ta ce "Ke kin ga hidima, ai ni dai Allah ya kashe ya bani, da yanzu sai dai mu ga ana yi wa waccan yarinyar jauhar"

Rahila ta kwashe da dariya ta ce "Ga mijinta can suna fama, amma wallahi ya fara son yarinyar nan, kai amma ba ƙaramin haƙuri take yi ba bala'i Allah ya kyauta" suka cigaba da hirarrakinsu, da shirin biki.

Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, suka fito daga taron meeting, daga ofishin jam'iyya, sakamakon gabatowar manyan zaɓuka da za a gudanar a cikin Nigeria.

Yau bai san iya adadin meetings ɗin da ya yi attending ba, suka jero da shi da mataimakin firaministan jam'iyya na jiha, ya ɗan yi miƙa ya ce "Kai, yau na gaji over"

"Kai honorable, da an yi babban zaɓe an wuce wurin, haka ne, ka san ban yi sati da shigowa daga Abuja ba, can ma wasu tarurrukan ne, abun duk babu sauƙi, ina ta ƙoƙari in sha Allah sai na kawowa excellency yankina, ina nan a satin nan zan yi empowerment na matasa, kuɗina duk sun tafi a campaign ɗin nan"

"Kar ka damu honorable, hannun jari ka saya, da an wuce wurin sama zaka din ga kwashe ribarka, ka mayar da uwar da ribar ka ɓace ba zasu sake ganinka ba, sai bayan shekara huɗu" suka kwashe da dariya.

Suka yi sallama, kowa ya nufi motarsa, ko da ya je gida, matarsa tuni tayi bacci, yayi wanka ya nemi wuri ya kwanta, dama ba yunwa yake ji ba, sai dai bacci ya gagare shi, ya din ga juyi a kan gadon, ga gajiya ga baccin yana ji, amma ya kasa ya ɓuge da lissafe-lissafe abubuwan da yake son yi idan ya dace ya samu ya ci zaɓen nan.
Ji yayi kamar kansa zai fashe, saboda stress kawai ya tashi ya É—auki mukulli, ko direba bai nema ba ya hau motarsa ya fice.

Yamma da gari yayi, ya hau kan titin gwarzo road kasancewar dare ne, titin babu ababen hawa, ya sauke glas ɗin motar kaɗan, yana tafe a hankali yana shaƙa wani abu a hancinsa. Sai d yayi nesa da cikin gari sosai, sannan ya yi parking a gefen hanya, ya rufe glasan motar, ya cigaba da shaƙa abun nan, kusan mintuna talatin, sannan ya juyo kan motar ya nufi dawowa yana tafe iskar kan titin nan na ratsowa cikin motar, sannu a hankali har ya koma gida.
Chapter 78 · 0% Book details