Sashe 63
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ana yin sallar isha'i ya dawo, mp É—in ta har da fitila.
Ta tashi tana yi masa sannu da zuwa, ya wani maze ya bata wata ledar, sannan ya zauna ya ce "Ki nemi wata ma'aikaciyar idan akwai a nan kusa, tayi miki, idan ki ka je wurin wancan É—an iskan na bakin hanya kuma ni da ke ne"
Ta saka hannu biyu ta karɓa, allurar zazzaɓi ce mai tsada ya sayo ya kawo mata, amma bai iya cewa ya jiki ba.
"To godiya nake master, Allah ya ƙara arziki ya sa a fi haka, na ga saƙo ma na gode sosai da sosai Allah ya sa afi haka".
"Amin".
Ta ce "Ga naka na ajiye maka"
Ya ce "Idan zan ci ba sai kin ce na ci ba, ki daina kuma wannan mugun tsoron, komai ya baki tsoro, idan ba haka ba ki kashe kanki a banza"
Jauhar ta rausayar da kai ta ce "Nima ban san ina jin tsoron ba ne. Amma kai ba ka jin tsoron sa ka riƙe shi da hannu?"
"Ban sani ba? Rannan kwaɗo yau ƙadangare, meye abun tsoro a jikinsu, har da suma saboda ƙadangare" tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Sai da ya gama sannan ta ce "Ka yi haƙuri to, ban san ya ake yi nake jin tsoron ba".
"Idan ma kina sane ki cigaba da yi mini ihu a gida kamar gyare".
Sai da ta yi murmushi ta ce "Zan koyi jarumta, zan daina jin tsoro in sha Allah. Yauwwa master yaushe zamu je ka kai ni na gaida su mama? Ba su taɓa ganina ba, ban taɓa ganinsu ba, su hajiya kawai na taɓa gani, yakamata ka kaini na gaishe su. Sai ayi girki mu je mu gaishe su, na ga haka ake yi".
Shiru yayi, yana tuna Ummansa, tana yawan cewa Allah ya raya mini babana na ga aurenka, in ga mai sa'ar da zata auri É—an autan mazana
Jauhar ta ce "Ka yi haƙuri idan na ɓata maka rai ne maganar da na yi"
Ya tashi tsam ya ce "Yauwwa, Ina sake jaddada miki, idan ba zaki iya zama ba, ko kin gaji zaki iya komawa gida, babu takura, na ga shekaranjiya kina ta koke-koke, idan da takura you are free to go" daga haka ya nufi É—akinsa.
Gabanta ya faɗi ta fara tunanin, me ta ce da zai ɓata masa rai har haka?.
Haka nan ta ji ba ta fatan abun da zai sake mayar da ita gida yanzu, da sunan zawarci ko ace ta kasa zama, saboda ta san dama mugunta ce ta saka aka aura mata shi.
A ranta ta ce 'Zan jure, in sha Allah zan bawa mara É—a kunya, in sha Allah, Allah ba zai kunyata ni ba, ba zan tagayyara ba"
Lokaci-lokaci yake leƙowa falo, sai ya hangota tana aikin stone ɗin ta, tana jin radio a mp. Yana so yayi mata maganar ta je ayi mata allura, amma ya fasa.
Bacci ta fara, ji ta tafi ta je ta kwanta, har ta fara bacci aka kawo wuta, hasken lantarki ya hasketa, ba shiri ta tashi, sai a yanzu ta tuna ba ta kashe ƙwayayen ba, ta fita falo dan ta kashe, taga Al'amin ya fito daga ɗakinsa, yana soke wuƙa a ƙugunsa.
Ta tsura masa ido tana kallonsa, bai san tana falon ba, yana É—aga ido, suka yi ido huÉ—u, É—aure fuska yayi ya zo zai fice.
Ta ce "Master ina zaka je a daren nan, kuma?"
Ai ko sake kallonta bai yi ba, ya nufi ƙofar fita.
"Dan Allah kar ka je in da za a illataka, zuciyata ba ta yi mini daÉ—i in ga kana zubar da jini".
Bai tsaya ba, sai da ya dangana da tsakar gida, ya kama katanga ya dira, ita kuma ta zauna a wurin ta fashe da kuka mai taɓa zuciya.
Ko da ya fita titi, liti ya zo a kan babur ya É—auke shi, suka tafi.
Unguwar shiru, kowa ya shige gida, suka maƙale a wani wuri su na shaye-shaye.
Can sai ga wanda suke hari, ya kwararo layin a kan babur, Al'amin ne ya fita da sauri, ya daki tayar gaban babur ɗin, aikuwa ya faɗi ƙasa da shi da babur ɗin.
Suka rirriƙe shi, Al'amin ya zagaya dai-dai kunnensa ya ce "Tijjani Faruk ko? Gargaɗi aka ce ayi maka, a kan rubuce-rubucen da ka ke yi a dandalin sa da zumunta, da waɗanda ka ke suka, da Switzerland na so na yi maka warning ɗin, amma a yadda ka ke ɗin nan, zaka iya ɗayewa idan nayi maka da ita, ko iraƙi na saka maka a jiki ba zaka shura ba.
Liti, duba bayana, ka ciro Russia ka yi masa rijiya a cinya, ka yi masa eleven da iraƙi a gadon bayansa".
Tijjani yana ihu, yana kururuwa, yana komai, liti ya caka masa wuƙa a cinyarsa, ya yage masa riga, ya yanke shi sau biyu a baya, ya watsar da shi a wurin yana kururuwa.
Can gida mama tana ta sintiri, har sha biyu saura, ba ta ji an ce Tijjani ya shigo gida ya É—auki abinci ba, ta din ga kiran lambar wayarsa amma a kashe.
Tana ta mita, aka kira baba a waya, aka sanar musu, an tsinto tijjani a hanyar dawowa gida, an yanke shi da makami, an tafi kai shi asibitin cikin gari, sashen bayar da agajin gaggawa.
ÆŠora hannu ta yi a ka, tana ihu tana ta shiga uku an kashe mata É—a.
Baba ya ce 'Ba cewa aka yi ya mutu ba, an yanke shi aka ce, ƙila masu ƙwacen waya ne ki bari mu je mu gani mana"
Ya fita ya kira maƙwabcinsa, ya ce ya raka shi asibiti, domin su ga a halin da Tijjani yake ciki.
Ala'amin bayan ya koma gida, a falo ya tarar da jauhar, sauro yayi dandazo a kanta yana cizo, sai ajiyar zuciya take yi ta ci uban kuka.
Tsayawa yayi yana kallonta, tare da jinjinawa taurin kanta.
Kamar ya tsallaketa ya wuce, ya durƙusa ya kwasheta kamar tsuma ya nufi ɗakinta da ita, yana zuwa ya kwantar da ita a kan gadon, ta buɗe idonta tare da ƙura masa ido.
Tsaki yayi ya fita, ta mayar da kanta ta kwantar a kan pillow.
Al'amin sawun keke ne, Allah kaÉ—ai ya san in da ya dosa, É—azu ya gama cewa idan ba zata iya zama ba, ta tafi gida, amma yanzu ya tsinto ta a falo ya kawota É—aki.
Da safe ta dafa tea, ta kawo masa da sauran meatpie ɗin da ya so jiya, yau bai yi rejecting ba ya karɓa ya fara ci.
"Master"
"Mmmm"
"Na iya irin wannan meatpie É—in fa, idan ka na so ka sayo mini kayan, na iya sosai mai daÉ—i".
Ya ce "To".
Da tana jin kunyar cin abu a gabansa, amma zuwa yanzu ta saba, ta gama cin nata, ta je ta kwaso kayansa da suka bushe, tana ninkewa ta saka zare da allura, tana É—inke masa waÉ—anda suka yage.
Yana kallonta tana yi, shi kuma ya karkace zai kunna sigari.
"Master, shan sigari yana cutar da lafiya fa, ka din ga ragewa dan Allah, kar ka yi rashin lafiya".
"Kin je an yi miki allurar?"
"Zan sha magani, ba na son allura ne tsoro nake ji"
Tashi ya yi zaune ya ce "Ƙadangare, kwaɗo yanzu kuma allura, sannu 'yar madara. Sai ki biyani kuɗin allurar da na saya" yayi maganar yana barsawa yana gyara gefen rigarsa.
Tayi dariya, jin yau ya kulata, har ya É—an yi doguwar magana da ita.
"To nawa ne, sai na tara da kaɗan-kaɗan na biya ka" yayi shiru yana cigaba da sakin hayaƙi.
Ta sake gyara zamanta ta ce "Master Mp nan fa tayi kyau sosai, Allah ya ƙara maka buɗi"
Ya jinjina mata kai.
Tijjani kuwa ba ma ya hayyacinsa, saboda ya zubar da jini sosai da sosai saran da su Viper suka yi masa, da ƙyar aka samu ya farfaɗo.
Cinyarsa sun yi masa rami da ɗan buda, likitoci sai ƙoƙarin ceto ransa yake yi.
"Sai oga"
"Yaya na ji shiru fa, haryanzu kuna tsare da yarona".
"Na sani, trape ɗin muke setting, idan muka yi gaggawa aikinmu zai kwaɓe"
"Ok ina saurarenku".
Jauhar sai murna take yi, zata je registration makarantar su, dama tun da aka kawota ba ta je unguwar ba.
Da safe tana ta shiri, ya fito zai fita ya ajiye mata dubu É—aya ya ce "Ki hau mota"
"Na gode sosai da sosai, Allah ya sa a fi haka, ya ƙara buɗi, ya tsare mini kai" ba shiri ya kalleta, ya ga ba shi take kallo ba, sai jujjuya dubun take yi tana murmushi.
"Da ina da wata ba zan kasheta ba, ina son sabon kuɗi sosai" tayi maganar tana ƙara faɗaɗa murmushin ta.
"Sai ki É—inka ta ki saka tun da riga ce"
"Kuma zata yi mini kyau fa, adawo lafiya, Allah ya tsareka"
Ya amsa da "Amin"
Jauhar ta ƙarasa shirinta, ta tafi makaranta, kamar yadda Baba ya ce mata ta je tayi registration, a nan ta haɗu da 'yan makarantar su, ta din ga murna sun haɗu da 'yan makarantar su, da malaman makarantar ma.
Ta din ga yi wa ƙawayenta mitar ba su je gidanta ba.
"Jauhar wa zai zo gidanki kina auren É—an daba? Ba ma za a bar mu mu zo ba"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Ku daina fakewa da haka, ni da muke tare, ya aka yi bai yi mini komai ba?"
"A'a ai ke matarsa ce, mu kuwa fa"
Duk da ba ta gaya masa ba, haka kawai ta ji tana son ta je gida.
Ganin ko ta fita ba hanata yake yi ba, ya sanya ta nufi hanyar gida.
Gaba É—aya sun yi mamakin ganinta, Anty ta ce "Yaya, ya na ganki yanzu meyafaru?"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Lafiya lau anty, registration na zo na ce bari na biyo, tun da kun ƙi zuwa".
Kallon jauhar suke yi, su ga ko akwai wani abu na tashin hankali a tare da ita, ko alamar duka ko makamancin haka, amma ba su gani ba, sai ma wata nutsuwa ta mussaman da suka gani a tare da ita.