← Book details Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 95

Sashe 58

Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D.P.O ya ce "Abun da nake so da ku shi ne, ku bi yaron nan a sannu a samu maslaha, kar ku yi wani abu da zai tunzura shi, ya fara yi muku fitina a unguwa, ku bari mu bi a hankali mu sasanta, ɗan ƙasa ne yana da damar zama a in da yake so, ku bi a hankali ayi musu sulhu".

Shi kuwa yana fita, ya kira wayar liti, bugu biyu ya É—aga. "Liti, nan da mintuna arba'in zuwa awa É—aya, ina son ka tattara mini, duk wasu yara marasa ji a arear unguwar nan da nake da kewayenta, duk wanda ya yi gardama, ayi masa É—aurin igiya da swizaland gaba da baya, a layin gidana nake son su taru".

Liti ya amsa da "An gama shugaba"

Sahura kuwa, sai da ta je har gidan maman halimatu ta ƙare mata cin mutunci, a kan yadda Al'amin ya je har gida, ya ƙare mata tanadi, a kan ta sai kayan matarsa, maman halimatu ta din ga ba ta haƙuri, ta ce su shiga gidansa su yi magana da jauhar ɗin, amma ta ce ai ba mahaukaciya ba ce ita, da zata shigar masa gida ya ritsata ya kashe.

Jauhar tana ta aikin stone, ta ji ana wata irin busa a unguwar, kamar da ƙaho ake yin busar, irin bushe-bushen da aka din ga yi, ranar ɗaurin aurenta, dan haka gabanta ya faɗi ta shiga cikin tsoro.

Sannu a hankali, hayaniya ta fara cika layin nasu, da surutan matasa, ɗaki ta gudu ta rufe ƙofar falo, dan tunani ta fara yi, ko yaran madaki ne, gashi ba waya ce da ita ba, balle ta kira Al'amin

Kafin ya ƙarasa layin gidan, liti ya kira shi a waya, ya sanar masa sun fara taruwa matasan, dan haka bai bi ta cikin ba ya bi ta baya.

Jifff! Ta ji dirar abu a tsakar gida, ta katanga ya diro gidan, ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar falon, amma a rufe ya jijjiga ya jijjiga amma ya ji a rufe. Ya shiga bugun ƙofar kamar yaƙi, ƙulewa tayi a ɗaki, ta hau addu'a, tare da tunanin ta ta ta ƙare, yaran madaki sun zo neman Al'amin, ko sun zo sassarata.

"Ke malama ki zo ki buɗe mini ƙofa" sai da ta ji muryarsa, sannan ta fito ta buɗe, ta kalle shi, ta leƙa tsakar gida ta ce "Ai ban san kai ba ne, biyoka aka yi ne?" Wani irin kallo ya yi mata, ya ce "Matsa ki bani wuri" ta matsa ta bi bayansa tana surutu "Master ka daina dirowa ta katanga dan Allah, gaba ɗaya na tsorata wallahi, na zata madaki ne, suka zo nemanka na ji sai busa ake yi ga warin kayan shaye-shaye...... Haɗiye maganar tayi, da ya waiwayo yana yi mata kallon warning.

Ta ce "Yi haƙuri, ka ga abokanka sun dawo da carfet ɗin, wai wanke shi suka yi, amma dai yakamata na je na bawa dillaliyar nan haƙuri, ai ka ga an shiga hakkinta, har gida ta zo tayi wa maman halimatu masifar abun da ka yi" ɗakinsa ya shiga, ya kulle ƙofar ya saka sakata ya bar ta a bakin ƙofa.

Sai abun ya bata dariya, kafin awa É—aya matasan nan sun kusa cika layin nan, sai hayaniya suke yi.

Malam lawan kuwa, a waya matarsa ta kira shi, ta ce kar ya kuskura ya dawo yanzu, 'yan daba sun cika layin nan.

Jauhar na É—akinta, tana aikinta, ta ji yana buÉ—e gate, a razane ta fito saboda yanayin bushe-bushen da ake yi, ya tabattar mata da akwai matsala.

Yana fita wurin yayi tsit, kamar ba su ne suke hayaniya ba da.

"Sai da kai sarki, ƙaramin dodo magajin babban, ko ma in ce ka ɗara shi. Mu na yi maka maraba da zuwa wannan unguwar, mun fito ƙwanmu da kwarkwata domin yi maka mubayi'a". Cewar guduma yana geɓare baki, yanayin yadda yake maganar kawai a buge yake.

Viper ya goya hannunsa a bayansa, ya ce "Manyanku sun kai ƙarata a kan yarjejeniyar zaman lafiya, sai dai ni da ku zan yi wannan yarjejeniya.
Abu goma a cire bakwai a tara da ɗaya zan gaya muku, a bi iyaye, ayi caji kaɗan saboda lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa, a kiyayi taɓa kayan wani. Babu zubar jini a tsakanin ku, ko duk wani wanda yake unguwar nan, abu na ƙarshe mafi muhimmanci da fari salin alin na so zama a unguwar nan, wataƙila na ɗan lokaci na baku wuri, amma tun da abun ya zo da haka, sarki biyu ba zai yi sarauta a zamani ɗaya ba. Ko dai mutum ya yi mubayi'a ko ya bar unguwar nan. Kar kuma a kuskura a matsi ramina idan ba haka ba, zan yi ɓarna. Mu haɗu da shugabannin dabar Unguwar nan da kewayenta gobe a station ɗin unguwar nan, domin yarjejeniyar zaman lafiya. Kuna iya samfewa"

Su ka din ga yi masa kirari, yana jin kansa yana sake fashewa.

Bayan sun watse, maman halimatu ta shigo, tana ba ta labarin abun da sahura ta zo ta yi mata.

Jauhar ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri maman halimatu, dan Allah ki bata haƙuri, ba yadda zan yi, na so mayar mata ma da kayan, ya ce idan na sake sayar da wani abu, zai ɓata mini rai. Wallahi yana ankare da komai, ko cokali na sayar zai gane, ni har tsoro yake bani, bari na baki dubu goma a kuɗin, ki kai mata ta ƙara ki bata haƙuri dan Allah"

Maman halimatu ta ce "To shikenan, Allah ya kyauta" ta bata dubu goma ta kaiwa dillaliya, ita kuma ta bata kyautar dubu biyu, sauran kuÉ—in kuma ta É—an yi musu cefane dan kuwa shi babu ruwansa.

Washegari tun ƙarfe biyu, su mai unguwa suka koma police station, suna jaddada dole a kori Al'amin, dan jiya kafin su je gida ya rigasu zuwa, ya tara musu dandazon 'yan daba a unguwa.

Al'amin bai je ba, sai ƙarfe huɗu tare da rakiyar su walid, da kuma matasan yara 'yan shaye-shaye da sun kai ashirin da wani abu.

D.P.O ya ce "Lafiya, waÉ—anan fa?"

Al'amin ya kalli mai unguwa, ya nuna masa guduma ya ce "Ka san wannan? Ko ba ka bani amsa ba ɗanka ne, meyasa ba ka kore shi daga unguwarka ba? Ko dan shi ɗanka ne?.  A wannan ba wannan matasan wakilai ne da suke jagorantar wasu yaran a ƙarƙashin su, wanda duk a cikin unguwarka suke, kana nufin a sati biyu da zuwana duk ni na lalata su? Har na tare a unguwar nan, ba su san waye ni ba, sai jiya da na saka a tara mini su.
Dama can kuna da lallatun yara, harƙallata nake, ba na lalata ɗan kowa, duk ɗan wanda ya lalace, dama lalataccen ne. Ina sake maimaitawa ba na harbi sai an matsi ramina ko in da nake.
Ga mafita zan bayar, wadda ba zan ƙara ko rage wani abu daga abun da zan faɗa ba.
Mafita biyar ce ba uku, ko dai a haɗa a kore ni, da ni da yaran nan, ko kuma ku yi wa gidana kuɗi ninki uku, yadda zai isheni na sai wanda ya fishi, na bar muku unguwa, idan ba haka ba....... Ba na ƙarasa magana sai dai na aikata.

Duk sai suka yi É—if D.P.O ya ce "Mai unguwa mai ku ka yanke?"

Shiru suka yi ba su ce komai ba, D.P.O ya ce "Tashi ka ja zugarka ka tafi, babu wani abu in sha Allah".

Ya miƙe ya ce "Galibi yaran nan secondary school drop out ne, wasunsu idan son zuciya ne ya kai su wannan halin, wasun su laifinku ne, ko dai ku nutsu ku gyara rayuwar matasan yaran nan, ko kuma su cigaba da lalacewa kuna rusa al'ummarku da hannunku" yana gama maganar suka fice da shi da su.

D.P.O. ya ce "Yaron nan fa ya san abun da yake yi, jiya kuna barin wurin nan, daga can unguwar su, Aka kira ni aka ce a gargaɗe ku, babu ruwanku da shi, yaron 'yan siyasa ne, dan Allah ku lallaɓa ku zauna lafiya da shi.

Bayan sun bar station ɗin, wani irin ɓacin rai ya din ga cizon zuciyarsa, a duk lokacin da aka samu matasa ire-iren sa, al'umma ba su da wani burin da ya wuce, yin watsi da shi, da nesanta kansu da ire-iren su, bayan su ne ƙashin bayar lalacewar ta su.

Yau abun na sa ya fi na kullum, domin kuwa a buge ya dawowa jauhar, wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, ya wuce ɗakinsa, ba ta kula shi ba ta koma gefe ta zuba masa ido.

Washegari da safe shiru bai fito ba, ta leƙa ɗakinsa, ta tarar da shi a kwance yana bacci, gefensa ga kwalin ashana da na taba, ga kwalabe.

Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa, a hankali ta fara magana "Sun san da haka suka aura mini kai, Allah na roƙi ka bani mafita ka zaɓa mini shi, Allah ka kawo mini mafita, Allah ka shirya mini shi, Allah shiriya taka ce, Ni da shi duk bayinka ne, Allah bai gagari ikonka ba, Allah ka shirya min mijina. Allah ka sa ya daina abun da yake yi, Allah kar ka sa ya mutu yana saɓa maka" ta yi maganar tana kuka.

A hankali ya yi juyi, satchets ɗin ƙwayoyi, suka zubo daga aljihun gaban rigarsa, ta saka hannu ta kwashe su, da kwalaben, ta hau caje ɗakinsa, duk wani nau'i na abun da ba ta yarda da shi ba, sai da kwashe daga ɗakin.

A hankali ya motsa, ya buÉ—e idonsa, ita kuma ta fice daga É—akin.

Da ƙyar ya iya tashi, dama bayan sallar asuba, ya sake yin shaye-shayen.

A yunwace, ba tare da ko wanke baki yayi ba, ya hau cin abinci, saboda kayan shaye-shayen sun rarake masa ciki, ji yaya ko tsayuwa ba zai iya yi a kan ƙafafuwansa ba, sai da ya gama ci ya dawo dai-dai.

Ya shiga banÉ—aki, ya wanke bakinsa ya fito falo, ko É—aga jauhar ba ta yi ba, balle ta kalleshi.

Ya je gabanta ya miƙa mata hannu.
Chapter 58 · 0% Book details