Sashe 45
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malaman islamiyyar suka yi wa su baba sallama, malam Jamil dama a kusa da layin da take zuwa karɓar shirin yake, yana yawan ganinta, wataran shi yake korata makaranta ko gida, tun da ya fuskanci halin da take ciki, yake ƙyaleta, dan watarn har gidansu take shiga, ƙannensa ƙawenta ne.
Shi ya din ga bawa baba baki, da bashi tabbacin jauhar ba yawo take tafiya ba, kamar yadda mama ke ta iƙrari.
Baba ya ce "Ni ma na san jauhar ba ta yawo, wannan abun da ya faru ma tsautsayi ne, Ubangiji Allah ya kiyaye gaba" suka yi sallama su malam jamil suka tafi.
Kusan awanni biyu, jauhar ta sake farfaɗowa, sai dai wannan karon da sauƙi, ba cikin razani ta farka ba kamar da farko.
Likita ya zo yana sake dubata, Mama ta ce "Likita kun dubata da kyau kuwa, wannan jinin na jikinta ba fyaÉ—e Æ´an daban suka yi mata ba?"
Dummm! Ƙirjin Jauhar ya buga, ba ita ba hatta baba sai da gabansa ya faɗi, suka kalli mama a tare.
Likitan ya girgiza kai ya ce "No, bana tunanin hakan, razani ne kawai".
"To amma meya kawo jini jikinta?".
Likitan ya yi shiru yana kallon jauhar.
Baba ya ce "Likita ka yi magana mana"
Jikin jauhar ya cigaba da rawa, tana nanata fyaÉ—e a zuciyarta, amma kuma da gaskiyar mama, meyakawo jini jikinta?.
Likitan ya ce "Zaki iya tuna abun da ya faru?".
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Na shiga layin kawai na ga ya kashe wani, da wuƙa a cikin sa, shi ma ƙafarsa tana zubar da jini"
"Kin san shi ne? Kin taɓa ganinsa?" Ta girgiza kai alamar a'a
Ya ce "Zaki iya tafiya?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
Ya cire mata ruwan sannan ya ce "Saukko ki biyo ni" ta yinƙura ta sauka daga kan gadon, ta bi bayan likitan, zuwa wani ɗakin daban, ya kira wata nurse ya ce ta duba masa jauhar, amma jauhar fafur ta ce ba zata buɗe jikinta ba, sai ma ta hau kuka.
Nurse ɗin ta din ga lallaɓata tana yi mata tambayoyi, ta saka ta ciro mata phant ɗin ta, ta duba ta ce wa likitan ba abun da aka yi wa jauhar ɗin mai kama da fyaɗe.
Wataƙila da ta suma ya taɓa ta, tun da ta ce shi ma da rauni a jikinsa, amma ba dai fyaɗe ba.
Likita ya koma ya yi wa baba bayani, baba ya din ga hamdala, mama ta ce likitan ƙarya kawai yake yi, babu yadda za ayi, ta samu jini a jikinta, idan ba fyaɗe aka yi mata ba.
Likitan ya ce "Amma dai ba ƴar ki ba ce hajiya, da taki ce ba zaki yi mata wannan mummunan fatan ba, bani da wata riba da zan ci, idan na yi muku ƙarya, kuma babu yadda za ayi ayi mata fyaɗe ku kawota a haka, ba wani rauni ko alamu na fin ƙarfi, dan babu ɗan iskan da zai yi wa yarinya fyaɗe ya tsaya mayar mata da kayanta a tsakiyar layi, kamar yadda muka karɓi report"
Baba ya ce "Doctor, a bar zancen ma gaba É—aya, ni dai na gode sosai da sosai, na gode Allah da babu abun da ya sameta, za a iya sallamar mu yanzu?".
Ya ce "Eh, yanzu zan sallame ta". Aka rubuta musu sallama suka tafi gida.
Maƙwabta suka din ga shigowa yin jaje, saboda labari ya cika tsukin, faɗan daba ya rutsa da jauhar, an tsintota can a sume.
Sai dai duk wanda ya zo, sai su mama sun bashi labarin, cewar cikin jini aka tsintota kuma jikinta babu rauni, ana kyautata zaton ko sun yi mata fyaÉ—e.
Jauhar hankalinta ya kasa kwanciya, ta din ga tunani daban-daban, ko da ƙarancin shekarunta, a science class take ss2, kuma tana zuwa islamiyya ta san duk wadda aka yi wa fyaɗe sai ta ji wani sauyi a tare da ita, amma ita ba ta ji komai ba, babu wani abu da take ji na sauyi a tare da ita.
Tun tana damun kanta, har ta watsar, sai dai ƙasan zuciyarta tana jin zafin abun da su mama suke faɗa, dan idan ta fita har tambayarta ake yi, wai da gaske an yi mata fyaɗe?.
Har fita ta so ta fara gagararta. Sati biyu da faruwar lamarin, Baba ya zo ya sanar musu da cewa, iyayen Alhaji mu'azzam za su kawo kuÉ—in auren jauhar.
Hankalinsu yayi mummunan tashi, daga su har ƴaƴan su. Suka ƙara tsananta tsangwama da kyarar jauhar.
Duk da tana da matuƙar juriya, da kawar da kai, har abun ya fara effecting ɗin ta.
Bai sanar da su lokaci ba, sai ranar da za a kawo ya sanar da su, hankalinsu ya ƙara tashi, sai dai ba su tsinke da lamarin ba, sai da aka kawo kuɗi masu yawan gaske.
Anty ta kira Rahila, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali take gaya mata, tare da tambayarta ko akwai wani zazzafan malamin ta haÉ—a su, a samu a watsa lamarin.
Rahila ta ce "Wallahi ni kaina a cikin matsala nake Zakiyya, yaron nan ya zame mini bala'i fiye da koyaushe, idan ya ga dama fa cikin gidan yake zuwa ya kwana a tsakar gida, gaya miki ne ban ba, sai da muka kwanta a asibi, ya ɗaga Abba ya buga da ƙasa saboda babansa ya hana shi zuwa gidan, gashi kamar ya fara jin tausayinsa, wallahi kamar na bawa tsinanne guba ya ci ya mutu"
"Innalillahi, rahila menene abun yi? Ni fa sonake maganar ta watse, a dawo mutumin ya auri hafsa".
Rahila ta ce "Aikuwa kin yi dabara, ina da wani malami, wurinsa nake son komawa, ina jin daɗin aikinsa sosai da sosai, duk da su ma malamn yanzu duk sun zama ɓarayi, su ci maka kuɗi babu biyan buƙata, amma nasa babu laifi".
"Wallahi kuwa, saka mana rana, ko da tsiya da masifa, lamarin ya dawo kan hafsa".
"Idan a shirye ki ke, kawai ki zo mu je, ba a bori da sanyin jiki"
Suka yi sallama a kan haka, ɓangaren mama ma, tuni ta zari mayafi ta tafi nata wurin malamin, a kan lallai al'amarin nan kar ya yiwu.
Haka ita ma anty ta shirya, ta tafi gidan rahila.
Ita kuwa jauhar, addu'a take ta yi, Allah ya sa mutanen unguwar su manta da sharrin su mama da suka yi mata, na cewar fyaÉ—e aka yi mata.
Maganar kawo kuÉ—in auren duk bai wani dameta ba, ita gaba É—aya ba ta jin dadin rayuwar ma gaba É—aya, gashi har a lokacin tana yawan tsorata, idan ta tuna abun da ta gani, haka take ganin abun a mafarki, sai dai tayi ta addu'a tana fatan Allah ya yi mata tsari da wannan mutumin mara imani.
Malamin ya gama surƙullensa, ya kalli su zakiyya ya ce "Za a iya watsa lamarin amma fa kafin dawowarsa, muddin ya dawo, babu yadda za ayi".
Zakiyya ta ce "Malam tayaya kenan?"
"Ko dai a aura mata wani, ko kuma a kasheta"
Tayi jimmm ta ce "Kisa kuma malam, a'a gaskiya ban da kisa, muguntar tawa ba ta kai nan ba, ni fa burina kawai ya auri Æ´a ta".
"Ta yaya zai aureta, alhalin yana ganinta?"
Rahila ta ce "Sai a juya masa tunani mana malam".
"Za a iya juya masa tunani, amma ba zai juyu yadda ake so ba, abun zai sake shi da wuri, dan su ma masu kuɗin ba da ka suke zaune ba, kuma maganin ba zai yi aiki a kansa ba, dole sai ya dawo ƙasar nan, zan haɗa laƙanin, ya manta da wannan ya auri wadda ku ke so, amma muddin ya dawo yayi tozali da wadda yake son ɗin, ƙasa ta nuna mini ba zai yiwu ba"
Zakiyya ta ce "Tirƙashi! Ana wata ga wata, ga ƙoshi ga kwanan yunwa"
Rahila ta ce "Malam mun gode, idan mun yanke shawara zaka ji mu, tashi mu je ki ji ina da shawara"
Suka sallami malamin, suka tashi suka fito, ta kalli rahila cikin damuwa ta ce "Wace irin shawara ce da ke?"
"Shawara ce mai kyau, amma ina ga mafita ce, tun da damuwar mu kusan ɗaya ce, me zai hana a haɗa ta aure da wannan fitinannen yaron na gidana, kin ga kun huta na huta, su je su ƙarata, ya bar ni da mijina da ƴaƴana".
Zakiyya ta buÉ—e baki ta ce "Ta yaya? Babanta kuwa zai yarda?"
"Ke dalla can, shiga zaki yi ki fita, idan ba haka ba wallahi daular da ki ke kallo ta gagareki, kin ga mun jefi tsuntsu biyu da dutse É—aya".
"Wallahi maganarki gaskiya ce rahila, zan yi magana da matar gidan, ta fi ni iya sarrafa shi yadda take so a kan yarinyar, zan je mata da zancen, ayi a ƙarƙare kan wancan ɗin ya dawo".
"Yauwwa, amma fa kar ki gaya mata wurin malami ki ka je"
Zakiyya ta ce "Hauka nake zan gaya mata haka? Ke dai ki saurare ni kawai"
"To shikenan, sai na jiki, yadda ku ka yi ki sanar da ni da wuri, nima zan wa babansa magana" suka yi sallama zakiyya ta tafi da ƙarfin gwiwar ta.
Ayshercool
08081012143
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Cike da ƙwarin gwiwa, zakiyya ta tafi gida, tare da hasaso daular da za su shiga, idan hafsa ta auri Alhaji mu'azzam.
Al'amin kuwa yana zaune ya miƙe ƙafarsa, da ta sha bandeji, hannun sa ɗaya riƙe da kofin shayi yana sha a hankali.
Walid ya miƙa masa buredi ya ce "Wai yaya aka yi har yaran nan suka samu suka sareka ne? Ni fa haryanzu mamaki nake yi"
Al'amin ya ce "Liti suka rufarwa da sara, shi na je karɓowa, saboda sun ga suna da yawa, shi ne nima suka yi tunanin za su yi mini taron dangi" yayi wani irin murmushi yana kallon walid.
"Murmushin me ka ke yi kuma?"