Sashe 89
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya tarar da Al'amin a zaune, hannunsa ana saka masa ruwa, ya ƙarasa gaban gadon Al'amin ya ce "Sannu ka ji" Al'amin ya jinjina masa kai.
"Yaron nan ba shi da imani ko kaÉ—an, tayaya zai saka a sakarwa yaro karnuka su je shi, zai ci ubansa da ni yake zancen, zan gani zuwa dare idan bai zo ba, sai na kashe shi wallahi" ya sake kallon Al'amin ya ce "Kai ba kai ne kuka tare a unguwar nan shekarun baya ba? Kuna zuwa islamiyyar dogon bene, kai da É—an uwanka ba?"
"Ni ne"
"Ina ɗan uwan naka? Meya haɗaka da madaki kuma, na ga kai ba irin su bane" Al'amin ya yi shiru, sannan ya ce "Kashe mini Sadik yayi, ba abun da yayi masa, ni kuma na ga ba zan haƙura ba sai na kashe shi nima"
Dodo ya ce "A'a dama yayanka ne aka ce mini an kashe a layin dawaki? Madaki yana fama da gigin daba, tun da ya samu masu tsaya masa, ya je prison ya haÉ—u da wanda suka fi shi rashin mutunci yake abun da ya ga dama. Zan ci ubansa kuwa yanzu me ka ke son ayi masa gaya mini"
Al'amin ya ce "Kawai sonake shi ma ya mutu, in soka masa almakashi kamar yadda ya yi wa Yaya" yayi maganar cikin damuwa.
Dodo ya dafa kafaÉ—arsa ya ce "Kwantar da hankalinka, yanzu dai fatanmu ka samu lafiya, za aje a sanar da babanka, ya zo asibiti ya duba ka, a samu mai jinyarka"
Ya girgiza kai ya ce 'A'a kar a gaya masa, zan koma gida kawai"
"Na ji ba za a gaya masa ba, amma sai ka zauna an kula da kai tukuna".
Madaki hankalinsa ya tashi, jin an kashe masa yaronsa na hannun damansa, a hannun wanda ba zai iya É—aukar fansa ba, dan gaba da gabanta.
Yana tsuma, suka tafi in da Dodo yake zama, aka ce sai dai su bishi asibiti, baya nan.
Asibitin gwamanti ne, Amma amenity dodo ya biya aka kwantar da Al'amin.
Madaki cikin girmamawa ya ce "Na amsa kira ranka ya daÉ—e".
"Ka san wannan ai?" Dodo yayi maganar yana nuna masa Al'amin.
"Na san shi"
"Daga rana mai kamar irin ta yau, idan kai ko wani daga cikin yaranka, ya sake taɓa shi, ko tsoratar da shi, wallahi sai na ƙarar da tarihin mutum a bayan duniya. Bana shiga harkar ƙananan dabarku, amma aka kuma ratso unguwar nan, aka taɓa shi, wallahi sai na yi abun da ba a zata ba. Ka durƙusa ka bashi haƙuri a kan cin zarafin da ka saka aka yi masa, ka sanya karnuka suka yi masa illa, yana ɗan adam ba dabba ba, sauran abun da ka yi masa kuma kai da shi ne".
Madaki ya kalli Dodo ya ce "Ni zan bashi haƙurin?"
Wani wawan mari, dodo ya ɗauke madaki da shi, da sai da ya kife ƙasa, "Ka shiga hankalinka, ka san da wa ka ke magana kuwa? Har ka mutu ba zaka yi iskancin da nayi ba, shekarata goma a ƙiri-ƙirin lagos, ba wani ɗan iskan da ban gani ba, ko ban sani ba, ka bashi haƙuri, ko na ciyar da macizaina namanka"
Madaki ya kalli Al'amin, shi ma ya kalleshi, ya kalli dodo sannan ya ce "Ka yi haƙuri, bisa abun da na saka aka yi maka da karnuka".
Al'amin ya ce "Ko ka bani haƙuri ko baka bani ba, gaba da ni da kai sai ranar da na rama zubar da jinin ɗan uwana da ka yi" sai da duk suka kalli Al'amin, Al'amin ba dai taurin zuciya ba.
Madaki ya fice a muzance, a gaban yaransa aka saka ya bawa Al'amin haƙuri, an wulaƙanta shi ƙarshen wulaƙanci, dan haka ya ƙullaci abun a ransa.
Al'amin har ya kwana huÉ—u a asibiti, Abbu bai neme shi ba, kullum abincinsa mai rai da lafiya yake samu ya ci, ga dodo shi ma kullum sai ya zo duba shi, ya yi ta yi wa Al'amin hira, har yaransa suka fara mamakinsa, dan Al'amin ba wani sakin jiki yake da shi sosai ba.
"Al'amin da gaske kana son ka rama abun da madaki yayi maka?"
Al'amin ya ce "Eh"
"Tunani mai kyau, amma ka sani shi ƙarfe dole sai da ɗan uwansa ƙarfe, yanzu an sallameka, mu je mu kai ka gida, sai ka din ga zuwa dressing, na biya kuɗin dressing ɗinka, duk abun da ka ke buƙata zan baka adress ɗina, a nan cikin unguwar, ka je ka same ni"
Al'amin ya jinjina kai ya ce "Na gode sosai" ya dafa kafaÉ—arsa ya ce "Kar ka damu Aminullahi"
Da ya koma gida, babu wanda ya tambayi ina yaje, tsawon kwanakin nan, ga jikinsa duk raunuka, amma babu wanda ya tambayi ya yake, sai ƙanwarsa shahida da suke uba ɗaya.
Tun da dodo yayi wa madaki iyaka da Al'amin, ya samu sassauci, ya cigaba da sabgoginsa, bai kuma sake bi ta kan dodo ba.
Da ƙyar ya samu aiki a wurin wani mai shayi, yake yi masa wanke-wanke da abun da ba a rasa ba, idan ba ya nan, da shi da ƙanin mai shayin ne suke riƙe wurin, hakan ya sanya ya fara rage damuwa da halin da yake ciki.
Sai dai ƙanin mai shayin ya nemi da su haɗa kai da Al'amin, su ɗan din ga ɗaukar wani abu, Al'amin ya ce ba zai yi ba, ba a jima ba, yaron ya yi wa Al'amin sharri wai yana ɗebar masa kuɗi, kuɗi kusan dubu talatin, mai shayi ya kai Al'amin wurin 'yan sanda aka daka aka yi rarrashin ya ce shi bai ɗauka ba, ba kuma zai amsa yayi ba. Aka yi ta kai ruwa rana, da ƙyar case ya mutu, bayan ya shafe kwanaki a hannun 'yan sanda.
Yamma liƙis, ya je ya samu ƙanin Habu mai shayi, har rumfar mai shayi, ya karya shi a hannun dama, aka kuma cafke shi zuwa wurin hukuma, aka nemi Abbu, amma ya ce ba ruwansa, tun da kangarewa ya ɗauka.
Ɗaya daga cikin matasan da suke yi wa dodo aiki, wato Walid, shi ya gaya masa halin da ake ciki. Da kansa yaje station ya karɓo Al'amin.
Ya saka shi a gaba, yana yi masa tambayoyi, a kan dalilin da ya sa, ya aikata abun da yayi. Ya kwashe komai ya gaya masa.
Dodo ya ce "To daga yau, kar ka sake zuwa ka nemi wata sana'a, duk abun da ba ka da shi, ka zo na baka. Na fuskanci tsohonka baya yinka, ni kuma ehhh kawai ka kwanata mini a rai, tausayi kake bani, kana rayuwa da kai da wanda aka bugoku cikin samfurin jini ɗaya, an ɗaye maka shi, ta ƙarfin tsiya. Amma ba komai, zaka rama ne"
Tun daga lokacin Al'amin ya zama yaron dodo, wurinsa yake zuwa ya karɓi kuɗin abinci, ya biya masa kuɗin registration, ya mayar da shi makaranta ya cigaba da HND, dama shekarunsa ba su kai shiga University ba, shiyasa ya fara zuwa poly.
Dodo harkar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi yake yi, babban distributor ne, har garuruwa yake rarrabawa kaya.
Bai damu da harkar daba ba, sai wannan sana'ar, Abbu bai taɓa tuhumar ya aka yi Al'amin ya koma makaranta ba, wace sana'ar ya fara duk bai tuhume shi ba.
Dodo yana da manyan yara da matasa, ciki har da sa'an Al'amin mai suna Walid. Sai dai Walid ya tsani Al'amin ganin yana neman ƙwace masa fada a wurin dodo babban sarki.
Ko aike babu wanda ya isa ya aiki Al'amin, dodo ne kawai yake sa shi ko ya hana shi, haka zai zauna a cikin su, su yi ta shaye-shaye suna ƙuƙƙula kayan maye, amma ba ruwansa da su, ko sigari bai taɓa gwada sha ba.
Idan yayi dare a yawonsa, sai ya tafi gidan dodo, yayi kwanansa, dodo har safarar makamai yake yi, babban criminal sosai da sosai.
Komai Aminullahi, komai Aminullahi, lokaci lokaci, ya kan tuntuɓi Al'amin, ko zai iya yafe wa madaki, amma ya ce har abada, har sai ya rama abun da yayi masa ya kan yi murmushi ya ce "Aminullahi kenan, in dai zaka zauna a haka, ba ka shirya ɗaukar fansa ba, ƙarfe dole sai da ɗan uwansa ƙarfe, roba ba ta tasiri a kan ƙarfe" baya gane mai dodo yake nufi, dan haka sai dai ya bi shi da to
Al'amin ya ce masa dan Allah ya samo masa sana'a, ko wace iri ce zai din ga yi. Dodo ya ce masa zai duba.
Duk abun da Al'amin zai yi, dodo bai yadda yaransa su yi masa wani abu na horo ko cutarwa ba, hatta kaya idan Al'amin ya cire, sai ya ce Walid ya wanke masa, wanda kan zuwan Al'amin shi ne na gaban goshi.
Sannu a hankali, ya fara aiken Al'amin kai kayan shaye-shaye wasu wuraren, cikin dare idan motar kaya ta isao, haka zai ɗauke shi, su tafi su karɓo kaya.
Wataran ya aike shi, hukumar hana sha da fataucin, suka kama shi, aka din ga tuhumar Al'amin, ya ƙi faɗan wanda ya aike shi da kayan, sai da aka kwana biyu ana nemansa, hankalin dodo ya tashi, aka bincika aka gano masa shi a hannun hukuma.
Ya je ya karɓo Al'amin, sannan ya ce "A bashi kayan da aka ƙwace ayi musu kuɗi zai saya, idan suna da wasu ma a haɗa masa ya saya. Kuma hakan aka yi.
Ya yi ta yi wa Al'amin faÉ—a, a kan dan me, ya zauna a hannunsu, bai saka an neme shi, ya fito da shi ba?.
Ta kai ta kawo, Dodo yana tafiya da Al'amin wurin 'yan siyasa, dan a nan ne suka haÉ—u da Indabo, a lokacin baya shan komai.
Duk da wannan abubuwan da suke wakana, Al'amin yana zuwa gida, ya ga Abbu, ko da kuwa zai yi masa faÉ—a ya kore shi, yana zuwa ya ganshi.
Yaran dodo sun sha attempting koya masa shaye-shaye, amma ya ƙi, tun Walid yana jin haushin Al'amin, har ya haƙura, manyan yaran dodo suka saka masa mai zamani, ya kori gwamantin Walid dan haka idan yana son zaman lafiya ya kiyayi mai zamani"