Sashe 52
Karfe A Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunani take yi, idan ta dafa taliya yau ma ko zai ci, tana tunanin ko shi ma sun fara isar shi. "Karfa ya ce ko ban iya girki bane, shiyasa kullum nake dafa taliya. To ai gidan bakomai sai su"
Ta É—an yi shiru, tana tunanin yau bari ta aika a sayo mata kayan miya, tayi da miya, so take ma ta nuna masa kuÉ—in da kakarshi ta ba ta, amma tsoronsa take ji.
Tana ta tunani, ta ji ana buga ƙofa, cikin murna ta tashi, ta san baƙi tayi sa ɗebe mata kewa.
Anty lubabtu ta gani, maƙwabciyar su, da ƙanwarta wadda take karɓar shirin dutse a gidanta, cikin murna tayi musu maraba.
Allah ya sa tana da ruwan pure water, ta basu.
Ta ce "Anty lubabatu shi ne sai yau zaku zo ko? An barni nikaɗai, ba wanda yake leƙo ni".
"Ki yi haƙuri jauhar, tun washegarin kawo ki, nake sintirin neman mai rako ni a gidanku, wallahi fafur 'yan gidanku da 'yan tsukin nan aka rasa masu zuwa su rako mu, wai tsoro suke ji, 'yan gidanku ma wai ba za su rakomu ba, mijinki ɗan daba ne, ni kuwa na ce ko menene zamu zo, sai kwatance suka yi mana".
Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Shikenan bakomai, yaya saifu ma ya zo, daga ni sai yaran maƙwabta, ni kaɗai nake wuni".
Samira ta ce 'Allah sarki, mma dai jauhar ba wata matsala dai ko?"
Tayi murmushi ta ce "Babu anty samira, ya shiri kin zo mini da shi?"
"Taɓ kina amarya, kawai sai na kawo miki shiri?"
Jauhar ta ce "Eh mana, zai din ga É—ebe mini kewa ai, dan Allah idan an samu mai zuwa, ki bayar da yawa a kawo mini, na din ga yi"
Anty lubabtu ta ce "Jauhar iyayen neman kuÉ—i".
Samira ta ce "Bar ta ta nema, rayuwar nan ba a zama haka"
Miya lubabatu ta soyawa jauhar, mai yawa ta sha naman kaji, da shinkafa da 'yan kayan buƙatu.
Jauhar ta ji daÉ—in hakan sosai da sosai, ta din ga murna, suka wuni tare har la'asar, sannan suka tafi.
Suna tafiya ta aiki almajiri, ya sayo mata salak da kayan haɗin sa, ta zauna ta shirya salak ɗin nan, ta juye miyar a tukunya, ta ƙara soyata tayi mata gyare-gyare ta ƙara mata su maggi da kayan ƙamshi ta kammala komai.
Ta É—ebarwa yaran da suke shigo mata abincin ta basu, ta É—ebe wani ta rufe, dan abincin da yawa, ta sake turara shinkafar ta zuba a wani flask mai kyau kamar a lokacin ta dafa ta.
Tana aikinta, tana jin radiyo a mp.
Ta bawa yara kuÉ—i, suka sayo mata ruwa da lemo mai sanyi.
Ta gama aikin, ta share kitchen ɗin, ta kwaso sharar abun da ta ɓata, ta fito kawai ta ga Al'amin a tsakar gida, aikuwa ta razana ta saki abun kwashe sharar tana ihu, ta zubar da sharar a wurin, har zata gudu sai kuma ta tuna kashedin da yayi mata, ta tsaya jikinta yana rawa ta ce "Yi haƙuri, tsorata nayi, ban san ka shigo ba" tayi maganar tana kare jikinta, saboda babu hijjabi a jikinta, bai jira ta gama maganar ba ma, ya shige falo.
Ta daɗe a tsakar gida, ta kasa shiga falon ma, ta lallaɓa ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi.
Ba ya falo, ta shiga É—aki ta sako hijjabi ta fito, sai dai ta kasa zuwa É—akin da yake.
Wanka yayi ya fito, ya tarar ta ajiye masa sabulun wanka, a cikin wanda ta zo da shi, banÉ—akin ta kai mas bokiti da ruwa, ga buta ita ma cike da ruwa.
Ya gama wankan, ya ɗora soson a kan sabulun yayi fitowarsa, da zai canza kaya kuwa, duddubawa ya din ga yi, da ya gan su a cikin wardrobe, sai da ya watso su gaba ɗaya ƙasa, sannan ya zaɓi wanda zai saka, ya bar su a wurin ba tare da ya gyara ba.
'yar siririyar muryata ya ji a bakin ƙofar ɗakinsa, tana ta sallama.
A fusace ya ce "Meye ne?".
Ta razana ta ɗan shigo daga bakin ƙofa ta tsuguna, ta ce "Dama tun washegarin kawo ni, wasu sun zo, da kakarka hajiya da wasu, suna nemanka na ce baka nan, suka bani kaya da kuɗi dubu goma, amma na sai maggi da ashana da omo, a ciki baka zama a gida, ban nuna maka ba, shi ne na kawo maka"
ÆŠan shiru ya yi, jin ta ce hajiya ta zo, ya ji babu daÉ—i da bai haÉ—u da hajiyar ba, dan rabon da yaje ya ganta har ya manta.
"Ga kuÉ—in" muryarta ta dawo da shi daga tunanin da yake yi.
"Bar nan wurin kafin na yi ball da ke, ba ruwanki da shiga sabgata na gaya miki, tashi ki ware" ta tashi ta ce "KuÉ—in fa" banza ya yi mata, ya tsaya yana kallon fuskarsa a mudubin É—akin.
Ganin ba zai kulata ba, ya sanya ta ajiye masa kuÉ—in, ta tashi za ta tafi, cikin tsawa ya ce "Ke!" A razane ta waiwayo.
"Kwashe kuÉ—in nan ki bar nan" jiki na rawa, ta É—auka ta ce "To bar mini ka yi" mugun kallon da ya yi mata ya sanya, ta juya da sauri ta bar É—akin.
Ta je kitchen, ta shiryo masa kwanukan abinci a kan tray, amma ta tsaya tana wasi-wasi, kar ta kai masa ya kuma korarta, ta shiga falon tana taradaddi.
Ta na shigowa yana fitowa daga ɗakin, take hannunta ya hau rawa, ta ji tana neman ta saki farantin da kwanukan, ta ƙarasa tsakiyar falon, ta ajiye ta ce "Fita zaka yi, ga abinci" ta juya ta koma kitchen ta ɗaukko ruwan roba da lemo, da ta saya masa ta ɗora a kan wani plate ɗin ta kawo. Tana zuwa taga ya zauna ya kame zai ci abincin, kasancewar yana girmama cikinsa, Al'amin yana son abinci, dan haka ba kowane tayi yake wucewa ba.
Maimakon ya É—ebi abincin, ya zuba a plate, kawai ya buÉ—e flask É—in, ya juye salad É—in a ciki, ya É—aga flask É—in miyar ya girgije a kai, ko kallon cokalin bai yi ba, ya zura hannu ya kama kai loma.
Duk da wani irin mugun tsoronsa take ji, amma haka cikin tsoron, ta tsiyaya masa lemo a kofi É—aya, É—aya kuma ta zuba masa ruwa.
Satar kallonta ya yi, yadda take komai a nutse, sai dai hannunta rawa yake yi, saboda tsoro, mamaki yake yadda take wani zuba masa ruwa kamar ya sakata.
Ya din ga tunanin ita kuwa wani zunubi ta aikatawa 'yan gidansu, suka zaɓa su aurar da ita ga shi? Gaba ɗaya yanayinta kalar 'ya'yan hutu ce, irin wanda ba sa son wahalar nan.
Sai dai yadda yake auna loma, yana basarwa ba zaka ce, ita yake satar kallo ba.
Ta koma can gefen kujera ta zauna ta yi tsuru, gabanta na cigaba da faÉ—uwa da zarar ta kalleshi, sai dai duk da haka, a ranta ta ji tana son yi masa magana a kan kakarsa, da sauran tambayoyi, duk da miskila ce, amma idan ta samu wuri akwai hira. Sai dai ko kusa ko alama, ba ta ga wannan fuskar ba.
Kan ta ankara ta gama zancen zucin, ya kawar da abincin cikin kula 'yar tsakiya, shanye ruwansa da lemo tsaf, ta zuba masa ido, duk da ba abun mamaki bane ba, ta saba ganin maza da shegen cin tsiya, dan tsaf Yaya Saifu zai iya cinye cikin babban flask, dan akwai ranar da suka din ga musu da surayya, ya ce zai iya cinye shinkafa rabin kwano a zama É—aya, dama taliya leda guda yake cinyewa.
Dan haka ba ta yi mamakin yadda ya cinye abincin ba, ya dubi carfet É—in ta, milk mai haske, ya goge hannunsa a kai ya tashi tsam ya bar mata wurin da kwanukanta a wurin.
A hankali ta ce "Na shiga uku, miya a kan carfet É—ina" da sauri ta kwashe kwanukan, ta É—ebo ruwa da omo, ta goge wurin da ya goge mata hannu a carfet, ta koma É—akinsa, ta sake kwashe kayan da ya zubar.
Ya watso su duka gaba ɗaya, ya cire na jikinsa duk ya watsar ya ƙara gaba.
Ta sake gyara masa, ta kwaso wanda ya cire, da wanda ta kwashe na wanki ɗazu, ta fito ta jiƙa su zata wanke.
Ta koma ta sake sharo falon, sai dai ta ga leda a in da Ya tashi, ta ɗauki ledar, ta taɓa ta buɗe, tana tunanin ko ita ta ajiye wani abun, amma ta ga wani abu kamar ganye a ciki, ta sinsuna ta kasa gane ko menene, kuma a iya tunanin ta, ba ta ajiye ba. Ta samu wani wurin ta ajiye, ta cigaba da aikinta.
Sallama aka din ga rangaɗawa a ƙofar gida, ta wanke hannunta ta ce "Waye"
Ya amsa da "Ni ne" ta saka mayafi, ta fita ta leƙa.
Wani jibgegen ƙato ta gani, jiki duk a murɗe, duk bai kai girman Al'amin ba ba.
A É—an tsorace ta ce "Sannu"
Ya ce "Yauwwa, matar gidan tana ciki ne?"
Ta ce "Eh meyafaru?"
"ÆŠan je ki ce mata ana sallama da Boss"
Ta yatsuna fuska ta ce "Waye hakan?"
"Mai dogon zamani nake nufi, ba shi ne maigidan ba?"
Jauhar ta ce "Ba wani mai irin sunan nan a gidan nan, ba sunansa kenan ba"
Ya ce "Kee, ni fa nake rako shi har gidan nan, ki ce mini ba sunansa kenan ba?"
Ta tsuke fuska ta ce "To shikenan idan ba ka yadda ba"ta mayar da ƙofa ta rufe.
Walid ya koma gefe ya kira Al'amin ya É—aga ya ce "Ya mai laya".
Walid ya ce "Na kiyayi mai zamani, maza na zo gidanka wata 'yar cika, ta leƙo ta raina mini hankali, na kusa kwarfeta, na ƙyaleta ne kar na kwafsa"
"Wacece ya aka yi?"
"Kai na zo nema, ina ta jiranka, yaran nan za su karɓi kaya su rarraba, ba ka zo ba, na biyo ka gida, wata jar yarinya nunar rana mai kama da 'yan china ta ce mini wai ba mai irin sunanka a gidan, na ce mata mai zamani wai ba gidan ba ne"